Showing 6001 words to 9000 words out of 115393 words

Chapter 3 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22938

Sosai hankalin sa ya tashi. Ya ce,
"Baiwar Allah lafiya, ko a kwai wata Marsala ne?"
"Babu wanda ya me neman inda nake, haka kuma kuma babu wanda hankalin shi zai tashi domin rashi na. Ba ni da kowa sai 'ya'ya na". Ta bashi amsa ta na shasshekar kuka.
Sosai mamaki ya shige shi, ya ce,
"Baiwar Allah ban fahimce ki ba Kamar ya ba ki da kowa? Da ma akwai dan Adam 'din da bai da ahali ne?"
Shuru ta yi ba ta bashi amsa ba amma kuma still ta na kuka. Ya ce,
"Dan Allah ki fa'da min damuwar ki, ni kuma na miki al'kawarin in sha Allah sai na taimake ki sai in da karfi na ya 'kare".
Maganganun shi ya sa taji natsuwa ya shige ta, ta 'dago ta kalle ni sai kuma ta sunkuyar da kai. Kusan second goma sannan ta fara bashi labari tun daga bugun 'kofar Naseer har korar karen sa Baba Kalla ya Mata.
Sosai ya shiga mamaki tare da jujjuya maganganun ta a kwakwalwar shi, ya ce,
"Kuma ke kin tabbata 'ya'yan shi be??"
Ba ta ji mamakin tambayar da ya Mata ba, sai ma murmushin da ta yi a 'Karo na farko sannan ta ce,
"Sam ni ba mazinaciya ba ce, shi ma idanun sa ne ya rufe shiyasa har ya min wannnan zargi tare da tozarta ni a idanuwar jama'a, amma wallahi 'ya'yan can jinin sa domin hatta waccan 'digon na kan kumatu mazan akwai shi a nashi kumatun, sak mahaifin su suka biyo, kuma ya'kin duniya za'a sake yi a Karo na biyu, bazan bashi 'ya'ya na ba.".
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce,
"Dan Allah ina so ki ba ni address 'din gidan Ku."
Kamar bazata bashi ba, sai kuma ta fa'da masa, saboda irin taimakon da ya Mata bai cancanci ta masa musu ba.
"Ki kwantar da hankalin ki, zanje gidan Ku yanzu in sha Allah ko mai zai zo da sauki, zaki koma gida ki kula da 'ya'yan ki."
Sosai ta ji da'di, domin idan har baba Kalla ya'ki amincewa ta dawo, bata San Ina zata nufa ba da 'ya'ya bιyar ba wanda nono ma ba isan su zai yi ba sai an ha'da da madara.



Share & Comment


*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*


🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )

Alhamdulillah! My aminiya is back again with her love and romantic story *KYAUTAR ALLAH* hurry nd buy it. It's just #300 via *0542703718 SA'ADATU ABDULLAHI, GT BANK.*
*DON'T WAIT FOR A THIRD PERSON TO GIVE THE STORY, GO FOR THE BOOK YOUR SELF*❤️😍🥰💖


*PAGE 6*


Bai sha wahalan gane gidan ba saboda Kalla sanannan mutum ne har a gaban anguwan su, can ne sa da gidan yai parking sannan ya fito daga motar tare da mi'kawa yaron da ya rako shi naira dubu. Yaron ya kar'ba ya na murna sannan yai gaba.
Cikin tafiyar shi ta natsattsun muta ne ya isa kofar gidan tare da kwa'da sallama.
Kalla na tsakar gida da 'yar 'karamar radio yana sauraron wakar Shata tare da auna tuwan dawa da miyar danyan kubewa a cikin sa. Mai zogala na daga can gyefan shi zaune akan tabarma ita ma ta na auna nata.
Tsaki Kalla ya ja tare da fa'din,
" waye kuma wannan zai zo ya damu mutun ya na tsaka da cin abinci? Yanzu haka ma yaronnan ne 'dan gidan Sagiru mai manja, daga jiya na ranci dubu uku a hannun sa, akan idan na samu Zan bashi shi ne zai zo ya tara min jama'a a kwar gida, to ni na fishi tijara wallahi".
"Kafin ka masa tijara ka jira ka fara jin nawa tijaran. Yanzu Kalla sabida iskanci kasan tun shekaran jiya nake nai man dubu da 'dari takwas nai zubin adashi. Kasan Marwa ta kusa haihuwa, kuma na San kaf unguwar nan jira ake a ga abunda Zan yi, kuma dai ai kasan irin gidan da take aure, gidan manya ne, Ashe har da Kai ake so inji kunya?"
"Haba mai Zogala ya zaki ce haka?"
Yo haka ne mana 'Kalla, idan ba haka ba ne to menene?
Zai bu'de baki ya sake magana aka sake kwa'da sallama. Ya kalli mai Zogala tare da fa'din
"ba ri na duba waye, ki ka sani ma KO ku'din ne ya biyo mu har gida".
Banza tai masa, shikuma ya mi'ke yai hanyar waje ya na su'de hannu har kwar gidan tare da fa'din
"waye haka da daddaran nan?"
Architect Naseer ya ba shi amsa da,
"Ni ne baba, ina yi ni?"
"Lafiya in ce dai lafiya yaro?"
"Eh to baba da dai zamu samu 'dan waje mu zauna zai fi".
Kamar zai tuttura masa zagi, ko mai kuma yai tunani, sai ya nuna masa dakali tare da fa'din,
"Muje can mu zauna, sai muyi maganar, na San dai ba akan maganar nai man aure ba ne, domin ni tuni na aurar da Marwanatu ta na can tana auran 'dan gidan alhj Mika'ilu mai gidan kajin naaan, ai nasan ka sanshi domin shi sanannan mutum ne."
Haushi ne ya turni'ke zuciyar Architect Naseer, wato 'yar dan uwan shi caan marainiyar Allah ya wula'kan ta, amma ya na koro masa bayanai cewa 'yar shi ta auri dan gidan mai kaji. Wato yanzu duniya kowa nashi ya sani. Danne fushin sa ya yi ta re da saisai ta muryan shi ya ce,
"Dama nazo ne akan maganar 'yar ka Mufeeda. Yanzu haka ta na asibiti ta haihu, aiki ma aka aiki. Baba don girman Allah ka yi hakuri Mufeeda ta dado gida ta zauna a wajan ka. Ka ga daganan sai Kai....."
"Uban waye uban na ka? Ka ga min 'dan iskan yaro. Oooohooo! ashe Kai ne 'dan iskan na ta ke nan da ka mata ciki. To amma dai Kai Allah dai ya 'debe maka albarka har da iyayan ka. Zaka bar min kwar gida KO sai na tara maka jama'a? Dan tijara ne ni da ka ke gani na ana. Tsohon dan tasha ne ni. Wallahi na shiga gida na fito na gan ka nan sai na maka rashin mutunci". Ya na gama fa'din haka fuuu yai ciki gida still ya na sababi.
Ba 'karamin mamaki ba ne ya Kama architect, guiwa sake ya mi'ke yai wajan motar shi ya shiga tare da reverse ya bar unguwar da sake-sake da yawa a zuciyar shi.
Mai Zogala ne ta fito ri'ke da tabarya a hannun ta, Kalla na bayan ta da gora. Wayam suka gani. Kalla ya ce,
"Dan iska da ka tsaya ma na, wallahi da ka koma da rotsattsan Kai.
Architect bai koma asibiti ba, Kai tsaye gidan aminin shi ya tafi wato doctor Haroon. Kiran shi yai a waya ya ce ya fito ya na waje.
Fitowa doc ya yi, bai gan shi a harabar gidan ba, gate ya tura ya fito, anan ya ganshi cikin mota. Bu'de motar ya yi ya Shiva tare da fa'din
"ya ya dai architect, mai yasa ba ka shigo ba??"
'Dagowa architect ya yi tare da fa'din,
"Aboki na akwai fa babbar Marsala?"
Gaban doc ya fa'di ya ce,
"Aboki na mai ke faruwa??"
Architect ya kwashe komai ya fa'da masa. Shi kan shi doc kan shi ya kulle, ya ce,
"To ya keke ga nin za'ayi kenan yanzu?"
"Samo 'yar dattijuwa zamu yi wacce zata kula da ita kan nan da sati biyu, ta warware, sai na 'dibe ta ita da 'ya'yan ta mu kuma komawa, wata 'kila KO dan darajar su zai kar'be." Architect ya fa'da.
"Haka ne. To amma ita ba ta da dangi uwa ne??" Doc ya jeho tambaya.
"Hmm wannan yarinyar fa abar tausayi ne. Duk yadda akayi a kwai wani babban al'amari a rayuwar ta. Sai dai idan ta bamu labarin ta kaaf. Don shi uban 'ya'yan ma Saki uku ya dan'kara Mata. In sha Allah gobe zanje inyi bincike ta 'bangaran shi, jibi Zan koma Kano, Zan bar maka amanar ta, kwana uku zanyi in dawo."
"Wannan ba matsala ba ne, yanzu dai bari in koma cikin gida, akwai wata dattijuwa dake wa Sumayya (Matar sa) aiki, sai ita ta kula da ita kawai, domin a daran nan babu in da zamu samu dattijuwan da zata kula da ita".
"Hakan ma ya fi, taho da ita kawai sai mu tafi".
Fita yai ya koma gida, minti goma sai ga doc ya fito shi da Baaba Habiba. Bu'de mata gidan baya ya yi ta shiga, shi kuma ya shiga gaba. Architect ya gai da baaba Habiba, ta amsa cike da fara'a, ya ja mota su Kai asibiti.
Zaune ta ke ta jingina bayan ta da gado idanun ta a lumshe, tunanuka iri-iri me Mata yawo a kwakwalwar ta, tunani ta ke Ina ma ta dangin mahaifiyar ta zasu 'kauna ce ta. To sun fi baba Kalla ma nuna mata tsana, shiyasa kwata kwata bata kwatanta bin hanyar gidan ba, ita ba ta san menene ma'kasudin wannan tsanar da dangin ta biyu suke mata ba, mahaifinta kuma tun ta na da shekara bakwai ya rasu, ba ta San komai dangane da mahaifiyar ta ba, Sai dai wani ma'kocin su ne ya ke bata tarihin mahaifiayar ta cewa mutuniyar kirki ce, sam ba ta San mai ya haddasa wannan 'kiyayyar ba.
'Karar bu'de 'dakin ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, idanun ta ne ya sauka akan nashi, tai saurin sunkuyar da kan ta. Doc Haroon ne ya 'karaso kusa da ita ya ce,
"My patient mai ke damun ki yanzu??"
A tausashe ta ba shi amsa da,
"Wajan 'dinkin ne ya ke min ciwo"
Doc ya ke. "Okay ba matsala dama zakiji haka, amma in sha Allah zai dai na".
Architect ya ce,
"Mufeeda ga Baaba Habiba nan za ta kula da ke daga nan har ki samu sauki a ba Ku sallama, daga nan za asan yadda za'ayi in sha Allah".
"Nagode Allah ya saka da alkhairi". Ta fa'da hawaye na silalo Mata.
"To kukan na meye kuma? Idan zaki dinga asarar hawayan ki gaskiya zamu samu Matsala. Kin ji KO?"
'Daga masa kai ta yi a hankali.
'Karamar wayar shi ya Ciro a aljihu ya mi'kawa baaba Habiba tare da fa'din,
"Baaba ni zanje na kwanta, idan akwai wani matsala ga waya nan, number ta ne kawai a ciki sai a Kira ni".
Baaba Habiba ta ce,
"to Allah ya tsare".

աasɦa ɢaʀɨ
Kamar jira ake gari ya waye, mutane wannan ya shiga, wannan ya fita duk 'yan ganin jarirai, har da marasa lafiyar da ke asibitin ma zuwa suke ganin 'ya'ya biyar 'din da Mufeeda ta haifa, ba 'karamin kyaututtuka suke samu ba. Akwai wata da take jinya a asibitin kuma mijin ta babban mutum ne, da aka fada masa, a take ya ce ta ba shi account details 'din ta, sai a Kai sa'a dai dai lokacin architect Naseer sun iso asibitin sai ta ce ba ta da account amma ga yayan ta nan ta nuna architect. Shi kuma ya ba da account number shi, a take yai masu forwarding 'din 2.5m Sosai su Kai masa godiya. Kowa da irin kyautar da ya ke ba da wa. Wasu pampers Wanda a 'Kalla za suyi shekara suna amfani dashi, wasu kuma kayan babies, Kai kyauta dai gashi nan kala-kala.
Sosai baba Habiba ta ke kula da ita, duk da ance ka da a saka Mata ruwan zafin nan mai uban zafi saboda aiki, amma baba habiba na kula da ita sosai, musamman ta saka aka kawo Mata maganin wanka, sannan kuma wajan tsarki ba ta masa wasa, sai ta tabbatar ta yi shi da kyau.
Doctor Haroon ya ce zata iya cin komai, sosai ta ke samu abinci lafiyayye taci, ga koko tea 'din da take sha safe da dare. Don yanzu 'yara sun iya Kama nono, sosai kuma suke da ci, gwara ma autar mace, ita ce mai 'dan sauki sauki.
"Ba ki fa'di sunan da za ai musu hu'du ba da shi ba"
Kan ta ta sunkuyar tare da fa'din,
"Yaya na, na baka wu'ka da na ma, ka saka masu sunan da ya dace"
Sosai architect ya ji da'din karramawar da ta mishi, amma sai ya ce,
"Naji da'di kwarai da wannan karramawar agare ki, amma ke ma nasan dole akwai sunan da kike da mura'di".
Shuru ta yi, can kuma ta dauki Usainin ta mi'ka masa tare da fa'din,
"Wannan ka saka mishi sunan ka, shi kuma wancan (Hassan 'din) ka saka masa sunan Mahaifi na (Ahmad) sauran matan kuma autar ka saka mata sunan mahaifiya ta (Zarah) sauran biyun kuma na bar maka za'bi"
Sosai yaji da'din takwaran da ta mishi. Daukar su ya yi 'daya bayan 'daya ya masu khuduba, sai da ya gama sannan ya dauki babban Wanda ta ce asaka masa takwaran mahaifin ta ya ce,
"Allah ya raya Ahmad (Abid)" sannan ya kuma 'daga mai bi masa ya ce,
"Allah ya raya Naseer (Ayaan).
Gaban ta ne ya ba da sautin duummm, kwata kwata ba ta kaunar 'kara Jin wannan sunan a rayuwar ta, da ta San sunan shi kenan, wallahi da ba tai gangancin ce ma ya saka ma 'dan ta sunan shi ba, amma ya zata yi, ba za ta iya ce masa ya canza ba.
Shikuwa architect bai ma ga reaction 'din ta ba, idanun shi naga 'ya'yan ta.
Sai ma nuna babbar ya yi tare da fa'din,
Allah ya raya Fatima Zahra (Irfana)
Asma'u (Husna) takwara yai wa mahaifiyar sa, ita ce ta biyun.
Safiyyah (Shahida) auta kenan.
"Allah ya raya su a tafarkin sunnah".
Baaba Habiba ta amsa da
"ameen summa ameen"
Ita kuwa a zuciyar ta ta amsa.
Tuni architect ya musu sallama akan ya tafi Kano nan da kwana biyu zai dawo. Duk sai take jin ta wani irin. Kwanan biyun da su Kai tare sun Saba don KO da yaushe ya na asibitin.
вarι мυ waιwaya 'вangaran naѕeer
Sai da ta jera masa maruka har guda biyar gyafan hagu da dama, ran ta ya matu'kar 'baci sosai. Ta ce,
"Da me kake ta'kama dashi? Kyau da dukiya ko? To ka sani, yanzu wallahi idan Allah ya ga dama cikin da'ki'ka sai ya canza maka kamannin ka. Wallahi ba na tunanin akwai yarinyar da zaka samu da za ta Kai wannan yarinya. Sai ka yi nadama Naseer, ranar kuka na man zuwan maka. Kuma wallahi idan wannan ranar tazo ka da ka nuna ka ma sanni balls kazo waje. Ba dai ka yi ma ta Saki uku ba, to wallahi wata daya na ba ka ka fito da matar aure KO in ce ita yar iskar dake hure maka kunne, tunda ita ka dai ka ke gani da gashi a ka. Fitan min a 'daki tun kafin na furta mummunar kalma a gare ka. Wawa wanda bai san ciwon kan shi ba".
Dafe ya ke da kuncin sa, tabbas mahaifiyar shi ba ta ta'ba 'daga hannu a man shi ba da wayan shi ba said yau. Wutar 'kiyayyar Mufeeda ce ta 'Kara nunkuwa a zuciyar shi. Kuma ya 'kudurta a ranshi babu Wanda ya isa ya saka shi ya kar'bi cikin da ba nashi ba.
Ficewa ya yi daga gidan gaba daya, dama a waje yai parking motar shi, bu'dewa yai ya shiga tare da firgar ta, bai tsaya a KO Ina ba, sai a wani tamfatsetsan gida. Horn ya yi, mai gadi ya, bu'de masa tare da fa'din
"barka da zuwa 'yallabai"
Wani abu yaji ya tokare masa a wuya saboda sunan da Shafi'u mai gadi ya Kira sa dashi, don't sunan tuna masa yai da Mufeeda, ya na 'daya daga cikin sunan da take kiran sa dashi.
"Kai shafi'u ka na San ka cigaba da aiki a gidan?"
"Kwarai kuwa yalla'bai" Shafi'u ya bashi amsa.
"To matu'kar ka cigaba da Kira na yalla'bai to abincin ka ya 'kare a gidan man". Ya na gama fa'din haka ya ja motar sa yai ciki.
Nasan masu karatu za suyi mamakindama Naseer ya na da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login