Showing 81001 words to 84000 words out of 115393 words

Chapter 28 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22930

shi a office.
Jiki na rawa, Naseer 'din ya nufi office 'din dr tare da addu'ar Allah ya sa babu abunda ya sa mu cikin sa.
"Have a seat". Dr ya fa'da tare da nu na kujera.
Zama Naseer 'din ya yi zuciyar shi na lugude.
Ajiyar zuciya Dr ya saki tare da fa'din,
"Alhamdulillah! Matar ka ta tsallake, sai da sakamakon kwayar zubar da cikin da ta sha mai 'karfi, ya sa mun kasa ceton cikin da ke jikin ta. Sorry to say, we loose the baby".
Wani irin mi'kewa Naseer tai tare da cin kwalar dr, saboda tsabar zafin zuciya maganar shi har in'ina ya ke. (Dama haka Naseer ya ke, ya na da matu'kar zuciya. Kamin yai fishin ne, amma idan yai to ko Mommah ba ta gane kan shi, dama² ma Ummu nah.)
"Ka na hauka ne da zaka ce mata na ta sha strong pill's na zubda ciki. Definitely there most be mistake somewhere. Gwara ma kuje ku duba da kyau. Mata na ba irin wa'dannan matan ba ne".
Yanye hannun Naseer yai da kyar a wuyan shi tare da fa'din,
"Za ka iya zuwa asibitin don tabbatar wa. Amma ni na tabbatar nan babu in da akai kuskure".
"Quite please!". Naseer ya fa'da da tsawa ka na ya cigaba.
"Na amince cikin jikin mata na ya fita, haka Allah ya 'kaddara. Amma bazan ta'ba yadda mata na ta sha maganin fitar ciki ba. Your not a professional doctor". Naseer ya 'kara da 'karfi tare da fita daga office 'din yai banging 'kofar SAI da doctor ya saka hannu ya to she kunne.
'Dakin da aka kai Mufeeda ya nufa. Kwance ta ke hannun ta akan cikin ta, rana 'daya kawai har ta rame ta 'kara hasken ciwo.
Hannun ta 'daya ya ri'ke ya na kallon ta, bai san Sadda wasu zafafan hawaye su ka zubo masa ba. 'Kasa² ya furta,
"Allah ya ba ki lafiya Qalby".
Kwanan su uku a asibitin. Ya 'ki bari kowa ya zauna da Mufeeda, SAI da Mommah tai kamar za ta cinye shi ka na ya hakura Mommah 'din ta kwana da ita, amma fa a asibitin ya ke wuni har aka sallame su suka koma gida.
Naseer bai fa'dawa Mommah abunda Dr ya ce masa ba. Ya dai sanar da ita cewar ta sa mu miscarriage ne.

Cikin hukuncin ubangiji, bayan wata biyu, Mufeeda ta kuma samun ciki, wannan karan bayan Naseer ba bu Wanda ya san da zaman cikin kasancewar ita ba mai laulayi ba ce. Sai da cikin ya kai wata hu'du, sannan Mashkura ta san da cikin, don ya 'dan tasa. Aikuwa hankalin ta idan yai dubu duk sun tashi, SAI dai ko a fuska ba ta nunawa Mufeeda ta san ma da zaman cikin ba.
Sati biyu da zuwan Mashkura, jini ya tsinkewa Mufeeda.
Wannan karan canza asibiti Naseer yai, amma ana zuwa still abunda ya faru baya, shi aka fa'da masa. Cewar matar sa ta sha maganin zubar da ciki. Still bai yadda ba yai ta bala'i tare da tattaro matar shi su ka dawo gida.
Wannan karan Mufeeda ta fi Naseer damuwa da fitar wannan cikin. Kuma har yau Naseer bai ta'ba fa'da mata abunda dr su ke fa'di a kan ta ba.

Wata 'daya tsakani Mufeeda ta kuma samun ciki. Wannan karan ba 'karamin taka tsan² Mufeeda da Naseer su ke ba. Ta dai na aikin komai. Ko 'dauke abu daga nan zuwa nan bai yadda tai ba.
Amma still abunda ya faru, shi ya 'kara faruwa. Don wannan karan ma, cikin ko wata 'daya bai kai ba, cikin ya fita.
Tuni Naseer ya 'daura question mark akan Mufeeda. Fitowa yai ya shaida mata abunda Dr su ke cewa akan ta tun daga cikin farko.
Sosai Mufeeda ke kuka dur'kushe a gaban shi ta na fa'din,
"Wallahi ko Qur'ani zan iya dafawa nai maka rantsuwa. Wallahi wallahi wabillahil azeem ko kalan maganin zubar da ciki ban ga ni da idanu na ba. Idan 'karya na ke maka, Allah ka da ya sa na kai gobe lafiya".
Wani irin numfashi Naseer ya ja tare da fa'din,
"Mai sona, abun ne akwai mamaki a ciki, different asibiti fa, duk abu 'daya suke fa'di. Wannan da kishiya gare ki, wallahi babu abunda bazai sa a zarge ta ba. Amma na barwa Allah ko mai, idan daga shine Allah ya sa wannan shine na 'karshe".
Fa'dawa jikin shi tai tare da fashewa da matsanaicin kuka.
Rungume ta yai ya na bubbuga bayan ta.

*BAYAN WATA BAKWAI*
Mufeeda ba ta 'kara samun ciki ba. Naseer ya da mu kwarai. Domin Allah ya yi shi mai matu'kar 'kaunar 'ya'ya. Amma ko a fuska bai ta'ba nu nawa Mufeeda haka ba. Soyayya su ke gwadawa junan su mai matu'kar burgewa.

Zaune ya ke a office 'din shi ya na saka hannu a wasu takardu da wata kamfani ta ke bu'katar bashi.
Wayar shi tai 'karar shigowar sako. Kasancewar ya san Mufeeda kan mai sa'ko akai² masu sanya nisha'di idan ya na wajan aiki.
Da murmushi a fuskan shi ya mi'ka hannu ya 'dauki wayar.
Wani irin zabura yai bayan ya gama karanta sa'kon.
'Kara kallon wayar yai ya na 'kara karanta sa'kon da ke ciki.

*_Assalamu alaikum. Na san za kai mamakin ganin wannan sa'kon gami da tashin hankali a duk in da Ka ke. Ya zama min dole in fa'da maka gaskiya, domin cutarwa da ake maka ya yi yawa. Dama haka rayuwa ta ke, kayi wa mutun inuwa, shi kuma ya maka rana. Ha'ki'kanin gaskiya, matar ka zubar da ciki ta ke yi saboda wani 'kungiya da ta ke CIKI a a WhatsApp ba su lamunci ta 'dauki ciki a yanzu ba, a cewar su, kyawun ta zai ragu, kuma za ta dai na bai wa customers sha'awar kasancewar wacce ake ji da ita cikin 'kungiyar isassun mata. Idan ba ka yadda da magana ta ba. Za ka iya bincika 'dakin matar ka, za kai arba da magungunan da ta ke sha a halin yanzu na hana 'daukar ciki, sannan kuma ka binciki WhatsApp 'din ta, zaka ga sauran baya ni da ban maka ba. Bissalam. MKR._*
Zufa ce ke ketowa a ko wani lungi da sa'kon jikin Naseer, ji ya ke har wani jiri² ya ke ji.
Lokacin tashi bai yi ba, ya dawo gida. Allah ne ma kawai ya dawo da shi lafiya saboda irin gudu da overtaking da ya ke ta yi a hanya.
Ko da yai knocking Mufeeda ta bu'de 'kofar, ra'be ta kawai yai tare da wuce wa sama. Abunda tun da su kai aure bai ta'ba faruwa ba.
Hankali ta she Mufeeda ta ni shi da idanu. Can kuma tai saman da gudu. Ba ya 'dakin ta. 'Dakin sa ta nufa tare da tura 'kofar ta shiga. Zaune ya ke a bakin gado ya dafe kan shi da hannun shi.
Zama tai gyefan shi tare da fa'din,
"Yallab'ai lafiya? Mai ke damun ka?".
Ko 'dagowa bai yi ba, balle ya kalle ta.
'kara maimaita tambayan ta ta a karo ba biyu.
SAI a wannan lokacin ya 'dago jajayan idanun sa ya sauke akan ta, kallon minti second biyu ya mata tare da 'dauke kan shi. Kamar bazai ce komai ba, SAI kuma ya ce,
"A office ne aka 'bata min rai, kuma kai na ke min ciwo".
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tare da fa'din,
"Hubby ka kwantar da hankalin ka, dama haka rayuwa ta ke, ba kullum ba ne ka ke samun komai 100%. Da Allah ka yi ha'kuri ka cire komai a ran ka. Ba ga ni kusa da kai ba. Zan faranta maka in sa Ka manta da 'bacin ran da Ka dawo da shi. Please smile. Wallahi idan kai fushi ba ka kyau.
Kasa murmushin yai sai ya'ke da yafi kuka ciwo tare da fa'din,
"Ki je ki aikin ki, zan sha magani yanzu. Ina so na 'dan huta ne yanzu kamin a kira magriba, ki kawo min ruwa yanzu".
Sa sauri ta mi'ke ta nufi 'kofa, har ta kai 'kofa ya ce,
"Yauwa ki taho min da wayar ki".
Da to ta ba shi amsa ba tare da ta kawo ko mai a ran ta ba. Don ya saba yi mata hakan, idan ya dawo mata da shi tai ta ga kati ne ya saka mata.
Ruwan ta kawo masa da wayan kana ta koma kitchen domin cigaba da girkin ta.
Cikin sauri ya hau WhatsApp 'din ta.
Messages ya ga ni sun kusa 'dari uku a wani group mai suna *SIRRIN MIJIN KI A TAFIN HANNUN KI* ko da ya duba message 'din duk bayani ne akan yadda zaki kula da mai gida.
Group na biyu kuma *MANYAN MATA MASU CLASS*, Shi ma dai irin na 'dayan ne. Na ukun ne ya 'daga mai hankali mai suna, *ISASSUN MATA GROUP 18*.
Babu abunda ke gudana a group 'din sai zallar batsa, kuma maza da matan aure da kuma 'yan mata ne a group. Ya fahimci hakan ne ta yanayin group 'din.
Domin wani Sabin member ne zai shigo ya ke cika 'ka'idojin group 'din kamar haka.
*_KAI WAYE? SHEKARUNKA NAWA? A WANI UNGUWA KAKE? KA NA DA AURE? MEYE SANA'AR KA? KA YADDA KA AMINCE DA DOKOKIN GROUP DIN KAMAR HAKA?*
*1. DUK MATAR DA KUKA HA'DA AP DA ITA, IDAN TA ZO KA GANE KA SANTA, KO KUMA KA SAN MIJIN TA, HAKAN ZAI ZAMA SIRRI TSAKANIN KU? 2. IDAN BUDURWA CE ITA MA HAKA. IDAN KA AMINCE KA AMSA, SAI KA ZAMA CIKAKKEN 'DAN KUNGIYA.*
Ko da Naseer ya ga ma karantawa, tsoro ya mamaye shi, hankalin shi ya tashi.
Ku ma a group 'din, kusan kowa sunan Mufeeda ke kira wacce su ka mata la'kabi da *BIG SHARK*.
Wata macece wacce ita ce leader na group 'din mai su na *BIGI FANTI* tai wa Mufeeda magana akan ta mata magana ta private.
Tuni Naseer ya bar group ya koma chart 'din. Aiko yai arba da conversation 'din su da ya Kusa haukata shi.
Mufeeda: Sai hajjajun mu
Bigi Fanti: Sai Big sharki, ya ki ke, ya jin nice?
Mufeeda: ko mai normal. Ya ta sa mu ne?
Big fanti: Hmm ai kwanaki kin 'bata min rai, kawai sai ki ka je ki ka 'kara kwaso wani cikin, so ki ke ki tsofe a dai na yayin ki?
Mufeeda: Tuni mai waje da shi, ina zan iya da wahala. Ni fa cikin ma ba na tuna min na Naseer ne, na fi tunanin na Oscar ne.
Big fanti: Shark ki na sha'anin ki. To yaushe za ki ha'da maku AP da alhj Suwaita? Ya takura min wallahi. Jifa 1.5mil ya tura min a account.

Ji ka ke tatsatsatsatsa, Naseer ya buga wayar Mufeeda a 'kasan tiles ta tarwatse, ji ya ke kamar yai ta kurma ihu ko zai samu sassauci a zuciyar shi.
"Me ki ke nema? Mai kike nema Mufeeda? Menen ba na miki da zaki fa'da wannan harkan, mai ya sa zaki ci amanata? Na tsane ki Mufeeda, na tsane ki, bazan iya cigaba da zama da ke ba. Za ma na da ke ya 'kare.
Shika'dai ke wannan maganar tare da wurgi da duk wani abun da ya ga ni a Kusa da shi.
Ita kuwa Mufeeda, ta na can kitchen ta na girki ba ta san abunda ke faruwa ba.
Da sauri ya ke saukowa daga step 'din har uku² ya ke ha'dawa ya na tsallakewa.
Kai tsaye kitchen 'din ya nufa. Dai² Mufeeda ta fi to 'dauke da faranti a hannun ta da ta ha'da mashi favourite 'din shi wato avocado juice.
Wani irin wancakali da tiren ya yi tare da dam'ko gashin ta da ta 'daure a tsakiyar kai ya watsar a nan kan tile a tsakiyar 'dakin.
'Karasawa yai ya sha'keta tare da fa'din,
"Uban me ki ka rasa a tare dani da zaki fa'da wannan harkan? Mufeeda ni? Ni zaki wa haka, ni zaki cuta? Ni zaki watsawa 'kasa a ido. Wallahi yau sai kin fa'da min Wanda ya ba ki shawarar shiga wannan harkan". Naseer ya fa'di hakan ya na kai mata duka ta ko ina a jikin ta.
Mufeeda kuwa idanun ta sun furfito saboda sha'kan da ta ji.
Mommah ce ta turo 'kofar ta shigo a ki'dime tare janye Naseer da ga jikin Mufeeda ta dunga Wanka masa mari. Dama bata ta'ba zuwa gidan ba sai yau, yai 'din ma hanya ce ta biyo da ita da Rabin zata ga wannan abu.
"Ka na hauka ne? Uban mai ta maka da zaka mata irin wannan dukan? Kashe 'Yar mutane za ka yi?".
Sai huci ya ke yi tare da fa'din,
"Mommah, na gama zama da wannan yarinyar, sa'kin ta zanyi".
"Kaji na rantse maka, ko shika 'daya ka bai wa yarinyar nan, ba ni ba ka". Ta na gama fa'din hakan ta kama hannun Mufeeda ta re da fita daga gidan.
Sosai Naseer ya zauna ya na kuka a tsakar 'dakin kamar 'karamin yaro. Can ya mi'ke ya hakura sama da gudu tare da shiga 'dakin Mufeeda ya samo mata binciki. Magunguna na zubda ciki da kuma na hana 'daukar ciki ya ga ni da yawa cikin drowern ta.
Wani Ron haushi, tsana, 'kishirwa da ba'kin cikin Mufeeda ya mamaye zuciyar shi.


*BAYAN KWANA BIYU*
Sai da Mufeeda ta kwana biyu, ka na ta koma gidan Naseer, bayan daddy da Mommah sun ha'dasu su duka sun wanne su tatas ba tare da sun tsaya sauraron 'daya daga cikin su ba. Sannan su kai masu sallama akan nan da kwan biyu ZASU tafi england saboda wani course da aka tura Daddy na shekara wata bakwai. mommah za ta bi shi ita da su twins su yi wata biyar a can.
Tuni Naseee ya ba da cigiyar gida a can cikin gheton malali, anyi sa'a ko aka samu ciki 'daya da palo sai bayi a ciki ba kitchen, gidan mutun 'daya ne. Ranar da su daddy su bar kasar, ranar Naseer ya mai da Mufeeda wancan gidan bayan ya mata dukan mutuwa.
Tun daga ranar Naseer ya ke jin kamar kullum 'kara rura masa tsanar Mufeeda ake yi cikin zuciyar shi.
Kullum sai ya mata dukan safe da rana da daddare, har baro office ya ke yi don dukan ta kawai. Har 'yan unguwan sun ga ne su. Tun wato tsohuwa mai suna Baaba hansai na zuwa ta na sasanci har ta dai na zuwa saboda Sam ba ta ganin ginsar gidan Naseer a idanun Mufeeda, don ita har wa yau ba ta jin haushin mijin na ta, kuma ba ta jin za ta iya rayuwa ba tare da shi ba.
Kwatsam ciki ya bayyana a jikin Mufeeda har na tsawon wata uku. Naseer ya buga tsalle ya dire akan shi ciki ba nashi ba ne.
Sabin bala'i da tashin hankali Mufeeda ta shiga akan haka. Domin Sam Naseer ya dai na kawo mata abinci balle ta ce, Gashi wannan cikin said yazo da laulayi. Tun ya na wata uku, amma sabida girman cikin kamar ya kai wata biyar.
Kwata² Naseer bai tausaya mata. Haka zai ta dukan ta yan a taka cikin tare da Koran shi shege.
Mufeeda duk ta bi ta ko'de ta lalace, baza ka ta'ba kallon ta ka ga ne ta ba, kurahe sun yanyame fuskan. 'Kashin wuya ya mata sarka. Idan ka ga Wuhan ta kamar mari'kin lema. Naseer bai kwana gidan idan na gan shi a gidan to yazo dukan same ne, ko na rana ko na dare.
A haka har cikin Mufeeda ya shiga wata na Tara, lokacin ne kuma su Mommah su ka dawo.
Dama Ashe tun suna can Naseer ya sanar da ita zai 'kare aure ta ce masa saam bai isa ba.
Shi kuma Naseer da yaga tabbas idan Mufeeda ta haihu, haka ya na ji ya na gani zai ri'ke shege ko shegiya tare da ciyar da shi/ita bayan ba shi ne uban sa ba. Dama tuni ya je ya sanarwa KALLAH abunda ke ciki, KALLAH ya ce ai dama tuni ya fa'da mata 'Yar iskan yarinya ce, don haka kawai ya sake ta.
Aiki a fusace ya dawo gida tare da laka'da mata duka ta na halin na'kuda ya kuma sake ta. Sai alokacin ma Mufeeda ta ga ne tuhumar da ya ke mata, amma Sam ba ta san labarin group na WhatsApp ba. (Ku waiwaya farkon labarin, za ku ga irin cin mutumcin sa Naseer yai wa Mufeesa)


*CIGABAM LABARI*

Mu ha'de gobe

*MAMAN UMMEE*
*AKA*
*MATAR SAYYADEE*✍🏼
[10/3, 12:54 PM] Meenal: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login