Showing 66001 words to 69000 words out of 115393 words
ficewa daga 'dakin.
Sosai Mufeeda ta ke jin da'din hira da 'kannan Naseer 'din, sun saki jiki da ita sosai, har labarin Naseer kaf sai da su Ka ba ta, makarantar da ya yi tun daga primary gar jami'a. A nan ne ta son Naseer 'din ya na matu'kar son yara. Burin shi idan yai aure Matar shi ta haifa masa 'yan biyu. Sannan su Ka ba ta labarin Ummu na ta 'kasar saudiyya da Naseer ya ke matu'kar so cikin 'kannan mahaifiyar sa kuma ita ma ta ke matu'kar son shi.
Mufeeda ta sha labari kala² a wajan twince.
A nan ne kuma ta ari wayar su ta kira Mashkura kasancewar ta haddace number ta ta shaida mata ta na asibitin dialogue tun jiya.
Cikin abunda bai fi minti goma ba, sai ga *KURAN* ta shugo kasancewar har number 'dakin ta fa'da mata.
Tun da ta shigo Mufeeda ta zuba mata idanu, ko ita da tai ciwo ba ta isa ta nuna mata rama ba. Idanun ta sun wani soye, fuskan ta yai fiyaut.
" *KURA*, mai ya same ki, kin gan ki kuwa? Ba ki da lafiya ne?".
"Mufeeda ke ce Marsala ta, duk abunda na ke so wajan ki ya ke zuwa ba waje na ba, na so Musa tsohon saurayin ki, har fa'da masa na yi, amma ya ce min in yi ha'kuri ke ya ke so. Na danne zuciya ta na ha'kura na bar miki shi. Tun da na fara ganin Naseer na ji duk duniya babu Wanda na ke so da burin aure sama da shi, rana 'daya ki raba dashi.ba ki daadalci Mufeeda. Duk irin soyayyar da na nuna miki, ke burin ki kawai ki ga baya na, duk abunda na ke so, wajan ki ya ke zuwa. Yaya bazan koma haka ba". Mashkura ta fa'di hakan cikin zuciyar ta, amma a zahiri sai cewa tai,
"Zazza'bi ne yai min mugun kamu, ga kuma mura da ya maka min ciwon ido".
"Ayya besty na, zazza'bin nan bai min adalci ba. Ai da kin yi zaman ki ma ba ki zo ba". Fa'din Mufeeda ci ke da tausayawa.
"Hmm ke ma kin san abunda ba zai yi ba kenan, besty na na asibiti, ni kuma ina kwance a gida. Ai na ji sau'ki. Wa ya kawo ki asibitin masu ku'din nan?".
"Naseer". Mufeeda ta ba ta amsa.
Wani irin gudumar ba'kin ciki Mashkura ta ji a cikin zuciyar ta, nan da nan hankali ta ya tashi.
Kallon twince ta yi, sai yanzu ta hango tsantsan kamannin da su ke yi da Naseer 'din.
"Ba zai yuwu ba. Sam bazata sa'buba bindiga a ruwa. Wallahi wannan karan zan yi ya'ki". Mashkura ta fa'da a cikin zuciyar ta.
Jijjiga ta Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Besty lafiya dai?".
Ya'ke ta yi tare da fa'din,
"Y'an biyu ne su ka 'dauken hankali".
Su ma 'yan biyu ita suke kallo. Zaheeda ta 'dauki waya ta soma typing message wa Zaliha.
" *SAM WALLAHI BA TA MIN BA, WANNAN BESTYN AUNTYN NA MU*"
Zaliha ta mata replay,
" *HMM WALLAHI KIN RIGA N FAD'A NE. NI WALLAHI HAUSHI MA TA KE BA NI, MUMMUNA DA ITA*".
Dariya Zaheeda ta kwashe da shi a fili bayan ganin replay 'din Zalihan.
Kallon su Mashkura ta yi, haka nan ta ji ta tsargu da dariyan na su.
"Sarakan charting". Mufeeda ta kalle su tare da fa'din hakan fuskan ta cike da murmushi.
"Wai har su yi sabo haka". Fa'din Mashkura cikin zuciyar ta.
Nan Mashkura ta yi ni har bayan magriba.
Bayan ta idar da sallah ne ta soma shirin tafiya. Dai ² lokacin kuma Naseer ya shigo hannun shi ri'ke da manya² ledoyi guda biyu. 'Daya cike da fruits dangin su abarba, kankana, apple, grapes da lemu. 'Dayan kuma yahuza suya ne da fresh milk a ciki.
Kaman ha'din baki sai ga Mommah ma ta shigo hannun ta ri'ke da basket.
"Sannu da zuwa Mommah". Mufeeda ta fa'da.
"Yauwa 'diya ta ya 'karfin jikin na ki?".
Kamin tai magana Naseer yai caraf ya ce,
"Wato ita Mommah kin gan ta, ni ne ba ki ga n ba ko?".
"Dan gidan ku ni kishiyar ka ce?". Mommah ta fa'da ta na watsa masa harara.
Sosa kyeya yai tare da fa'din,
"Mommah ni ba ta gaishe ni ba ne".
"Ta'ki ta gaishe ka 'din, iyayan son girma".
Dariya su Zaheeda su ka kwashe da shi.
"A baka cin recharge card 'din ku".
Kama kunnuwan su su kai tare da fa'din,
"Double sorry bro".
Harara ya watsa masu.
Mashkura da ke tsaye kamar statue ji ta yi kamar ta kurma ihu don ba'kin ciki.
"Yanzu ke nan har maman shi ma ta San da zan can soyayyar su". Mashkura ta tambaya kan ta cikin zuciyar ta.
"Ina wuni?". Dakyar Mashkura ta iya harha'do kalmomin ta gaida Mommah.
Mommah ta amsa ba tare da ta kalli fuskan Mashkuran ba, domin lokacin ta na kiciniyar zubawa Mufeeda lafiyayyaan jolof 'din couscous din da yaji kayan lambu da hanta.
Wani 'kululu ya tokare wuyan Mashkura.
"Ni da kai na zan baki abinci a baki, don 'dazu a tambayi Zaliha kin ci abincin da na aiko driver ya kawo. Ta kuma shaida min ba k wa ni ci sosai ba". Fa'din Mommah.
"Yauwa Mommah, haka zaki ri'ka mata idan ba ta son cin abinci".
Harara Mommah ta watsa masa tare da fa'din,
"Maza kaje gida kai wanka ka ci abinci sa kai dawo, ka tafi da su Zaheeda suje su hutu"
"Mommah anan zamu kwana".
"Baza ku kwana anan ba, kuma ba ni son musu".
"Masoyiya, ba ri na je nadawo". Fa'din Naseer ya na kallon Mufeeda.
Kunya duk ya kamata, sai tai kaman ba ta ji ba.
Murmushi ya saki tare da fita daga 'dakin, twince su ka bi shi a baya suna 'kun'kunai.
"Besty ni ma zan wuce".
Sai a lokacin Mommah ta 'daga kai ta kalle ta.
"To besty nagode sai da safe".
Ta'be baki Mommah ta yi, hakanan ta ji Mashkura ba tai ma ta ba.
Ficewa Mashkura tai da sauri ta na addu'ar Allah ya sa su Naseer ba su wuce ba.
Aikuwa addu'ar ta ba ta kar'bu ba, domin ta na zuwa wajan motar su naa tashi.
Cizar yatsa tai tare da ficewa ta tari keke napep.
*_Satin ta d'aya aka sallame ta_*
Mufeeda ta ga gata da soyayya wajan 'yan uwan Naseer. Domin mahaifiyar Naseer da kan ta ta kai Mufeeda har gida kasancewar lokacin da aka ba su sallama Naseer 'din na banki.
Mahaifiyar Naseer ta tambaya *MAI ZOGALE* akan menene dalilin da yasa ta ke 'daurawa Mufeeda tallah.
Kwarjini mahaifiyar Naseer tai wa *MAI ZOGALE* shiyasa ta ba ta amsa da,
"Kin ga Muheeda ta isa aure, kuma ba 'karfi gare mu ba, shiyasa na ke 'daura masu tallah ita da 'Yar uwar ta, su samu su tara kayan aure".
"To idan dai haka ne. Ki kwantar da hankalin ki, 'da na ya ce in fa'da miki ya 'dauki nauyin kayan 'dakin ita 'yar wajan ta ki da kuma ita Mufeeda". Fa'din Mommah.
Zaro idanu da dafe 'kirji *MAI ZOGALE* ta yi tare da fa'din,
"Dagaske Hajiya? Kai amma nagode Allah ya saka da alkhairi. In share Allah kuwa daga yau sun bar tallah har abada".
"Nagode ni ma, kuma in sha Allah gobe ko jibi, iyayan Naseer za su zo nai man auran Mufeeda".
"Babu komai sai sun zo, Allah ya kai mu".
"To nagode". Fa'din Mommah tare da aje mata dubu goma sannan ta le'ka Mufeeda tare da mata sallama ka na ta wuce gida cike da takaicin *MAI ZOGALEN*.
Tun daga ranar *MAI ZOGALE* ba ta kuma 'daurawa Mufeeda talla ba.
Kamar adda
Mommah ta fa'da wasa bari iyayan Naseer maza su a zo su ka be ma mass auran Mufeeda wajan KALLAH.
Ba tare da wa ni bincike KALLAH ya ba su auran Mufeedan. A take kwa su ka ba da sadakin ta dubu Dari biyu, kuma take KALLAH ya saka biki dai dai da lokacin bikin Marwanatu ka wato nan da wata biyu masu zuwa.
*WALLEH HANNU NA KAMAR ZAI TSINKE. YAU NA YI 'KO'KARI, KUMA INA SON GANIN RUWAN COMMENTS SOSAI KO IN JE HUTUN SATI UKU*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 34_*
Mufeeda ta 'dan samu sauk'i a wajan *MAI ZOGALE*. Ta dai na saka ta aiki. Yanzu ma kwata² ba ta cika zaman gidan ba kullum ta na kan fita akan biki dake gaba towa.
'Bangaran Mufeeda da Naseer wani irin soyayya su ke yi mai wuyar misaltuwa. Domin kuwa Mufeeda sai yanzu ta ga ne ashe da can ma ba 'kauna ta ke yi ba, yanzu ne ta ke asalin 'kauna.
🟣🟣🟣🟣🟣
"Wai ba za ki fa'damin abunda ke damun ki ba Mashkura? Kin zauna kullum sai kuka, gashi sai 'karewa ki ke yi. Yanzu ni ban isa ba kenan. Ban kai ba da za ki iya fa'damin matsalar ki ba ko? Ba komai kije ki yi ta yi". Mama na kai wa wannan wajan ta fashe da matsanaicin kuka mai ta'ba zuciya.
Mashkura ta 'dago idanunta da duk sun kod'e saboda kuka ta ce,
"Mama ko na fa'da miki ba zaki iya min komai ba, wallahi Mama ina cikin tashin hankali. Kuma wallahi idan zuciya ta bai samu abunda ta ke so ba, wallahi za ki iya rasa ni Mama". Mashkura ta 'karashe maganar tare da rushewa da kuka.
Zama sosai Mama ta yi tare da dafa ta ce,
"Mashkura fad'amin abunda ke damun ki, ni kuma in sha Allah zan miki maganin matsalar ki Idan bai fi 'karfi na ba". Mama ta fa'da ta na mai tsurawa Mashkura idanu.
Jan majina Mashkura ta yi, ka na ta gyara zaman ta tare da fad'in,
"Mama aure na ke so".
Wani irin washe ha'kora Maman ta yi ta re da fad'in,
"Alhamdulillah Allah na gode maka. Yo ke wannan ai abun farin ciki ne ba na kuka da tashin hankali ba. Abunda ba da'de ina jira. Yanzu ai sai ki ba Jamilun dama ya turo magabatan shi".
Share hawayan da suka zubo mata tai tare da fad'in,
"Mama ba Jamil na ke so ba, Naseer na ke so".
Saurin kallon ta tai tare da fad'in,
"Waye kuma Naseer? 'Dan gidan waye?".
Ajiyar zuciya Mashkura ta sauke mai 'karfi tare da fad'in,
"Ina nufin Naseer wanda Mufeeda za ta aura".
Wani irin duuum Mama ta ji a cikin kunnan ta. Saurin karka'de kunnuwan ta tai tare da fad'in,
"Maimaita, me ki ka ce?".
"Naseer Wanda aka sawa rana da Mufeeda, shi na ke so". Mashkura ta fad'a tare da fashewa da wani irin matsanaicin kuka.
Kau! Kauuu!! Kauuu!!!
Mama ta yankawa Mashkura zafafan maruka a kumatun ta hagu da dama tare da fad'in,
"Allah ya tsinewa wannan lalatacciyar zuciyar da ta raya maki wannan mugun abu. Mashkura! Mashkura!! Ke ce ki ke fad'in wannan magana da bakin ki? Ashe dama duk tausayi da soyayyar da ki ke nunawa Mufeeda na k'arya ne? Lallai ke 'din muguwa ce ta bugawa a jarida. Kuma ki bud'e kunnuwan ki da kyau ki ji ni, wallahi babu hannu na a cikin wannan iskanci da shashancin na ki, kuma wannan umarni ne na ba ki a matsayina na mahaifiyar ki, wallahi tallahi ban amince ma ki akan wannan batu ba ki ba, kuma ko mutuwa za ki yi, sai dai ki yi. Amma idan ina numfashi ba za ki ta'ba auran Naseer mijin aminiyar ki in sha Allah ba. Sha sha sha kawai". Mama na kawo wa nan ta juya za ta fita.
"Hmm ba abun mamaki ba ne idan kin furta hakan, na da'de da sanin nid'in ba 'yar ki ba ce ta cikin ki, shiyasa ba za ki damu da damuwa ta ba, shiya ba za ki so abunda na ke so na".
Har Mama ta kai bakin 'kofa tai wani irin juyowa saura kad'an ta kife saboda tsananin kaduwa da abunda Mashkura ta furta. Gaban ta ta dawo zuciyar ta na wani irin tsallan kad'uwa da tsoro ta ce,
"Mashkura, a ina kika ji wannan maganar? Wa ya fad'a miki ke ba 'ya ta ba ce? Duk Wanda ya fad'a miki 'karya ya ke yi".
"Hmm na fi shekara uku da sanin 'dauko ni ku kai ke da baba a gidan marayu tun ina da shekara uku a duniya. Na ga takardu da shaidan hakan a tsohon akwatin baba da naje binciken date of birth d'na da primary certificate di'na lokacin da aka buk'ace su a school. A nan na ga komai. Nayi kuka² akan sanin ba kune asalin mahaifa na ba. Daga baya na cire komai a raina domin naga irin tsananin kula da na ke samu a wajan ku. Wallahi idan har ba za ki biya min bu'kata ta ba, zan gudu na bar miki gidan ki".
Wani irin zufan tashin hankali ke karyo wa Mama, tsoro ya dabaibaye ta. Ta kasa cewa komai sai bin Mashkura ta ke yi da idanu.
*DAN ALLAH KU YI MANAGE ZAMU HA'DU GOBE*
[9/12, 1:09 PM] Maman Ummee: *بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 35_*
Mi'kewa Mashkura ta yi tare da barin mata 'dakin ta koma tsakar gida ta zauna ta dasa sabon darasi na kuka.
🟡🟡🟡🟡🟡🟡🟡
"Assalamu alaikum, wai ana sallama da Mufeeda inji Naseer". Wani 'dan 'karamin yaro da bai wuce 8years ba ya fa'da a tsakar gidan su Mufeedan.
Mufeeda da ke 'daki tana linke kayan ta da ta wanke. Murmushi ta saki tare da mi'kewa ta 'dauki hijjab ta saka tare da fitowa ta ce wa yaron,
"Ka je ka ce, ta na zuwa".
Ficewa yaron ya yi.
"Ta'kalmi ta saka, har ta kai tsakiyar gidan, *MAI ZOGALE* ta fito tare da fa'din,
"To so maza, daga yaro ya zo kiran ki, ko irin dan dakatawar nan ma wasu minti na irin Wanda 'yan mata ke yi saboda aji baza ki iya ba, saboda an ga mai ku'di ko, ki ji na rawa. Maza jeki, wata 'kila ma 'dan yankan kai ne". Harara ta maka mata bayan ta gama maganar ka na ta koma 'daki.
Mufeeda kuwa, murmushi kawai ta yi, ka na ta ficewar ta, tasan babu abunda ke cin *MAI ZOGALE*, Illa tsabar bak'in ciki da hassada.
Tsaye ya ke a jikin ginin gidan, sanye cikin jallabiya kalar maroon, sai 'katuwar rigar sanyin da ya 'daura akai saboda mun shigo lokacin sanyi. Kan shi kuma, hulan sanyi ce mai kunnuwa, yai bala'in kyau.
Kallo na ya yi tare da sakar min narkakken murmushi. Sanye take cikin doguwar atamfa kalar sararin samaniya, sai hijjab 'din ta shima sky har guiwar ta.
"Ina wuni". Mufeeda ta fad'a murmushi kwance a fuskan ta.
"Ni dai wallahi ina azabtuwa da rashin jin muryan ki, duk lokacin da mu ka rabu. Shiyasa ma yanzu kamin na zo, sai da na biya cikin gari na sayo maki waya. Ga ta 'karama ce dai sai kiyi ha'kuri da ita kamin ki shigo daga ciki". Ya fa'di hakan ne tare da mi'ka mata wata leda mai walwali.
No'kewa ta yi ta'ki kar'ba, aikuwa yai kicin² da rai tare da fad'in,
"Kin rai na ne, saboda na ce 'karama