Showing 60001 words to 63000 words out of 115393 words

Chapter 21 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22915

Da "To" ta ba shi amsa tare da jin wani sanyayyar da'di a zuciyar ta. Ita kan ta ba ta 'kaunar wannan shegiyar tallar.
"Tashi muje in raka ki gida".
Mi'kewa tai, shikuma ya ri'ke farantin su ka soma tafiya, sai da suka kusa 'kofar gidan ka na ya ka ya tsaya tare da tura hannun shi a cikin aljihu ya zaro dubi biyar ya aje bisa farantin ya mi'ka mata farantin tare da fa'din,
"Gashi, Allah ya tashe mu lafiya. Said mun ha'du gobe".
"Nagode". Shine abunda Mufeeda ta fa'da tare da karban tiran. Tabbas da ta dauki ku'din a kan faranti ta ji su dumus, amma ba ta kawo 'yan dubu² ba ne ba.
Sai da ya ga ta shige gida sannan ya juya ya tafi gidan kamar shi da ke can gaban gidan su Mufeedan sosai.
Sallama tai. Zaune ta samu *MAI ZOGALE* ta na jiran dawowar ta. Aikuwa ta na ganin ta na bu komai a faranti, kuma sannan robar fallasar ma babu komai ta nufo wajan ta tun kan Mufeedan ta 'karaso.
Ku'din Mufeeda ta mi'ka mata. Kasancewar a kai yalwar hasken kwan fitila a tsakar gidan, sai a lokacin Mufeeda ta ga ku'din, dubi 'dai² ne gida biyar. Gaban ta ne ya shirya lugude ta na shirin jiran saukar mari a fuskan ta, amma sakamakon haka sai kawai Mufeeda ta ji an rungume ta.
Sosai abun ya ba ta mamaki. *MAI ZOGALE* sai ca tai,
"Wani 'dan albarkan ne ya waye kayan nan?".
Mufeeda ta ba ta amsa da,
"Wani ne ya min juye ya rabawa almajirai".
"Kai amma Allah mass albarka. Daga yai wajan sa za ki ri'ka kai kaya, kin ji ni".
"Eh Inna na ji". Mufeeda ta fa'da tare da shigewa 'dakin ta.
" 'Yar iska, ni ba ruwa na. Ko jikin ki za ki ba da a miki juye, ni bai same ni ba. Ni dai buried na kawai in ga ku'din in samu na fita kunya a bikin Marwanatu". *MAI ZOGALE* ta fa'da tare da cigaba da irga ku'da'dan a karo na bakwai.




*MATAR SAYYADEE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )

*STILL FOR U, SALIS _MKZ_. ALHERIN ALLAH YA KAI MA KA A DUK IN DA KA KE.*

*_PAGE 32_*

Kwanciya Mufeeda ta yi, kasancewar sai da tai sallah ka na ta tafi tallah.
Juyi tai ta yi akan gado ta na tunanin maganar da Naseer ya mata.
Murmushi ne ya su'buce mata.
"Tabbas Naseer ya na da kyawun da babu macen da za ta kalle shi ba ta 'kara a karo na biyu ba. Zan amince masa ko dan fitinar gidan nan na mu. Bazan iya jurewa tallah ba sam a wannan unguwa na mu da babu tarbiya". Mufeeda ta fa'da a zuciyar ta.
A haka tunane² su kai ta bijiro mata har bacci 'barawo ya zo ya tafi da ita.
Washagari as usual ta tashi tai duka ayyukan gida, ta na so ta je gidan su *KURA*, amma ta rasa ta yadda za ta tunkari *MAI ZOGALE* da maganar. Don jiya ma don ta fita ne shiyasa ta sa mu hanyar fita daga gidan.
Kamar a cikin mafarki ta jiyo muryan *KURAN* na sallama. Sosai gaban ta ya fa'di don har ga Allah ba ta son damuwa da sassafan nan.
Saurin fitowa tai daga 'daki ta ja hannun Mashkura su kai 'dakin ta da sauri don ka da *MAI ZOGALE* ta gan ta.
"Ke Mashkura ba kya jin magana wallahi. So kike ki saka ni a uku? Kin fa san halin matar nan". Fa'din Mufeeda.
Ta'be baki Mashkura ta yi tare da fa'din,
"Na san dai wannan gida ba na ta ba ne. Don haka ba ta isa ta hanani shigowa ba. Ni ba ke ba ce da ke nuna tsoran su a fili. Duk wacce ta min ina dai² da ita wallahi".
"Ni dai don Allah ki rufa min asiri, ki ta shi muje na raka ki, dama ni ma in son zuwa wajan ki".
"Kin san Allah, wallahi ba bu inda za ni. Idan ma za ki ha'kura, to ki ha'kura. Ni ma na baro Mama can ta na ta mitan da ta saba akan na'ki fidda miji". Fa'din Mashkura ta re da yaye gyalan da ke jikin ta ta aje akan katifar da su ke zaune a kai.
Ajiyar zuciya Mufeeda ta sauke. Ta san halin Mashkura, idan ta ce za tai abu, sai ta yi shi. Haka idan ta ce ba za tai abu ba, to fa babu Wanda ya isa ya saka ta ta yi shi.
"To ya Tallar na ki ta kasance jiyan?". Mashkura tq jeho mata tambaya ta na hararar ta.
Wani ajiyar zuciya Mufeeda ta saki tare da wani shu'umin murmushi.
"Da ga ganin wannan murmushin na ki akwai magana a 'kasa. Dan Allah shafamin na ji". Fad'in Mashkura.
Murmushi ta 'kara yi tare da fa'din,
"Mun had'u da Naseer".
Daaam gaban Mashkura ya fad'i. Sai da ta d'an diririce wajan fad'in,
"Wa..wani Naseer d'in?".
Farrr ta 'kara yi da idanu sannan ta ce,
"Naseer dai abokin fad'a na".
Shuru Mashkura ta yi gaban ta na lugude tana kuma addu'ar Allah ya sa ba abunda zuciyar ta ke zargi ba ne akan Mufeeda da Naseer d'in.
Hannu Mufeeda tai mata waving a fuskan ta tare da fad'in,
"Hy lafiya na ga kin tsare ni da idanu kin kasa cewa komai".
Saurin dawowa cikin hayyacin ta ta yi tare da fad'in,
"Abun ne ai ya ba ni mamaki, wai auduga da wuta ne ake shiri kuma yanzu".
"Tun kamin na ba ki labari abunda ya faru shi ne za ki ce shiri. Ai kya tsaya dai ki ji yadda mu kai".
"Alhamdulillah". Fa'din Mashkura cikin zuciyar ta wanda har sai da far in cikin ta ya bayya na a fili.
Tun da Mufeeda ta soma labarta mata tun san da Jazuga ya zo wajan sana'ar ta da har rako ta gida da ya yi da kuma abunda ya fa'da mata.
Kuuuuuuuu.... Kulululululuuuuuu...kuiiii.
Sautin da ke fita daga cikin Mashkura ke nan saboda tsabar ki'dimewa da labarin da Mufeeda ta zo mata da shi. Kan ta ne ta ji ya na sarawa, idanuwan ta na ciccikowa da hawaye tai saurin mai da su ka da Mufeeda ta ga ni.
"Na yanke shawarar amince masa kawai. Ni ma na huta na tafi gidan miji na nai bautar ubangiji".
Ya'ke Mashkura ta yi tare da fa'din,
"Aikuwa dai kam. Na ji mi ki dad'i kam, don Naseer mutumin kirki ne. Ga kyau ga dukiya. Ga kuma uwa uba kyawun hali".
Rungume ta Mufeeda ta yi tare fa fad'in,
"Wallahi ina son shi ni ma. Ban san dama ina son shi ba, sai jiya da ya furta min".
Wasu hawaye ne masu 'dumi su ka saukowa Mashkura tai saurin saka bayan hannun ta ta goge tare da danne kukan da ya ke taho mata ta ce,
"Ai dama an ce duk in da na ga mace da namiji sun cika fad'a, to ka bincika da kyau akwai 'kamshin soyayya a ciki".
Sa ke ta Mufeeda ta yi tare da fad'in,
"Yanzu fa ya ce bazan sake tallah ba, kullum na fito na same shi a in da mu ka tsaya jiya. Zai saye gaba daya ya rabawa almajirai".
"Aikuwa kin ga Kin huta wallahi. Allah ya bar 'kauna". Fa'din Mashkura tare da mi'kewa bayan ta 'dau gyalan ta ta yafa.
"Aah ya haka? Ina kuma za ki je?". Mufeeda ta ri'ke tsaye ta na tambayar ta.
"Dama fa da ga nan wajan Zabba'u mai wara na yi. Don mun yi zamu ha'du yau za ta koya min yadda ake wara, zan rri'ka yin na ci a gida". Fad'in Mashkura.
"Ai wallahi da ya fi da zuwan da Ki ke yi cinye jari". Gaba 'daya su kai dariya su ka tafa.
"Ba wai kin rama ni ba, kin san dai halin Innar ta ki". Fa'din Mashkura.
"Duk da haka muje ko kwar gida na raka ki". Fa'din Mufeeda.
Mashkura ba ta 'kara cewa 'kala ba tai waje. Mufeeda ta bi ta a baya.
Cikin hukuncin ubangiji kuwa ba by kowa a tsakar gidan har Mufeeda ta raka ta, ta dawo d'aki.

Had'a hanya kawai Mashkura ta ke yi ba tare da sanin in da ta ke jefa 'kafa ba. Sau uku ta na tuntu'be har sai da Babar yatsar ta tashe. Ko tsayawa duba 'kafar ba ta yi ba, domin tashin hankali da ta ke ciki ya fi fashewar 'dan yatsar na ta azaba. Tafiya ta ke yi hawaye na zubo mata kamar wacce aka aikowa sa'kon mahaifiyar ta ta rasu.
Babu abunda ya mata da'di irin rashin ga ni Mama a tsakar gida. Hakan ya ba ta damar shigewa 'daki ta kullo kofa tare da fa'dawa kan 'katuwar katifar ta ta ma fa'din,
"Na shiga uku! Na shiga uku!! Na shiga uku na!!! 'Kawa ta ya ke so. Aminiya ta ya ke so ba ni ba. Ka da ka min haka Naseer. Ni ce ya cancan ta ka so. Ni ce ba ke 'kaunar ka tun tuni. Wayyoo Allah na, nauyin baki na ya jawo min. Saboda kai na 'ki kula kowa. Saboda kai na 'ki fidda miji. Kai na ke jira ka taho gare ni, shine zaka min rashin adalci ka tafi wajan aminiya ta. Ka dawo gare ni. Zuciya ta bazata iya 'dauka ba. Na da'de ina mahaukacin son ka. Bazan iya rayuwa da wani 'da namiji a matsayin miji idan ba kai ba. Ya Allah ka sa mafarki na ke yi²". Mashkura ke fa'din haka ta na dukan katifa kamar wata zararra. Tun ta na kuka ba sauti, har sautin kukan ta ya ta shi Mama da ke bacci.
Wani durowa Mama ta yi ta fito da gudu. Mama na matu'kar 'kaunar Mashkura, kasancewar ta 'ya 'daya da ta mallaka a duniya.
Hankalin Mama bai da'da ta shi ba, said da ta ji tabbas kukan Mashkura ne Ka ta shi daga 'dakin ta.
"Ko ma menene wannan, ba 'karamin abu ba ne". Fa'din Mama, kasancewar ta San da wuya ka ga hawayan Mashkura saboda ta na da taurin zuciya.
'Karisawa tai wajan 'kofa ta na bugawa tare da kiran sunan Mashkura akan ta bu'de mata 'kofar.
Biris Mashkura tai da ita, sai dai ta rage saurin kukan na ta. Haka mama ta 'kariki tsayuwar ta ta ma bubbuga kofar amma Mashkura ba ta bu'de kofar ba.


*8:15pm*
Yau ri'din dubu da 'Dari biyar *MAI ZOGALE* ta yi, gya'da kuma ta dubu biyu.
"Maza 'Yar albarka zo ki 'dauka. Yau ma ki sayar duka. Ki kai wa Wanda ya miki juye jiya. Duk abunda ya ce miki, ka da KI sake ki masa musu. Kin ji ni?". Fa'din *MAI ZOGALE*.
"Eh na ji Innah". Mufeeda ta fa'da tare da 'daukar farantin gya'dar a kan ta, robar ri'din a hannun ta ta fice daga gidan.
"Shegiya ki je ki ta bawa maza kan ki su na miki juye. Wannan ba damuwa ta na ne, buri na kawai, ki kawo min 'yan silalla. Mai ya fi rai na". *MAI ZOGALE* ta fa'da tare da shigewa 'daki.
Kallo 'daya ta masa ta, ta kauda kan ta. Don wani abu ta ji ya baki zuciyar ta.
Marwanatu ta kece da dariya tare da fa'din,
"Yar tallah a dawo lafiya, a dai yi a hankali ban da biye² maza".
Musa da ke jingine jikin katanga, ya ka sa 'dauke idanun shi akan Mufeeda, haka nan ya ke jin can 'kasan zuciyar shi kamar ya na wani abu da bai da kyau.
"Kallon me ka ke mata haka? Ko ka koma son ta ne?". Fa'din Marwanatu ta na kika masa da wata uwar hararar da kishi ke cin zuciyar ta.
"Kallon kyama na ke mata wallahi. Na rasa ya akai tun farko ba ke na ce ina so ba".
Wani faaarr tai da idanu tare da fa'din,
"To ai yanzu dai ko mai ya wuce".



_******************_
Ta na kwanar lungun in da su ka tsaya jiya, caraf ta ji an rungume ta ta baya. Saki tiran kan ta ta yi, gya'dar ya zube k'asa, za ta kwalla 'kara aka toshe mata baki ana kuma kiciniyar kwance mata zanin ta.
Sosai kokawa ya 'balle tsakanin ta da wannan 'dan iskan.
Ganin da yai kamar ana nufan wajan kasancewar ba wuta hasken touchlight ya ga ni. Wai ya wani irin hanka'da ta, kan ta ya bugu da bango sosai shikuma ya arce. A take ta sume a wajan saboda buguwa da kan ta ya yi.
Da uban gudu ya 'karaso wajan, ya na haskawa. Aikuwa idanuwan shi yai tozali da abunda ya ke zargi.
Mufeeda ce kwance jini na zuba daga kan ta. Ai bai san san da ya cicci'be ta ba, da gudu yai bakin hanya. Alla ya so yau ya taho da motar shi. Bu'de motar yai ya saka ta a ciki, bai tsaya ko INA ba wai asibitin dialogue, kasancewar gaba daya gidan su ma nan suke da falimy card.
Cikin gaggawa aka kar'be ta a kai emergency da ita domin ceto ran ta.
Shikuwa sai patrol ya ke yi a wajan, a zuciyar shi kuma ya na rantsuwar ko wa ya tsaywa iyayan ru'kon Mufeeda ta dai na tallah. Duk abunda su ke bu'kata shi zai masu.


*10:35pm*
" 'Yar iskan yarinyar nan fa har yanzu ba ta dawo ba, jiya da ta fita ai ko away 'daya ba tai ba ta dawo min da robar ri'di da farantin gya'da. To ko dai ta na can 'dakin 'dan iskan da ya mata jute be jiya? To idan ma haka ne NI dai buri na a kawo min ku'di. Ya gama kwashe albarkan jikin ta, ni kuma a kawo min ku'di wannan ba damuwa ta bane". Fa'din *MAI ZOGALE*.

Har 'karfe sha 'daya Mufeeda ba ta farfa'do ba, hankalin Naseer yai 'kololuwar ta shi.
Wayar shi ce ta soma 'kara. 'Dauko wayar ya yi daga cikin aljihun wandon shi. *Mommah* ya ga ni a jikin screen 'din wayar. Saurin latsawa yai tare da karawa a kunne.
"Ina ka shige ne? Hajiya (kakar sa) ta kira a waya ta ce yau ba ta gan ka ba. Ga shi after eleven yanzu baka dawo gida ba".
"Mommah akwai Marsala fa". Fa'din Naseer.
Gaban Mommah ya fa'di tai saurin fa'din,
"What's the problem?".
"Mom ina yarinyar nan da Ummu nah ta ba ki labarin ta?". Fa'din Naseer.
"Eh. Go straight to the point". Fa'din Mommah.
Naseer ya kwashe komai ya fa'da mata.
"Subhanallah! I'm coming right now". Mom tq fa'da tare da katse wayar".
Dai dai nan dr ya fito tare da shaida masa ta farfa'do, sai dai sun mata allurar bacci, amma zai iya shiga ya gan ta.
Cikin sauri ya shigo 'dakin da aka aje ta ita ka'dai. Hannun ta manner da 'Karin ruwa. Kan ta kuma an nanna'de shi da bandeji.
Kallon ta ya ke yi, wani tausayin ta na mamaye zuciyar shi.
"In sha Allah ko mai ya zo karshe. Zan tura iyaye na gidan ku ai mana aure kawai ki huta". Naseer ya fa'da ya na ri'ke da hannun Mufeeda ta na 'karin ruwa.
Turo 'kofar da aka yi ne ya mai da hankalin shi izuwa 'kofar.
Mommah ce hankakin ta a tashe.
Ya na ganin ta ya saki hannun Mufeeda tare da isa wajan mom 'din ya rungume ta ya na hawaye.
Petting 'din bayan shi ta yi tare da 'karasawa wajan gadon ta kalli fuskan Mufeeda.
Wani irin jaa da baya ta yi tare da dafe kirji.......




Ko mai ya sa Mommah tai hakan? Said kun biyo ni a next page don jin yadda za ta ka ya.



*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login