Showing 9001 words to 12000 words out of 115393 words
irin tamfatsetsan gida mai uban kyau haka shi ne ya kai matar shi wancan a kurkin. Hmm Ku dai bi ni a hankali, zakuji labarin Mufeeda mai cike da sar'ka'kiya.
*Share and comment*
*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)
ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 7*
Horn ya yi a kofar 'katotan gate din gidan su. Mai gadi ya wangale masa shikuma ya Danna hancin motar tare da yin parking a wajan aje motoci sannan ya fito hannun shi ri'ke da briefcase ya nufi wajan mai gadin tare da dan russunawa ya gaida shi.
Cikin fara'a baba mai gadi ya mi'ka masa hannu su kai musabaha tare da fa'din,
"barka da dawowa Mal Nasuru, ya wajan aikin?"
"Alhamdulillah baba mun same Ku lafiya?"
"Lafiya 'kalau Mal Nasuru, Allah ya maka albarka ya kuma kawo zuri'a na gari."
"Ameen baba nagode". Naseer ya amsa cike da kunya, don shi mutum ne mai kunya.
"Baba bari na 'karasa ciki, sai na fito karatu"
"To mal Nasuru a huta lafiya"
Cikin gidan ya shige, part 'din hannun daman shi ya fara shiga.
Tun daga shigowar shi har parking 'din motar shi a idanun ta ya yi. Wani irin kyau da kwarjini ta ga ya 'Kara yi Mata. Mai makon ya yo part 'din mahaifiyar sai ya nufi na matar da tafi tsana a rayuwar ta, tuni annurin fuskar ta ya 'dauke, sakin labulen ta yi tai saurin juyawa. Bibbiyu take tsallake steps 'din. Kai tsaye ta fa'da Mata bedroom ba tare da knocking KO sallama ba, a firgice haj Jummai ta juyo a 'Dan firgice saboda yadda aka turo 'kofar ta ce,
"Lafiya baby? What's wrong with you?".
Wacce aka Kira da baby ta ba ta amsa da,
"Mom yaa Nas is back, kuma ya wuce 'dakin wancan munafu'kar matar. Was ya san ko wani asirin zata bashi yau".
"WHAT!!! ki na nufin Naseer ya dawo? Kuma bai shigo, ya na 'dakin ba'kar munafukar matan can? Noooo bazai yu ba, bazata raba ni da yara na ba, wannan Karan Zan nuna Mata 'karfin uwa". A matu'kar hargitse haj Jummai ta fa'di hakan.
"Yauwa mom ai gwara kije, idan ba haka ba wannan matar sai ta rabaki da duk abunda kika mallaka, munafuka don taga ita ba ta haihu ba".
"Assalamu alaikuma"
"Ameen wa'alaikumussalam. Muryar wa na ke ji kamar na 'da na Naseer?" Ta amsa sallamar me ya yin da take fitowa daga bedroom. Sanye take da dogon hijjab har 'kasa.
"Wallahi Umma ta ni ne, dawowa na kenan daga Kaduna na ce na yi missing 'din Umma na da kuma dadda'dan kunun gya'dan ta".
Haj Zulfah tai murmushi tare da fa'din,
"Aikuwa kazo a sa'a, don yanzu na gama na juye a flask, daddyn Ku ya ce min zai dawo anjima ka'dan in dama masa, had da alala ma na yi".
"Kai Alhamdulillah Ummah a kawo min, dama na kwaso yunwa ta". Naseer ya fa'da tare da shafa cikin sa.
Murmushi ta yi tare da nufan kitchen 'din, ta zubo masa kunun cikin wani cup mai kyau, sannan ta 'bare masa alala a wani 'Dan ma daidai cin plate da yaji kayan ha'di ha'de da kwai a ciki ta ta yayyanka masa da wuka yadda zai masa da'din ci, ta kawo ta aje masa anan tsakiyar center carpet 'din dakin don't ta San shi bai fiye son con abinci a dinning ba.
Saukowa ya yi ya zauna a 'kasa tare da fa'din,
"Kai ummah ta ki na ji dani" cup 'din ya 'dauka ya kai baking shi ya kur'bi kunun. Wani gar'din da'di ya ratsa kunnuwan shi ya lumshe ido tare da karka'de kunnuwa irin yadda yara suke yi. Ya kai bakin shi zai kur'bi na biyun kenan aka banko kofar da 'karfi sai da haj Zulfah ta tsora ta. Da sauri haj Jummai ta 'karasa wajan Naseer tare da ka'be cup din kunun da me hannun sa, rabi ya zube a kasa,, rabi a jikin shi. Zafin kunun ya ratsa cinyan shi sai da ya rumtse idanun.
Ta na huci ta nuna shi da yatsa tare da fa'din,
"Wato son ni ban isa in fa'da maka magana kaji ba KO? Yanzu ace ka yi tafiya har na tsawon sati biyu, ka dawo amma ka rasa fara shigowa inda na ke sai wajan wannan azzalumar mata mai raba 'da da uwa".
"Mummyyyy! Haba dan Allah, ita ma fa mama na ce, idan na shigo na gaida ta ai ba matsala ba ne, dan Allah ki dai na kawo wani tunani daban".
Hannu ta saka ta make mashi baki tare da fa'din,
"Dalla yi wa mutane shuru, sha-sha kawai. Dama an riga an gama da kai, an baka abincin da aka yi barba'de barba'de mai zaka game" sai ta mai da kallon ta izuwa ga haj Zulfah da tunda ta fara sababin ta ba ta ce 'kala ba sai ma murmushin da ke kwance a fuskar ta, don idan da sabo to ta saba da rigar uwar gidan ta ta.
"Annamimiya, dole ki koma gyefe ki na murmushi saboda kin samu abunda ki ke so, kin raba UWA DA 'DAN TA (Sabon littafi na mai zuwa) kuma bari in fa'da miki, idan baki fita al'amura na da na 'ya'ya na ba, sai na miki abunda ba ki ta'ba tunani ba". Ta na gama fa'din haka ta juyo ta kalli Naseer tare da nuna masa hanya.
Kallon Umma ya yi fuska a shagwa'be, it's kuma ta gya'da masa Kai alamar ya bi umarnin mahaifiyar shi. Hannu ya saka ya 'dauki plate 'din alalan ya nufi 'kofa.
Da Saudi haj Jummai ta fizge plate 'din ta yi jifa dashi a tsakar 'daki sannan ta masa dun du a baya ta tura 'kyeyar shi waje.
Dama Baby na baki 'kofa ta na kuma jiyo duk abunda ake yi a ciki. Ya na fitowa da ita ya fara cin Karo, aikuwa ya sakar mata wani uban harara tare da Jan tsaki yai hanyar part 'din shi domin kayan jikin shi da ya ba'ci da kunu sannan yai wanka ya kuma huta.
Haj Jummai ta kalli Baby ta re da fa'din,
" kije ki ha'da masa ruwan wanka".
Kamar dama jira baby take yi, sai ta bi bayan shi da sauri da tuni shi ya ma shige. Mur'da handle 'din kofar ta yi tare da tura Kai ciki, wani dadda'dan kamshi ya daki hancin ta sai da ta lumshe idanu. Daura 'kafar ta ta yi a kan carpet sai da 'kamarfa ta nutse don taushi.
"Yaya Nas akwai tsafta da gayu". Ta furta cikin zuciyar ta
Wani hoton shi ta 'kurawa ido. Sanye yake cikin suit, kuma a tsaye ya ke, wando ba'ki rigar fari, sai ya ratayo ta sama a kafa'dar shi, dayan hannun shi kuma ya na cikin wando, ya saki tattausan murmushi. Ba'karamin kyau ya Mata ba. Ba'ki ne shi, irin colour 'din black American nan, amma kyakkyawa ne ajin farko. Hancin shi dogo har ba'ka, domin kamannin shi 'daya da daddy har da tsayin, ka na ganin shi like father, like son. Bakin shi 'dan 'Karami dai dai da shi, ga dimple da ya 'Kara masa kyau a duka side chick 'din sa, idanuwan sa ba masu girma ba ne, sannan kuma ba 'kanana ba.
"Uban me kike min a 'daki? How many times do I have to warn you to stop stepping your legs to my room? Leave now before I chop you into pieces, useless human being" da tsawa ya fa'di hakan da ya saka ta daburce da kyar ta iya gano kofa ta mur'da handle 'din ta fita da gudu sai part 'din mummy.
Ji ta yi kawai an fa'do mata ajiki. A tsorace ta 'dago tare da fa'din,
"My goodness, wai me yasa baby ke kullum ba ki da burin da ya wuce ki rin'ka frightening 'dina ne"
Mai makon ta ba ta amsa, sai ta fashe da kuma. Haj Jummai ta ce,
"Lord in heaven. Yanzu kuma mai ya faru?".
Turo baki ta yi irin na shagwa'bar nan ta ce,
"To ba yaa Nas ba ne ya min tsawa wai na fitar masa a 'daki".
Shafa kan ta ta yi tare da fa'din,
"Its all right, ka da ki damu. KO ya 'ki ko ya so, ke ce dai matar da zai aura".
With soo much excited ta ce,
"Mom really??"
Shafa kan ta ta kuma yi ta re da fa'din,
"Don't worry my daughter, I'm very sure. Ka da ki damu da duk wani abundan ya ke miki da zaran ya zama naki shikenan." Cike da farin ciki ta rungume haj Jummai tare da ba ta peck a chic 'din ta, sannan tai sama da gudu. Girgiza Kai haj Jummai ta yi ta na murmushi. Sosai ta ke jin 'yar 'kanwar tata a cikin ran ta.
Wanka ya ke yi, amma gaba daya tunanin Mufeeda ne ke masa yawo, tunanin hanyar da zai taimake ta ya ke. Ya da'de a cikin ba yi kamin ya fito daure da towel a 'kugun shi, days kuma ya na goge man shi. Gaban mirror ya je bayan ya gama goge jikin shi. Man shafawan shi ya dauko mai matu'kar 'kamshi da taushi ya shiga yafawa black shinny skin 'din shi, sannan ya 'dau cumb ya taje gashin shi da ba wani yawa gare shi sai kamshi yake fidda sabida wanke shi da ya yi da mayuka masu matu'kar 'kamshi. Body spray ya fesa kusan Kala biyar, tuni 'dakin ya 'dume da 'kamshi mai da'din gaske. Closet 'din shi ya nufa ya dauko short da vest tare da wata dakakkiyar gezna kalar ruwan goro, sai da ya fara saka na cikin sannan ya saka shaddar. 'Dinkin zamani aka masa ba 'karamin 'Kara fito da kyawun sa 'din kin ya yi ba. Shi kan shi da ya 'Kara kallon kanshi a madubi, sai da ya murmushi. Wajan takalman sa ya nufa ya 'dauko wani half cover 'kalar baki sai shinning ya ke, ga wash stones multicolor masu walwali da akawa saman takalmin kwalliya da shi. Har zai fita haka sai kuma ya dawo ya dauki bakar hula zanna ya murza a kan shi.
*Share and comment*
*MAMAN UMMEEN KU CE*✍🏼
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
( _'kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi_)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
_laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadama_.
*Story and written by*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( _Maman Ummee_)
ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 8*
Ko da ya fito daga 'dakin shi, sai ya hangi motar daddy a parking space. Part 'din mummy ya nufa. Sallama ya yi sannan ya mur'da handle 'din kofar, ba kowa a palon sai TV da ke ta 'karar banza. Kai tsaye ya hau sama, a 'kofar mom yaja burki tare da knocking. Haj Jummai ta San sai ba baby ba ce, don ita ba 'dabi'ar ta ba ce yin knocking ko sallama, kuma Sam haj Jummai ba ta kwa'bar ta a kan hakan.
"Yes come in haj" Jummai ta ta fa'di daga ciki a da'kile don ta San wake knocking 'din.
Tura kofar ya yi ya shiga, zaune ta ke a bakin gado ta na 'da'd'daga lesukan da ta fito dasu daga wardrobe, baby ce ta dame ta akan ta ga wani swiss pitch kuma shi take so ta 'din ka. Zama ya yi gyefan ta tare da daura man shi a kan kafa'dar ta tare da fa'din,
"Allah sarki mom ba ki missing autares 'din ki ba ne, naga fuskar ki a turni'be".
"Ba ka na da wacce ta fini a wajan ka ba, so ka tattara a koma can na yafe mata Kai". Ta fa'di hakan ne domin taga reaction din sa. Narkar da fuska ya yi tare da fa'din,
"Mom pleaseee, a duniyar nan kaf, ni ba ni da kamar ki, ke ce fa kika dauke ni tsawon wata tara a cikin, ki kazo ki ka sha wuya kika haife ni sanadiyar hakan ma kika kamu da hawan jini, sannan kika Raine ni ki ka nuna min so da kauna fiye da sauran 'yan uwa na. To mom a duniya akwai wacce za ta yi kusa da ke ne balle kuma ace har ta fiki. Mom ke ta daban ce a nan". Ya nuna sai tin zuciyar shi.
Ba 'karamin da'di maganganun sa suka mata ba, sai taji babu wani sauran bacin rai a tare da ita, 'dago man shi ta yi ta masa peck a goshi tare da fa'din,
"Son Kai da Saudart ban 'kaunar kuna zuwa wajan matar can wallahi, Ku baza Ku ga ne ba ne, poisoning mind 'din Ku ta ke yi"
Mai makon ya bats amsar maganar ta, sai ya dauko Mata wani zancan daban. Ri'ke cikin sa ya yi tare da fa'din
"Wasshh Mom i'm hungry, ciki na zafi, juya min yake yi" a shagwa'be ya fa'di hakan.
Aikuwa da sauri mom ta ru'ko hannun sa ta ce,
"Muje dinning ga abincin can, dama tuni na saka maid ta ha'da mama favorite 'din ka".
A tare suka sauko su na 'Dan hirar uwa da 'da har suka iso wajan dinning 'din. Har ya ja kujera ya zauna, mom ta ce,
"Son please go and get baby, nasan ta na can ta na karance karancan novel" kamar zai yi musu sai kuma ya mi'ke ya nufi 'dakin ta tare da kwan-kwasawa. Daga cikin baby ta ce,
"Waye ne??
"Ki fito mom na kiran ki" ya ba ta amsa tare da barin wajan.
Da sauri tai jifa da takardan sannan ta diro daga kan gadon ta yo waje.
A dinning ta same su, ita ma ta ja kujera ta zaun.
"Ya kika zauna kuma? Ki tashi ki serving 'din shi ma na".
"No ta barshi kawai, Zan yi da kai na". Yai saurin katse ta tare fa bu'de cooler. Roasted Fish ne ya sa kayan amshi harda irish ga kuma smoothie a gyefe sai tururin sanyi yake yi. Tuni ya ha'diye miyau tare fa fara serving 'din kan shi.
"Shi kawai za ka ci? Ga fa Paraguay rice nan Baby ta ha'da maka".
Ya ba ta amsa da,
"No wannan kawai ma ya ishe ni'.
Sosai baby taji haushi duk da ba ita tai girkin ba, don ita ko gas ma ba ta iya kunnawa ba. Kuma ta San saboda mum ta ce masa ita ta yi shiyasa ya'ki ci.
Babu abunda ka ke ji sai 'karan cokala. Tissue ya 'dauka ya goge bakin shi da shi tare da fa'din
"Alhamdulillah". Ya ja kujera baya ya mi'ke.
"Mum bari naje company na duba abunda ke gudana a can, kin san kwana biyu ba na nan."
"Hakene gaskiya. To Allah ya kiyaye. Amma na zaci zaka 'dan kwanta ne ka Hutu saboda ka sha hanya" mom ta fa'da.
"Eh hakene, amma ba da'dewa zanyi ba shiyasa". Sai ya mai da kallon shi wajan baby tare da fa'din,
"Kije ki gyaramin 'daki na, sauran idan na dawo in ga ba dai dai ba". Da to ta bashi amsa. Shikuma ya fice.
Kai tsaye part 'din haj Zulfah ya wuce, don tun da bai ga daddy a side 'din mom ba, hakan ya tabbatar mishi a 'dakin Umman shi ya ke. Sallama ya yi tare da knocking. Daga ciki aka bashi izini ya mur'da handle 'din ya shiga.
Daddy kishingi'de a kan kujera, haj Zulfah na daga gyefan shi, ga dukkan alamu labari take bashi mai sanya nisha'di. Don sai sakin murmushi ya ke yi. Don wannan 'dabi'ar haj Zulfah ne, idan har mai gidan a 'dakin ta ya ke, gaba daya lokacin ta take bashi, haka zata saka shi a gaba ta na masa tausa tare da bashi da'da'dan labaruka masu sanya nisha'di bayan ta gama cika masa ciki da da'da'dan abincin ta. Domim ita gwana ce wajan girki. Duk da ita kan ta haj Jummai 'din ma ba baya ba ce, kawai ita kishi ne ya rude Mata idanu ta kasa kula da mijin ta yadda ya kamata. Kullum sai tashi hankali.
'Karasowa yayi tare da dur'kusawa har 'kasa ya ce,
"Daddy Ina wuni? Na same Ku lafiya?"