Showing 33001 words to 36000 words out of 115393 words
su". Fa'din Naseer.
"To sai ka dawo".
Sai da Naseer ya 'kara kallon Mufeeda na kusan second goma sannan ya juya ya fita.
Doguwar ajiyar zuciya haj Zulfah ta sauke, sannan ta furta can 'kasa 'kasa yadda ita 'kadai za ta ji,
"Lallai akwai 'kurar da ke tunkaro gidan nan nan gaba. Allah ko ma menene ka sa ya zo mana da sauki".
*************
Ya na wanka, amma fuskar Mufeeda ya ke ga ni ta cikin mirror ba yin ta na masa tsadaddiyar murmushin ta. Wani sanyayyiyar murmushi ya saki ya na 'karewa kan shi kallo a jikin mirror.
"Ba'kin fata da farar fata". Shi ne abun da Naseer ya furta tare sakar wa kanshi shower.
(Hmmm Naseer ke nan)
Bayan ya fito daga bayi ya kimtsa jikin shi, kai tsaye part 'din mahaifiyar sa ya nufa jikin shi a sanyaye. Cikin zuciyar shi ya furta,
"Ke ka'dai zaki kawo min cikaas, amma in sha Allah sai na shawo kan ki".
Ba kowa a parlour, kai tsaye ya haura sama. Sallama yai tare da tura kofar da'kin a hankali.
Kwance ta ke a kan makeken royal bed 'din ta , idanun ta a rufe. Amma jin 'karar 'kofa sai ta bu'de idanuwan ta da su kai jazur kamar garwashi ta sauke a kan shi. Juyar da kan ta tai idanun ta na zubda hawaye. Da sauri ya 'karasa wajan ta sabida hawayan da ya ga ni ya na zubawa a idanun ta.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Mummy wallahi hawayan ki masifa ce a gare ni. Don girman Allah ka da ki jefa ni a halaka. Ki yafe min". Sai ya fashe da kuka tare da ru'ko hannun ta.
"Naseer ni zaka wa haka? Naseer ni? Ni? Ba ko mai. Zulfah ta fini a wajan ka".
"Mummy Wallahi babu wacce ta fi ki a waje na. Dan girman Allah ki dai na zubda hawayen ki. Na ro'ke ki".
"Naseer a kan ka mahaifin ka ya ke cewa zai rabu dani rabuwa na har abada. Naseer kai da kan ka ka 'dauko abunda zai yi sanadin rabuwa ta da mahaifin ka. Naseer wani irin soyayya ce ban nuna ma ka ba! Har 'yan uwan ka 'korafi su ke a kan na fi nuna son ka a kan su. Amma ni zaka watsawa 'kasa a ido ko Naseer".
Sosai Naseer ya ke kuka, ya ce,
"Mummy ki fa'di abunda kike so, ni kuma in sha Allah zan yi miki shi. In sha Allah kin dai na hawaye a kai na daga yau".
Tashi haj Jummai ta yi ta zauna tare da kamo hannun shi ta ce,
"Naseer so na me ka fita har kan wancan matan da kuma yarinyar can da ka 'dauko da sunan taimako... Ba na so ka 'kara cin abincin ta, ka dai na shiga 'dakin ta. Idan ka min haka, ni kuma zan dai na zubda hawaye na a kan ka, idan kuwa ka kasa min haka, bazan yafe maka ba".
A ki'dime ya ke kallon ta, can kuma ya saki wani irin ajiyar zuciya mai 'karfi tare da sunkuyar da kan sa ya na zubda hawaye masu 'dumi. Cikin zuciyar shi kuwa cewa ya ke,
"Mummy mai ya sa zaki min wannan mummunar katangar a lokacin da na tsunduma a 'kaunar Mufeeda".
Ture masa hannu ta yi tare da fa'din,
"Dama na sani, ai na sani. Ba za ka ta'ba iyawa ba. Zulfa'u ta riga ta asirce min 'da".
Kamo hannun ta ya yi tare da fa'din,
"Sam ba haka ba ne mummy, Ummah ba ta asirce mi ki ni ba, ni 'din na ki ne. Kuma zan cika miki abunda ki ka zayyano. In sha Allah zan kiyaye duk abunda ki ka fa'da. Sai dai ina so ki min wata alfarma guda 'daya".
"Ina jin ka fa'di alfarman da kake so na maka, idan har zaka fita harkan Zulfa'u, ni kuma zan maka wannan alfarman". Fa'din haj Jummai.
Ajiyar zuciya Naseer ya sauke tare da fa'din,
"Naji na aminta da shara'din ki, sai dai zaki min alfarmar shiga 'bangaran domin gaishe ta kawai. Kuma na miki al'kawarin bazan sake cin abincin ta ba".
Rungume shi ta yi, tare da fa'din,
"In dai wannan ne na yi maka, auta na. Kuma na dai na fushi da kai. A kwai wani albishir da zan fa'da maka, yayan ka JAWAD ya na hanya gobe". (Jawad ya na tare da 'kanin mahaifin su (ALIYU) wanda suke kirq da small daddy da ke 'kasar *GERMANY* Shi ma a can ya ke aiki, matar shi 'daya mai suna *Naina* a can GERMANY suka ha'du, iyayan ta mazauna can ne. Small daddy ne ya shige mass gaba har akai auran. NAINA irin Mayan nan ne masu bala'in kishi. Ko Kusa ba ta Kaunas wata ta ra'bi mijin ta, ko da yaushe ta na na no'ke da shi har office ta ke bin shi, ya na duba patients, ta na gyefan shi. 'Dan su 'daya *Ahmad*. Kasancewar jinin su ya ha'du da 'kanin mahaifin na su shi ya sa ya gudu can wajan shi. Shi ma doctor ne.).
Da "To" kawai ya amsa mata. Don gaba 'daya ma ya dai na fahimtar maganfanun ta. Kan shi ne ya ke wani irin sara masa ga wani zazza'bin lokaci guda da ya dirar masa. Mi'kewa ya yi ya na jin wani irin jiri na 'diban sa. Ya ce,
"Mum ba ri na je 'da ki na huta. Ban ji ma da dawowa ba".
"To Auta na, je ka huta".
Ficewa yai daga 'dakin zuciyar shi na masa wani irin suya.
Tun haj Zulfah na zuba idanun ga nin Naseer, har ta cire ran ta, duk tunanin ta bacci ne ya kwashe shi. Sabida ta San akwai gajiya a tartare da shi.
Shi kuwa Naseer na can kwance a 'dakin shi, sai ku ka ya ke kamar 'karamin yaro ba bu mai lallashin shi.
*WASHA GARI*
Yadda Naseer ya ga rana, haka ya ga dare, don Sam ko runtsawa bai ba. Misalin 'karfe uku, daddy tai kiran sa a waya akan yazo 'dakin haj Zulfah ya same shi yanzu. Sai da gaban shi tai mummunar fa'duwa, ba don komai ba sai don bai son ya ga fuskar Mufeeda, don ya tabbatar ya kamu da 'kaunar ta mai zafi. Haka nan ya mike don cika umarni mahaifin na shi. Ka na ganin shi kasan wani abu na damun shi. Abunka da mutumin da ya saba faran faran.
Fitowa yai daga side 'din sa ya nufi na haj Zulfah gaban shi na bugawa. Sallama gai tare da mur'da handle 'din ya shiga. Ai kuwa reras ya same su a da'kin. Daddy zaune akan center carpet quintuplets zagaye da shi a cikin gadon jariran su. Haj Zulfah zaune gyefan shi na dama. Baaba Habiba kuwa zaune kan 3sitter ta zubawa talabijin idanu. Ya yin da sanyin idaniyar ta sa ke zaune kan 1sitter cikin wata doguwar rigar shadda kalar baki an mata aiki da purple 'din zare. Ba wani kwalliya ba ne a fuskan ta, amma ba 'karamin kyawu ta yi ba. Wani series film ta ke kallo da ake haskawa a tashar *NOVELA E*. Gaban sa ne ya bugs da 'karfi, don ji yai kamar an 'kara da'ba mass 'kahon kaunar ta a zuciyar sa.
Dur'kusawa yai tare da fa'din,
"Daddy, Ummah na ina yini?". Haj Zulfah ce kawai ta amsa, daddy kuwa zuba masa idanu ya yi.
"Mai ke damun ka Son?".
A bazata tambayar ta zo masa. Amma sai ya sai sai ta kan sa tare da fa'din,
"Daddy tun da na dawo jiya, kai na ke wani irin sara min Lamar zai rave gida biyu".
Wani irin juyowa Mufeeda tai tare da zuwa masa idanu. Card idanun su ya ha'du da na juya. Tai saurin janye na ta.
"Asshsha! Da ma sai da na tunanin haka wallahi. Tun da naga Baka dawo jiya ka ci abinci ba na ce, ko bacci ka ke, ashe ma lafiya ce ba ka da ita. Allah ya sawake. Ka je asibiti a duba ka a back magani".
"Zan can asibiti kuma ai ya 'kare tunda ga 'dan uwan shi nan *JAWAD* a hanya. Yanzu kiran da na masa ma so na ke yaje ya 'dauko shi a airport".
"Ahhhh ka ce muna da ba'ko yau a gidan. Likita bokan turai". Fa'din haj Zulfah.
"Ai ba'kin za ki ce ba ba'ko ba, domin had da Matar shi da kuma 'kanin sa LUKMAN, ashe ya je can wajan shi ziyara, shine suka tawo tare. Kin San fa kusan shekara bakwai kenan rabon su da mahaifin su, shi uban na su shi ma ba zuwa ya ke ba, balle yq turo 'ya'yan na shi, Inna ta yi fa'dan ta yi fa'dan har ta gaji. Kusan shekara ashirin fa". (Naseer shi ke bi wa LUKMAN, shi ma ba a 'kasar ya ke ba, a Hong Kong yake karatun sa, Naseer ya riga shi kammalawa. Shi yanzu ya soma aiki ma. Kuma bai da mata.)
"Ahhhhhh ba ri na ta shi na soma kiciniyar abunda zan tari ba'kin na mu da shi". Fa'din haj Zulfah.
"Naseer za ka iya 'dauko su ko in saka Lado ya je ya 'dauko su??".
"Daddy zan iya, bari na hanzar ta ka da su yi ta jira".
"Lallai kam gwara ka hanzar ta, bari ni ma na saka Jalila (Baby) ta gyara was Jawad da matar shi part 'din can na baya".
" To daddy sai na dawo".
"Sai ka dawo Allah ya tsare".
Da sauri ya juya ya kalle ta, gaban shi na fa'duwa. Iya tsayin muryan ta da yake ji a kunnan shi, iya adadin wutar kaunar ta da ya ke ruruwa a zuciyar shi.
"Ameen" ya amsa mata a 'Kazan le'ban shi tare da saurin ficewa a 'dakin.
*AIRPORT*
Ya na isowa jirgin su na sauka. Wani kyakkyawan saurayi na ga ni Lamar su 'daya da Naseer, sai dai Naseer ya fishi duhun fata. Shi ya 'dan 'dauko hasken fatan mahaifiyar su. Sanye yake cikin wando jeans da t-shirts fuskan shi manne da glass irin NO RESPECT 'din nan. Sannun shi ri'ke da travelling bag, 'day an hannun kuma ya sa'kalo hannun kuma ya sa'kalo sweater a wuyan shi. (LUKMAN KENAN). Bayan shi kuma wani kamilallan mutun ne a bayan shi, gaba daya kamannin mum ya 'dauko idan ka 'dauke idanuwan shi da side dimples 'din mahaifin shi da ya kwaso, shi ma kyakkyawa ne ajin karfko, (DR JAWAD KENAN) bayan shi wata kyakkyawar siririyar mace ce fara ba irin caaan 'din nan ba,( NAINA MATAR JAWAD) hannun ta ri'ke da wani kyakkyawan yaro da bazai wuce 5years ba, kamannin shi sak na wannan kamilallan mutumin ( AHMAD 'DAN JAWAD).
Da sassarfa Naseer ya 'karasa wajan su tare da rungume su ya na jin murnan ganin 'yan uwan nashi har cikin zuciyar shi. Kallon Naina ya yi tare da fa'din,
"Aunty Naina ina yini? Maraba da zuwa kano".
Murmushi ta yi tare da fa'din,
" Yau dai ga ni a Kano".
"Ai kuwa." Naseer ya fa'da tare da kamo hannun Ahmad ya ce,
"Yaya muje mota ko". Ya na fa'din hakan yai gaba dauke da Ahmad a hannun shi suma duka rufa masa baya.
Bayan sun shiga mota ne ya gaishe da yayun nashi. Suka amsa cike da 'dokin ganin Autan na su. Minti talatin ya kai su gida. Kai tsaye part 'din haj Zulfah suka fara nufa.
Naseer ne ya mur'da handle 'din tare da sallama ka na ya shiga. Ba bu kowa a palon said Mufeeda da ta fito daga kitchen yanzu hannun ta ri'ke da kofin kunun tsamiyar da haj Zulfah ta ha'da mata.
Caraf idan NASEER, JAWAD, DA KUMA LUKMAN duka sauka a kan ta. A tare zuciyoyin su ya bugs lokaci 'daya.
"Alhamdulillah! Na ga matar da na da'de ina burin samun irin ta, in sha Allah na yi matar aure". Fa'din Lukman da ya ke kallon ta from head to toes.
" Tsarki ya tabbata ga maliccin wannan yarinyar. Lallai na sa mu mata ta biyu, kuma in sha Allah ka min nna bar garin said an 'daura mana aure". Fa'di. JAWAD.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! An ya zan iya daurewa kuwa. Wallahi Mufeey ke ce bugu. Zuciya ta". Fa'din Naseer da ya ke ji zuciyar shi na wani irin tsalle kamar zata faso zuciyar shi ta fito.
BABBAR BALA'I
KO
YA
WANNAN
CAKWAKIYA ZATA KASAN CE.
HMMMM KU DAI BI NI A SANNU , DON YANZU AKA SO MA LABARIN.
*MAMAN UMMEEN KU CE*
*INA JIRAN RUWAN COMMENTS*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 18*
Naina ta dubi mijin ta Jawad, sannan ta mai da kallon ta ga Naseer da kuma Lukman. Hankalin ne yai matu'kar ta shi tare da wani wutar kishi da ke taso mata. A matsayin ta na wacce ta karanci ilimin halayyar 'dan Adam (psychology) kallo 'daya tai wa wa'dannan 'yan uwa guda uku ta fahimci gaba daya sun kamu da 'kaunar wannan yarinya (Mufeeda).
Idanuwan ta ta 'kan'kace tare da watsawa Mufeeda kallon tsantsan tsala. Ita Sam ba ta da damuwa don Lukman da Naseer su na son Mufeeda ko da hakan na nufin zasu kashe kawunan su. Matsalar ta guda shi ne mijin ta da take matu'kar 'kauna kuma ta ke fatan kasancewa matar shi guda 'daya taak har gaba da abada. Don ita ko sallah ta yi ta na wa mijin ta addu'ar ka da Allah ya ba shi matan aljanna ko da guda 'daya ne balle har dubu saba'in.
Mufeeda cike da kunya saboda irin kallon da 'yan uwa uku suke bin ta da shi ta ce,
"Sannun ku da zuwa. Kun iso lafiya?".
Lukman ne kawai yai 'karfin halin furta mata,
"Lafiya 'kalau alhamdulillah. Ina mutanan gidan?".
"Su na sama, ba ri na je na kira su". Fa'din Mufeeda ta re da saurin yin sama, don har ga Allah ji ta ke zuciyar ta kamar zai tsinko ya fa'do don wani irin bugawa ya ke yi. Ta rasa dalili kuma.
Kai tsaye 'dakin haj Zulfah ta nufa tare da knocking. Daga ciki haj Zulfah ta ba ta izinin shigowa. Shiga ta yi, ta sami haj Zulfah zaune a palo ta na yayyanka fruits a wani 'dab madaidai cin bowl.
"Ummie ba'kin fa sun iso". Fa'din Mufeeda tare da 'kurban kunun tsamiyan da ke hannun ta.
Haj Zulfah tai saurin mi'kewq tare da fa'din,
"Aaah bari na je na same su, dama na gama shirya masu ko mai a dinning. Daddyn su ma wanka ya ke yi, yanzu zai fito". Ta fa'di hakan ne tare da saka wannan fruits 'din da ta yanka a cikin fridge 'din da ke palon ta fita Mufeeda ta rufa mata baya. Sai dai ita 'dakin Baaba Habiba ta nufa da ke ta fama da yara. Haj Zulfah kuma tai parlour.
Naina sai wani ciccin magani ta ke yi. Kowa ya nai mi waje ya zauna ban da ita. Sai aikawa Jawad harara ta ke yi kamar idanuwan ta zasu fa'do 'kasa. Jawad na kallon ta ta 'kasan idanu. Kasancewar ya San halin matar tashi ciki da bai. Kuma ta san ita 'din ta na da san akan halayyar 'dan Adam (psychology). Ya san ta na nan ta darsa wani abu a zuciyar ta, jira ta ke su ke'be ta sauke masa kwandon bala'i. Kuma wata 'dayan da ya ce zasu yi, zata ga Wanda ya isa ya sa suyi wata daya. Kwana biyar za su yi su koma in da suka fito.
"Maraba lalle da 'ya'ya na. Jawad idanun ka kenan? Ka juye ka zama German ka man ta da 'kasar ka na haihuwa ko?".
Murmushi Jawad ya yi, daman shi tun asali haka ya ke, shi bai cika magana ba sai dai yai murmushi kawai. Ya na da sanyi sosai. Shi ya sa ma NAINA taga lagon sa. Sai dai ka da ka saki ka 'kure shi har ya baiyanar da fusatar shi.
"Ina wuni Ummah? Mun same ku lafiya?". Jawad ya gaida haj Zulfah.
"Lafiya 'kalau Jawad". Haj Zulfah ta fa'da tare da Kamo Ahmad ta kuma ri'ko hannun Naina ta ce,
" 'Ya ta zauna mana, kya tsaya a tsaye".
Zama Naina ta yi tare da fa'din,
"Ina wuni?" Duk da ta na jin hausar sosai, amma ta na magana zaka san cewa girman turai ce.
"Lafiya lau 'diya ta".
"Allah sarki! Ni kamar ma ba'a ganni ba". Fa'din Lukman ya na wani karyar da kai.
Kunnan shi haj Zulfah