Showing 54001 words to 57000 words out of 115393 words
ta kashe wayar.
"Ohh Allah ka sa ta amince". Naseer ya fa'da tare da wani wuntsulowa daga kan kujera kamar wani 'karamin yaro.
********************
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka.
Biology B2
Physics C2
Civic Edu C4
Mathematics C2
English B2
Chemistry A1
Economic A1
Islamic studies B2. Kai Allah nagode maka". Mufeeda ta fa'da cike da farin ciki.
" 'Kawa ta ya NI da addu'a, Allah ya sa ni cikin dan shin ku". Mashkura ta fa'da a sanyaye.
Dafata Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Da izinin ubangiji mai rahama za ki fito da flying colour".
"Allah ya sa". Fa'din Mashkura a sanyaye.
Runtse idanuwa Mashkura ta yi dai dai lokacin da ake printing result 'din ta. Mufeeda ce ta 'karba.
"Bu'de idanun ki *KURA* ki ga abun alkhairi".
Saurin bu'de idanu Mashkura ta yi tare da amsar papern hannun Mufeeda.
Wani tsalle ta buga tare da rungume Mufeedan ita ma ta na fa'din,
"Alhamdulillah, Allah na gode maka. Duk da dai ba su kai na ki kyawu ba, amma wallahi na ji da'di bazan sake zaman zana wani neco ba, sai dai mu jira weac".
"Sai dai ku jira dai. Ni ina na ga ku'din biyan weac. Wannan ma dan dai gomnati ne tai ma na taimako ta biya mana".
"Ka da KI cire hope, in sha Allah sai ki ga Allah ya turo mai bi ya maki". Fa'din *KURA*.
"To Allah ya biye bakin ki". Fa'din Mufeeda.
Mashkura ce ta bi ya masu ku'din printing 'din ka na suka fito daga shagon.
"Mashkura mu yi sauri ka da nai wani laifin wajan Inna, gashi rana ta yi, karfe sha biyu fa da minti shida yanzu. Dan Allah mu yi sauri na je na 'daura na rana". Fa'din Mufeeda tare da jawo hannun Mashkuran su ka soma sauri.
Dogon tsaki Mashkura ta na tare da fa'din,
"Allah ya wadaran halin ki feedy, a CE mutum ba zai tashi ya kwatarwa kan shi 'yancin kan shi ba. To wallahi ki na tare da wahala".
"Eh na ji. Ke ba za ki ga ne ba ne. Ni dai mu yi sauri ba dogon surutu na ke so muja ba da zai sa mu yi tsaikon isa gida da wuri na 'daura girki".
"Ke dai ki ka sa ni". Mashkura ta fa'da.
A hanya su ka rabu, Mufeeda tai Fulani road, ita kuma *KURA* ta tsaya a Layin sarkin margi.
*________________*
"Almura, sai yanzu ki ka ga damar dawowa daga gantalin? Tamba'da'd'diya, watsatstsa". *MAI ZOGALE* sake gindin rijiya ta fa'da ta na jehowa Mufeeda harara.
"Ki yi ha'kuri Inna, wallahi layi mu ka sa mu a shagon". Fa'din Mufeeda.
Wata uwar hararar *MAI ZOGALE* ta kuma jifan ta da shi tare da fa'din,
"Iskancin ma har layi ake masa kenan?".
Shuru Mufeeda ta yi, kan ta a 'kasa.
"Ai sai kizo ki 'daura mana girkin rana. Kuma ki sa ni, baza ki 'daura min sanwa da najasa a jikin ki ba, ki je ki wanke najasar da wani 'katon banza ya zuba miki tukun kamin ki ta'ba min tukunyar girki. Tunkiya kawai".
Wani tu'ku'kin ba'kin ciki ya mamaye zuciyar Mufeeda, amma sai ta daure ta hana hawayan ta kwaranya.
Wankan ta yi kamar yadda *MAI ZOGALE* ta bu'kata. Sannan ta canzo kayan da ta ke sakawa idan za ta yi girki. Gawayi ta fara hurawa sannan ta 'daura tukunya ta saka ruwan zafi kamin ta gama jajjagen kayan miya.
Karfe 'daya ta kammala komai. Kasancewar taliya ce 'yar murji ta dafa.
Kamar yadda ba ta samu Karin safiya ba, haka wannan taliya Yar murji da ta ji manja da kayan miya ya zama haramiyar ta. Don ko su'din tukunya *MAI ZOGALE* ba ta bar mata ba. Da ta gama kwashe taliyar, sai ta ce mata ta antayawa tukunyar ruwa.
Sosai taliyar nan ya burge Mufeeda, dama gashi ta kwaso yunwa da zafin rana. Kasancewar ba ta karya ba. Jiya dai ta samu ta ci ragowar shinkafa da waken da ta dafa. *MAI ZOGALE* ta mance ba ta kwashe ba ta kankare 'kanzo ba kamar yadda ta saba kullum sannan ta antayawa tukunyar ruwa.
'Dakin ta ta shiga tare da 'dauko tsohuwar jakar ta da take ajiyar ku'di ta 'dauko naira 'dari ta fita bakin titi ta sayo garin rogon talatin gyadar ashirin da sugar ashirin ta dawo gida ta ha'da tasha tai gyatsa tare da kishingi'da. Nan da nan kuwa bacci ya kwashe ta. Daman fashin sallah ta ke yi.
*BAYAN SATI 'DAYA*
" *KURA*, Musa fa ya dai na zuwa gidan mu. Tun ranar da ya zo bayan dawowar su daga Cameron, bai sa ke zuwa ba, wallahi hankali na ya tashi, ban san ko lafiya ba. Ni dai na san haka nan lafiya Musa ba zai 'ki zuwa gidan mu ba har tsawon kwana bakwai".
"To ke kin ne me shi?" Fa'din Mashkura.
" *KURA* ta ina zan fara nai man sa?". Fa'din Mufeeda kwallah ya taru a idanun ta.
"Ga waya ta, saka numbern shi ki Kira shi sai ki ji dalilin, ni na san ya na can shi ma ya na kewar ki". *KURA* ta fa'da tare da murmurshi a fuskan ta, ta na mi'ka mata wayar.
Amsa Mufeeda ta yi tare da dannna numbobin wayar Musa. Aikuwa bugu biyu ya 'daga tare da fa'din,
"Hello, wa ke magana?".
Jiki a sanyaye Mufeeda ta ce,
"Assalamu alaikum".
Sai da yai jiim kasancewar ko cikin mafarki ya ji muryan ta sai ya ga ne. Sannan ya ce,
"Amin wa'alaikissalam, wacece ke magana?".
Gaban Mufeeda ya buga daam, domin ta sha kiran sa da numbobi da dama, kuma ta na magana ya ke ga ne muryan ta. To me yasa yanzu zai yi pretending kamar bai ga ne ita ce 'din ba.
"Idan ba za ki fa'di ko wacece ke ba zan kashe waya ta. Ban san rainin wayau". Musa ya katsewa Mufeeda zancan zucin ta. Kamar za ta yanke kiran, sai kuma ta ce bari dai ta tabbatar da abunda ke ran ta. Sai ta ce,
"Ni ce?".
"Ke ce wa?". Ya sake antayo mata tambayar rainin wayau.
"Mufeeda ce". Ta fa'da zuciyar ta na lugude.
"To na ji. Fa'di cutar ki". Musa ya fa'di hakan ya na wani ya mutsa fuska. Amma deep down ji ya ke zuciyar shi na ba'ki'k'kirin.
Shuru Mufeeda ta yi. Ta kasa cewa komai har tsawon second 15.
'Din 'din 'din ta ji ya yanke wayar.
Ciro wayar ta yi daga kunnan ta tana kallon screen 'din wayar kamar za ta ga Musa ta cikin wayar hawayan ba'kin ciki na kwaranyowa daga idanun ta.
"Lafiya? Feedy mai ya ce maki". Mashkura ke tambayan ta tare da jijjigata.
"Ya dai na so na". Mufeeda ta ba ta amsa.
"Kamar ya ya dai na son ki?". Mashkura ta jeho mata tambaya tare da tsare ta da idanu.
"Ke wa yai wai in fa'di cuta ta?".
"Kamar ya ki fa'di cutar ki? Asibiti ki ka je? Shi likita ne? Wannan ai salon rainin hankali ne da iskanci". Fa'din Mashkura rai a 'bace.
"Hmm" shine abunda Mufeeda ta fa'da kawai tare da share hawayan ta.
"Ki kwantar da hankalin ki Mufeey kin ji. Wata 'kilan wani abun ki ka masa ke ba ki sa ni ba. Amma in sha Allah zai sauko. Ni na san zai nai me ki".
Shuru Mufeedan ta yi, cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke,
"Allah ka sa ba rabamu akai ba".
Mashkura kuwa sai lallashin ta ta ke yi tare da kwantar mata da hankali. Dama gidan su Mashkuran ta je, kasancewar *MAI ZOGALE* ta ce unguwar Mu'azu can wajan 'kanwar ta. Mashkura kuma ta tafi yawon ta. Shine ta rufo gidan ta zo wajan Mashkura.
"Mashkura ba ri na je gida ka da su dawo su taras ba na nan".
"Ta shi muje na raka ki. Kin ga idan ma basu dawo ba, sai na taya ki hira da 'daura girkin dare. Don ba na son ki zauna ki na tunani".
Mi'kewa Mufeedan ta yi tare da sanya hijjab 'din ta. Mashkura ma ta saka na ta. 'Dakin mahaifiyar Mashkura su kai sallama tare da shiga.
"Ah Mufeeda har kin fito kenan?".
"Eh mama, zan koma gida na 'daura girki".
"Ki yi tq ha'kuri kin ji Mufeeda, ko mai yao farko zai yi karshe, in sha Allah nasara na tare da ke. Ke dai ki ri'ke Allah kin ji". Fa'din mahaifiyar Mashkura.
"In sha Allah mama. Nagode".
"Yauwa Allah ya taimaka". Fa'din mama.
"Mama zan raka ta, daganan zan 'dan zauna na tayata ayyukan gida". Fa'din Mashkura.
"To ba damuwa, sai kin dawo. Allah yai maku albarka".
Da "Ameen" su ka amsa tare da mi'kewa su kai waje.
A 'kofar gida Mashkura da Mufeeda su kai turus, sakamakon ganin Marwanatu ta ci uban kwalliya Musa na gyefan ta kamar zasu ha'diye junan su don soyayya.
Mashkura ta kalli Mufeeda, Mufeeda ma ta kalli Mashkura. Gaba 'dayan su suka zubawa Marwa da Musa idanu da tsantsar mamaki.
"Kallon uwar me ku ke mana haka". Fa'din Marwanatu.
"Ni wallahi idanuwan su ma tsoro ya ke ba ni". Fa'din Musa, amma a can cikin zuciyar shi sai ya ke ji kamar ya na wani abu da bai kamata ba.
"Masoyi, warware masu komai su dai na mamaki". Mashkura ta fa'da ta na wani karairaya.
Musa ya gyara tsayuwar sa tare da fa'din,
"Ka da ku ji wani mamaki, dama ni na da'de ina 'kaunar Marwanatu. Ban san yadda akai kwatsam na fara sonki ba". Ya nuna Mufeeda tare da cigaba,
"Yanzu hankali na ya juyo, na gane wacce na ke so da 'kauna. Da ma can ina ga asiri ki kai min. To yanzu idanuwa sun bu'de. Maganin da ki ka min ya bar aiki".
"Dalla rufe mana baki solo'biyo kawai. Mufeeda ta maka asiri ko kuwa wacce ke tsaye gyefan ka ce ta maka asiri. Kuma bu'de kunnuwan ka da kyau ka ji, wallahi sai ka yi mummunar nadama a rayuwar ka na rasa kyakkyawa kuma mai tarbiyya kamar Mufeeda". Fa'din Mashkura kamar za ta tsinkawa Musan mari. Don sao da ya na da baya ma. Don *KURA* irin masifaffun Mayan nan ne.
"Ke ki iya bakin ki wallahi, ni ba sa'ar uwar ki ba ce, yanzu sai in karya banza wallahi". Fa'din Marwa ta na wani gantsaro kirji.
*KURA* za tai magana, Mufeeda ta fizgi hannun ta su kai saurin shiga cikin gida.
Sai fizge fizge *KURAN* ta ke yi tare fa'din,
"Barni in je in ci kutumar bura uban ta wallahi. Ita 'karamar mushirika ce, shegiya tsinanniya mai suffar *JADU*". (🤣🤣 *JADU* fa na film din India mai su na *KOI MIL GAYA*🤣).
"Don rahamar ubangiji, Mashkura idan dai don ni kike matar mata da martani, ki bari don Allah. Ki bar ta da halin ta, dama Musa ba miji na bata ne, idan kuma miji na ne, sai ki ga aje a dawo 'din, ni ce matar sa, idan kuma dama cen Allah ya yi ita ce matar sa, to wallahi ko mutuwa zan iya yi akan haka. Ki bar rabo Mashkura. Ni dai kawai ki min addu'ar samun Wanda ya fishi".
"In sha Allah sai kin samu Wanda ya fishing sai million".
"Allah ya sa". Mufeeda ta fa'da. Amma deep down kuka take yi cikin zuciyar ta. Lokaci² takan share hawayan ba tare da ta bari *KURA* ta kula ba.
*BAYAN ISHA'I*
"Naji tamba'dar da ku ka yi wa Marwa ke da tsinanniyar kawar ki, to wallahi ahir din ku. Ku ma aure ne tsakanin Musa da Marwa kamar an yi shi an gama. Sai dai ki mutu. Yo ko tunda ya ga ni ki na 'yan biye² mazan ki, dole ko ya janye ya je ma wajan mutunci. Kuma wallahi duk ranar da na 'kara ganin 'kafafuwan 'Yar iskan 'kawar ki a gidan nan, sai na sabartaki. Ki tashi ki je ki ba ta ha'kuri a 'dakin ta ki dawo kuma nan ki same ni".
Da to Mufeeda ta amsa tare da barin 'dakin ta je 'dakin Mashkura.
Saurin tura kazar da ta ke ci bayan katifar ta ta yi. Sai kuma ta na dogon tsaki tare da fa'din,
"Shegiya kin ban tsoro, na ma za ci *MAI ZOGALE* ce. Uban mi ya kawo ki 'daki na?".
"Nazo ne na ba ki ha'kuri akan abunda ya faru ne 'dazu. Don girman Allah ki ui ha'kuri".
"Shegiya mai kan agwagwa. Na ji tashi fitar min a 'daki. Saura kuma in ji labari wajan *MAI ZOGALE* cewar kin ga ni ina cin kaza. Sa'ar da KI kai kenan ma, da yau irin dukan da zan miki Allah ne zai CeCe ki. To gar'din kaza ba zai bar ni ba. Ki je ma ha'du gobe".
Ficewa Mufeeda tai daga 'dakin ta na girgiza kai. Ita abun ma dariya ya ba ta. Mahaifiyar ka ka mata rowa, to uban waye ma ba za kai wa ba.
Komawa 'dakin *MAI ZOGALE* ta yi tare da fa'din,
"Inna ga ni na dawo".
"Yauwa to bu'de kunnan ki da kyau ki ji ni. Bikin Marwa na gaba towa. Dole ai bikin kece raini a unguwar nan. Saboda haka daga gobe, zan fara 'daura miki tallar dafaffiyar gya'da da ri'di mai sukari. Kuma da daddare ne za ki rika tallah kasancewar maza sun yi sayan irin abubuwan nan da daddare wajan 'yan mata. Kuma saura wajan tallar in ji labarin ba ki sa kin jikin ki da fuskan ki. Wallahi na lahira sai ya fiki jin da'di. Don na ga ba'kin ciki ki ke da cigaban Marwanatu a gidan nan".
*INA SON GANIN RUWAN COMMENTS IDAN KU NA SAN GA NI UPDATE GOBE*
*MATAR SAYYADEE CE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 30_*
Hankalin Mufeeda idan ya yi dubu duk sun tashi. Idan akwai abunda ta tsana a rayuwar ta to *TALLAH* ne. Don ta San mafiya yawan 'yan matan yanzu _A SANADIN TALLAH_ su ke lalacewa.
"Gaskiya idan aka mun haka ba'a min adalci ba". Mufeeda ta fa'da cikin zuciyar ta.
Kau! Kau!! Kauuu!!! *MAI ZOGALE* ta 'daura mata maruka hagu da dama a fuskan ta, sakamakon maganar zucin da ta yi da ya fito fill.
Mufeeda ta dafe kuncin ta da hannuwan ta biyu idanuwan ta na tsiyayar da hawaye.
"Dan uban da ya haifi uwar ki, har ni zan fa'di abu ki ce min ba ai miki adalci ba. Ke da adalcin kun ci uban ku. Kuma wallahi *TALLAH* kamar kin yi kin gama. 'Yar iskan yarinya". *MAI ZOGALE* ta fa'da ta na huci kamar za ta fashe.
"Ki yi ha'kuri Innah". Fa'din Mufeeda ta na hawaye.
"Ha'kuri? Na zuba shi rariya na bi shi da ruwa. wallahi ko wa ya tsaya miki, sai kin yi min *TALLAH*, na samu na sayawa Marwa 'yan abubuwan zamani na kwalliyar 'daki".
"To Inna, zan yi *TALLAR*".
"Ai dama wannan kam ya zama dole". Fa'din *MAI ZOGALE* ta na an taya mata harara.
"Ta shi fitar min a 'daki, kuma ki shirya, gobe za ki fara *TALLAH*".
Da "To" ta amsa tare da fita daga 'dakin tai 'dakin ta tare da zubewa a 'yar yaloluwar katifar ta ta na fashewa da kuka mai ta'ba zuciya.
"Allah ya ji'kan ku da rahama iyaye na. Tabbas Allah bai barin wani dan wani. Da kuna nan, nasan hakan bazai faru da ni ba. Wannan na cikin 'kaddara ta. Allah ka sa na ci wannan jarabawar. Ya Allah ka kare ni daga Sharron duk mai sharri. Allah ka kare ni daga Sharrin samarin zamani". Sosai ta ke kuka tare da kifa kan ta a kan gadon.
*WASHA GARI*
Da sassafe *MAI ZOGALE* ta fice a gidan. Bayan ta shiga 'dakin Mufeeda ta kankara mata warning akan ta fito tai ayyukan gida da kuma abun kari.
Bayan fitan ta Mufeeda ta tashi tai komai as usual. koko tai da 'kosai. Sai da ta kimtsa komai sannan tai wanka ta fice gidan aminiyar ta Mashkura.
Sallama tai, ka na ta danna kan ta cikin gidan.
Mama ta samu a tsakar gida ta na shanya.
"Maraba da Mufeeda". Fa'din Mama.
'Karasawa wajan ta Mufeeda ta yi ta re da fa'din,
"Ina kwana mama?". Ta fa'di hakan ne tare da jawo bokitin kayan da Mama ke shanya ta soma shanyawa.
"Lafiya 'kalau 'yar albarka, ai da kin bari ma na 'karasa". Fa'din Mama.
Murmushi kawai Mufeedan ta yi.
"Ga malalaciyar 'kawar ta ki can a 'daka sai sharar