Showing 72001 words to 75000 words out of 115393 words
ya 'kira akan su zo su nuna nasu bajin tar ta wajan rawa.
Aikuwa sun nuna d'in. Domin abun mamaki ya bai wa Mufeeda, domin komai a tsare suka yi shi yadda kasan dama can sun tsara hakan. Musamman yadda suke bin rawar in step.
Mufeeda ba ta gama shan mamaki ba, sai da aka kirawo su ita da Naseer aka saka masu gasa akan duk Wanda ya fi wani iya rawa a cikin su.
Ko da Naseer ya mi'ke, saurin rik'o hannun shi ta yi tare da marairai cewa ta ce,
"Yalla'bai ni ban iya rawa ba". Harara ya maka mata tare da sunkuyowa sai tin kunnan ta ya furta,
"Ah haba, wane ke. Ai twins sun ba ni labarin shashewar da KI Ka yi a bridal shower".
Hakan da suka sai ya matu'kar burge 'yan kallo, domin da wani irin salo suke maganar tare da sakarwa junan su wani zazzafar kallon da su kam su basu san su na yi na. Aiko sai 'kararrakin tafin su ka ke ji.
Nan kuwa ango Naseer ya ri'ko hannun amaryar sa Mufeeda su ka shigo filin. DJ ya saki wa'kar hamisu breaker a taken wa'kar shi ta _JARUMA_.
Tuni Naseer ya kar'bi MIC 'din da ke hannun MC ya shiga bin wa'kar ya na jujjuyawa tare da zagaye Mufeeda ya na bin wa'kar.
_*Ashe da rai na ke son ki jaruma ba da zuciya ta ba, ko mai ruwa da iska akan ki ba za na dai na ke wa ba. Idan na sa mu zarrar samun ki ba za na tan ka kowa ba. Ni ban ga mai harara ba, balle na waiwaya ahh. In dai akan ki ne zana jure wahalar zuwa garin nisa. Da an tab'aki a jira ni dan ko tilas nazo na d'au fansa. Jimirin jiran ki nai dan kizo na kalle ki gimbiyar mata. Sirri na rayuwa ta ke ce kawai da kin kira ni na amsa. Zuba a baki dad'i gare ta kin ba ni taki na lasa. In dai a kan ki ne na yi nisa dan ba kiran da zan amsa. Tilas ganin mu, tilas barin mu, 'kaunar ki tun da nai nisa. Sam ba batun na FASA ko za ace min in ba da rai fansa. Tsarin zubin ki dai dai ne. Ya kama zuciya ta ne. Ina jin kamar mafarki ne. Na San ki so mataki ne. Ni ban da damuwa in had zan bu'de 'yan idanuna, in kalle ki ga ki dab dani to me zaya damu 'kalbi na. Yau za na yo amooo tunda na gane ki na da tause na. Dan yanzu na zamo ya mafatauci mai bid'ar gurin kwana. Na kwalla shela don Sanar da 'iya ma'd'diya kalamai na. Daga zuciya na ke kwantanta ina zayyino jawabai na. Idan babu ke inaa zan saka zuciya ta bar yawon 'kuna. Kowa da NASA ammmani kece cikar muradi na. Yau ga ni a ruwa kusa da kada zo ki ceci 'karko na. Ko mai da maffita kar da KI saba da furta banjama'a.*_
Wak'ar na kawo nan MC ya canza wa'kar zuwa _ATEWO_. Tuni Ango ya cire malun² ya mi'kawa KB ya hau 'dikar rawa har da su kwaso shokey. Tuni hall 'din ya hargitse da ihun jama'a.
'Karfe sha biyu aka tashi, kowa ya watse. Ango da kan shi yai driving, daga shi sai matar shi su kai gidan su.
Mashkura kuwa, ikon Allah ne ya kai ta gida lafiya. Dama ta fa'dawa Mama komin dare gidan za ta dawo, domin babu kwanar gidan amarya.
Ko da ta shigo, yanayin ta ka'dai Mama ta kalla ta San cewa ba 'karamin 'karfin hali Mashkura ta yi ba da ta tsaya aka gama komai ba bikin Mufeeda da ita. Ba ta ce mata komai ba, ta bata hanya ta wuce. Don ba ta son ta jefe ta da tambaya, ta tada mata da miki, tunda ta riga da ta San kwanar zancan.
A hankali ya ke tu'ki da hannu 'daya cike da shau'ki, 'dayan hannun shi kuma, ya kamo hannun Mufeeda da tuni ta 'bingire da baccin gajiya. Hatta 'daurin turban 'din da aka mata ya kwance, kyakkyawar gashin kan ta ya bayyana da aka kamashi akai mata parking a tsakiya tare da 'yin donut. Said 'kamshi ya ke fitarwa da she'ki. Ita kan ta wani dadda'dan kamshi mai kashe jiki ke fita daga jikin ta.
Kasancewar a hankali ya ke tafiya, minti arba'in ne ya kawo su gida.
Shi da kan shi ya fita ya bu'de get, don bai so yai wa mai gadi horn ya tashe ta daga bacci.
Bayan ya bu'de, ya koma motar ya shigo da ita tare da yin parking tare da fitowa domin ya kulle get 'din.
Sai alokacin mai gadi ya fito da gudu tare da fa'din,
"Waye nan". Murya faal bacci.
"Shiiiii! Kul de na 'daga muryan ka, ka da ma sake ka tada min mata da wannan mummunar muryan naka". Fa'din Naseer ya na zubawa mai gadi harara.
Cikin ra'da mai gadi ya ce,
"To 'yalla'bai".
"Wuce 'dakin ka, kar ka sake ka fito har sai na bar harabar gidan nan na shige 'daki".
"An gama yalla'bai. Fa'din mai ggadi tare da saurin shigewa 'dakin na shi.
Juyawa Naseer ya yi tare da bu'de motar a hankali ya ciccibo Mufeeda tamkar wata 'yar tsana. Ko rufe motar bai yi ba, wai don ka da Mufeeda ta ji 'kara ta farka.
"Yalla'bai sauke ni zan taka da 'kafafu na". Fa'din Mufeeda.
"Subhanallah! Sai da KI Ka tashin ke nan". Fa'din Naseer tare da cigaba da tafiya ba tare da ya sauke ta ba.
Mutsu² ta soma ta na son sauka, aikuwa ya ri'ke ta gam sai da ya kai ta tsakiyar bedroom ka na ya dire ta.
Saurin shigewa bayi ta yi tare da rufo 'kofar. Shi dariya ma abun ya ba shi tare da ficewa daga 'dakin domin ya sa mu shi ma yai wanka.
Wanka ta yi da da'dad'an sabulan da ke bayin. Jikin ta said sul'bi da santsi ya ke yi. Ta kwashi wajan minti goma ta na durzan jikin ta, ka na ta fito 'daure da towel bayan ta leka ta ga ba kowa a cikin d'akin.
Gaban madubi ta isa wajan da aka jera kayan kwalliya da mayuka da kuma turaruka daban².
Shafe jikin ta ta yi da wani mai mai 'kamshi. Ka na ta bi lungu da sak'on jikin ta ta fesa turare.
Wajan wardrobe ta je ta bu'de, ta 'dauko wani goguwar rigar bacci mai kauri ta saka a jikin ta tare da hijjab har 'kasa da safa, sannan ta zo ta shimfi'da darduma ta tada sallar isha'in da ake bin ta.
Ko da Naseer ya dawo 'dakin, Mufeeda har ta idar da isha'i, shafa'i da wuturi ta ke yi.
Aje wani faranti mai kyau dake hannun shi yai a side bed, Wanda ke 'dauke da dakwa² kaji da kuma fresh milk da cup biyu na glass mai 'dan karan kyau. Shima sanye ya ke cikin doguwar rigar jallabiya fari 'kar.
Bayan Mufeeda ta idar ta sha addu'a. Bacci faal idanun ta. Naseer ya umarce ta da ta tashi su yi sallah don nunawa Allah godiya da wannan rana.
Mi'kewa Mufeeda ta yi, shikuma ya shimfida wata daddumar a gaba ta ya ta da sallah.
Raka'a biyu yai ya sallame. Juyowa tai ya fuskance ta. Ita kuma sai wani lumshe idanuwa ta ke yi, don bacci ta ke yi.
Yadda take yi da idanuwan ta sai ya kashe masa jiki, domin Mufeeda wani irin idanu gare ta masu matu'kar daukan idanu. Idan ba farin sani ka mata ba, za ka rantse da Allah iyayi ne gare ta, alhali haka halittar idanuwan ta suke.
"Finally". Fa'din Naseer.
Sunkuyar da kai Mufeeda ta yi, haka kawai ta ke jin wani matsanaicin kunya kamar ta nitse. Wai yau ita ce daga ita sai na miji a 'daki. Sai abun ya mata wani iriii.
Bata ankara ba ta ji hannun Naseer dafe da kan ta ya na kwararo addu'a.
_*Allahummma inni as'aluka khaira ha, wa khaira ma fiha, wa khaira ma jabaltaha. Wa'aouzu bika min sharri ha, wa sharri ma fiha, wa sharri ma jabaltaha*_
Ya na kaiwa nan ya cigaba da kwararo masu addu'ar zaman lafiya da kuma soyayya mai 'daurewa bi sa tafarkin Allah da manzon sa da kuma zuri'a 'dayyi ba. Nan ya shiga jeho mata tambayoyi akan addini.
"Ya ake wankan janaba?". Naseer ya fa'da.
Shuru Mufeeda ta yi na tsawon mintu uku. Wani kunya ne ya lullu'be ta. Ta ma rasa ta ina zata fara.
Har Naseer ya bu'de ba ki zai yi magana, sai yaji saukar muryan ta. Ka na jin muryan kasan ba 'karamin tattaro kwarin guiwa akai ba.
"Wankan janaba ya kasu kashi biyu ne, akwai siffatu kamal, akwai kuma ijzah. Farko mutum zai 'daura niyya, sai ya samu tsaftataccan ruwan sa a mazubi. Idan siffatu kamal zai yi, sai ya fara da bismillah tare da wanke al'auran shi zuwa cinyoyin shi. Ka na ya daura alwala kamar yadda yake alwalar sallah, amma ba zai wanke 'kafafu ba. Wasu malamai sun ce, bai halasta kai tsaye mutum ya antayawa kan sa ruwa ba, saboda lafiyar jikin sa. Ya karkata bokitin ya 'dibi ruwa ruwa har say uku ya cu'da kansa dashi, saboda 'kofifin gashi duk a bu'de suke. Bayan mutum ya wanke al'aurar sa, sai ya wanke b'arin jikin sa na da ma, ka na ya wanke na hagu. A 'karshe sai ya 'kari she alwalar sa. Ma'ana ya wanke 'kafafuwan sa da bai wanke ba. Wasu malamai da dama sun ce, mutum zai iya sallah da wannan wanka ba tare da ya sake alwala ba. Sai kuma siffa ta biyu, wato siffatu ijzah. Shikuma wannan wanka, bayan mutum ya 'daura niyya tare da basmala, zai wanke al'auran sa ne zuwa cinyoyin sa. Ida shower mutum gare sa, zai iya bu'dewa ya cuccu'da jikin sa, idan ma tafi ne, mutum zai iya fa'dawa yai wankan sa. Ku ma duka Wanka iri 'daya ne. Niyya ce kawai ke banban ta. Ma'ana wankan Haila, wankan Janaba da Ku ma na bi'ki. Wallahu a'alam". Mufeeda ta fa'da tare da sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Jijjiga kai Naseer yai alamar ya gamsu. Nan ya cigaba da danno mata wasu tambayoyin. Irin su yadda ake alwala, farillar alwala, farillan sallah, sunno nin ta da sauran su.
Mufeeda kuwa ba laifi, ta na ta bashi amso shi yadda ya ka mata. Kuka yaji da'din hakan sosai. Hakan ne ya ke nuna matar tasa ba jahila ba ce. Sai da ya ga ta soma hamma, ka na ya 'dauko farantin kazar nan ya aje a gaban ta tare da fa'din,
"Bismillah, nasan yunwa ki ke ji".
No'kewa Mufeeda ta yi tare da fad'in,
"Yallab'ai wallahi bazan iya cin komai ba, idan dare ya shura haka ban iya sakawa komai ciki na saboda ya na saka ni ciwon ciki".
Jinjina kan shi yai tare da kallon agogon bango dake manne a d'akin.
Zaro idanu yai da ya ga lokaci. Karfe 2:15am. Fresh milk 'din ya tsiyaya a cup tare da mi'ka mata ya ce,
"Dan Allah karb'i, ko wannan ki shanye. Ban so ki kwana babu komai a cikin ki".
Ba musu ta 'karba ta shanye. Zai 'kara tsiyayawa ta narke fuska tare da fa'din
"Pleaseeee yallab'ai, wallahi ya ishe ni, bacci na ke ji".
Aje cup 'din ya yi tare da aje parantin a gyefe ya mi'ke tare da mi'kar da ita ta na no'kewa. Hijjab 'din ya soma kiciniyar cire mata, ita kuma ta ri'ke gaam.
"Ban son musu faa, ka da KI kasance cikin jahilan matan da suke wa mazajan su 'kudundune. Ki saki jikin ki. Beside, ni babu abunda zan miki".
Ba ta 'kara masa gardama ba. Shikuma ya cire hijjab 'din tare da 'daura ta kan gado ya cire mata safar 'kafar ta. Ka na shima ya cire jallabiyar da ke jikin shi, ya kashe wutan 'dakin tare da hawa gadon ya jawo ta tare da lullu'ba masu bargo.
Gaban Mufeeda sai dukan uku² ya ke yi.
A kunne ya ra'da mata,
"Malama ki saki jikin ki, na ce babu abunda zan miki. Idan kuma ki ka cigaba, hmm".
Tun tana 'dari² har bacci mai dad'i yai awon gaba da ita.
💤💤💤
Kasancewar ba su kwanta da wuri ba, sai da su ka makara, domin 'karfe bakwai Naseer ya farka. Shi ya soma tashi ya shiga ban 'daki. A gurguje ya 'dauro alwala ya fito ya saka jallabiyar sa ya ta da sallah. Sai da ya idar sannan ya matso Kusa da gadon ya soma jaan dogayan yatsun 'kafan ta.
Cikin bacci Mufeeda ta ji ana jan yatsun ta. A hankali ta soma bu'de idanun ta har ta bu'de su duka akan shi.
"Sleeping beauty, ki tashi mun makara. Karfe bakwai har da minti sha biyar.
Da sauri ta waro manyan idanuwan ta tare da saukowa daga kan gadon jikin ta duk a mace saboda har yanzu bacci bai bar idanun ta ba.
"Yi a hankali dai ka da Ki fa'di. Bari ma in 'dauke ki na kai ki bayin kawai".
Mufeeda ba ta San sanda ta kwasa da gudu ta shige bayin ba.
Dariya ta kama shi. Ya bu'de murya ya na fa'din,
"Yarinya za ai lokacin da, da kan ki za ko ri'ke ni akan in 'dauke ki.
Sai da tai wanka ka ba ta 'dauro alwala. Towel ta 'dauro tare da lekowa ta ga ko ya da 'dakin, aikuwa tai sa'a bai 'dakin.
Sai dai ta na zuwa tsakiyar 'dakin shikuma ya na shigowa hannun shi 'dauke da farantin kazar jiya wai tururi ta ke, kitchen ya je ya 'dumamo ta tare da soyayyan plantain da kwai. Sai ruwan Lipton ba madara, amma irin Lipton 'din nan ne masu kamshin da kuma kayan kamshi.
Wani irin juyawa tai zata koma bayi, sai jin saukar muryan shi ta yi ya na fa'din,
"Umarni ne na baki, ka da 'kafarki tai stepping forward. Ki dawo ki zauna ki abunda za ki yi".
Jikin ta a mace, ta dawo ta isa gaban wardrobe tare da bu'dewa ta 'dauko wani uban su less kalar purple da ratsin ba'ki, kayan sun ji stone. Doguwar riga ce 'dinkin abuja bubu.
Rasa yadda za tai ta saka kayan tayi, domin gaba 'daya idanun sa na yawo a kan ta.
Gashi inner ta ke so ta saka kamin ta saka kayan.
Hakan da ya ga ni ne ya sa yai murmushi tare da fita daga 'dakin.
Aikuwa cikin sauri² ta saka brezia da pant da underwear, ka na ta saka doguwar rigar less 'din da ya amshi jikin ta, farar fatan ta kuma ya 'kara fito da aihanin kyawun da kayan suka mata.
Hijab ta saka ta tada sallah. Bayan ta idar, sai ta 'karisa gaban madubi ta shafa mai tare da dandatsa kwalliya ta kuma feshe jikin ta da turare kala². Ka na tai 'dauri mai kyau. Ita kan ta said 'kara 'karewa kan ta kallo ta ke yi, a jikin mirror.
Dai² lokacin da take 'karewa kan ta kallo, Naseer ya dawo 'dakin.
Galala ya tsaya ya na kallon ta, ba 'karamin kyau Mufeeda ta masa ba. Bai ki ya kwana ya na kallon ta ba.
"Ya dai? Kar fa ka cinye ni". Fa'din Mufeeda ta ra da 'dage masa gira.
"Ai dama zan iya cinye kin da ba huta. Don har ga Allah ban son ana kalle min ke. Ina kishin ki da 'kaunar ki Habibty".
"Ni ma ina tsananin 'kaunar ka Habibi Da'iman".
Wayar sa ya 'dauko ya shiga 'daukar ta hotuna, ita kuma ta na masa style kala². Daga baya suka ko ma yin selfie. Sun yi matu'kar kyau.
"Yanzu dai zauna in ciyar da ke, ba san sannan cikin ya na kukan yunwa". Naseer ya fa'di hakan tare da matso da tray 'din bayan ya shimfi'da 'katuwar darduma.
Haka su kai ta ciyar da kan su cike da shau'ki da 'kaunar junar su.
Bayan sun gama su ka tattare kayan su ka kai kitchen.
Da kyar Naseer ya amince mata akan zata 'dan kakka'be 'dakin. Da ya na ce, akan bacci za ta koma ta cigaba, don ya ga baccin a idanun ta. Nacewar da ta yi ne ya sa ya bar ta, shi ma tare su kai ko mai tare da saka turaran wutar da Mommah ta saka aka yo mata shi a Maiduguri da Sudan.
Ai kaman jira ake su gama gyaran, sai ga ba'ki 'dangin Mommah da manya² robonin zuba ruwa cike da cincin, alkaki, dublan da nakiya.
Har ga Allah Mommah har cikin zuciyar ta ta ke jin Mufeeda 'kamar 'diyar ta.
*MATAR SAYYADI*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da