Showing 1 words to 3000 words out of 115393 words

Chapter 1 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22941

[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*

*🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟*



('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
ىtɷɾʏ aŋɖ wɾɩttҽŋ bʏ ʑųɭʆa'ų ىa'ҽҽɖ ɩbɾaɧɩm
ѧҡѧ mamaŋ ųmmҽҽ 😘
ѧҡѧ aųŋtʏ ʑųɭҽҽʏ 💖
ѧҡѧ mataɾ ىaʏʏaɖҽҽ👌


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )

ҍíՏʍíӀӀɑհíɾ ɾɑհʍɑղíɾɾɑհíʍ.
Godiya ga Allah SWA da ya ba ni ikon fara rubuta wannan littafin. Allah na ke ro'ko yadda ya ba ni ikon farawa, ya ba ni ikon kammalawa lahiya. Ameen.



*PAGE 1*


Fuskan ta ca'b-ca'ba da 'kuraje, ga uban 'katotan ciki a gaban ta kamar ka ce kyat ta haihu. 'Kafafuwan ta sun yi wani uban kumbura, wuyar ta kamar mari'kin lema saboda tsabagen rama.

Le'ban ta sun bushe duk sun farfashe kamar wacce take rayuwa a Sahara.

Zaune take akan sokawe tana wanke gajerun wanduna da singiletin mai gidan ta. Idan tayi wankin tai wankin, sai ta sake ta cije le'be ta shafa bayan ta.
Wani irin bugun 'kofa ake yi kamar za'a 'balle kofar gida Wanda ya saka tai muguwar razanar da sai da abunda ke cikin ta ya dun'kule waje 'daya. Ba kowa zai Mata bugun 'kofar nan ba fa ce Naseer wan da ta mishi la'kabi da Mr Right, Habibi Da'iman, Heaven sent ko kuma 'yallabai. Duk ta na kiran sa da wa'dannan sunan aduk lokacin da ta ga dama.


"Wallahi na irga uku
baki zo kin bu'de min kofar nan ba, na lahira sai ya fiki jin da'di tsinanniyar mata kawai".

Naseer ne ya fa'di hakan da wata irin fusatacciyar murya.
Kirjin ta ne ya bugu, wani irin tsoro ya lullu'be ta, kasan zanin ta ta kalla sabida wani sanyi da taji, sai ta ga ashe fitsari ta Saki. Da kyar ta iya yun'kurawa ta mi'ke ta na dafa bango ta isa har kofar gidan ta bude.

Gashin kan ta ya dam'ko da 'karfi idanuwan shi sun ka'da sunyi jazur. A matukar fusace ya ce,

"ke dan kutumar uban ki dama maza kike bi? Wannan abun da ke cikin ki ba ni ne uban sa ba, ko ki fa'di min uban cikin nan ko kuma in kusan kashe ki anan gidan, kuma ba uban da zai tambaye ni dalili".

Wani irin jiri taji ya na 'diban ta saboda abunda kunnuwan ta ya jiye Mata, wasu zafafan hawayan ba'kin ciki ya wanke fuskan ta da ya yi ba kyan gani saboda 'kuraje, muryan ta na rawa ta ce,

"Wallahi wanna cikin naka ne, jinin ka ne, ban ta'ba sanin wani 'da namiji a rayuwa ta ba sama dak..."
Wani irin wal'kiya ne ya gifta a idanun ta, kunnuwan ta suka mata wani duuumm, can kuma ta fara jin kukan tsuntsaye. Dafe kuncin ta ta yi tare da sakin wani marayan kuka ta ce,



"'Yalla'bai kar Kai min haka, a tunani na duk duniya idan akwai Mai ba da shaida ta to Kai ne, ka sanni, ka San ko ni wacece ka kuma San halina".
"Karya ki ke yi karuwa, 'yar iska kawai, wacce ta zubar da 'Kimar ta da aure a kan ta". da 'karfi ya fa'di hakan tare da 'kare dam'ke gashin ta ya ha'da ta da bango.
Ba ta San sanda ta Saki razanannan 'Kara ba ta rukunkumeshi.
Wani irin jifa ya yi da ita sai da cikin ta ya bugu da tiles din dake shinfi'de a tsakar gidan. 'Dif wuta ya dauke Mata, take kuma numfashin ta ya tsaya caak.
Naseer bai bi ta kan ta ba ya shige 'daki a matukar fusace, Kai tsaye bedroom ya shige ya jawo durowar mirrow ya dauki biro tare DA yago paper ya rubuta saki, sannan ya zaro belt a jikin wandon jeans din wandon shi ya fito daga bedroom din yai wajan fridge ya dauki pure water da har ya soma 'kan'kara ya fito ya fasa ruwan nan ya sheka Mata.
A matukar firgice ta farfa'do tare da wawware idanuwa tana 'ki'k'kifta su. Ba ta gama dawowa daga hayyacin ta ba ta ji saukar belt a jikin ta. Wani 'Kara ta Saki Mai uban 'Kara tare da ru'ko 'kafafuwan shi ta na fa'din.....



Kubiyoni dumin jin yadda wannan cakwakiyar zata kaya.

*Comment and share*



*MAMAN UMMI✍️*
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*


🌟NI DA SHI ABU 'DAYA NE🌟

('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
ىtɷɾʏ aŋɖ wɾɩttҽŋ bʏ ʑųɭʆa'ų ىa'ҽҽɖ ɩbɾaɧɩm
ѧҡѧ mamaŋ ųmmҽҽ 😘
ѧҡѧ aųŋtʏ ʑųɭҽҽʏ 💖
ѧҡѧ mataɾ ىaʏʏaɖҽҽ👌


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*PAGE 02*


"Kayi wa girman Allah ka dubi halin da nake ciki ka tausaya min, wallahi ni ba mazinaciya ba ce, duk Wanda ya fa'da maka hakan wallahi so kawai yake yaga ya raba mu, wallahi ban ta'ba bawa wani kai na ba, dan Allah ka dubi maraici na yalla'bai".


Maganganun da take yi ma kamar 'Kara tunzura shi ta ke yi, janye 'kafafuwan shi ya yi tare da fa'din,

"Ba'kar munafuka, kalle ki kamar ta Allah amma zuciyar ki fal mugunta ce da she'danci, to bari ki ji wallahi yau ko wa ya tsaya miki sai kin bar gidan nan, matsiyaciya kawai, Allah ya isa tsakani na da ke, kuma kije na sake ki Saki uku tsinanniya kawai".

Ya 'karasa maganar tare da jifan ta da takardan.
Wani razananniyar 'Kara ta saki, ba ta San ta na da saurin 'karfi a jikin ta ba sai da ta Gan ta a tsaye ta ri'ke shi gam ta na wani irin narkakken kuka.
Karfin shi ya saka ya ture ta a jikin shi, ba dadin Allah ya ba ta sa'a ta yi saurin ri'ke bango ba da ba 'karamin faduwa za ta yi ba.
Bu'de kofar gidan ya yi ya hanka'do ta waje ba kin ta sai da ya bugu da siminti, a take kuwa ya fashe ya kumbura yai fushi.
'Daga kan da zata yi taga ma'kota 'yan gulma dan'kam a kofar gidan ta, alamu ya nuna sun ji duk abunda ke faruwa Dan sun jima a wajan.
Shiko Naseer bai damu da mutanan da su Kai cirko cirko a wajan ba, ya hau laftar ta da belt 'din hannun shi tare da 'kumduma Mata ashariya ya na kuma aibatata.
Wata tsohuwa ce ta taho da dauri ta na fa'din,


"Nasuru ashe baka da mutunci ban sani ba, yarinya da tsohon ciki ka hau kilan ta har kwar gida jama'a na kallon ka, lallai anyi tujararran 'da a wajan nan. Halan ba uwa ce ta haihe ka ba?".

Har kusa dashi tazo ta fizge belt 'din hannun shi ta shiga zazzabga masa tare da an taya masa ashariya.
Har wani jiri-jiri take gani, ga jinin da ya fara bin 'kafafun ta, ta dafe bango ta mi'ke ta saka saurin 'karfin ta ta warce belt 'din da ke hannun wannan tsohuwar ta re da fa'din,
"Ba'aba Hansai dan Allah ki bar bugun sa, Ina ga wani abun aka masa a waje shi yasa ki ka ganshi a haka, ni Ina kaunar miji na, nasan zuwa anjima zamu shirya kan mu"
Galala Ba'aba Hansai ta yi ta na kallon ta, can kuma ta soma tafa hannu ta na sallallami tare da fa'din,

"Dama abun da ake hi'di akan ki wannan yarinyar (Sunan 'diyar ta ta fari ta ke da shi, shi yasa ba ta kiran sunan ta ) gaskiya ne? Lallai kin yi asara kuwa, Mai kika Mai 'da namiji? To ga ki nan gashi ai, shi zai yi ajalin ki dama ai iyayan ki ba damuwa su Kai da ke ba, sha sha shar yarinya".
A cikin 'yan gulma wata ta ce,
"To ke ma Ba'aba Hansai ana shiga hurumin Naseer da Mufeeda ne, gashi nan dai kullum cikin wahala ta ke amma ba ta so a fa'di aibin mijin ta".
'Daya ma tai caraf ta cafke ta ce,
"Ke ni dama ai sai dai nazo na bawa idanuwa na abinci, na kuma samu na fesawa 'kawaye na a islamiya ".
Ba'aba Hansai ta ce a fusace,
"To KO wacce ta wuce gidan ta ko kuma in ciwa yarinya uwayen ta wallahi"
'Daya bayan 'daya suka fara wucewa, dan kowa yasan masifar Baaba Hansai, amma ba haka suka so ba, sun so suga kwal uwar daka, wasun su ma komawa su Kai su na le'ke ta Katanga.
Shi ko Naseer sai huci ya ke yana aiyana irin rashin mutuncin da zai wa wannan tsohuwar Mai masa shisshigi a al'amuran shi.




_Idan kunji daɗi naji commet idan banjiba kowa ya huta🤗_



*Comment and share*




*MAMAN UMMI CE✍️*

[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*



🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.

*STORY AND WRITTEN*
By
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ sake)


*PAGE 03*

"Ke tsohuwa ki fita a harka ta wallahi, me ye ha'di na da ke ne kike min shishshigi a rayuwa ta? Wannan Mata dai tawa ce ba taki ba, ehe!".
Kalmar Mata da ya dangan ta Mufeeda da shi sai ya saka ta ji wani sanyi na ratsa zuciyar ta, ke nan ya janye sakin da ya mata, tunda gashi har ya na kiran ta da matar shi.
Tsohuwa Baaba Hansai kuwa ce wa ta yi,
"Lallai Nasuru Kai 'din ba ka da albarka, yanzu kalle ni na haihi uban ka ma ba Kai ba, amma har ka iya kallon tsabar idanuna ka fa'di min magana?".


"To tsohuwa da kin Kama girman ki zan zo har gidan ki in fa'da miki magana ne? Ke ce ba ki ri'ke girman ki ba, Ina ruwan ki da sha'ani na?".


Girgiza Kai tsohuwa ta yi tare da kallon shi ta ce,
"Kwarai ka na da gaskiya, amma ka je duniya za ta koya maka hankali, don tunda ba ka ga girman wacce tai sa'a da kakar ka ba, to iyayan ka na gida ma ba neman albarka kake a wajan su ba".

sai ta mai da kallon ta izuwa wajan Mufeeda ta ce,
"Ke kuma ki zauna har ya kashe ki wawuyar yarinya kawai, wa ya sani ko asiri ma ya miki".


"Mufeeda ta ce,

"ki yi hakuri Ba'aba Hansai ranshi ne a 'bace amma ya na da biyayya, kuma wallahi ba asirin da ya min, ni dai ina kaunar miji na har zuciya da 'bargo na."
Haushi ya saka Ba'aba Hansai 'kala ba ta 'Kara cewa ba tai hayyar gidan ta.
Naseer kuwa belt 'din shi ya 'dauka ya ci gaba da lafkar ta, ta na ihu har cikin ya ke saka 'kafa ya na duka. Sosai jini yake zuba daga 'kasan ta.
Da taga fa tabbas idan ta tsaya tabbas Naseer zai iya kashe ta, tuni ta soma rarrafe, duk da haka bai bar dukan ta ba har suka fito daga layin. Gashi Safiya ce ko wani magidanci ya tafi nemo na cefane balle ta samu 'dauki daga wani.
Wani magidanci ne ya fito daga gidan shi, idanun shi suka masa arba da abunde ke faruwa, da Sauri ya 'karaso wajan ya ce,


"Subhanallah, Malam lafiya? Ba ka da imani ne? Mace da ciki ga jini na zubar Mata amma kake dukan ta da belt".


"Malam ba ruwan ka, matata ce, kuma wannan cikin ba nawa bane, maza ta ke bi, acikin 'yan iskan da take bi wani ya mata ciki yau kuma asirin ta ya tonu, ba ka San halin ta ba ne, annamimiya ce, na tsane ta. Uwar ta da ta haife ta ba ta tsugunna ta haifi komai ba fa ce annoba, bala'i da masifa a doran 'kasa, wa ya sani KO uwar tata ma karuwa ce, a can wajan karuwan cin ta ta samo ta aka li'ka wa uban ta".

Tunda su Kai aure da Naseer ba ta ta'ba jin 'digon kaunar shi ya ragu a zuciyar ta ba, amma yau da ya aiba ta mahaifiyar ta a gaban wani mutumin har ya ke kiran ta da karuwa, sai taji duk fa'din duniya ba bu Wanda ta tsana sama dashi, ba ta ta'ba ganin mahaifiyar ta ba, amma labari yazo Mata akan mahaifiyar ta kamilar ma ce ce, wacce ake alfahari da ita kaf layin su har ake kwatance da ita a wajan sauran 'yan matan layi na wancan zamanin. Yau wani irin wutar 'kiyayyar Naseer ne ke yawo a zuciyar ta, ji take yi gwara SHAI'DAN da shi.
'Dago idanu ta yi ta watsa masa wani irin kallon 'kiyayya Wanda sai da ya razana, bakin ta har rawa yake yi wajan furta NA TSANE KA. DA 'dai 'dai 'dai maganganun suka fito.
Wani yarrr ya ji a cikin jikin shi amma wani irin haushin ta ya yun'kuro masa, ya yunkura zai dake ta, wannan mutumin yai saurin ri'ke shi ya ce,


"Aboki na ka bi komai a sannu, ka kasance mai bin cike kamin ka aikata Abu, idan ba haka zaka kasance cikin masu DA NA SA NI"
"DA NA SA NI!!! In dai akan wannan wacce uwar ta tai asarar haihuwar ta ne wallahi bazan ta'ba yi ba".

Naseer ya fa'din hakan kamar zai yi bindiga.


"Ni dai shawarar da zan baka idan zaka dauka, ka dauki matar ka kai ta asibi, idan ta haihu sai ai DNA test daga nan likita zai tabbatar maka da abun da ke cikin ta jinin ka ne ko ba naka ba ne, kaga daga nan sai ka dauki Mata ki, amma ba a yanke hukunci Kai tsaye".
"Kai Malam dakata! Ni ba na bu'katar shawarar ka, domin na tabbata cikin jikin ta ba nawa ba ne, kuma ma ni na riga da na sake ta Saki uku, ta Kama hanya ta tafi gidan su Ehe" .

ya na gama fa'din haka ya juya ya wuce.
Cike da mamakin rashin imanin Naseer wannan bawan Allah ya bi shi da kallo har yasha kwana, ajiyar zuciya ya sauke tare da dawo da duban shi ga baiwar Allah Mufeeda ya ce,


''Baiwar Allah sannu, bari na tsayar miki dq adai-dai ta ki tafi gidan ku iyayan ki suga halin da kike ciki, Allah ya saka miki ".
Mufeeda ba ta iya magana ba saboda azabar da take ciki sai 'daga masa Kai kawai ta yi.
Napep ya tsayar Mata, da kyar ta iya fa'di masa sunan unguwar su, wajan Shiga ma sai da wannan bawan Allah ya taimake ta. Bawan Allahn nan ya zaro kudi ya bawa Dan adai-dai ta tare da fa'din Allah ya raba lafiya.
A kofar gidan su ya sauke ta, da kyar ta iya fitowa daga napep 'din jini na bin ta. Girgiza Kai Mai napep din ya yi tare da jan machine din shi yai gaba.
Tun kafin ta 'karasa kofar gidan ya daka Mata wani uban tsawo ya na fa'din,


"Wallahi 'kafarki ta taka min dandamalin gida na sai na sabarta ki, shegiya la'ananna. Ooh wato shi mijin na ki ya koro ki sabida abun kunyar da kika jawo, shi ne ni zaki kawo min gida na. To wallahi ahirr 'din ki, ki zo ki wuce duk in da ma zaki ki tafi amma wallahi bazaki zauna min a gida na da cikin shege ba".
Mufeeda azaba ya ishe ta, domin na'kuda ne ya taho Mata gadan gadan, ga wa'dannan maganganun dake fitowa daga bakin 'kanin mahaifin ta da ya 'Kara jefa ta a tashin hankali. Kallan shi ta yi azaba na nu'kur'kusan ta ta ce,


"Baba Kai min rai, Ina zani a cikin wannan halin, wallahi Baba babu in da nake dashi sama danan, Dan girman Allah ka da ka kore ni"
Kan ta ya taho a fusace ya dinga kwa'da Mata Mari yana fa'din,


"Wallahi sai dai ki mutu amma ba gida na ba, don Mai zogala ma bazata Bari ki shiga cikin gidan nan ba, wallahi idan ma gidan karuwai zaki koma sai dai ki koma, amma bazaki shigar min gida ba".


Tuni mutane sun cika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login