Showing 27001 words to 30000 words out of 115393 words

Chapter 10 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22910

kawai yaji bai yadda da ita ba. Slid window kawai ya ga ni an 'dan bu'de shi, shi kuma yasan Umman shi ba ta bu'de wannan window 'din sabida 'kadangaru. Sai ya sa ka hannu ya mai da window 'din ya rufe, sannan yq juyo yai sallama tare da shiga 'dakin haj Zulfah. Baaba Habiba da haj Zulfah suna kitchen suna 'dan 'kara kimtsa abubuwa. Ita 'kadai ce zaune a parlor da shayar da Ayaan ta ke da ya farka ya na 'yan koke koke, da kuma ta jiyo muryan shi sama sama ta jikin window, sai ta bar shayar da shi ta kwantar da shi tare da gyara jikin ta.
"Ina kwana yaya?".
"Lafiya 'kalau 'kanwa ta Mufeey, ya 'karfin jiki kuma da ba'kon waje?". Ya fa'di hakan ne tare da zama ya 'dauki Ayaan da idon sa biyu. 'Kurawa yaron ido ya yi, shima yaron kallon sa ya ke yi.
"Jiki ya yi sauki, alhamdulillah". Fa'din Mufeeda.
"To Alhamdulillah haka ake so ai. Ina su Ummah na da baaba Habiba?".
"Gamu nan" fitowar su kenan daga kitchen haj Zulfah ta amsa mashi.
"Ummah ta ina kwana? Ya 'yan jikokin na ki?".
"Gasu nan Alhamdulillah. Yau zaka fita da wuri kenan, don naga shirin fita ka yi."
"Eh zan fita, zanje Company, kusan sati ban le'ka ba, kuma akwai wa'yanda na saka P.A ya ha'da min zama da su karfe 10. Sannnan akwai Wanda zai zo ga ni na karfe 9".
"Eh gaskiya kam, gwara ka hanzarta. Ka karya??".
"Eh na karya, fitowa na kenan daga wajan mummy, tare muka karya ma da daddy".
"To Alhamdulillah tun da ka 'karya, dama ni fita ba'a karyan ba ce ban so".
" To Ummah ki min addu'a zan tafi". Sai kuma ya kalli baaba Habiba da run dazu take kallon shi ta na murmushi ya ce,
"Baaba an ta shi lafiya?"
"Lafiya 'kalau 'dan albarka". Baaba Habiba ta bashi amsa.
Aje Ayaan ya yi, kana ya mi'ke tare da fa'din
"sai na dawo".
" To Allah ya ki ya ye hanya". Duk suka ha'da ba ki suka fa'da. Shi kuma ya fice.


*"""""""""""""""""""""*
Zaune ta ke a gyefan haj Jummai ta zuba urban tagumi. Duk bayan second 10 sai ta ce,
"Uhmmm" sai ta wani Ja shi ma yadda duk Wanda ya ji yasan akwai wani abu.
Zuba mata idanu haj Jummai ta yi tare da fa'din,
"Wai lafiya Baby ki ke ta faman Uhmmm?"
Ta'be ba ki ta yi tare da 'kara fa'din,
"Uhmmm! Mummy ba dole ki ji ina ta fa'din uhmm ba, ke ki na nan ba ki san abunda ke faruwa ba. Hmmm wallahi mummy gwara ki ta shi tsaye akan yaa Nas."
Tuni hankalin Mummy ya ta shi, gyara zama ta yi ta re da fa'din,
"Ke baby ban san shirme, ki tafi straight to the point ki min magana, wallahi hankali na ya tashi".
Gyara zama Babyn ta kuma yi harda wani gyaran murya, sannan ta ce,
"Wallahi Mummy yaa Nas ya 'dauko miki bala'i. Ina wannan Matan da na ce miki yaa Nas ya dawo tare da su jiyaaa, har na ce miki har da jarirai guda biyar?".
Cike da 'kaguwa haj Jummai ta ce,
"Eh mai ya faru? Dan Allah ki fa'da min". Ta fa'di hakan ne gaban ta ya na wa ni irin bugawa, wadda idan har zai cigaba na wasu mintina, ba makawa hawan jinin ta ya tashi.
Baby ta ta'be ba ki tare da fa'din,
"To wallahi ba dangin wacce munafukar matar ba ce kamar yadda yaa Nas ya fa'da miki, don da kunne na na ji yau suna magana ita da daddy. Wai taimakon ta su ka yi, zaku ma su ri'ke ta ita da 'ya'yan kamar su suka haife ta".
"To ni mai ya shafe ni da hakan? Suje can ta matse musu 'yan dangin taimakon tsiya".
Haushi ya cika Baby saboda gulmar ta bai samu shiga ba. Amma sai ta gyara zama tare da fuskan ta haj Jummai ta ce,
"Ayya Mummy, ai ke ce abun tausayi ma a ciki. Abun dubawa anan shi ne, mai ya sa yaa Nas ya miki karyan cewa su 'din 'yan dangin ta ne? Ce wa fa ya miki 'yar ko 'kanwar ko yar ta ce, ta haihu zata zo mata yasan arba'in, shi ne ta saka shi ya taimako ya taho mata da su. Wallahi mummy akwai ayar tambaya akan wa'dancan mutanan. Kuma idan ba ki mi'ke tsaye ba, zaki iya jin an li'ka masa 'ya'yan a matsayin uban su".
Wani irin zabura haj Jummai ta yi tare da fa'din,
"Wallahi Sam bazata sa'buba, bindiga a ruwa".
Wayar ta ta raruma tare da danna wa architect Naseer kira. Shikuma a wannan lokacin wayar shi na meeting. Don sun shiga meeting da mutanan da ya sa a ha'da mishi meeting da su.
Sai da ta masa kira ya kai goma bai dauka ba. Sannan tai jifa da wayar ta fito fuuuuu kamar kububuwa.
Dai dai lokacin da haj Zulfah, Baaba Habiba da Mufeeda suka fito zasu shopping, baaba Habiba goye da Abid sannan Husnah a hannun ta. Haj Zulfah kuma goye da Shaheeda, Irfana a hannun ta. Ita kuma Mufeeda, Ayaan ne a 'kafadar ta, don bai kaunar goyo Sam. Duk sun ci kwalliya, bazaka ta'ba kallon Mufeeda ka ce ita ta haifi wa'dannan 'ya'ya ba. Ta yi kyau abunta, kurajan fuskan ta ne kawai suka mata cikaas.
Wani wawan burki ta jaaa a gaban su tareda 'kan'kance idamuwa ta nuna haj Zulfah da hannu tare da fa'din,
"Wallahi ki fita daga hanya ta da kuma 'ya'ya na, idan ba haka ba sai kin bar gidan nan wallahi. Wani munafuncin kuma kike shirin shiryawa da 'dana? To wallahi Allah ya fiki. Wa'dannan karuwar da kika kwasho don ku shirya yadda zaku kwashe dukiyar 'dana da kuma miji na, Allah bazai ta'ba baku sa'a ba. Kuma ki sa ni, wa'dannan...." Ta nuna baaba Habiba da Mufeeda wacce tuni tai sumar tsaye gaban ta lugude.
"Bazasu zauna a gidan nan ba. Sai dai idan gidan mai dattin hula da dattin 'dan kwali za'a kai su".
Wani murmushi haj Zulfah ta saki, idan da sabo ta saba da haushin uwar gidan na ta. Ta kalle ta tare da fa'din,
"Yaya lafiya? Wani abun na miki ban sani baa, fa'da min na ba ki hakuri babbar yaya ta, uwar gidan alhj Mudassir".
Wani 'kululu ne ya zo ya tsayawa haj Jummai a wuya, ta tsani wannan hali da haj Zulfah ta ke da shi. Sai ta takale ta da fa'da, mai makon ta bi ye masa sai ta saki wani shegen murmushi tare da 'kan'kan da kan ta irin ni bazan biye miki 'din nan ba.
"Munafuka annamimiya, yadda ki ke tunanin kin raba ni da miji na, wallahi ba ki isa ki raba ni da 'ya'ya na ba".
"In sha Allah bazan raba ki da kowa na ki ba yaya ta, uwar gida ta." Haj Zulfah ta fa'da ta na sakin wannan murmushin da ta saba. Sai ta 'kara da fa'din,
"Uwar gida, shopping zamu je in yi wani 'diya ta da kuma jikoki na, mai kike bu'katar na tawo miki da shi".
"Kan mai dattin hula da mai dattin 'dan kwali". Fa'din haj Jummai. Baby da ke bayan ta ta fashe da wani dariya irin abun ya ma ta da'din nan.
As usual haj Zulfah ta kuma sakin murmushi ta kalli baaba Habiba da Mufeeda ta ce,
"Ku gaishe ta, mahaifiyar Naseer ce kuma uwar gida ta".
Mufeeda ce jikin ta na rawa, don fisabilillah ta tsorata da Matar, a duk tsammanin ta haj Zulfah ce mahaifiyar Naseer. Ta ce,
"Ina kwana mummy?".
"Kan uwar ki kinji ko? Shegiya mai fuskar aljanu. 'Yan dangin karuwai da mayu".
Tsoro 'karara ya bayyana a fuskar Mufeeda, don jikin ta har rawa ya soma yi. Hakan da haj Zulfah ta ga ni ne, sai ta kama hannun Mufeeda da 'dayan hannun ta suka soma tafiya. Da ma ita Sam baaba Habiba ba tai niyyar gaishe ta ba. Tunda haj Zulfah tai presenting 'din ta a matsayin mahaifiyar Naseer ta ce saaam bai gaji halin ta ba, Na mahaifin sa ya gada.
Ita kuma haj Zulfah 'Dan juyowa tai ta kalli haj Jummai ta re da fa'din,
"To sai mun dawo yaya".
"Ku ma mutu a hanya, 'yan iska kawai". Fa'din haj Jummai.
Ita kuwa haj Zulfah ba ta kuma kallon in da ta ke ba, suka nufi wajan mota suka shiga, Bala driver ya ja suka bar gidan.
A cikin mota kuwa sai kuka Mufeeda ta ke yi. Haj Zulfah tai lallashin amma ta'ki yin shuru. Sai da haj Zulfah ta nuna matu'kar 'bacin rai akan kukan sannan ta yi shuru. Ta kuma 'kara mata da cewar ka ka da ta saki ta ta da hankalin ta akan maganganun da haj Jummai ta yi, sam babu wanda zai Kore su a gidan, ai ba zaman ta suke yi ba,ba kuma iita ce mai gidan ba. Mai gidan da kan sa ya saka aka kawo su, don haka ba mai korar su.
Ba 'karamin sayayya haj Zulfah tai masu 'yan uku da su kan su ba, daga kan irin madarar da ya kamata 'yan biyar su sha (Dr Haroon ya rubuto ya turo ma architect) duk ta sayo masu uban yawa. Ga kayan sawan Mufeeda irin su abaya, readymade, atampopi, lesuka har da shadda da takalma. Baaba Habiba ma ta sayan mata. Daga nan shagon 'din ki aka yi da su direct. Daga shago 'dinki su kai wajan cosmetic, mai shagon ya kalli Mufeeda da yanayi skin 'din ta ya ha'da mata mayuka masu saka laushin fata da kuma gyara jiki, sannan kuma ya ha'da mata na 'kurajan fuskar ta.
Sun da'de a kasuwa, sai da 'yan biyar suka fara koke-koke ne su juyo gida. Ba 'karamin ku'di haj Zulfah ta kaso ba. Haka suka dawo gida da kaya ni'ki-ni'ki.
Baby iyayan gulma, ta ma hango su ta juya ta kira haj Jummai ta re da nuna mata su da irin waya da Bala driver da Mai mai bawa flowers ruwa suke kwasa suna kai wa part 'din haj Zulfah.
Kwafa ta yi tare da fa'di,
"Da ni kuke zancan, wallahi Zulfah sai na saka kin kwashi kashin ki a hannun ki".



*_KADUNA_*

" 'Yar kasuwa! 'Yar kasuwa!! 'Yar kasuwa"
Wata matashiyar budurwace ta ke kiran wata budurwa dake Raman fifita wuta tana tuyan awara. Wacce ake kira da 'Yar kasuwa ta 'dago ta kalle ta tare da fa'din,
"Yauwa Mashkura kamar kin san ina nai man ki wallahi".
"To ai ga ni yanzu a gaban ki". Wacce aka kira da Mashkura ta fa'da tare da 'daukar awara guda 'daya da yanzu aka tsame a cikin mai, zama ta yi akan wani dakali masu sayan awara suke zaman jira idan akwai layi ko kuma ya na kan wuta ba ta tsame ba.
"Zabba'u gashi inji innar mu ta ce in kawo miki ku'din awarar ki da ta aiko Salmanu jiya kika ce ya koma da ku'din ba ki da canjin dari biyar". Wani 'Dan yaro ne ya mi'ka mai suyar warar naira saba'in. Kar'ba ta yi tare da fa'din,
"To shehulle nagode". Ta karbi ku'din tare da kuma mi'ka masa awara kuda 'daya. Aikuwa ya karbe tare juyawa ko godiya.
"Ke dai wallahi Zabba'u bazaki ta'ba canza halin ki ba, ni mamaki na ke ma da had yanzu jalin warar nan bai 'kare ba. Ke kenan kullum kyauta da kayan sana'a. Sai ka ce abunda kika fito yi kenan". Fa'din Mashkura ta ya yamutsa fuska tare da 'kara 'daukar wara 'daya ta jefa a baki.
Murmushi Zabba'u ta yi, cikin zuciyar ta tace,
"kaji min 'ya, bayan ita ma duk tazo waje na sao ta ce kusan fin ta 'dari ha hamsin kuma ba ko sisin ta, dan kawai na 'dauki ta goma na ba Shehulle shi ne ta ke mita. Idan da zan karye ai da tuni ke kika fara 'karya ni". Amma a zahiri sai ta ce,
" ke kuwa Mashkura ai babu ko mai, Wanda ka bayar ai shine na ka, kuma ni sadakar ce ma take 'kara bu'damin kasuwar".
Mashkura kuwa 'kara ta'be baki ta yi tare da fa'din,
"Ke dai ki ka sani. Ni nai man me kike min?".
Sai da Zabba'u ta kwashe awaran da ke cikin mai, ta zuba wani ka na ta juyo ta fuskanci Mashkuran tare da fa'din,
"Kura, abunda na ke ji a gari gaskiya ne?" Wani lokacin haka suke kiran ta, sai su cire farkon sunan.
Mashkura ta yamutsa fuska Wanda ya kasance 'dabi'ar ta tare da fa'din,
"Wace magana kenan?"
Zabba'u ta 'kara gyara zama ta kalle ta da kyau ta ce,
"Ji nai a gari ana ra'de-ra'din wai zaki auri Naseer mijin aminiyar ki Mufeeda".
"To meye na saka _WAI_ kuma? Ai ya wuce wai. Haram ne auran mijin 'kawata da suka rabu".
"Suka rabu ko kika raba su? Wallahi Kura ina jiye miki tsoran Allah. Wallahi kin zalinci Mufeeda, kin ci amanar ta, kuma Allah ba zai kyale ki ba akan zagon 'kasan da kika ma ta." Fa'din Zabba'u.
"Allah ko? To ki fara saka mata ma ke da kan ki ka mun Allah ya saka mata. Ni babu abunda nai wa Mufeeda, ita tai wasa da damar ta. Kuma auran Naseer ba bu Wanda ya isa ya hanani". Ta na gama fa'din hakan ta Ja tsaki tare da barin wajan.
Girgiza kai Zabba'u ta yi tare da fa'din,
"lallai makashinka na tare da kai. Allah ka tsare mu ka kare mu daga ma'kiyan mu, ka kuma sa mufi karfin zukatan mu, mukuma cika da kyau da imani".


*______________*
"Marwanatu bazan bada ba, idan zaki tattaro ki dawo to ki dawo, idan kuma bazaki dawo ba. Ki yi ta zama. Kwandala bazan sake turo miki ba. Nagaji wallahi na gaji da kawo kawon ku ke da mahaifiyar ki, a wajan mahaifin na ki ma ba tsira nai ba, shegen ro'kon shi ya ishe ni, yai ta kunya ta ni cikin jama'a kamar ba siriki na ba. Jiya na aiko miki da dubu takwas, yanzu kuma ki kira ni ki ba fa'damin madarar ki ta 'kare, kuma kina bu'katar pampas shi ma ya 'kare bayan na san 'karya kike yi. Yau satin ki biyu da zuwa wankan gida. A cikin sati biyun nan ba ba ki ku'din da suka haura dubu hamsin. To wallahi ban 'kara baki kwandala. Idan kin ga dama ki dawo, idan kuma bazaki dawo ba. Ki yi ta zama ni dai kwandala ban 'kara baki". Ya na gama fa'din haka ya katse wayar shi."
Juyowa tai ta kalli mahaifiyar ta ta tare da fa'din,
"Mai zogale kinji fa cewa yai ko kwandala bai 'kara ban, idan zan dawo in dawo, idan kuma bazan dawo ba in ta zama shi bazai 'kara ban ko kwan'dala ba".
Mai zogale ta buga cinya tare da fa'din,
"Ohh haka 'dan iskan ya fa'da miki? To zai ko ci kan babbar bura uba shi. Dani ya ke zancan. 'Dan kudin nan fa da nake sakawa kina kwa'kulowa da shifa nake miki zubin adashi ke ma ki fita kunyar facalolin ki. Ki ri'ka Shiga ana ca'bawa dake, ke ma ki fiito a 'yar masu shi, amma shine zai mana ba'kin ciki. Ayya ma kina amfani da magungunar da nake aiko miki da shi kuwa?".
" wallahi Mai zogale ina amfani da shi, har Wanda kika aiko min 'din nan mai kama da kuka Wanda kika ce, a duk lokacin da nake so wani abu wajan shi ba barba'da shi akan harshe na kamin na mishi magana". Fa'din Marwa.
"Yauwa 'yar gari, duk abunda na aiko miki dashi, ki ri'ka 'korarim amfani da shi".
" Yauwa Mai zogale, ki yi wa baba magana ya rage yawon zuwa wajan baban Abulkhairi ro'kon ku'di. Kin ga yauma sai da ya 'kara goran ta min".
"In dai Kallah ne, ki bar ni da shi, zai zo ya same ni. Kuma batun mijin ki, bazaki koma ba sabida ku'din nan da ya ki turowa, sai na yi maganin shi".
"Gaskiya mai Zogale ka da a 'dau lokaci da yawa, don nasan halin Musa wallahi zai iya kyale ni, ko kuma wannan shegiyar uwar tasa ta ce masa ya rabu dani yai wani auran, kin san fa ba sona take ba".
"Kada ki damu Marwa, har ita zan miki maganin ta".
"Yauwa Mai zogale, shiyasa nake kara sonki kullum." Tare da kai mata hannu suka tafa.



**********
"Ka sani, babu hannu na a cikin wannan auran da za ka yi. Ka da ka sake ko da wasa ka kawo min ita nan gidan. Ko fuskan ban so na ga ni. Kuma na shaidawa Mummyn ka ta saudiya komai. Kuma ta ce ta kira wayar ka ba ta shiga. Idan ka ga dama ka kira ta. Tashi ka bar min 'daki". Mahaifiyar Naseer ne ke wannan maganar.
Naseer da ke dur'kushe a gaban ta kamar tsohon munafuki ya ce,
" ki yi hakuri mom"
"Get out!!" Ta fa'dq a tsawace.
Sum sum ya mi'ke ya fice. Kai tsaye gidan sa ya nufa, ji ya ke duniyar ta masa zafi gaba daya.
Zama yai akan 3sitter ya lumshe idanun shi, can kuma ya sauki wayar shi yai dialing wata number, bugu biyu aka 'daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login