Showing 45001 words to 48000 words out of 115393 words

Chapter 16 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22905

nuna ma ta.
A gyefe guda kuma ga kusan mummu'ke da *Mai zogale* ta ke yi ma ta, amma da ya ke ita mace ce mai hakuri, sai ta nuna halin ko in kula ko, wannan dalilin ne ya sa ta ke ganin kamar Fatima ba ta da wayau.
Marwanatu ta bai wa Mufeeda sati biyu, amma kan su 'daya. Mufeeda na da wani irin kyawu da ta jawo mata farin jini wajan jama'a, kullum daga ma'kota sai anzo an 'dauke ta, sai dai idan ta yi kukan yunwa a kawo ta tasha nono. Wannan abu ba 'karamin ba'kan tawa *MAI ZOGALE* rai ya ke ba. Gashi Ahmadu ya na 'ko'kari wajan sayawa 'yar shi da kuma matar shi sutura mai kyau.
Haka rayuwa ta cigaba, yau da da'di, gobe babu da'di har marwanatu da Mufeeda su kai shekara 3-3, sun yi girma abun su, kyawun Mufeeda ya da'da fitowa, ga kyau ga fari ga dogon gashi. Tun su ba 'kanana *MAI ZOGALE* ta koyawa Marwanatu 'kiyayyar Mufeeda a ran ta. Da Mufeeda ta fita tsakar gida Marwa zata kwa'de ta, gashi jikin su ma ba iri 'daya ba ne. Marwa irin masu jiki 'din nan ne. Ita ma fara ce, amma idan ta tsaya Kusa da Mufeeda za ka ga ta koma 'yar duna blaky.



*RANAR DA TSAUTSAYIN YA AFKA*

Wata ranar juma'a da daddare 'yan uwan Fatima su ka zo gidan ta abunda bai ta'ba faruwa BA tsawon shekara takwas da auran ta. Ba'karamin jin da'di Fatima tai BA har ta rasa in da za ta tsoma kan ta, duk da anyi anyi su shiga 'daki sun 'ki sun ce su a nan tsakar gidan ZASU tsaya. Jiki NA rawa Fatima ta 'dauko tabarma ta shimfi'da masu, nan ma suka 'ki zama. Ita kuwa *MAI ZOGALE* sai dariya ta ke yi tare da jefa habaici wai Fatima ta yi abun kunya shiyasa dangi suka juya mata baya. Su ko dangin Fatima ko kallon *MAI ZOGALE* BA su yi ba, sai ma kallon Fatima da au kai su ka ce mata idan taga dama ta shirya za su je can Dutsi an ce wan mahaifin ta ba lafiya kuma ya ce dole a zo da ita ya ka son ganin ta. Sannan suka kora mata garga'din ka da ta saki tazo da Mufeeda, don ba su bu'katar zuri'ar boka a cikin su. Su na gama fa'din haka su kai ficewar su. Sosai jikin Fatima yai sanyi, wani guefan zuciyar ta kuma da'di ta ke ji yau 'yan uwan tq sun kulata.
Kasancewar mal Ahmadu ba ya nan ya na wajan aiki, ya na kuwa dawowa ta shaida masa yadda su Kai da 'yan uwanta. Aikuwa ya ce atafau babu in da zata. Tai lallashin amma ya'ki. Aikuwa a daran sun yi tashin hankalin da tun da su kai aure basu ta'ba ba. Daga baya ne mal Ahmadu ya ha'kura ya ce ta shirya gobe sai ta je. A nan ne kuma ta ke shaida masa ba da Mufeeda za ta ba. Bai ce mata 'kala a kam haka ba, duk da a can 'kasan zuciyar shi bai ji fa'din hakan ba.
Aikuwa tafiya ce da Fatima ta yi ba ta dawo ba. Domin sa'ko ne ya same shi su Fatima sun yi hatsari akan hanyan su nazuwa dutsi. Aikuwa Ahmadu har 'karamin hauka sai da ya yi. Gashi kullum Mufeeda kukan ta ke masa akan a kai ta wajan mahaifiyar ta.
Tun daga wannan lokacin kulawar Mufeeda ta koma wajan *MAI ZOGALE* har sai mal Ahmadu ya dawo daga aiki. Mufeeda duk ta rame tai ba'kin sabida azaba da take ci wajan marwanatu da *MAI ZOGALE*. Kullum idan baban zai fita zuwa gareji haka za tai ta kuka, ya nai wucewa kuwa *MAI ZOGALE* ta jibga iya son ran ta sannan ta ri'ke mata kunne akan duk ranar da ta 'kara kuka idan baban ta zai fita sai ta yan ka ta. Tun daga ranar kuwa MufMufeeda ta dai na kuka. Mal Ahmadu kuwa ya ji da'di don a tunanin shi *MAI ZOGALE* na kula mata da 'diyar sa ne.
Lokacin da Mufeeda ta shiga shekara bakwai ta na primary 1 ita da Marwanatu a wata private school mai sau'ki da mal Ahmadu ya maka su, a makarantar ne kuma suka ha'du da aminiyar ta *MASHKURA* wacce baza ta wuce sa'ar ta ba, ko mai tare su ke yi, ku ma SAI akai sa'a unguwar su ma 'daya, layi 'daya tsakanin su kuma islamiyyar su daya *TASHIHIL IMAN* Dake nan badarawa. Idan ka nai mi Mufeeda ba ka gan ta ba, to due ba gidan su Marwanatu, haka ma idan ka nai mi Marwanatu ba ka gan tq ba, to duba ta gidan su Mufeeda.
Haka suka taso, a duniya babu wacce Mawanatu ta tsana ta bu'de idanu ta ga ni sama da Mufeeda, babu abunda ke 'kona mata rai kamar kyawun da Allah ya bar ta. Ko wani irin kaya Mufeeda ta saka sai sun kar'bi jikin ta.
Haka rayiwa ta cigaba, Mufeeda na 'kara girmadon yanzu shekarunta sha daya, arzi'kin mal Ahmadu ya na da'da bun'kasa. Don ya sayi wani fili da ke Kusa da gidan sa ya ha'de ya na son ya ha'de da gidan sa.
*MAI ZOGALE* kuwa idan ran ta yai dubu to ya 'baci ta so ace mijin ta ke wannan samun. A hankali tai ta tura wa mijin ta mummunar a'kidar hassadar 'dan uwan sa a cikin zuciyar sa. Aikuwa KALLAH ya hau kan wannan turba ya zauna daram dam dam (🤣🤣🤣🤣 har na tuno da former vice President🤣)

*RANAR TASHIN HANKALI*
mal Ahmadu ya na gareji har akai kiran magriba ya na gyaran wata mota. Da ya ji kiran magariba sai yai hanzarin mi'kewa ya je ya wanke jikin shi tare da saka kayan sa masu kyawu tare da 'dauro alwala ya nufi masallaci. Bai fito ba kasancewar har yau ya na nai man ilimi sai ya tsaya 'daukar karatun da ya ji ana gabatarwa a masallacin. Ba su su ka kammala ba sai 8:30 su kai isha'i kana ya fito daga masallaci ya nufi wajan mashin 'din shi boxer sabuwa fil don a can mando ya ke aiki shiyasa ya sai abun hawa saboda sau'kin tafiya.
Ashe tsautsayi ne ya sa yai dare a can wajan. Aikuwa tawagar 'yan kidnapping su ka fito da irin mashinan shi hannun su ri'ke da bindugu, hasken mashina ya ga ni can ne sa da shi sun kusa hamsin, aikuwa ya buga nashin mashin 'din kasancewar ya ji labarin 'yan kidnapper 'din haka suke yi. Aikuwa a guje ya mur'da mashin da uban gudu, ashe suma 'yan kidnappers 'din ma artabu su ke yi 'yan sada.
Shikuwa mal Ahmadu dakyar ya sa mu ya sha. Ashe kuwa wani 'dan sanda ya na biye da shi daga baya. Ya ga kuma in da ya shiga.
Shikuwa Mal Ahamadu ya na shiga gida hankali a tashe ya fa'da 'daki ya na mai godewa ubangiji saboda ku'butar da shi da ya yi.
Aikuwa cikin dare sai ga motan 'yan San da har uku sun shigo gidan mal Ahmadu da manya manyan bindigu.
Hankali ta she duk suka fito, aikuwa wannan 'dan sandan ya na ido biyu da mal Ahmadu ya nuns shi, aikuwa aka zagaye shi tare da saka masa ankwa aka fita da shi.
Mufeeda ta rushe da uban kuka har ta na suma.
Daga baya KALLAH ya bi su a baya sai bayan asubha ya dawo. Large 11am 'yan sandan nan suka sake zagaye gidan, wasu suka shiga, aikuwa sai ga bindigu guda biyar manya manya. Suka tasa kyeyar KALLAH su ka tafi dashi. Aikuwa ma'kota suka firfito suna jimami, wasu kuwa har sun fara baza maganan cewa an ka malAhmadu ashe dama 'dan kidnapper ne shi.
Mufeeda kamar zata haukace, duk da alokacin ma ba wai tq girma sosai ba ne, shekarunta sha 'daya. Sai bayan la'asar KALLAH yadawo ya ke shedawa jama'a anti wa 'dan uwan shi sharri cewan shi 'dan kidnapper ne kuma sun ce kashe shi ZASU yi, don gobe ma za'a mi'ka su kotu.
Washa gari aka Kai su kotu, ta ke aka yanke masu hukunci kisa ta hanyar rataya har da mal Ahmadu sakamakon ka mashi da akai da bindigu a gidan sa da kuma shaidan karya da 'dan uwan shi KALLAH ya ga da. Domin cewa yai shi kan shi ya da'de ya na zargin 'dan uwan na sa don wata rana sai tsakiyar dare ya ke dawo wa gida, kuma sai yai ta shigo wa da manya manyan gana must go na 'ku'dade da maka mai, tsoro ya ke ji ya nuna masa ya San abunda ya ke yi shi ma ya kashe shi don ka da asirin shi ya tonu.
Akai kuwa akai prison da su akan sati mai zuwa zaka rataye su shi da sauran mutun hu'dun da aka kama.
KALLAH ya dawo unguwa yai ta rusa kuka akan cewa anyi wa 'dan uwan shi sharri gashi za'a kashe shi sati mai zuwa za'a. Mutane da yawa sun ji tausayin shi, ban da wani ma'kocin sa guda 'daya da yaje kotun lokacin da abun ya faru, kuma yaji shaidar da KALLAH ya ba da. KALLAH ya ba shi tsoro sosai, shiyasa yaja ba'kin shi yai shuru bai fa'dawa kowa ba, saboda ya na tsoran mai KALLAH zai iya masa.
Sati mai zuwa kuwa KALLAH yazo ya ka ta rusa kuka ya na fa'dawa mutane an kashe dan uwan sa.
Mufeeda kuwa tun da ta ji mahaifin ta an kashe shi ta sume. Mahaifiyar Mashkura ne tazo ta na lallashin ta tare da ba ta baki. Duk ta susuce ta yi ba'kin. Da ta 'kalli kofar dakin mahaifin na ta SAI ta rushe da kuka.

Ru'kon Mufeeda ya koma hannun *MAI ZOGALE*, sabuwar nau'in azaba iri iri ta ke sha a hannun Marwa da Mai zogale.
*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE 24_*

Ba'kar azaba Mufeeda ta ke sha a hannun *MAI ZOGALE* da Marwanatu. Wanki da gugan kayan su duk Mufeeda ke yin sa har da kayan *KALLAH*. Ga girki da aikace aikacen gida da kullum ita take yin sa. Makarantar da mal Ahmadu ya saka su ta private cire ta akai aka mai da ta na gomnati.
Mashkura ce ke 'dan zuwa ta na taimaka mata, duk da wata rana korar kare *MAI ZOGALE* ke mata. Ga abincin ma sau biyu kawai suke ba ta a rana, duk da kuwa ita ke girkin gidan.

*_BAYAN SHEKARA BIYAR DA RASUWAR IYAYAN MUFEEDA_*

Shekarun Mufeeda goma sha bakwai, kyawun ta ya da'da masifar fitowa. Allah ya yi mata 'kira, Mufeeda irin matan nan ne da ake wa la'kabi da figure 8. Fara ce taaas mai matsakaiciyar tsawo, tq na da yalwar gashin gira da zarara gashin idanu. Babu abunda yafi 'daukar hankali a jikin Mufeeda irin idanuwan ta. Wasu idanuwa gare ta farare 'kar 'kar, yankan su mai ban sha'awa. Idan ta 'dago ta kalle ka, za kai tunanin iyayi ne da ita, amma hakan halittan ta suke. Don **KALLAH* ya sha falla mata mari wai ta na hararar shi.

Tafe suke ita da Mashkura 'kawar ta ri'ke da hannun juna su na 'dan hirar su ta 'kawaye. Mashkura ta kalli Mufeeda ta ce,
"Feedy mu 'dan 'karasa wajan Zabba'u mana mu 'dan ci awara da kabeji".
Harara Mufeeda ta maka mata tare da fa'din,
"Wallahi *KURA* baki da hali. Haka ake yi? Kullum muje mu cinyewa yarinya jari bayan kin San ba kar'bar ku'din mu take ba. Ko in ce ba ba ta ku'din ki ke ba sai dai kawai da ta tsame ki saka hannu ki kwasa ki saka a plate ha'de da barba'da yaji da kabeji. Ni wallahi kunya ma kike ba ni ki ta cin abinci a kan titi".
"Ba *KURA* ba *DAMUSA*. Ai kayan Allah na annabi ne, kin ta'ba jin ta yi 'korafi akan haka ne? Mtsww kin cika 'korafi wallahi feedy". Fa'din Mashkura tare da hararar Mufeey.
"Matsala ta da ke kenan *KURA*. Ba ki ta'ba gane mutun ya na miki kawaici wallahi". Fa'din Mufeeda.
"Ke ce dai ba ki San halin Zabba'u ba, ba ta da damuwa Sam wallahi. Abun hannun ta bai rufe mata idanu ba. Ba ta da rowa. Amma tunda kin yi 'korafi, mu tafi gida kawai". Fa'din *KURA*.
"Aikuwa da yafi". Fa'din Mufeeda.
Birki Mashkura ta ja tare da fa'din,
"Feedy ga mutumin fa, mu canza hanya dan Allah. Wallahi ba na son wannan sa'in San da kuke yi".
Saurin juyawa Mufeeda ta yi ta kalli saitin da ya ke tahowa, dogon tsaki ta ka tare da fa'din,
"Banza kawai, wai shinan 'dan masu ku'di, sai wani fa'di ya ke yi don wannan 'dan kyawun da ya ke da shi".
Mashkura ta kalle ta ta ce,
"Alhamdulillah tunda ke ma dai ki na ganin kyawun. Don ba 'karya wallahi gayan nan ya ha'du, ban San mai ya sa jinin ku bai ha'du ba".
Yamutsa fuska Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Ni Sam bai min ba, jin kan shi na ba ni haushi, shi ba uban kowa ba, idan giyar ku'di ne ke ibar shi, to kafin shi an yi 'karuna". Ta 'karasa maganar tare da Jan tsaki ta ka hannun *KURA* su ka so ma tafiya. Dai dai shi kuma ya zo Kusa da su, har ya gitta ya dawo baya ya sha gaban su.
Cike da tsiwa Mufeeda ta ce,
"Dan Allah Malam jaye ka bawa mutane waje, ka wani zo ka tsayawa mutane a hanya se'ke'ke kaman wani service".
Kafin yai magana karaf Mashkura tai saurin cewa,
"Dan Allah yaya Naseer ka yi ha'kuri kada ka tanka ta".
Wani murmushi ya sa ki da ya 'kara futar da tsantsan kyawun shi. Kallon Mufeeda ya yi from head to toes. Kamar zai yi magana sai kuma ya 'kara sakin wannan murmushin da haka nan ya ke saka zuciyar Mufeeda na bugawa da sauri da sauri.
"Mummuna kawai". Abunda Naseer ya da'da ke nan a hankali. Domin le'ban shi ne kawai yq motsa, idan ba ma kallon shi ka ke ba, bazaka ta'ba sanin ya yi magana ba. Kuma ya na fa'din hakan yai gaba.
Zaro idanu Mufeeda ta yi, sai kuma ta bi bayan shi da kallon ka na ta mai da kallon ta izuwa ga Mashkura ta nu na bayan Naseer da hannun ta ta ce,
" *KURA* kin ji abunda ya ce?" Sai ta nuna kan ta tare da 'kara fa'din,
"Wai ni zai kalla ya ce wa mummuna".
Murmushi Mashkura ta yi tare da fa'din,
"Dan Allah share shi, ai ko makawo ya shafa fuskan ki ya San ke 'din shugaban kyawawan mata ce. Ya fa'di hakan ne kawai don ya ga ran ki ya 'baci. So please forget about him".
Kwafa Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Lallai ma! Wai ma ya akai wancan yaron ya rai na ni ne?".
"Dan Allah mu ki share shi. Muje gida, kin San fa anjima habibin ki zai zo, ka da ki bari wannan yq 'bata miki mud 'din ki". Fa'din Mashkura.
Wani sanyayyiyar murmushi Mufeedan ta saki tare da fa'din,
"Har kin sanyayamin zuciya. Muje gida na kammala ayyuka na da sauri. 'Dazu Marwa ta aje min wanki na mata. Mu yi sauri ma ka da ta dawo ta taras ban ma ta ba. Kin San idan haka ta faru, ko shugaban 'kasa ne zai zo waje na anjima ban isa na Fifa ba".
"Kwarai ni ba San haka, mu hanzar ta muje gida". Mashkura ta fa'da tare da ka ma hannun ta su ka so ma sauri.


*PLEASE MANAGE, ZAMU HA'DU GOBE*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )

😡😡😡😡😡
*BA RI KUJI! NI FA BA WAHALALLIYA BA CE BA DA ZAN RI'KA CIRE LOKACI A CIKIN LOKUTA NA MASU AMFANI IN ZAUNA INA MAKU TYPING BA COMMENT BA. MUST ESPECIALLY GROUP 'DIN _NI DA SHI ABU 'DAYA NE_. SAURAN GROUPS 'DIN DA NAKE TURAWA MA WALLAHI SUN FI KU YIN COMMENT. ACE MEMBERS SUN HAURA 'DARI DA, AMMA MUTUN UKU ZUWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login