Showing 69001 words to 72000 words out of 115393 words

Chapter 24 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22919

ce?".
Saurin sa hannu ta yi ta kar'ba tare da fad'in,
"Wallahi ba haka ba ne, ba rainawa na yi ba".
Murmushi ya yi tare da fad'in,
"Ni ma nasan ba rainawa na ki ka yi ba, na fad'i hakan ne don ki karb'a d'in".
Murmushi ta yi tare da fa'din,
"Kai ko?".
"Ke ko?". Shima ya fad'a tare da wani marairaice wa.
Fashewa tai da dariya wanda ya k'ara fitar da asalin kyawun ta.
K'uri yai yana kallon ta domin ba k'aramin kyawu tai masa ba.
Iska ta hura masa a idanu tare da d'age girar ta 'daya ta re da fad'in,
"Ya dai? Wannan kallon fa? Kamar zaka cinye ni".
Ajiyar zuciya ya sauke ka na ya ce,
"Ke ce kike son sumar da ni, wallahi ina matu'kar 'kaunar ki Mufeeda, na 'kosa ranar ta zo, sai na ga gaba d'aya bai sauri".
Murmushi ta yi tare da fa'din,
"Ni kuma da har ina cewa a 'kara wata kamar irin shidda haka".
Wani irin zaro idanuwa Naseer ta yi tare da dafe 'kirjin shi ya na wani 'yan 'kananar tari.
"Lafiya? Mai ya sami rabin rai na? Wayyo zuciya ta, ka tausaya min Ka dai na wannan wasan, zuciya ta baza ta iya d'auka ba".
'Dagowa yai ya kalle ta ya na sakin murmushin jin dad'i ya ce,
"Idan har irin dad'ad'an kalaman nan, aikuwa kullum zan r'ika narke miki domin in ri'ka samun wad'annan maganganu masu sanyaya zuciya".
Wani siririyar dariya Mufeeda ta yi tare da fad'in,
"In dai irin wad'annan maganganun ne ka same su ka gama 'Yalla'bai".
Dariya su kai gaba d'ayan su.
Naseer na matuk'ar jin da'din yallab'ai da ta ke kiran sa da shi.


⚫⚫⚫⚫⚫

Mama ta sha kuka sakamakon ganowa da Mashkura ta yi akan ba su ne iyayan ta na gaskiya ba. Ta shiga tashin hankali matu'ka akan hakan.
Da kyar Mama ta shawo kan Mashkura har ta mata alk'awarin ta bar maganar Naseer har gaban abada.
Sosai Mama ta ji dad'in hakan, kuma Mashkura ta saki jikin ta sosai. Hakan ya sa Mama ta ji dad'i sosai. Kuma ta shiga yi wa Mashkuran addu'ar samun mijin da ya fi Naseer d'in.
Mashkura kuwa a zahiri ta bar batun Naseer, amma can cikin zuciyar ta, ji take ba za ta ta'ba dai na son Naseer d'in ba, kuma al'kawari ne ko ta halin 'ka'ka sai ta auri Naseer d'in, kuma ba za ta ta'ba had'akan miji da Mufeeda ba.
Sosai ta saki jiki ta kuma cigaba da hada hadan bikin Mufeedan da ke gabatowa. Domin komai ita Mufeedan ta saka akan gaba, kasancewar ta babbar 'kawar Mufeedan.

Tun biki saura sati uku, Mommah ta turo mai gyara jiki tun daga Sudan ta shiga gyarawa Mufeedan jiki har da Marwanatu a can gidan su Mashkura.
Mashkuran kan shiga d'aki Mama ta sha kuka kamar ran ta zai fita, kana ta wanko fuska ta dawo a cigaba da hidima da ita.


💖💖💖💖💖💖💖
Mufeeda ce kwance a kan 'katuwar katifar Mashkura waya ma'kale a kunnan ta. Ba'a jima ba da mai gyaran jiki ta gama mulke ta da dilka. Ba 'karamin kyau ta 'kara ba, jikin ta har wani sul'bi ya ke yi, ga wani uban kamshi da jikin ta ke fita. Maganin sanyi kam ta shashi har ya kawo mata wuya, daga bisani ta 'daura ta akan magungunar gyarar jiki. waya ta ke da Naseer, Mashkuran na mata tsifar kan ta da aka mata kitso 'kanana da a'kalla zai kai dari biyu saboda ta na da yawon gashi.
"Ina jin ka, yalla'bai".
"Wallahi na 'kosa na ganki kusa dani". Fa'din Naseer.
"To me ka ke ci na baka ke zuba, saura sati biyu fa yau".
"Ke kin san yadda na ke jin sati biyun nan kuwa? Wallahi kamar shekara na ke jin sa".
Dariya Mufeeda ta yi ta re da fad'in,
"Lallai kam. Wake jin wa'ka Kusa da kai?".
"Ni ke ji, idan ina ji ke ke fa'do min a rai na, ji na ke kamar ni ke rera maki shi". Fa'din Naseer.
"To rera min inji". Fa'din Naseer.
"Yanzu kuwa". Fa'din Naseer.

💖❤️💝
What would I do without your smart mouth?
Drawing me in, and you kicking me out
You've got my head spinning, no kidding, I can't pin you down

What's going on in that beautiful mind?
I'm on your magical mystery ride
And I'm so dizzy, don't know what hit me, but I'll be alright

My head's under water
But I'm breathing fine
You're crazy and I'm out of my mind

Cause all of me
Loves all of you
Love your curves and all your adges
All your perfect imperfections

Give your all to me
I'll give my all to you
You're my end and my beginning
Even when I lose I'm winning

Cause I give you all of me
And you give me all of you, oh

How many times do I have to tell you
Even when you're crying you're beautiful too
The world is beating you down, I'm around through every mood

You're my downfall, you're my muse
My worst distraction, my rhythm and blues
I can't stop singing, it's ringing, in my head for you

My head under water
But I'm breathing fine
You're crazy and I'm out of my mind

Cause all of me
Loves all of yo
Love your curves and all your adges
All your perfect imperfection

Give your all to me
I'll give my all to you
You're my end and by beginning
Even when I lose I'm winning

Cause I give you all of me
And you give me all of you.

Har wani bacci² Mufeeda ta fara yi saboda za'kin muryan shi, said ta ji ma ai ya fi John legend 'din iya wa'kar.
"To ya ki ka ji wa'kar tawa?".
"Perfect". Fa'din Mufeeda.
Mashkura kuwa, tsaida tsifar ta yi, duk da ba hands free wayar ta ke ba, amma ta na iya jiyo muryan Naseer 'din ra'dau a kunnan ta. Hawaye ne wani na bin wani ke zubowa a idanun ta. Saurin sa hannu tai ta share hawayan tare da 'kudurtan wani abu a ran ta.
"Yauwa ke ma ina jin ki, rera min taki wa'kar da idan ki ka ji kike tunawa da ni". Fa'din Naseer.
Dariya Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Na maka al'kawari, idan har mukai aure a gaban ka zan rera maka shi".
"Zan ma fi son haka". Fa'din Naseer.
Nan suka shigaba da musayar kalaman soyayyar, ya yin da gefe 'daya suke 'kona zuciyar Mashkura da 'kara hura mata wutar 'kiyayyar Mufeedan a zuciyar ta da kuma 'kara 'dammarar cika burin ta da ta 'dauka.


🛑🛑🛑🛑🛑🛑
Yau saura kwana biyu bikin Mufeeda da Mashkura, kuma yau ne za'ai bridal shower da twince su ka shirya. Wani halla suka kama 'dan 'karami kasancewar 'kawayen amarya ne kawai da 'yan uwa mata za su je.
Mai gyaran jiki daga Sudan ita ta zanawa Mufeeda lalle mai 'dan karan kyau, kasancewar ta, sai fatan ta mai she'ki ya haska lallan.
Sanye ta ke cikin wani doguwar riga wacce daga 'kasan ta take a bu'de kamar pink, ta sha makeup ta yi matu'kar kyau. Ga 'daurin da aka da head kalar blue. Ta yi matu'kar kyau. Wai wannan kwalliyar da aka ratayo mata shi mai 'dauke da rubutun *bride to be* da kalar blue.
Su Mashkura ma dai dukkan su sanye su ke da doguwar riga kalar sky blue. Suma sun yi kyau. Kasancewar Mufeeda ba wasu tarin 'kawaye gare ta ba, sauran duk 'kawayan Mashkura ne daga cikin su har da Zabba'u mai awara, ta yi kyau ita ma.
Haka su kai shagalin su cikin natsuwa.

(Hmm fans 'din Mufeesa, ina kuke? Darma ashe haka Mufeeda ta iya rawa. Abun sai Wanda ya ga ni).

Washa gari akai kamu. Nan ma Mufeeda ba 'karamin kyau ta yi ba.
Sanye ta ke cikin wani dakakken les kalar maroon da mint green, fuskan nan ya ci makeup. Jakar hannun ta mint green ga mi da takalmi da jaka.
'Dangin muji da zasu bu'de fuska, ba 'karamin ku'di aka zubawa Mufeeda ba. Shi ma Naseer sanye ya ke da shadda gezna kalar mint green, hula da takalmi kalar ba'ki. Abun ya 'kayatar sosai.

*RANA BA TA 'KARYA*
Yaune 'daruruwan mutane suka shaida d'aurin auran Naseer Muhammad da Mufeeda Ahmad, Mashkura Kallamu da angon ta Musa.

Kamar kuwa yadda Naseer yai alk'awari, shi yai wa Mashkura kayan d'aki game da kayan kitchen wanda duk Wanda ya ga ni sai ya yaba. Gadon ta seti MBF da kuma kayan kitchen masu matu'kar kyau da kuma tsada.
*MAI ZOGALE* kamar ta zuba ruwan a 'ka sa ta sha don dad'i. Sai habaice habaice take saki a tsakar gida wai 'yar ta tayi goshi.
Ita kuwa Mufeeda da ya kasance yaune ranar farin ciki a gare ta, sai ta shige 'daki tai ta kuka har sai da idanun ta suka kumbura, sakamakon ganin 'yan uwan *MAI ZOGALE* ko ta ina, amma ita babu dangin mahaifiyar ta ko 'daya.

Mama ce ke ta kwantar mata da hankali.
Ko irin nasihar nan idan za'a kai amarya gidan miji, *MAI ZOGALE* ba tai wa Mufeeda shi ba, ma'kota ne su kai mata da kuma Maman Mashkura.
Bayan magriba aka kai Mufeeda gidan ta da tasha kuka kamar zata shi'de.
A masu rakiyar ta har da *MAI ZOGALE* domin bawa idanuwan ta abinci.
Aikuwa tasha 'duwawukan mamaki, domin kusan haukacewa ta Kusa yi da taga irin tan'kameman gidan da aka kai Mufeeda.
Wawakeken palour ne mai 'dauke da setin kujeru biyu irin king set 'din nan. Ga uban 'katoton plasma a jikin Bango. Labulaye kawai abun kallo ne a 'dakin Mufeeda, balle akai ga sauran kayan 'daki.
Kitchen kuwa yadda kuka san shagon kayan sai da kayan kitchen. Freezer har uku, ga gas cooker irin wawakeken nan. Fridge kuma, idan ki ba kallon kwana casa'in to irin wannan fridge 'din ne mai two door.
Sama kuwa, akwai madaidai cin palo da set 'din kujeru da tan'kamemen plasma. Da'kunan bacci guda uku. Ko wanne akwai set 'din gado Italian a ciki.
*Kai masu karatu, idan na tsaya zayyano masu irin kayan da ke gidan Mufeeda, zamu kwana mu tashi. Kawai ku hasaso da kan ku*
Kusan da hawan jini *MAI ZOGALE* ta koma gida. A kabar Mufeeda da Mashkura da wasu 'kawayan Mashkuran, kasancewar za su dinner anjima ka'dan.
Mashkura kuwa, ta ma fi *MAI ZOGALE* Shiva tashin hankali sakamakon arba da gidan da aka kai Mufeedan.


💝💝💝💝💝💝
Sanye take cikin wedding gown fari 'kal wai walwali yake da wasu irin 'kananan stones 'kalar gold.
Ta sha makeup 'din da ta masifaffan kyau. Ga head 'din ta kalar golden anti mata 'daurin turban.
Wuyan ta da kunnuwan ta sar'kan gold ne, haka takalmin ta shi ma golden ne.
Babu wanda zai kalle ta bai sake na biyu ba.
[9/14, 9:16 AM] Maman Ummee: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE 36_*

Su Mashkura kuwa, wani material ne a jikin su pitch colour, su ma sunyi matu'kar kyawu.
Wata ce daga cikin dangin ango, kamannin su 'daya da Mommah, ta zo ta kama hannu Mufeeda su ka fito harabar gidan.
Wata dandatsetsiyar mota ta gani a tsakar gidan, kasancewar akwai yalwar haske kamar rana.
Hannun ta wannan matar ta kama har izuwa wajan motar nan, kana ta bu'de gidan baya ta saka ta a ciki ta rufo 'kofar.
Gyefan ta kuwa, Naseer ne sanye cikin dakakkiyar shadda kalar golden, 'dinkin yar ciki da malum² da yasha aiki mai azabar kyawu. Kan shi ba hula Sai gashin shi da ya sha gyara sai uban 'kamshi ya ke zabgawa.
Hannun ta ya ruk'o tare da furta mata cikin kunnan ta,
"Finally, u'r mine. Na fi kowa sa'ar kyakkyawar mata".
Mufeeda ta bu'de baki za tai magana, driver ya figi mota.
Saurin kallon shi Naseer ya yi tare da fa'din,
"Hey KB! Easy mana. Ka tafi da mu a hankali, ba gudun ceton rai muke ba".
"Shege aboki na, wato ba gudun ceton rai muke ba ko? To kwantar da hankalin ka, zan tafi daku a hankali kamar yadda kunkuru ke tafiya". Fa'din abokin sa Kabiru.
K'ala bai kuma cewa ba, sai ma juyawa yai yanawa Mufeeda magana k'asa² kamar zai shige jikin ta.
KB na kallon su ta madubi, sai ya kunna radio mota tare da kunna wak'ar John legen _All of me_.
Aiko Naseer ya shiga bin wakar tare da kallon Mufeeda ya na sakin mata lallausar murmushi.

💞💞💞💞💞💞
Can wajan taron kuwa, decoration d'in da akai a wajan ma kawai abun kallo ne. Fad'i 'bata baki.
Abokan ango kam gaba d'ayan su sanye suke da shadda kalar ba'ki da yaji aiki da ba'kin zare kana aka bi shi da fari. Sun yi matu'kar ba da kala.
Gaba 'daya kowa ya hallaru. Zuwan amarya da ango kawai ake jira.
KB ne yai parking tare da fa'din,
"Ka da ku fito, bari naje na sanar da zuwan ku tukun". Ya na gama fa'din hakan sai ya fice da sauri hannun shi 'dauke da malun² 'din shi ya na 'ko'karin sakawa.
Yuuu 'kawayen amarya su Mashkura da kuma sauran abokan ango suka yo wajan motar su Mufeeda.
Daga can ciki kuwa, dama tuni KB ya sanar wa MC zuwan amarya da ango. Nan MC ya shiga shaidawa jama'a ga amarya da angon ta nan shigowa.
Mashkura ce ta tsara abun, abokan ango ne gaba, sai Amarya da ango a tsakiya, kana 'kawayan amarya a baya hannuwan su 'dauke da kyalkyalin da ake fesawa amarya da ango.
Hannun Mufeeda na cikin na Naseer. Abokan ango suka soma tafiya, ya yin da ango da amaryar sa suke bi musa a baya kamar baza su taka ba. Su Mashkura na biye dasu tare da fesa musu wannan abun mai kyalkyali.
Tuni DJ ya saki wa'kar romantic na _korede Bello_.
Su na shigowa ido gaba 'daya ya koma kan su, ya yin da kowa ke fa'din albarkacin bakin sa akan dacewar da wa'dannan amarya da ango su ka yi.
Tuni DJ ya canza wa'kar ya maye ta da wa'kar Recado _Easy jeje_. Aikuwa abokan ango cikin malum malum sai 'dikar rawa suke. Daga bisani suka raka ango har wajan zaman sa shi da amarya sannan kowa ya koma wajan zaman sa. Don an yi abun a tsare ne. Wajan zaman k'awaye da kuma abokai da ban ya ke. Abokai su na ta side 'din amarya, ya yin da 'kawaye su ke a side d'in ango.
Tuni shagali ya soma. Farko dai Zaheeda da Zaliha MC ya kira tare da ba su waje domin su baje kolin murnar su a ranar auran wansu. Aiko MC ya saka masu wa'ka mai sauti. Sun cashe iya cashewa, sannan sun sha li'ki. Bayan komawar su wajan zaman su, MC ya kira amarya Mufeeda akan ta zo ta tsa a stage.
Bayan ta fito, MC ya sa aka kawo caton d'in Chapman har guda biyar, sannan yai sanarwa da duk mai son amarya ta koma ta zauna a mazaunin ta, sai an saye Chapman d'in nan duka, kuma duk guda 'daya dubu biyar. Kuma duk guda caton 'daya 12 ne a cikin. 12×5 zai ba da 60. Kuma 5000×60=300,000.
Tashin farko KB ya fito ya 'dauki Chapman 'din nan guda uku ya mi'kawa MC tare da fa'din,
"Ga shi nan kai ta sha". Tare da li'kawa Mufeeda sababbin 'yan 'dari biyar² har dubu sha biyar.
Ya na komawa wajan zaman sa, wannan matar da ta saka Mufeeda a cikin mota mai kama da Mommah, ta fito ta d'auki Chapman guda hud'u, tare da likawa Mufeeda 'yan dubu² har dubu ashirin.
Mashkura ma tai 'karfin hali ta fito ta 'dauki Chapman 'daya tare da li'kawa Mufeeda dubu biyar 'yan 'dari biyar² zuciyar ta na suya tare da 'kara jin tsananin kishin Mufeeda.
Ita kuwa baiwar Allah Mufeeda kan ta na 'kasa, Sam wannan li'ki da ake mata bai wani burgeta ba, don ga ni ta ke almubazzaranci da kud'i ne.
Haka dangin ango da abokan sa da 'kawayan Mommah su kai ta siyan Chapman 'din nan har ya 'kare, ka na MC yai masu jinjina tare da cewa Mufeeda za ta iya komawa wajan zaman ta.
Abokan ango da 'kawayan amarya MC

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login