Showing 93001 words to 96000 words out of 115393 words

Chapter 32 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22932

da kafa'dun mal Ahmadu.
Mal Ahmadu ya na hawaye ya kalli KALLAH da yai tsuru² kamar an tsare kwarto a 'daki. Ya ce,
"KALLAH ka cutar da ni, ka cuce ni, bazan yafe maka wannan mugun abu daka min ba. 'Ya ta da tsohon ciki ta na halin na'kuda, amma ka koreta a gidan uban ta da duka saboda ba ka da 'digon imanin a zuciyar ka. Bayan u'kubar da kuka gallaza mata kai da Matar ka. Allah ba zai ta'ba barin ka ba wallahi".
KALLAH ya rugo da gudu ya du'ka gaban Ahmadu tare da fa'din,
"Wallahi sharrin *MAI ZOGALE* ne, ita ta saka ni yin komai. Ita ce ta ha'dani da mutanan da suka ba ni bindiga na saka a 'dakin ka saboda 'yan sanda in sun zo bincike su ga ni. Ita ta saka min kishin ka da ba'kin cikin tare da hassadar 'daukakar da kake sa mu a sana'ar ka. Wallahi duk laifin na *MAI ZOGALE* ne".
Gaba d'aya mutana wajan aka 'dauki salati tare da tsinewa KALLAH da Matar sa *MAI ZOGALE*. Mal Ahmadu kuwa maruka uku zafafa ya 'dauke KALLAH da shi tare da fa'din,
"Tur da halin ka! Idan *MAI ZOGALE* ta ce ka saka hannu a cikin wuta za ka saka? Na ce zaka saka?".
Shuru KALLAH yai ya na hawayen nadama mara amfani.
Mal Ahmadu zai yi magana, sai ga 'yan sanda guda uku sun shigo cikin gidan. Kai tsaye in da KALLAH ya ke su ka nufa tare da kama 'kugun shi.
IDcard 'din su suka nuna tare da fa'din,
"An ba mu damar tafiya da kai cikin ko wani irin hali". Su na fa'din haka su ka taxa 'keyar sa. Da sun so tafiya da *MAI ZOGALE*, amma da su ka le'ka su ka ga halin da ta ke ciki, sai suka ka bar ta acewar su zata zama masu liability. Shikuma KALLAH sai ihu ya ke ya na kiran sunan mal Ahmadu akan ya tai make sa ka da a yafi da shi.
Daddy da ke bayan su ya shigo tare da 'daga mal Ahmadu ya ce,
"Ka yi hakuri na boye maka wasu abubuwa game da 'diyar ka Mufeeda. 'Dana ne mijin ta da suka rabu, ko in ce ya Kore ta tare da tozarta ta".
Saurin kallon shi mal Ahmadu ya yi tare da fa'din,
"Alhaji 'Dan ka fa ka ce".
"Kwarai 'dana ne". Fa'din daddy tare da cigaba da cewa,
"Ka tashi mu je can gida. Zan maka bayanin komai".
Jinjina kai mal Ahmadu yai tare da mi'kewa ya bi bayan daddy da yai waje. Sauran mutanan cikin gidan ma duk su ka fito waje cike da mamakin mugunta da zaluncin KALLAH.
Mutane na watsewa, Marwanatu ta tattaro yinata² ta saka cikin jaka tare da kiran 'kawar ta kursum akan ta shirya ina zata same ta su wuce TAFAN.

Bayan mal Ahmadu sun isa gida, Daddy ya shi ga bashi ha'kuri akan rashin Samar da shi ko mai akan Mufeeda. Tare da yi masa al'kawarin in sha Allah duk in da Mufeeda ta ke sai ya binciko ma shi ita.
Washa gari da duku dukun Safiya mal Ahmadu ya nufi can gidan sa, ko kallon 'dakin *MAI ZOGALE* bai yi ba ya shige can wajan hanyar kewaye. Ya soma ha'ka 'kasa. Ya da'de ya na ha'kewa kamin ya soma ganin 'dan karamin akwatin da ya rufe a wajan. Ciro sa yai tare da kakka'be 'kasar, ka na ya bu'de. Wata doguwar envelope ya ciro daga cikin akwatin, kamar yanzu aka ba shi ya saka. Mai da 'kasar ya yi tare da rufewa, kana ya 'dauki envelope 'din ya fito daga gidan gaba 'daya ya koma can gidan daddy.
Sai wajan sha d'ayan safe suka ha'du da daddy. Dadd ya mi'ka masa hannu su ka gaisa tare da fa'din,
"Na fito 'dazu, amma sai na ga 'daki a bu'de baka nan".
Ba tare da mal Ahmadu ya ce ko Mao ba, ya 'dauko wannan envelope 'din ya mi'ka masa tare da fa'din,
"Ga abunda na je 'dauko wa nan".
Hannun daddy na rawa ya kar'bi envelope 'din tare da bu'dewa.
Gaban shi ne ya buga da 'karfi tare da fa'din,
"Y'ata ce, wallahi y'ata ce. Da ma na fa'da. Tun ranar da na fara ganin ta jiki na ya ba ni hakan. Allahu Akbar. *UMAYMAH* 'diyar ki na nan ba ta mutu ba. Ashe canje akai miki". Sharrrr sai ga daddy ya na zubda hawayen farin ciki.
Zungureriyar takardan da ke ciki ya fiddo ya soma karanta abunda ya 'Kusa. Sosai hawaye ke zuba daga idanun shi har ya kai 'karshan rubutun. Rungume mal Ahmadu yai ya na kuka kamar 'karamin yaro tare da fa'din,
"Allah ya saka maka da alkhairi mal Ahmadu, Allah ya biya ka da mafificin aljannah". Daddy ya sake shi tare da fita daga cikin 'dakin da sauri ya nufi side 'din sa. 'Dakin Mommah ya nufa. Ta na tsaye gaban gado ta na nannad'e blanket ta ji an rungume ta. Saurin juyawa tai taga daddy ne. Cike da murmushi ta ce
"Yau kuma da aka tuna". Hawayan da taga ya na zuba daga idanun shi ne ya saka ta firgita tare fara jeho masa tambayoyi.
Envelope 'din hannun shi mai 'dauke da hotuna ya mi'ka mata tare da wannan wasi'kar da ke hannun shi.
Wasi'kar ta soma karanta wa, ka na ta jikin ta na rawa ta soma kallon hotunan da ke hannun ta. Luuuuuu ta yltafi a sume. Cikin sauri daddy ya taro ta.

~*KANO*~
Janye bakin shi Naseer yai tare da dafe kan shi. Dai ² lokacin haj Zulfah da baaba Habiba su ka shigo parlour sakamakon ihun WHAT? 'din da baby da haj Jummai su kai.
Mufeeda kuwa jikin ta ne ya 'dauki wani irin rawa ta ka sa kallon kowa da ke parlon.
Lukman kuwa a fusace yai kan Naseer tare da fa'din,
"Who gave you the right?".
"We are been doing it since before she comes here". Fa'din Naseer ba tare da tsoron ko mai ba.
Zaro idanu Mufeeda ta yi ta na girgiza kan ka. Haj Zulfah kuwa sai bin su da idanu ta ke yi ta na so ta gano ainahin abunda ke faruwa.
Haj Jummai ko hannun ta 'daura a Ka tare da fa'din,
"Shikenan na shiga uku, Zulfa'u kin cuce ni kin lalata min 'dana. Allah ya isa tsakani na da ke. Muguwa mai ba'kar aniya. Don kin ga ba ki haihuwa ba, shi ne no ki ke son gur'ba ta min 'ya'yan na".
'Kala haj Zulfah ba ta ce mata ba, sai kafe Mufeeda da ta yi da idanu ta na son sanin ainahin abunda ke faruwa. Ita kuwa 'kasa tai da kan ta jikin ta sai mazari ta ke yi.
'Daga hannun Lukman yai tare da wanke fuskan Naseer da mari tare da nuna shi da yatsa. Kamin ya ce wani abu Naseer ya 'daga hannu ya wanke fuskan Lukman da mari hagu da dama.
Cikin second biyu dambe ya kaure tsakanin su, babu abunda ka keji sai 'karar nausussuka.
Fashewa da kuka haj Jummai ta yi, ya yin da haj Zulfah da baaba Habiba su ka shiga kiciniyar raba damben. Da kyar su kai nasarar rabasu, bayan sun dambatu tare da bawa hammata iska. Kowa ya koma gyefa ya na mai da numfashi. Domin ba 'karya dukkan su sun daku.
"Wani irin hauka ne kuke yi haka Lukman? Da girman ka, shine zaka biye wa 'kanin ka kuna dambe kamar 'kananan yara. Mai ya ha'da ku?".
Ka min Lukman 'din yai magana Naseer yai caraf ya ce,
"Wallahi Ummah ta ki fa'dawa masa ya rabu da Mufeeda. Ba bu abunda ya shafe shi da ita. Mufeeda tawa ce ni ka'dai".
"Tunda tare uwar ka ta haife ku, ai dole ta zama taka kai 'daya. Shegen yaro sallamamme. Akan wannan shegiyar mai 'konannan fuska ku ke san kashe junan ku? Da ma na sani, wannan wani tarko ne ko ka 'dana domin ganin baya na da na 'ya'yan na". Fa'din haj Jummai ta na kallon fuskan haj Zulfah da ke gyefe baki a hangame don tsananin mamaki. Duk wannan uban dambe akan Mufeeda a Ka yin sa. Ba ta ta'ba 'dauka abun zai kawo har haka ba.
"Bazan rabu da ita d'in ba, kuma muna nan da kai zaka mi'ko min hannu ka na fa'din Allah ya ba da zaman lafiya".
"Will you stop that nonsense". Haj Jummai ta fa'da a tsawace tare da cigaba da fa'din,
"Wallahi sai na nuna miki iyakar ki Zulfah, sai na nuna miki na isa da 'ya'ya na. Ku ma wannan 'Yar iskan.." Ta nuna Mufeeda ta re da 'karasawa wajan
"Sai ta koma in da ta fito. Ba zai yu karuwa ta zo gida na ta na nai ma rabamin kan 'ya'ya na ba. Saboda tsabar sabo da iskan ci har kin iya tsayawa agaba mutane ki na kissing 'dana ko?". Haj Jummai ta 'kari ke maganar ta na zazzarowa Mufeeda idanu.
A matu'kar mamakance haj Zulfah ta ke wa Mufeeda kallon abunda haj Jummai ta ke fa'da gaskiya ne.
Saurin du'kar da kai Mufeeda tai idanun ta na tsiyayar da hawaye.
Hannu haj Jummai ta 'daga zata zabgawa Mufeeda mari, Naseer yai saurin shiga tsakiya marin ya sauka a fuskan shi.
Saurin jaa da baya Mufeeda ta YI tare da fashewa da kuka mai sauti. Haj Jummai kuwa a mamakan ce ta ke kallon Naseer 'din tare da fa'din,
"Son ni zaka wa haka? Ka manta al'kawarin da Ka min ne? Ba ka ce min ba ruwan ka da wannan yarinyar ba?. Ka manta ka min al'kawarin idan ba gaisuwa ba, ba zaka 'kara shigowa 'dakin wannan annamimiyar matar ba?".
"Mummy ki yi ha'kuri, amma wallahi na kamu da 'kaunar Mufeeda, mummunar kamu ma kuwa. Ku ma wallahi idan ban aure ta ba zan shiga marsala". Fa'din Naseer kamar zai yi kuka.
"Aikuwa zaka mutu. Don wallahi bazan bari ka auri wannan ragowar titin ba har da 'ya'ya biyar". Fa'din haj Jummai ta na zabgawa Naseer 'din harara.
"To kuwa sai ya aure ta. Ke ma ai lokacin da Mudansuru ya ce ke zai aura, ban amince ba. Ya na ce min har da ha'da ni da many a na, ba yadda na iya haka na amince ya aure ki. Amma ni ba 'kaunar ki na ke ba. Don haka kamar yadda 'dana bai min biyayya ba ya aure ki, haka kema wallahi ko zaki mutu sai Nasuru ya auri wacce ya ke so". Fa'din Inna Huwaila da shigowar ta kenan Abubakar biye a bayan ta, shi yaje ya gari ya gari har jigawa. Ku ma tai masa warning ka da ya sa ke ya fa'dawa kowa zuwan ta.
Har 'kasa haj Zulfah ta du'ka tare da fa'din,
"Inna ina wuni? Kin iso lafiya?".
"Eh to alhamdulillah, na iso lafiya. Sai dai yanzu ne rai na ke son 'baci daga zuwa na. Ku ma wallahi in yi tsinuwa da 'batanci wa mutun idan ya nai mi jayayya da ni".
Murmushihaj Zulfah ta yi tare da fa'din,
"In sha Allah ba wanda zai yi jayayya da ke Inna".
"Yo to ama yi mana. Abu ne mai sau'ki a waje na in yi 'batanci wallahi". Ta fa'di hakan ne tare da nai man waje ta zauna ta na hura hanci.
Naseer ya fara gaida ta tare da zama gyefan ta. Ka na Lukman ya na wani shan 'kamshi.
"Uban ka kewa shan 'kamshi ba Huwaila ba. 'Dan iska mai hali irin na uwar sa. Yo idan ba hali irin na Jummai ba, yaushe za ka zo daga uwa duniya amma ka kasa zuwa nan nan da jigawa gaishe ni. Amma ai ka iya gaida iyayan ka".
Dogon tsaki Lukman yaja tare da ficewa daga 'dakin.
Bu'de murya Inna Huwaila ta yi tare da fa'din,
"Allah ya 'debe maka albarka. Shege mai ba'kin baya". Sai ta mai da idanun ta izuwa ga haj Jummai tare da fa'din,
"Sannun Jummai. Ina yini?".
"Ina yi ni Innah? Kin zo lafiya?". Fa'din haj Jummai a kumbure.
"Ban yi ni ba. Ku ma nazo lafiya sumul idan ma ba haka ki ka so ba. Sai da na soma gaida ki, sannan ki ka sa mu bakin gai da ni. To ri'ke gaisuwar ki ko in la'ance ki yanzu".
Shuru haj Jummai ta yi ta na harare² 'kasa.
Inna Huwaila ta mai da duban ta ga Mufeeda da har yanzu ta ke a 'kame kamar statue tare da fa'din,
"Wannan kyakkyawa yarinya daga ina? Ni kamar ma na ta'ba ganin ki".
"Anya kuwa, ita fa daga Kaduna ta ke. Ku ma ita ce wacce na ke son aura". Fa'din Naseer.
"Toooo! Ita kuma daga wani zuri'ar ta ke? In ce dai 'diyar mutunci ce?". Fa'din Inna Huwaila.
Karaf haj Jummai ta cafe zancan da fa'din,
"Wallahi wannan 'ya da ki ke gani ba 'diyar mutunci ba ce, domin har cikin shege ta yo, ta haifo 'ya'ya biyar, su na nan yanzu haka a gidan nan".
Wani irin mi'kewa Inna Huwaila ta yi tare da dafe 'kirji ta na fa'din,
"Zurfa'u, dagaske ne wannan yarinyar ta haifi 'ya'ya biyar a cikin ta?".
Jiki a sanyaye haj Zulfah ta ce,
"Eh Innah. Dagaske ne yanzu haka ma 'ya'yan su na 'daki na".
Jikin Naseer ne ya soma rawa, domin yasan muddin Inna Huwaila t ce bazai auri Mufeeda ba, to ta riga ta zauna babu kuma Wanda ya isa ya canza mata ra'ayin ta.
A bazata su ka ji muryan Innar ta na fa'din,
"Maza Zurfa je 'dauko 'ya'yan na gani. Ai wallahi ban ga uban da ya isa ya hana wannan aure tsakanin ka da wannan 'Yar albarkan yarinya mai haihuwar biyar lokaci 'daya ba. Ka ce ni ma zuri'a ta za'a samu 'yan biyar. Ban barin garin kano sai an 'daura wannan aure. Ni da na ke so zuri'a ta su cika kano da jigawa. Alhamdulillah Allah". Innah Huwaila ta fa'di hakan ta na 'daga hannu sama alamar ro'kon Allah.
Cikin sauri haj Zulfah da baaba Habiba su kai sama tare da kwaso quintuplets su ka kawo nan parlour.
Ai Inna Huwaila na arba da 'ya'yan nan ta fashe da kuka ta na fa'din,
"Allah gagara misali, Allah abun godiya. Ya Allah ka sa idan Nasuru ya auri wannan 'Yar albarkan yarinyar ta haifo masa 'ya'ya biyar kamar yadda ta haifo wa'dan nan".
Haka ta dunga 'daukan 'ya'yan 'daya bayan 'daya ta na yaba kyawun su. Can kuma ta kalli haj Jummai da take ji kamar zata fashe tsabar ba'kin ciki. Ta ce,
"Almura, da ki na so ki min ba'kin cikin jikoki 'yan biyar. To ta Allah ba ta ki ba. Wallahi na 'kara jin bakin ki ya furta ba ki son aurar wannan 'Yar albarka da Nasuru, sai na 'debe albarkan ki kuma na saka Mudansuru ya sake ki ki koma gidan ku. Dama ba da son rai na aka auro ki ba".
Fuuuuuu baby ta fice daga 'dakin ta na kuka.
"To, to, tooofa. Ita kuma wancan agwagwar fa? Ko fa gaishe ni ba ta yi ba. Aikuwa har 'daki zan bi ta in 'debe mata albarka. Bayan cin arzikin 'dana da take yi, shine zata min rashin kunya. Kamar ni Huwaila ta ka sa du'kawa ta gaida ni. Ko da yake, tarbiyyar ce ba'a koya mata ba". Inna Huwaila ta 'kari'ke maganar ta na mai gallarawa haj Jummai harara.
Haj Jummai cike da takaicin Naseer ta ja sandar 'kafafun ta ta fice daga 'daki Abubakar Babban 'dan ta ya bi ta a baya.
Ta'be baki Inna Huwaila ta yi tare da fa'din,
"D'an banza. To ba ason ran ta kazo duniyar ba. Da so samun ta ne ma da tuni ta rariya ka wuce". Sai kuma ta mai da kallon ta izuwa Mufeeda ta re da fa'din
"Ke! Ya ki nan ki ba she ni labarin ki. Domin da kai na zan je bi'dar nai man auran ki".
Kasa motsi Mufeeda ta yi.
"Ke! Ba da ke nake magana ba? Ko so ki ke na 'debe miki albarka, ki tafi ki na susan takashi?".
Dariya ce ta Kusa kufcewa haj Zulfah, tai saurin controlling kan ta tare da fa'din,
"Inna ba ri na je, na ha'do miki abinci".
"Da dai ya fito. Don yunwa na ke ji".
Nufar kitchen 'din haj Zulfah ta yi, baaba Habiba na biye da ita a baya.
Mufeeda kuwa da kyar ta iya Jan 'kafa ta zauna a 'kasa wajan 'kafafuwan Innar.
"Ke dalla ni ban san munafunci, tahi ki zauna kan kujera".
Tashi Mufeedan ta yi tare da zama kan kujerar.
"To maza ina jin ki. Ya akai ki kai cikin shege? Ke ba ki iya 'yan dabarun nan ba ne irin na wayayyu? Yanzu hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login