Showing 96001 words to 99000 words out of 115393 words

Chapter 33 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22927

wani saurayin ne ya yaudare ki ya 'dirka miki ciki ya kuma gudu ya barki da wayyo Allah. To mai ya sa ba ki amfani da wannan abun na turawa ba, condami ya ke ko condo? Ke oho su suka san sunan shi dai".
Cike da mamaki Mufeeda ke kallon Inna Huwaila.
"Ke bar min wannan kallon ko in 'debe miki albarka. Ke da ki kai shege ban miki wannan kallon ba, sai ni dan na ce condami za ki min wannan kallo. To kalle ni da kyau, har na gama 'yan matan ci ba, ko yatsa ta namiji bai ta'ba ta'bawa ba".
Sunkuyar da kai Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Ni ma ban ta'ba iskanci ba, suna da uba. Rabuwa mu ka yi".
"Allahu Akbar kabira? Ki ce Jummai sharri ta biki da shi. Dole naje har 'daki na la'ance ta. Bani labari mai yafaru kuka rabu".
Mufeeda ba ta 'boye mata komai ba ta shaida mata labarin ta.
Inna Huwaila har 'yan guntun hawaye. Tuni ta shige 'debewa Naseer Kaduna albarka tare da la'antar shi.


*SORRY FOR THE LATE UPDATE. WALLAHI NETWORK 'DIN KADUNA NE SAI A HANKALI. GABA 'DAYA EMERGENCY YA KE NUNA MIN*
*LOVE YOU ALL FANS*

*MATAR SAYYADEE*
بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE 45_*
Baaba Habiba dauke da abinci ta aje kusa da Inna Huwaila tare da fa'din,
"Inna ga abincin".
Kallon sama da 'kasa Inna Huwaila ta wa baaba Habiba ta re da fa'din,
"Ke kuma daga ina haka?".
Baaba Habiba ta ce,
"Ai tare muka zo da Mufeeda, ni ke taya ta raino 'ya'yan ta".
"Ah to madallah. Kin kuwa kyauta. Kira min ita Zurfa'un". Fa'din Inna Huwaila.
Da to baaba Habiba ta amsa tare da nufar kitchen 'din. Tare su ka dawo da haj Zulfah.
"Ga ni Inna". Fa'din haj Zulfah.
"Yauwa, dama cewa nai ki gyara min waje a nan shashan ki. Domin nan zan sauka, kuma so na ke na zauna Kusa da wa'dannan 'ya'ya". Fa'din Inna Huwaila.
"Am gama Inna". Haj Zulfah ta fa'da tare da nufar sama. Baaba Habiba bi ye da ita a baya.
"Ohhh yau ni na shiga uku. Ke ba yanzu ki ka ce min rainon 'yan biyar ki ke taya wannan 'diya ba. Shi ne kuma duk in da Zurfa ta saka kafa ki ke biye da ita". Fa'din Inna Huwaila.
Baaba Habiba ta juyo tare da fa'din,
"Inna zan shiga ne na 'dan taya ta kimtsa 'dakin da za ki zauna ke da 'ya'yan jikan ki".
Washe baki Inna Huwaila ta yi tare da fa'din,
"Ahh to shikenan je ki abinki. Wai ma na ce ba. Miye sunan ki ne?".
"Habiba". Fa'din baaba Habiba ta re da wucewa saman.
"Ni zaka wula'kanta Naseer? Ni zaka watsa ma 'ka sa a idanu. Har ka na gwa'da kwanji da wanka akan karuwa".
Naseer da ke zaune akan resting chair da ke bedroom 'din haj Jummai ya ce,
"Ki yi ha'kuri mummy, wallahi Allah ne ya jarabce ni da 'kaunar Mufeeda. Kuma wallahi 'kaddara ce ya afka mata har suka rabu da mijin ta. Amma wallahi ba karuwa ba ce. Wa'dancan 'ya'yan da uban su ba shegu ba ne".
Hannun haj Jummai ta saka ta bite masa baki tare da fa'din,
"Rufe min baki sha³ kawai wanda bai san ciwon kan sa ba. Kuma in dai ni ce mahaifiyar ka, ban amince ka auri yarinyar nan ba. Wannan bala'i da me yai kama? Har 'ya'ya na biyu".
Naina da tun 'dazu ta na 'dakin ta na harha'da wa haj Jummai kayan ta cikin drower da mai guga yakawo mata ta bu'de ba ki tare da fa'din,
"Mummy na Naseer da Lukman kawai ki ka sa ni, ko in ce ya fito fili. Amma wallahi har da Jawad ma son ta ya ke yi. Hanzu haka maganar da na ke miki. Ya rubuta resignation letter ya tura Germany akan ya bar aiki dasu zai dawo 'kasar sa da zama duk kuma saboda yarinyar ne".
"Ke ba ni son hauka. Ka da ki kawo min hauka a nan. Wani Jawad 'din ne ya rubuta resignation lettern?". Haj Jummai ta fa'da.
"Wallahi Jawad na ki. Na kira small daddy na fa'da masa komai. Kuma ya ce min in sha Allah nan da sati biyu ko kamin haka zai zo Nigeria ya ji dalilin".
Zufa ce ke ketowa haj Jummai ta ko ina. Hankalin ta ya tashi matu'kar. Tun ni ta soma sintiri a 'daki zuciyar ta na zafi.
Naseer ko ji ya yai wani malulun ba'kin ciki da kishi sun turni'ke shi. Kenan ba Lukman ba ne kawai ke son shiga gonar shi. Lallai dole ya 'dauko mataki tun wuri. Fuuu ya tashi ya fice daga 'dakin.
Da idanu haj Jummai ta bi shi da shi. Naina kuwa ta'be bakin ta tayi tare da cigaba da saka kayan mummyn a cikin drower.
Lukman hannun shi ri'ke da zabgegiyar doruna a gaban gadon baby da ke ta kyarman tsoro. Zazzaro mata idanu yai tare da fa'din,
"Za ki min baya ni ko sai na shiga tsula miki a jikin ki. Ya akai Mommah ta san abunda ya faru har ta zo 'dakin Ummah (haj Zulfah)".
"Tsaya ka ji ya Lukman".
"A tsayan na ke ai". Fa'din Lukman rai 'ba ce.
"Ya Lukman haka kawai ta ce min jikin ta ya bata akwai abunda ke faruwa a 'dakin Zulfah. Shine ta ce muje na raka ta".
"Da ki ke kiran tada Zulfah kai tsaye, ita 'din sa'ar uwar ki ce?".
"A'a ina nufin aunty Zulfah". Baby tai saurin fa'da ta na 'kara shigewa jikin bango kamar her life depends on it.
"Mummy na da Allahn musuru ne? Za ki min baya ni ko sai jikin ki ya fara gaya miki". Lukman ya fa'da da tsawa.
"Wallahi ni ce ba fa'da mata komai. Na ji cacan bakin da ku kai da ya Naseer 'din ne a 'kofar garden shi ne na fa'da mata irin rashin kunyar da ya Naseer 'din ya maka".
"Shegiya munafuka! Ki ka fa'da mata rashin kunyar da ya min, ko ki ka ce mata ka'dan ya rage mu yi dambe har ina kai masa naushi ko".
Rufe baki baby ta yi da tafukan hannun ta tare da zazzaro idanu ta na kallon shi.
Bulalan ya shimfi'da mata 'daya a baya. Tai wani irin tsalle ta rungume shi da 'karfi ta na ba shi ha'kuri.
Mummy ce ta turo 'kofa tare da shigo 'dakin. Turus ta tsaya ta na kallon su. Domin irin rungumar da baby ta wa Lukman ba bu yadda za'ayi ka ce ta tsoron duka ne.
Lukman 'din ne ya janye baby daga jikin shi. Babyn na ganin Mummy tai bayan ta da gudu. Har mummy za ta ce wani abu, sai kuma ta canza maganar da fa'din,
"Alhamdulillah! Na gama da naka matsalar". Lukman bai kawo komai a ranshi ba, don shi rungume mace ba komai ba ne a wajan shi don a turai ya ke rayuwar shi.

*BAYAN ISHA*
"Inna ai da kin fa'da min zaki zo, da kai na zan je na 'dauko ki". Fa'din daddy.
"To ai ba laifi, tunda ga Abubakar ya je ya 'dauko ni. Duk da wasu da dama ba su so zuwa na ba, kuma sai dai a fa'din a zuciya, mutum ya fito da shi fili, in la'ance shi tare da 'debe albarkan mutum".
"Wa ma ya isa ya ce bai ji da'din zuwan ki ba Inna". Da'din daddy.
Kasancewar gaba 'dayan su su na babbar parlour daddy ne, daga 'ya'ya har jikoki da surukai. Har da baaba Habiba da Mufeeda da 'ya'yan ta. Ko minti biyar ba su yi daga cin super ba.
Ta'be baki Inna Huwaila tai tare da fa'din,
"Oho, ni dai abunda ya sa na ce maka gaba 'dayan mu mutaru ana shine, maganar aure tsakanin Nasifa da Nasuru kaman anyi an gama".
A mamakan ce alhj Mudassir ya kalli Naseer 'din ta re da fa'din,
"Wacece kuma Nasifa?".
"Kai ma dai ka tambaya Mudan, wani irin suna ne kuma Nasifa, sai ka ce Masifa".
Naseer 'din ne ya bu'de ba ki tare da fa'din,
"Ba Nasifa sunan ta ba, Mufeeda".
"Ko ma dai uwar miye lu kuka sani. Ga sunaye nan na matan manzon Allah, ba za ku saka wa 'ya'yan ku, sai wasu 'ka'kalan banza da wofi. Haka fa da nake tambayan suna yan 'yan biyar. Sai ca min akai wai Adin(Adil) da Aya(Ayaan). Ka ji wata lukutar masifa, wai harda Aya a sunan 'dan Adam. Matan kuma 'dayar sunan ta Ifana(Irfana). 'Dayar ce ma mai sunan mutunci Husna. Ita kuma 'dayar kuma wai ko Shahuda(Shahida). Kuma fa duk sunan yanka. Ni dai da asalin sunan su zan ri'ka kiran su".
"Ai 'yan zamanin nan sai su". Fa'din alhj Mudassir.
"To ni dai na gama magana. Nasuru zai auri Nasifa, idan da mai ja sai yai magana in kuwa 'debe albarka da la'antar mutum".
Shi dai alhj Mudassir har yanzu bai fahimci inda zancan ya dosa ba. Sai kallon Naseer yai tare da fa'din,
"Ban fahimta ba, wake son Mufeeda? Kuma Mufeeda ta gidan nan".
Kamin ma Naseer ya ce wani abu, carf Inna Huwaila ta ce,
"Eh ita 'din fa. Nasuru ke son aura ta. Ko ka na da jaa ne yanzu in 'debe maka albarka ko kuma ka biya ni nono na daka sha".
"Wane ni da jaa da maganar ki Inna. Kawai ban ga ne zancan ba ne shiyasa nai tambaya. Ban san Naseer 'din na san ta ba ai".
"To yanzu ka sa ni. Ai naji labarin komai. Nasuru shi ne ma wanda ya kawo ta gidan nan. Don haka na yanke hukunci. Kuma ina sha Allah da kai na zan je kadunar nai man auran yarinayar har wajan la'anannan 'kanin mahaifin na ta".
"Ba matsala Inna in dai har ita Mufeedan ta na son shi. Kuma dama Aliyu ya sanar da ni ya na zuwa nan da sati biyu. Sai mu tafi da NI dashi shi da ke da Mufeeda har da Naseer 'din tunda shi ya san gidan na su".
"Yauwa 'dan albarka. Nasan 'ya'ya na ba su tsallake magana ta. Shi kuma Aliyun zai zo ya sa me ni. Wa ya 'ki zuri'a a rayuwan shi. Daga na yi masa gwanin ta, shine zai 'dauke ni ya saka ni cikin rai. Allah dai ya kawo shi lafiya".
Wani sanyayyar da'di ne ya mamaye zuciyar Naseer, Naina da haj Zulfah. Ya yin da a 'bangare guda dun'kulallan ba'kin ciki ya mamaye zuciyar Lukman, Jawad, Baby, da shugaba haj Jummai.
Jawad kuwa addu'a ya ke cikin zuciyar shi da Allah ya sa bai yi saurin tura resignation lettern da ya rubuta ba.
Ko da kowa ya watse, baby 'daki ta shige tare da rufo 'kofa ta dunga rusar kuka tare da tsinewa Inna Huwaila. Can ta jawo drowern ta tare da 'debo kayan mayan ta. Su cocaine, wiwi, cosine tare da tukunyar shisha za ta yi mix.
Lukman ne ya turo kofar tare da shigowa kamar ya san abunda ta ke shirin aikatawa.
"K'arasawa wajan da take yai tare da 'dagota a du'ken da take gashin ta duk ya hargitse. Kai a 'dakin ma, babu abunda ba ta hargitsa ba.
"Do you think this is the solution to your problem? Ur just adding salt to the injury. Just let him go. You can't be happy with him cus his mind is somewhere else. Ko da kuwa mummy ta tursasa shi akan ya aure ki, ba zaki ta'ba samun farin ciki ba. Delete him in your heart. Don't ruin your life. Ke 'yar uwa ta ce. Wallahi shaye² masifa ce ga 'da namiji ma ba 'diya mace ba. Idan za ki iya, kuma zaki amince, ki ba ni dama in maye gurbin Naseer a zuciyar ki. Zan soki kuma in kula dake fiye da duk wani 'da namiji a duniyar nan".
Zuba masa idanu baby ta yi tare da 'dunbin mamaki baki sake. Ji tai kan ta ya 'kulle. Tun da ta ke a rayuwar ta, ba ta ta'ba jin makaman cin wa'dannan kalmomi a bakin wani 'da namiji ba. Kai ita a rayuwar ta ma, idan ba Naseer ba, ba ta ta'ba son wani ba. Abunda ta ke so a rayuwar ta kawai shine shaye² da ta koyo a jami'a.
Rungume ta Lukman yai tare da fa'din,
"I love you Jalila".
Samun kan ta ta yi da zagaye shi da hannun ta.
Mummy da ke la'be ta share hawayan far in ciki. Domin ba ta ta'ba tunanin za ta samu kan Lukman cikin sau'ki haka ba. Gashi ya yi abunda ta ce masa yai, duk da ta San shi ma 'din ba son Babyn ya ke yi ba.
Shikuwa Lukman ba 'karamin 'karfin hali yai ba wajan furtawa baby Kalmar so Wanda a zahiri Mufeeda ya ke so ba ita ba.
Kawai ya bi umarnin mahaifiyar shi ne don ka da zafin ya zama mata biyu.

*KADUNA*
Da sauri daddy ya 'dauki goran faro ya bu'de ya zuba mata a fuska. A gigice Mommah ta farfa'do tare da 'kan'kame hannun daddy ta na fa'din,
"Allah sarki Umaymah, ashe 'diyar ki ba ta mutu ba".
D'ago ta Daddy yai tare da fa'din,
"Tun ranar da na fara ganin ta, naji a jiki na Mufeeda jini na ce. Shiyasa tun daga wannan lokacin ban huta ba wajan bincike akan ta".
"Yanzun nan zan kira Umaymah in sanar da ita wannan abun farin cikin". Fa'din Mommah.
"Ka da ma ki soma. Ki bari su zo ta ga ni da idanun ta. Yanzu idan ki ka fa'da mata. Kin san inda Mufeedan ta ke ne? Ki bari, ai mijin na ta ya gama programme 'din shi tun wata biyu baya. Don an rage masa shekara 'daya. Yanzu haka sun kusa dawowa Nigeria. May be ma cikin watan nan ko wanda zamu shiga".
"Alhamdulillah! Ai shikenan, amma duk da haka, zan kira ta in ce mata ina da albishir mai girma idan ta dawo". Fa'din Mommah.
"To shikenan ba matsala, za ki ya fa'da mata hakan".
Tashi su kai tare su ka nufi wajan mal Ahmadu don 'karin baya ni.

"Mama na fa'da miki komai ne domin ceto Mashkura daga halakan da take shirin shiga ciki, ko in ce ta ke ciki. Ni nasan ba ki san komai ba shiyasa nazo na fa'da miki".
Mama da ke kuka sosai, ta kalli Zabba'u tare da fa'din,
"Wallahi na san komai Zabba'u, nasan irin cutar da Mashkura tai wa aminiyar ta Mufeeda. Tun da na ji labarin Naseer ya saki Mufeeda na san tabbas akwai saka hannun Mashkura a ciki. Na kira ta na mata nasiha, amma wallahi ba ta saurare ni ba. Na rasa yadda zan yi da Mashkura. Ba ta jin magana ta tunda na gane ba ni ce wacce ta haife ta ba. Mashkura ta fi 'karfi na yanzu".
Sosai Zabba'u ta zaro idanuwa tare da fa'din,
"Mama dama ba ke ce ki ka haifi Mashkura ba?".
"Kwarai kuwa, adopting 'din ta mu kai a gidan marayu. Ni ban ta'ba haihuwa ba". Fa'din mama.
"Inna lilahi wa'inna ilaihirraju'un. Wallahi babu Wanda zai ce ba kune kuka haife ta ba. Yadda kuke kula da ita kamar 'diyar ku ta cikin ku". Fa'din Zabba'u.
"Hmm ita ba ta ga hakan ba ai. Yanzu ya za ta yi da hakkin wannan 'Yar marainiyar yarinyar Mufeeda? Ni zan je gidan har gidan ta na mata nasiha ta bar abunda ta ke yi. A kan 'da namiji Mashkura ta jefa kan ta a harkan bin malamai".
"Gaskiya dai mama ki 'dau mataki, tun ka min abun yai nisa".
"Yanzun nan zan tafi gidan". Fa'din mama tare da 'daukar gyalan ta.
*MASHKURA*
"Dan girman Allah Naseer ko ka'dan ne ka ba ni gurbi a zuciyar ka ko da bai kai na Mufeeda ba. Wallahi ina sonka, nafi Mufeeda 'kaunar ka".
"Ke!". Naseer ya daka mata tsawa tare da cigaba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login