Showing 78001 words to 81000 words out of 115393 words

Chapter 27 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22928

yanzu, don za ta hanasu rawan gaban hantsi.
Ta na tafiya, cikin sauri Mufeeda ta 'kara kintsa gidan tare da saka turaran wuta. Ka na ta nufi 'daki tai wanka tare da tsantsara kwalliya cikin wando jeans pencil kalar royal blue, rigar kuma pink mai gajeran hannu. Sai ta 'daure gashin ta da pink 'din ribbon jelar gashin ta ya sauka gadon bayan ta, sai ta nanna'do shi tai donut da shi. Ba 'karamin kyau ta yi ba. Jikin ta ta feshe da turaruka, sannan ta sauko 'kasa tare da shiga kitchen don ha'da masa abinci. Naseer ya fison abinci da zafin shi. Bai cika son abinci ya dad'e a cikin kula ba.
Ta na cikin yanka cucumber ta ji door bell. Da sauri ta nufi 'kofar don tasan ko waye. Aiko ta na bu'dewa tai arba da shi ri'ke da 'kugu ya na sakar mata murmushi.
Tsalle tai ta fa'da jikin shi tare da fa'din,
"Welcome home, Habibi Da'iman".
Hannun shi ya zaga yo ta tare da fa'din,
"I miss you a lot wallahi, gashi aiki ya yi yawa ko samun daman hira sosai ba mu yi a waya ba". Ya fa'di hakan ne tare da 'daukar cak su kai parlour.
Sai bayan ya zauna, ya kuma aje ta kan cinyar shi sannan ta ce,
"Yallab'ai daga fitar ka, zuwa dawowan ka, ka kira ni sau bakwai fa, ni har tunani na ke ma anya ka na mai da hankali wajan kula da customers kuwa?".
"Sosai ma kuwa, Sai dai rabin hankali na ya nan gida wajan ki. Ke ina kallon computer ma, Sai in ga fuskan ki na ke ga ni ciki, shiyasa kike ganin ina ta kiran ki akai²".
Rungume shi ta yi tare da fa'din,
"Love you soooooo much yallab'ai, irin wujiga² nan fa".
"Har ya kai irin son da na ke miki Habibty?".
Hararar wasa ta maka mashi tare da fa'din,
"Allah na wa ya fi naka".
Zaro idanu yai tare da fa'din,
"Harda ha'dawa da Allah, to maza tufar da yawu, don Allah nawa yafi naki".
Nan su ka hau musu. Wannan na nawa yafi, wannan ma na nawa yafi. Daga 'karshe dai su ka ha'kura akan sunawa junan su soyayya da 'kauna dai² da na juna. Amma kowa 'kasan zuciyar shi, ga ni ya ke nashi ya fi.
'Kaurin da suka ji a kitchen ne ya sa suka nufi kitchen 'din dukan su. Aikuwa tukunya har ta kama.
Naseer ya sauke tukunyar ta re da fa'din,
"Muje nai wanka, Sai muje restaurant mu ci abinci a can. Don ba ni so ki wahala wajan 'daura wani girkin". Ya na gama fa'din hakan ba tare da jin mai za ta ce ba, Wuff ya 'dauke ta yai hanyar sama da ita.
Dariya ta ke ta na fa'din,
"Yallab'ai ka dai mai da ni yar tsana. Kai ba ka gajiya da 'dauka ta ne?".
"Ba na gajiya, kuma ba zan ta'ba gajiya ba". Fa'din Naseer.
Bai aje ta ko ina ba sai cikin bayi, a cikin jacuzzi.
"Ahhh, ya haka? Ya ka kawo ni ba yi kuma, bayan na yi wanka?".
"Eh. Sa ke wa za muyi tare".
Za tai magana ya saka 'dan yatsar shi d'aya saman lab'b'an shi tare da furta,
"Shiiiiiiish! Ban son musu".
Tuni ta had'iye maganar ta.
Tare su kai wanka yamar yadda ya bu'kata. Ita ta taya shi shiryawa cikin 'kananan 'kaya da suka matu'kar 'kara fidda halittan kyawun shi. Shi ma kuwa ya taimaka mata ta shirya cikin atampa riga da siket da suka amshi jikin ta, sannan ya 'dauko after dress mai kauri ya 'daura mata akan kayan, don kishin ta ba zai ba ri su tafi haka da mayafi kawai ba. Nanna'da mata gyalan ya yi Ka na ya 'dauko ma ta wani flat shoe jaa ta saka. Sannan ya kama hannun ta suka fito bayan ya 'dauki keyn mota.
Bayan sunje restaurant sun ci abinci, super market su ka biya yai mata sayayya tare da tarkacan kayan za'ki irin su chocolate da ta ce ta na so.
Daga nan gidan Mommah su ka yi, aikuwa twins da Mommah sun ji da'din ganin ta. Ta kuma saki jiki dda su sosai, sakin jikin da ta yi ko Mommah ta ji da'din hakan.
Sai da su kai sallar isha'i su ka tafi. Bayan Mufeeda ta 'dibawa twins chocolate. Mommah kuwa ba ta gajiya da kyauta. Wannan karan ma, turaruka ta ha'do ta da shi, da wani jarka rabin abod cike da tsimi. Wannan zuwan da sukai ma, sai da ta bata manya² goran swan guda hu'du. Tuni ta shanye saboda da'di da kuma za'kin shi a baki. Ba ma wani sanin amfanin shi tai ba. Sai dai abunda ta lura, duk lokacin da ta sha, tana jin canji a jikin ta, ya na 'daya daga cikin dalilan da ya rage mata jin zafi yayin da Naseer ya zo mata.
Sai tara su ka iso gida, don su a malali su ke, kuma can ciki sosai.
A gajiye Mufeeda ta ke, kayan bacci ta canza tare da yin brush da kuma 'kara feshe jikin ta da turare, ka na ta kwanta.
Naseer tsaye jikin madubi, shima yana fesa turare, ya ce,
"Allah ya sa dai ba bacci za ki yi ba, don aiki gare ki fa".
'Dagowa tai duk da nauyin da idanun ta su ka soma yi ma ta saboda baccin. Ta ce,
"Wani aiki ne yallab'ai? Fa'de shi yanzu nai maka".
Kashe wutan 'dakin yai tare da hawa kan gadon ya jawo ta, cikin kunnan ta ya ra'da mata,
"Twins za ki kar'ba da daran nan in sha Allah. Wallahi ina matu'kar son yan 'biyu. Kuma irin identical 'din nan. Ko duka maza, ko duka mata".
Gashin da ke kwance a kan shi tta shafa tare da fa'din,
"I'm all yours, ka yi yadda ka ga dama".
"Thank you". Ya furta mata cikin kunne tare da ja masu bargo.
********
Abun da ke matu'kar damun Mufeeda yanzu shine, duk Saturday and Sunday Mashkura sai ta zo gidan, bayan ta San Naseer ma aikacin banki ne, wa'dannan ranakun ne ya ke amfani da su ya baiwa Mufeeda lokacin shi gaba da'ya. Amma *KURA* ta hana su rawan gaban hantsi.
Tun Naseer ba kawaici, har ya fito yai wa Mufeeda 'korafi akan hakan. Ita kuma ta rasa ta in da zata farawa Mashkura magana.
Naseer 'din ne dai da ya gaji ya fito da wata dabara. Mai gadi ya sanar wa, duk lokacin da Mashkura ta zo in dai weekend ne, ya ce mata babu kowa a gidan sun fita. Da wannan dabarar su ka sa mu suka tsira daga yawon zuwa gidan da ta ke masu duk weekend.



🤍🤍🤍🤍
*BAYAN WATA UKU*

Zaune ta ke akan gado, ta jingina da jikin gadon, shi kuma yai filo da cinyar ta. Gyefan ta kwallin popcorn ne, hannun ta ri'ke da waya ta na karanto masa online novel mai suna BA NI NA KASHE TA BA, na Mummyn Mihal. Idan tai karantun sai ta 'dauki popcorn da yanzu shi ne ya zame mata abincin ta, ta saka a baki.
"Wai ka na ma saurara ta kuwa?". Fa'din Mufeeda.
"Ina jin ki Habibty".
"Yauwa na sha ba ka saurara na, ne". Fa'din Mufeeda ta re da iban popcorn ta zuba a bakin ta.
"Ni fa gaskiya idan ki ka cika bakin ki da popcorn 'din nan ki na magana, ba na gane me kike fa'da".
"To ba ri idan na ha'diye na ba ki na, sai na cigaba". Fad'in Mufeeda.
"Yauwa gwara dai haka". Fad'in Naseer.
Sai da ta ha'diye ta cigaba. Ta yi nisa sosai ta na karatun. Ta ji shuru ba comment. Kallon fuskan shi tai taga idanuwan shi a rufe ya na bacci. Aikuwa ta 'dauki kwalin popcorn 'din nan ta juye masa a fuska.
Ta shi yai zaune ya fashe mata da dariya. Aikuwa ta mi'ke, shikuwa yai wajan 'kofa.
Biyo shi tai da gudu, shi ma kuwa ya antaya da gudu. Tsautsayi ya sa tai missing step, aikuwa ta zame ta fa'di ta dunga gungurowa.
Tunda Naseer ya ke, bai ta'ba tashin hankali irin wannan ba, da gudu ya taro ta. Babu in da ta ji ciwo, amma kuma saboda firgicin da ta yi lokacin da ta kai 'kasa, sai ta suma.
Ciccibar ta yai ya maka ta a cikin mota, daga shi said gajeran wando. Yai saurin komawa ya dauko jallabiya ya saka tare da shiga mota ya nufi asibiti da ita.

*ASIBITI*
"Alhamdulillah! Sir ka kwantar da hankali ka, babu abunda ya same ta, kuma alhamdulillah, cikin jikin ta shi ma bai samu matsalar komai ba, nan da 30min ma za ku iya wuce wa gida, mun 'dan bata hutu ne".
Waro idanu Naseer ya yi tare da fa'din,
"Dr mai ka ke son fa'da min? Mata ta Mufeeda na 'dauke da ciki na? Dr ka fa'damin ba mafarki na ke ba dan Allah".
Dariya Dr yai tare da zagayowa in da ya ke, ya dafa shi tare da fad'in,
"Sir, tabbas matar ka na 'dauke da ciki, na sati takwas, domin har scanning na mata. Ma'ana ta na 'dauke da cikin ka na wata biyu".
A ta ke Naseer ya zube tare da yin sujada. Ya nan mi'kewa kuma ya rungume dr tare da fa'din,
"Forward your account details to me".
Washe baki Dr yai tare da fa'din,
Right now sir". Ficewa Naseer yai tare da komawa 'dakin da Mufeeda ta ke. Ta ma zaune, ba zaka ta'ba cewa ita ce wance ta fa'do 'dazu ba. 'Daga ta yai cak ya na mata rawa.
"Finally Allah ya 'karbi addu'a ta, Rabin rai, ki ba 'dauke da ciki ba har na tsawon wata biyu".
Zaro idanu tai tare da 'boye fuskan ta cikin 'kirjin sa.


💖💖💖💖💞
Bayan kwana biyu, Naseer ya shigo 'dauke da gashashshan masara cikin leda, domin tun daran jiya ta ke masa magiya ita masara za ta ci gasassa. Jiyan ma haka ya dunga yawo bai samo ba, sai yau. Don ko aiki bai je ba.
Wuff ta fizge ledan, domin kamshin masarar har wani fizgan ta ya ke shi (🤣🤣kamar yadda takwara ta ke yi idan ta ga waina. Har miyau zaku ga ya na zuba a bakin ta🤣lol).
Bin key 'din da ya fa'do daga ledar tai da idanu tare da du'kawa ta 'dauka ta ma kallon shi.
'Dage mata gira yai tare da fa'din,
"Gift 'din ki ne, ba kyautar budurcin ki da kuma sani farin ciki da KI kai na 'daukar ciki na a jikin ki".
Ai Mufeeda ba ta San Sadda tai wurgi da masarar ba tai waje da sauri. Naseer biye a bayan ta ya na dariya.
Wata dalleliyar mota ta ga ni 'kirar camry2021 ba'ka sai 'daukar idanu take yi ta na she'ki. Gaban motar ta isa ta na shafa ta cikin tsananin farin ciki. Cikin zuciyar kuwa cewa ta ke,
"Ashe ni ma zan shiga mota nawa na kai na in tu'ka".
"Kwarai kuwa gashi ma a gaban ki. Na ki ne, halas malak".
Da wani irin farin ciki na nufe sa tare da rungume shi ka na ta fashe da kuka mai sauti.
Bayan ta ya shiga bubbugawa tare da fa'din,
"Ya isa haka. Haka ake nuna farin cikin? Ni dai gaskiya ba ta wannan sigar na ke so ba. A min wani abun daban".
"Fa'di duk abunda ka ke so yallab'ai, ni kuma na yi maka al'kawarin yi maka shi yanzun nan".
Saitin kunnan ta ya kai bakin shi sannan ya furta mata.
"Ke na ke bu'kata yanzun nan".
"Idan dai wannan ne, an gama yallab'ai. Ai ni 'din ta ke ce".
"To ki je ki bu'de motar ki ga cikin ta mana. Nan da Sati 'daya ni da kai na zan koya maki mota".
Kiss ta manna masa a kumatu kana ta nufi wajan motar tare da bu'dewa ta shiga wajan zaman driver.
"Yallab'ai aron wayan ka please" fad'in Mufeeda.
Wayar ya mi'ka mata. Ita kuma ta dunga 'daukar kan ta a waya sannan ta fito daga motar ita ma tai ta 'daukar ta.
Cak Naseer ya 'dauke ta re da fa'din,
"Bar 'daukar hoton nan, muje aji dani".
Sama ya nufi da ita tare da kullo 'kofa.

********
Da daddare Mufeeda ta tura hotunan da ta 'dauka a wayan Naseer ta saka a status tare da kwararowa mijin na ta addu'a da kuma 'karin bu'di.
Mashkura ce ta fara gani, aikuwa ta zabura ta mi'ke ta na 'kara zooming 'din hoton. Sharr sai ga hawaye a idanuwan ta.
"Wallahi ba zai yu ba". Ta fa'da da 'karfi.

🖤🖤🖤🖤🖤🖤
Washa gari takwas a gidan Mufeeda tai mata, lokacin ko minti talatin Naseer bai yi ba da barin gidan zuwa banki. Kasancewar shine manajan bankin.
Jefar da gyalan ta Mashkura tai tare da fa'din,
"Sai naga abun alkhairi a status".
"Ke dai bari Mashkura, wallahi ni kai abun a mamakance ya zo min. Masara gasassa na ce ya sayo min, to da ya sayo, I a yaga ledar sai ga key 'din mota".
Mashkura kallo ta dunga bin Mufeeda da shi tare da fad'in,
"Rabin rai ba dai har ba YI 'diya ko 'dana ba".
Dariya Mufeeda ta YI tare da fa'din,
"Aiko kinyi, domin 'diyar ko 'dan ki ne su ka jawo min wannan kyautar arzikin". Fa'din Mufeeda.
"Ahh alhamdulillah, su Mufeey za'a zama uwa. Congratulation. Ki ce Naseer na son haihuwa?".
Zaro idanu Mufeeda ta ji tare da fa'din,
"Wallahi *KURA* ban ta'ba ganin mai son haihuwa kamar yallab'ai ba, shi fa bai 'ki duk shekara bai ta haihuwar 'yan biyu ba".
Wani irin munafukin murmushi Mashkura ta saki tare cewa cikin zuciyar ta,
"Anzo dai² wajan, wallahi sai na sa kin kwashi kashin ki a Hannun ki. Sai kin yi nadamar zuwan ki duniya. Sai na rusa 'dan 'karamin farin cikin da kike ta'kama da shi.
Amma a zahiri sai ta ce,
"Ahh da gaskiyan shi, masha Allah". Daga nan Mashkura ta sauya zancen zuciyar ta fal farin ciki.


*MAFARIN LAMARIN*



HMMMM ku biyo ni gobe don jin *MAFARIN LAMARIN* idan naga ruwan comments.


*MAMAN UMMEE*
*AKA*
*MATAR SAYYADEE✍🏼*
*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*


Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*_PAGE 39_*

Tun daga wannan rana Mashkura ba ta 'kara zuwan gidan Mufeeda ba sai da aka kwashi sati biyu.
Ko da ta zo 'din ma ba ta jima ba ta koma gida. Sai dai fa tun da ta zo wayar Mufeedan ke hannun Mashkura ta tare da sanin Mufeeda ba, domin sai ta shiga kitchen ta ke 'dauka ko kuma idan ta haura sama.
Cikin Mufeeda ba mai irin laulayin nan ba ne, sai dai ta na za'ben abinci. 'Dan wake ne ya koma abincin ta da kuma Pepsi mai sanyi.
Wata ranar lahadi, Naseer zaune, Mufeeda ta yi filo da cinyar shi ta na cin gya'da dafaffa, shi kuma ya na mata tsifa.
Wani irin zabura tai tare da ri'ke marar ta ta ce,
"Wash! Inna lillahi wa inna ilaihirraju'un".
Ru'dewa Naseer yai ya na tambayan ta lafiya.
Ka sa ba shi amsa tai ta na ta mur'kususu a nan tsakiyar 'dakin.
Da gudu ya haura sama tare da 'dauko keyn motar shi tare da cicci'bar ta da har jini ya soma bin jikin ta.
Lokacin da suka isa asibiti har Mufeeda ta fita daga hayyacin ta. Kar'ban ta akai emergency.
Sun shafe kusan awa 'daya a kan ta, kamin su ka ceto ran ta, kana su ka kai ta 'dakin hutu.
Dr ne ya fito tare da kiran Naseer 'din akan ya same

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login