Showing 39001 words to 42000 words out of 115393 words

Chapter 14 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22904

maganganun Mufeeda su ka ba. Ji ya yi wani farin ciki na ziyar ta zuciyar shi. Ga dukkan alamu ta wajan ta bazai sha wahala ba. Babbar bala'in dai ya na wajan mummy.
Mi'kewa ya yi tare da fa'din,
"Ina zuwa 'dan jira ni". Ya na fa'din haka yai bedroom 'din shi. Can ya fito hannun shi ri'ke da wata sabuwar waya phantom 9 ya mi'ka mata tare da fa'din,
"Tun tuni na ke son na baki wayar nan Allah bai yi baya sai yau. Naa saka miki simcard a ciki. Kin ga ke nan ko ba ki ganni ba, za ki ji murya ta".
Kar'ban wayar ta yi tare da fa'din,
"Nagode Allah ya saka da alkhairi."
Da ameen ya amsa mata.
"Zan koma ka da Ummie ta ji shuru".
"To shikenan. Ko gaida min da Ummah na, sai nai shigo".
"Bayan yanzu ko shigowa ba ka yi. Da kai kullum sai kazo ka ci abinci. Breakfast da dinner". Saurin ri'ke bakin ta ta yi, domin maganar zuciya ce ta fito. Da gudu ta kwasa.
"Ki yi a hankali, kin San fa akwai aiki a jikin ki". Naseer ya fa'da da 'dan karfi yadda za ta ji. Murmushi 'dauke a fuskan shi.


*******************
Lukman ne zaune akan wata kujera da aka yi ta sak royal amma na siminti sai aka mishi penti. Akwai shi guda bakwai a waje da ban da ban a nan cikin garden 'din. Waya ce a hannun shi ya na browsing yadda zai shawo kan budurwa.
Kaman ance ya 'daga idanun shi, aikuwa ya hango baby ta na shan shisha ta na fesar da haya'ki cike da kware wa, har wani o o ta ke yi.
A matu'kar fusace ya mi'ke yai wajan...........





*KADUNA*

" KURA Allah ya wadaran halin ki wallahi. Yanzu baaba ki ji kunya ba? Ni kike kawowa katin gayyatar auran ki da mijin aminiyar ki?" Fa'din Zabba'u rai a 'bace.
"Ke ni fa wallahi zan iya yin tsirara mu daku da ke a nan wajan idan ki ka 'kara cewa mijin aminiya ta. Wa ya ce tai sake? Ta yi sake, ni kuma na dafe".
"KURA wallahi 'karshan ki bazai yi kyawu ba. Maciya amana irin ki, mutuwar wula'kanci suke yi."
"In Allah ya yarda bazan yi mutuwar wula'kanci ba, shegiya mai mugun baki". Fa'din KURA tare da yin gaba ta bar Zabba'u da ke tuyar wara da tagumi.


*WAI WACECE WANNAN KURAN NE DA ZABBA'U KE I'KIRARIN TA CI AMANAR AMINIYAR TA?*

*BARI DAI MU WAIWAYE BAYA MUJI SHIN ITA KAN TA MUFEEDA WACECE ITA*



*WAIWAYE ADON TAFITA*



*SAI KUN BIYO NI A NEXT PAGE DON JIN ASALIN LABARIN MUFEEDA IDAN NAGA RUWAN COMMENTS*



*MAMAN UMMEEE CE*✍🏼

*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE 20_*


*WAIWAYE ADON TAFIYA*
*TUSHAN LABARIN MUFEEDA*


*___________________________________*
Malam Datti da Indo mai kalwa 'ya'ya biyu kawai suka haifa a duniya. Ahmadu shi ne babba sai 'kanin sa Kallamu(Kallah).
Su 'yan asalin jahar Bauchi ne. Tsangwama ce ta maido su garin Kaduna.
Mal Datti mutum ne mai son duniya da kuma budurwan zuciya. Sa'banin Indo mai 'kalwa. Ita macece mai hakuri, kau da ido ga kuma faran faran da mutane.
Sun 'dau tsayin shekaru min Allah a ba su kyautar cikin Ahmadu. Sosai kuwa su kai farin cikin da wannan kyauta da Allah ya basu.
Mal Ahmadu ya samo sunan malam ne kasancewar sa malamin Allo, ya na tara almajirai a zauran gidan shi ya na masu karatu.
A zahiri shi mutumin kirki NE, kuma kowa kallon mutumi kirki ake masa. Amma a ba'dini, shi akasin haka ne. Domin shi 'din malamin duba ne. Shi kan sa baza iya 'kirga adadin matan aure da 'yan matan da ya yi mu'amulan aure da su ba da sunan magani ya ke masu.
Da wannan ci da addinin da ya ke yi ne har ya samu auran Indo. Mahaifin ya ba shi ita sadaka. Sun jima ba su sa mu haihuwa ba. An yi ji'ke ji'ken, an yi tsubbace tsubbacen, amma ba'a da ce ba har sai lokacin da Allah da kan shi ya ga dama ya ba ta. Wanda shi kuma gogan yake tunanin 'yan tsubbace tsubbacen shi ne yai sila.
Sam Indo ba ta jin da'din zama da Datti, kawai biyayyar mahaifin ta ta ke yi. Ga shi zaman ma ba da'din shi ta ke ji ba. A haka har Allah ya sauke ta lafiya ya ba ta 'da namiji, aka saka masa sunan mahaifin Indo wato Ahmad. Sai ta ke kiran shi da mai sunan baba.
Mai sunan baba ya ta so cikin natsuwa, duk da irin sangartashi da mahaifin na shi ya yi, hakan bai sa ya lalace ba saboda 'karfin addu'a irin na mahaifiya. Sosai ta dage wajan ba shi tarbiyya. Da kan ta take koya masa karatu kasancewar ta 'diyar malamin da ake ji da shi a cikin 'kauyan na su.
Mal Datti ba fasa abun da ya ke aikatawa ba, duk da cewar matar tashi ta kamashi kusan say biyu. Na farko ta je kai masa abinci a 'dakin sa na zaure idanun ta su kai mummunar ga ni. Na biyu kuwa da matar makwabcin sa ta ka mashi turmi da ta'barya.
Aikuwa mal Datti yai tsubbun shi ya rufe mata baki yadda bazata ta'ba fa'dawa kowa ba, kuma bazaata bar gidan sa ba.
Sai da Ahmadu yai shekara bakwai ka na Indo ta 'kara samun wani cikin.
Wannn lokacin 'dokin da mal Datti ya yi fiye da wacce yai lokacin da Indo ta sa mu cikin Ahmadu. Lokacin ko da ta sauka, ya na 'daga 'dan ya ce ga magajina. Nan ya masa huduba da suna *KALLAMU* ya na Kiran sa da *magaji*. Su na akai na ke ce raini kowa sai da ya San irin soyayyar da mal Datti ya ke wa Kallamu.
Kallamu ya taso like father like son. A sangarce ya taso, tun ya na 'dan shekara 10 mahaifin sa ya koya masa 'yan tsubbace tsubbacan sa. Idan ko Kallamu ya maka sharri ko kai wanene ba ka fita.
Da ma tuni Indo ta fara sana'ar kalwa. Idan Kallamu ya ma ta baki, akan baza tai ciniki ba, to kuwa baza ta yi shi ba haka za tai kwantai. Muguntar shi tun daga 'kan mahaifiyar shi ta soma, kana ta koma wajan jama'ar gari. Kwata kwata kallah bai da tausayi a zuciyar shi.
Ya na da shekara goma, 'dan uwan sa kuma na da sha biyar. Ahmadu shi ke noma, shi kuwa Kallah atafau ya ce bazai yi aikin wahala ba hannun shi yai kan ta. Da ya ke Ahamadu mai ha'kuri ne, sai ya ce a bar shi shi zai yi.

A wata shekara ne dubun mal Datti ya cika, domin kuwa wata 'dalibar sa mai suna Hinde ya durkawa ciki. Kuma ita ma dai mahaifin na ta na baya ba wajan bugun 'kasa da tsubbace tsubbace. Hinde ta zo ta sami mal Datti ta fa'da masa ita fa ciki ne da ita.
Ai kuwa mal Datti ya hau bala'i tare da zagin ta. Sai da ya mata taaas sannan ya mata koran kare. Ai ko Hinde ta je ta fa'dawa mahaifin ta. Shi kuwa mal Alqah ya buga ihu ya ce aikuwa baza ta sa'bu ba. Sai ya koya wa mal Kallah hankali. Idan zai rainawa kowa hankali ai shi bai isa ya rai na masa ba.
Aikuwa hakan aka yi, bayan sati guda mal Datti ya fito ya dingi kurma ihu a kwar gida sai da mutane suka ha'du ka ce wani sarkin ne ya zo ko gwamna. Aikuwa mal Datti ya shiga to na wa kan shi asiri da duk matan aure da kuma 'yan matan da yai amfani da su. Aikuwa tuni labari ya je gun mai gari, mai gari ya sa ka fa'da wa suka kawo masa mal Datti da kuma duk matar auran da ya ke'be da ita. Aikuwa hakan aka yi. Mai gari ya sa akawa mal Datti bulala 250, duk da wasu a wajan sun ce jefe shi ya kama ta a yi a addimin musulunci tun da shi mi aure ne. Amma sai mai gari ya ce a'a ya kore su shi da matar shi da 'ya'yan shi da kuma matan auran da suka ba shi kan su. Kuma awa guda ya ba su akan s tattara su bar masa gari ko kuwa wallahi jefe su zai yi.

Aikuwa cikin abinda bai fi awa 'dayan ba, mal Datti ya kwashi iyalan shi da suke ta kuwa da takaicin abinda ya aikata, amma fa ban da Kallah. Su ka tattara su kai Kaduna............



*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
*RASHIN COMMENTS 'DIN KU SHI YA JA MAKU TYPING KA'DAN*
😏😏😏😏😏🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE_ 21*

Mal Datti kasancewar ya na da 'dan wasu ku'da'de a jikin sa, da su yai amfani ya kama haya a unguwar shanu. Ahmadu da Kallah kuwa dama ba karatun boko suke yi ba. Da su ka dawo Kaduna, Indo mahaifiyar su ta saka Ahmadu a wajan kanikanci na moto, shikuma Kallah ta saka shi wajan koyan 'dinki, amma ko sati bai rufa ba ya dai na zuwa. A cewar shi wai sun mai da shi jaki kullum shine akan titi ya na yawon sayo masu kayan 'din ki da kuma abincin da zasu ci. Indo ta yi fa'dan ta yi fa'dan amma Kallah yai kunnan uwar shegu.
Shikuwa bawan Allah Ahmadu, ya dage da zuwa wajan sana'ar shi, gashi kuma ya jefa kan shi a makarantar addini na dare. Kullum ana idar da magriba za su soma karatu, sai kuma karfe tara. Sai su yi isha'i kowa ya kama gaban shi.
Mal Datti kuwa likafa ce ta cigaba. Domin a hankali a hankali ya cigaba da sana'ar shi ta duba shi da mataimakin sa Kallah har ya kasance mata layi suke masa kamar mai raba zakka. Don har canza masa suna aka yi da *DATTI AIKIN KA YANKAN WU'KA*.
Ba 'karamin ku'di ya ke samu ba da kuma dabbobi, a 'kalla kullum gidan sa sai an yan ka kaji da zabbi kusan ashirin. Sai dai Indo da 'dan ta Ahmadu saam basu ci. Idan ma kwa'dayin su ke ji, sun gwammace su sayo a titi su ci.
Lokacin da Ahmadu yai shekara ashirin da bakwai. Sosai ya gwanance a aikin kanikan ci don Oga ne mai zaman kan shi. A lokacin ne kuma ya tara 'yan ku'da'dan sa ya sa yi wani 'karamin gida a badarawa. Ciki daya guda biyu sai ciki da palo.
Nan ya tattara mahaifiyar shi suka koma, don ya yi rantsuwa mahaifiyar shi baza ta cigaba da zama da 'batacce ba, don shi kan shi ya San cewa mahaifin shi boka ne, kuma zama da boka haramun ne don ya zama kafiri. Duk wanda zai ha'da Allah da wa ni kam kafiri ne.
Mal Datti kuwa ya ce shi bai sakin ta, ta je dai tai ta zama da auran shi a kan ta. Ahmadu bai damu da abunda mahaifin na shi ya ce ba, ya tattara mahaifiyar sh suka koma badarawa in da gidan shi ya ke.
A lokacin ne kuwa Allah ya ha'da shi da wata kyakkyawan yarinya mai nutsuwa ana badarawan mai suna FATIMA.
Fatima yarinya ce mai nutsuwa da shiga rai. Mahaifin ta mutum ne mai sani, kuma ana matu'kar ganin darajar shi a unguwar su, don shi ne ma limami a unguwan su. Fatima yarinya ce mai biyayya.
Tunda Ahmadu ya kyallara idanu ya ga FATIMA 'kaunar ta ya ka ma shi. Sai da ya fara zuwa ya nai mi izinin a wajan mahaifin ta, kamin ya soma zuwa zance wajan ta. Mahaifin Fatima ya san Ahmadu sosai, kasancewar kullum sai ya gan sa a masallaci. Kuma ya na zuwa darasin da shi ya ke koyar da shi, kuma kullum zaka gan shi a sahun gaba.
A hankali soyayya mai 'karfi ya shiga tsakanin Ahmad da Fatima.
Mahaifin Fatima ya na gab da taran Ahmadu akan ya ce masa ya turo magabatan shi, aka tare shi da fa'din Ahmadu fa 'dan mace ne. Ma'ana bai da mahaifi. Hankalin mahaifin Fatima ya ta shi, amma kuma daga ba ya sai yai watsi da zancan kasancewar ya San hassada irin na aure, amma a zuciyar shi ya 'kudurta yin gaggawan bincike. Sabida shi bincike halas ne a wajan nai man aure. Kamin mahaifin Fatima ya gama binciken sa, tuni labari ya kara'de dangin Fatima cewar yaron da ke zuwa wajan ta 'dan boka ne kuma kwanaki 'kanin sa yai wa wata ciki , kuma aka 'daura aure ba tare da ta haihu ba. Aikuwa hankalin wannan dangi ya tashi matu'ka. Mahaifiyar Fatima ta saka ta a 'daki tai mata dukan kawo wu'ka tare da mata kyakkyawan gargadi akan idan ta 'kara ganin ta da dangin boka sai ta yanka ta da wu'ka.
Ai kuwa Fatima tai ta kuka ta na fa'din sharri ne, Ahmad 'din ta ba boka ba ne ba.
Mahaifin ta ya ji labari, kuma maganar ya girgiza shi, domin shima binciken shi ya tabbatar ma sa da mahaifin Ahmadu da ''kanin sa bokaye ne. Amma in DQ hankalin shi ya 'dan kwanta shine, wa'danda ya 'daura kan binciken sun tabbatar masa da cewar shi Ahmad da mahaifiyar sa ba sa goyan bayan abunda su ke yi, wannan dalilin ne ma ya sa shi Ahmad 'din ya sa yi gida tattaro mahaifiyar sa su ka dawo nan. Wannan dalilin ne ma ya sa ya ke jin kamar zai iya ba shi auran 'yar ta sa. Tunda mutane da dama sun masa kyakkyawar shaida.
Hmm ba 'karamin rikici a kai ba, domin kaf dangi ba su yadda da batun auran Fatima da Ahmad ba, idan ka 'dauke mahaifin ta da ita Fatiman.
Ba 'karamin 'kura a kai ba, domin kaf dangi sun zare hannun su akan auran. Mahaifiyar Fatima kuwa cewa ta yi, idan an yi auran ko in da ta ke ka da ta nai ma, idan kuma ta nai ma ba ta yafe mata ba.
Ba 'karamin razana Fatima ta yi ba da wannan batu. Domin ihu ta ri'ka yi akan ita wallahi ta fasa auran ba zata auri Ahmadu ba. To dama mahaifiyar Fatima hakan ne ba har zuciyar ta ba, ta dai fa'da ne don Fatima ta ji tsoro. Aikuwa mahaifiyar Fatima na jin haka ta jawo ta jikin ta ta CE,
"Na yafe miki Fatima da ma ni na fa'di hakan ne kawai don ki janye ra'ayin ki. Allah ya miki albarka".
Sosai Fatima ta ji da'din maganar mahaifiyar ta ta. Nan suka koma kamar yadda su ke da. Fatima ta fita Harkan Ahmad duk da kuwa son da ta ke masa. Duk da ta San daurewa kawai ta ke yi. Yai aiken, yai aiken amma Fatima ta 'ki fitowa. Ahmad duk ya rame ya fita haiyacin sa. Mahaifiyar sa ke tausan sa.
Katsam wata ranar asabar, mutane su na zazzaune a tsakar gida sai ji su kai daga masallaci ana sanar da daurin auran Fatima da Ahmad. Ba 'karamin girgiza familyn Fatima su ka yi ba. Aikuwa ta ke mahaifiyar Fatima ta yan ke jiki ta sume. Ita kuwa Fatima duk ta gigice sai kuka ta ke yi. Aikuwa dangi su kai ma ta caaa, dama auran zumunci ne tsakanin mahaifin Fatima da mahaifiyar ta. Duka suka hau ta da shi wai ta na sane da komai uban ta ya 'daure mata gindi.
Mahaifin Fatima na shigowa ya ce umarni ne ta harha'da 'yan kayan ta ta bi mijin ta ya na waje ya na jiran ta. Kuka sosai Fatima ta yi. Dakyar mahaifin na ta ya rarrashe ta tare da yi mata nasiha mai ratsa zuciya ka na ya rakota har bakin 'kofar gida in da Ahmad ke tsaye ya ce mata ya ja matar sa su wuce.
Dama dangi sun ce ko mahaifin ta bai yi haka ba, su bazazu rakata gidan zuri'ar boka ba. Kuma sun mata concrete warning akan ko 'kafar ta ka da su 'kara ga ni a gidan ko mai ya faru.
Haka Fatima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login