Showing 108001 words to 111000 words out of 115393 words
na shaida mata komai. Aikuwa tuni ta aminci. A take na rubuta mata check na million 3. Jikin ta na rawa tai duk abun da ya kamata ka na ta na'do jaririya ta kawo mana. Har zamu bar asibitin, sai kuma nai wani tunani na koma na cewa nurse 'din duk yadda za'ai zuwa gobe ina bu'katar hoton asalin mahaifan yarinyar nan don cikin kwanan uku zamu bar 'kasan. Aikuwa kamar yadda na bu'kata, washa gari sai ga hoton mahaifan yarinyar nurse 'din nan ta kawo min. Ya na kawo nan da maganar shi ya fashe da kuka tare da 'kara dam'ke hannu na ya cigaba da fa'din,
Washa gari muka 'dauki hanyar Kaduna a mota na, daga nan muyi abuja don acan zamu hau jirgin *DUBAI* daga can mu yi India. To a hanyar mu ta zuwa Kaduna ne muka gamu da wannan hatsarin, cikin mu jaririyar ce kawai ko kwarzane ba tai ba, amma mu ka na kallon mu kasan lokaci muje jira
Bawan Allah dan girman Allah taimako 'daya zaka mun, ga wannan envelope komai ya na ciki, don Allah duk daran da'dewa ka kai wannan yarinya wajan asalin mahaifan ta, sannan ka ro'kan mun gafarar su duk da nasan da wuya su yafe min. Ya na kawo wa nan da maganar sa ya dan'ka min wannan envelope, sannan ya kalli nurse 'din da ke gyefe na tare da fa'din ki bashi yarinyar. Dawo da idanun shi yai gare ni tare da sakar min murmushi tare da fa'din nagode. Tun da ya fa'di hakan, komai na jikin shi ya tsaya cak. Allah ya kar'bi abun shi.
Sosai hankali na ya ta shi, haka na fito hannu na ri'ke da wannan envelope ita hawaye. A lokacin ni kuma nurse ta kira ni ta shaida min sai ha'kuri mata na ta haihu sai dai 'yar ba ta zo da rai ba. Hankali na ya tashi, domin muma mun da'de muna nai man haihuwa Allah bai ba mu ba. Kuma gashi doctor ya shaida min mahaifar mata ta ta samu Matsala ba zata sake haihuwa ba. Na shaidawa matata komai game da jaririyar a nurse ta kawo min. Ita kuma ta na ganin yarinyar ta ce Allah ya 'dauke mata wata ne ya kawo mata wata ta wani hanyar daban.
Mun shaidawa jama'a mata na 'yan biyu ta haifa amma 'daya ba ta zo da rai ba, wannan shine dalilin da ya sa babu Wanda yasan cewa Mufeeda ba 'diyar mu ba ce ta cikin mu. Kuma tunda bawan Allahn nan ya bani wannan envelope, ban ta'ba bu'de shi ba, balle na ga abunda ke ciki. Mun cigaba da ri'ke Mufeeda tamkar mine asalin mahaifan ta ba tare da nai man asalin mahaifan ta ba". Mal Ahmadu ya 'karishe maganar da fa'din
"Dan girman ku yafe mana, na cutar da ku, duk da nasan akwai wasu baya nai da wata'kila idan na bi zan iya sadaku da 'yar ku. Amma sai nai son kai na ri'ke ta a waje na don 'kaunar da na ke mata". Sosai mal Ahmadu ke kuka shi da matar shi.
Inna Huwailah ta ce,
"Kai bawan Allah ban fahimci maganar ka ba, ka na nufin ita Nasifar ba 'diyar ka ba ce? In dai ko ba 'diyar ka ba ce, to wabillahi Nasifa jika ta ce 'diyar Aliyuu ce".
Small daddy, Mufeeda da Naseer kano a tare su ka mi'ke tsaye.
Small daddy ya ce,
"Wallahi tun da na ga yarinyar nan nasan akwai wani ala'kar jini tsakani na da ita, ashe 'diya ta ce. Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un".
Mufeeda kuwa kallon su ta dinga yi kamar wata sha tara, can ta saki wani irin tsumamman kuka tare da fa'din,
"Baba, mama, ku na nufin ku ce min ba Ku ne asalin iyaye na ba?".
Fatima ta mi'ke tare da ru'ko Mufeeda ta ce,
"Kwarai Mufeeda, ba mune asalin iyayan ki ba". Sai ta nuna Ummu Nah (Umaymah) tare da fa'din,
"Ita ce mahaifiyar ki ta asali". Sai ta kuma nuna small daddy (Alhj Aliyuu) ta ce,
"Shine mahaifin ki, mahaifiyar Naseer kuma, 'yar mahaifiyar ki ce uwa 'daya uba 'daya. Shikuma mahaifin Naseer, kawu ya ke a wajan ki, domin da mahaifin mahaifiyar ki da mahaifiyar shi, uwa 'daya uba 'daya su ke. Duk nan 'yan uwan ki ne, ki na cikin dangin ki ne".
"Kwarai ki na cikin dangin ki, domin nan gidan dai dangin mahaifiyar ki ne, su kuma 'yan kano dangin mahaifin ki". Fa'din daddyn Naseer.
*SAI KUN 'KARA HAKURI DA NI, DOMIN DAI HAR YANZU FAMA MUKE DA RASHIN NETWORK, SANNAN JIKI DA JINI KUMA. AMMA KU NA NAN MA'KALE A RAI NA. SAURA NA JI KIN YI WATA MAGANA @DARMA DON NA SANKI DA SHEGEN ZOLAYA😜*
*MATAR SAYYADEE CE* 😍😍😍😍
[10-31 2:19 PM] Mai Daddawa: 🪄🪄
*NI DA SHI ABU 'DAYA NE*
✨✨✨✨✨✨
💫💫💫💫
🪄🪄
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️
( *Home of qualities and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*NARRATED & WRITTEN BY*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM*
( _*MATAR SAYYADEE*_)
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 50_*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
A gabanta ya tsaya, sai da ya kalleta na kusan second goma, kana ya du'ka bisa guiwowin sa tare da fa'din,
"Mufeeda nasan babu abunda zan miki da zai dawo da 'kima da mutuncina a idanunki, amma abu 'daya nake so ki sani, wallahi tallahi duk abunda nai miki ba cikin hayyacina nake ba, ke kin san irin 'kauna da soyayyar da nake miki, wallahi asiri ba karya bane. Juyamin tunani na tayi".
A zafafe Mufeeda ta juyo tare da fa'din,
"Enough Naseer! Idan abunda kazo fa'damin kenan, to ja tsummar rayuwarka ka barnan, ban son jin tatsuniyar ka".
Hangane baki Naseer yai tare da kallon ta, domin yaune karan farko da yaji ta ambaci sunan sa, zai iya cewa iya tsayin rayuwar da suka yi bai ta'ba jin ta ambaci sunan sa ba, sai dai tace, yallab'ai ko kuma Habibi Da'iman.
Gittashi tai zata wuce, yai saurin mi'kewa tare da 'kara shan gaban ta ya kuma aza guiwowin sa a 'kasa kana ya ce,
"Naji duk abunda ko kika ce, amma ina son ro'kan alfarma guda a wajanki, don soyayyar da Allah ke wa manzon sa (SAW) ki gafartamin duk abunda nai miki ba tare da sanina ba". Ya fa'di hakanne wasu zafafan hawaye na zubo masa cikin idanuwan sa. Ayaan na ganin mahaifin sa na hawaye, sai ya fashe da kuka tare da rungume mahaifin nashi, Abid ma yazo da gudu ya fa'da jikinsa shima ya saki nashi kukan.
"Kin gani ko? 'Ya'yan mu suma suna tayani ro'kar gafarar ki".
Itama hawayan ne ya taho mata, amma sai tai jarumtar mayar dasu kana ta ce,
"Ka tashi na yafe maka, Allah ya yafe mana muna".
Mi'kewa yai tare da fa'din,
"Nagode Allah ya saka miki da alkhairi".
Batare da ta 'kara cewa komai ba, ta juya da sauri ta shige part 'din Mama Fatima wasu hawaye masu 'dumi na zubo mata a kan fuskan ta.
Tunda ta juya ya kafeta da idanuwa har ta b'ace masa da gani, kana ya saki sanyayyiyar ajiyar zuciya tare da kama hannun su Ayaan su kai part 'din Mama Fatima domin yaje ya gaida ta.
Ita kuwa Mufeeda da man tasan zai shigo, sai bata tsaya a parlour ba, kai tsaye ta wuce 'dakin ta. Ko su Irfana da suke mata magana, bata kula su ba.
Sallama yai tare da tura 'kofar ya shigo, Irfanan, Husna, da Shahida suka ruga da gudu suka rungume shi suna fa'din,
"Oyoyo daddy".
Rage tsayinsa yai tare da rungume su a jikin sa yana mai jin tsantsan 'kaunar mahaifiyar su da ta haifo mashi su.
"Ina kaka?" Naseer ya fa'da yana shafa kan Shahida.
Batare da Shahidan tayi magana ba ta juya da gudu tai 'dakin mama Fatima. Tare suka fito tana jan hannun ta har suka iso tsakiyar parlourn.
"A'ah Naseer kai ne? Sannu da zuwa. Ya wajan su maman naka?".
"Lafiya 'kalau. Ina wuni Mama?".
"Lafiya kalau alhamdulillah, ya aiki da kuma jikin na ka".
"Alhamdulillah naji sau'ki ai mama". Fa'din Naseer.
"To Allah ya 'kara sauk'i, bari na kawo maka abinci".
"A'a Mama alhamdulillah. Dama nazo gaisheki ne, yanzu haka ma jirana Kabiru ya ke yi zamu fita".
"To shikenan, bari na kira Mufeedan ku gaisa".
"A'ah mama ki barta ai mun gaisa, yanzu ta shige ciki".
"To shikenan nagode, a gaida Kabirun".
"Zaiji" Naseer ya fa'da tare da mi'kewa ya matsar da Ayaan dake kan jikin shi kana yace,
"Zanje in dawo anjima, mai zan sayo maku?". A tare suka ha'da baki wajan fa'din "Chocolate!".
"Shafa kawunan su yai tare da fa'din, "To kuyi min addu'a in sha Allah, zan tawo maku da shi".
Tsalle suka shiga yi su na fa'din "Allah ya caye (tsare) dayi (daddy)".
*KANO*
Allah shine mai iko mai kuma gyara wadda yaso a duk lokacin da yaso. Domin kuwa idan kaga Baby bazaka ta'ba cewa itace mai shaye shayen nan ba da, domin yanzu wani natsuwa ya shige ta tare da girma, dama a wancan lokacin harda 'kuruciya da kuma rashin mai tsawatarwa ta saka ta lalace. Tun shigowar Lukman rayuwar, ta fara canzawa, domin bai barta haka ba. Duk da ya koma *GERMANY*, kullum ma'kale suke a waya ko kuma video call yana nusar da ita illar shaye² da kuma gutsiri tsoma. Sosai Baby kanyi dariya ita ka'dai duk lokacin da ta tuna da fa mutum bai isa yai wata maganar sirri a gaban ta ba, domin idan mutum yai haka kamar a gidan radio vision yayi maganar sa. Takan yi dariya sosai idan ta tuna fa'duwar da tayi har bakin ta ya kumbura don tsabar gulma na cinta bata kula da hakan ba don kawai ta kai gulma tare da 'kara gishiri a miya. Ta kan 'daga hannu sama ta godewa Allah akan yaye mata wannan cuta ta gulma da take da shi, domin da tai aure da shi ba 'karamin wahala zata sha ba.
Wai Baby yanzu ita kewa Mummy nasiha akan wasu abubuwa da ta ke yi a bai kamata ba musamman akan hajiya Zulfah don baby yanzu ta zama 'yar gidan Hajiya Zulfah wanda hakan ya 'kara wutar 'kiyayyar Hajiya zulfan a zuciyar ta, don ita har yanzu bata sauko ko saduda akan 'kiyayyar da ta ke wa Hajiya Zulfah ba. Don a ganin ta asiri taiwa duk 'ya'yan ta da mijin ta suke 'kaunar ta.
*GERMANY*
Tunda alhaji Aliyu (mahaifin Mufeeda) ya ga tsohuwar matar sa, yaji wani tururin 'kaunarsa ta dawo mata sabuwa dal a zuciyar sa, sai dai kash ta dawo masa alokacin da ta haramta a gare sa. Wannan dalilin ya sa yaji ba zai iya 'kara tsawon lokaci a Nigeria ba, tuni ya tattara yanasa² ya koma Germany. Sai sai wannan karan Inna Huwaila ta ce, ko ya naimi aure ko kuma ta la'ance sa tare da 'debe masa albarka. Abun mamaki kuma Inna Huwaila sai ta masa tayin Baaba Habiba, kasancewar baaba Habiba ba wata babba bace, bazata wuce sa'anar Hajiya Zulfah ba. Kuma cikin ikon ubangiji bai'ki tayin nata ba, domin shi idan aka ce masa ya naimo matar da kansa, bai san ta inda zai fara ba. Hajiya Zulfah da Mufeeda kuwa da suka ji labari, ba 'karamin da'di sukaji ba. Alhaji Aliyu bai bar Nigeria ba sai da igiyar auran Baaba Habiba, kuma tare suka wuce shi da matar sa. Kuma alhamdulillah suna zaune lafiya, idan kaga baaba Habiba sai abun ya baku mamaki. Domin kuwa ta goge fatan jikin ta yai lugui² gwanin ban sha'awa, dama can harda talauci ya fito da tsufanta, amma a zahiri ba wata babba bace can, domin idan tayi wuta ta kai 43. Kuma alhaji Aliyu yana matu'kar jin da'din zama da ita. Don ta iya kula da miji da kuma tarairayar sa. Ta mai da shi kaman wani 'dan 25years. Naina gidan ta take wuni kasancewar basuda wani nisa tsakanin su. A wajan Baaba Habiba da ta koma Habibaty a wajan alhaji Aliyu, Naina ke 'kara koyar course na kula da miji. Baaba Habiba ce ta 'kara wayar mata da kai matsanaicin kishin da take nunawa akan mijin nata. Ta nuna mata shi kishi halas ne, amma idan yai yawa yana zama hauka kuma yanasa miji ya tsani matarsa. Ta nuna mata ta ri'ka danne kishinta akan wasu abubuwan.
..............shirya shiryen biki dai ya kankama, domin dai yanzu su Ayaan sun kusa wata takwas da yaye. Domin magana wajansu kamar uwar aku. Abunda yasama ba'ai bikin tuntuni ba, Naseer 'din ne ya tafi course *INDIA* na wata shidda, SAI aka sanya bikin wata bakwai akan da ya dawo da wata 'daya sai biki. Su lukman kuwa lokacin da aka ce an saka biki wata shidda ji yai kamar yai bombing domin a gaskiya ya gaji da jira, gashi Inna Huwaila ta ce dole ha'da bikin za'ayi. Kuma tace idan ya saki ya 'kara mata 'korafi sai ta la'ance shi kuma ta soke auran nashi gaba 'daya. Tunda Lukman yaji haka, bai 'kara kallon hanyar jigawa ba domin yasan wannan ka'danne daga cikin aikin Inna Huwaila ta aikata abunda tace 'din.
Yanzu biki dai ya rage kwana goma sha shidda. Da farko dai Inna Huwaila ta saka daru akan dole fa Nasifa (Mufeeda) ta dawo nan kano, da kyar da su'din goshi alhaji Mudassir ya lalla'bata akan tai hakuri ai bikin a can Kaduna gidan iyayan ri'kon naka, hakanne zai saka suji da'di akan ba'a nuna musu fin 'karfi da isa ba. Hakanne ya saka ta amince tunda dai gaba 'daya Mufeedan ai kano zata dawo da zama.
*KADUNA*
.............Naseer duk da ya tabbatar Mufeeda ta haramta a garesa, ba zai yu su sake zaman aure ba tunda saki uku ya mata. Amma hakan bai saka shi shiga mugun tashin hankalin da ya jawo masa tashin hawan jinin sa ba. Sosai ya shiga rashin lafiya, KB ne ke tausarsa, duk da a baya ya shiga sahun masu fushi da shi sakamakon basusan duk abunda ya aikata ba cikin hayyacin sa bane, shike kwantar masa da hankali. Dama tuni mommah da daddy sun ha'kura sun sauko daga dokin fushin da suka hau. Daddy ya mayar masa da duk abunda ya kwace nashi, sannan ya saka an mai da shi a wajan aikin shi, dama shi yasa aka dakatar da shi sannan ya ce su suna korar sa su kai gaba 'daya saboda rayuwa ta koya masa hankali. To tunda ya gane duk abunda ya aikata aikin sihiri ne, said ya yafe masa ya kuma mayar masa da komai nasa.
Tattarawa yai gaba 'daya ya koma gidan Ummu nah da zama, ita ke lallashinsa tare da nuna masa komai mu'kaddari daga Allah. Ta ce masa ya 'dauki dangana tare da fidda Mufeeda a ransa, Allah zai musanya masa da wacce ta fita. Amma fir ya'ki amincewa da shawarar ummun. Kullum cikin kuka da tunani, aikin ma hutu ya 'dauka domin ko yaje bai iya aikata komai. Takai takawo da yayi tari jini ne ke fita daga bakin shi. Ranar da Ummu Nah ta fara ganin jinin da ke fitowa daga bakin Naseer kusan 'karamin hauka ta kusa YI, ta gigice ta shiga tashin hankali. Asibiti sukaje aka bashi taimakon gaggawa. Likita ya fa'da masu a gaskiya Naseer ya saka wani abu cikin ranshi da ya haifar masa da ciwon zuciya. Kuma lallai idan bai daina tunani ba, to zuciyar sa zata buga. Da Mommah taji haka sai da ta 'buya tai hawayen tausayin 'dan nata. Ummah ko duk ta bi ta rikice har ta yanke wani tunani cikin ran ta. Kai tsaye kuma ta naimi shawarar mijinta, kuma shima ya bata goyan baya 'dari bisa 'dari.
Kwanan Naseer shidda a asibiti, lokacin bikin Mufeeda saura kwana goma.
Amarya Mufeeda sai gyara take sha ta ko wani 'bangare, Mommah tayi, mama Fatima tayi. Gyaran da take sha ko auranta na farko bata sha shi haka ba. Maganin sanyi kuwa dama tun biki saura wata 'daya aketa 'dirka mata su kamin nan maganin gyaran jiki ya biyo baya. Tuni Ayaan, Abid da Husna suka koma gidan Mommah gaba 'daya. Yayin da Irfana takwaran mama Fatima