Showing 75001 words to 78000 words out of 115393 words
zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 37_*
"Har ga Allah ni dai an shiga 'hakki na". Fad'in Naseer cikin zuciyar shi.
"Sannun ku da zuwa aunty Nafeesa". Fad'in Naseer ya na 'ya'ke da kuma sosa kai.
Aunty Nafeesa ta kalle shi tare da fa'din,
"Ango², an tashi lafiya?, ya matar ta ka?".
"Lafiya k'alau aunty. Ga ta nan". Naseer ya fad'a tare da nu na Mufeeda.
"Sannun ku da zuwa aunty, ina kwanan ku?". Fad'in Mufeeda.
Aunty Nafeesan ta 'karaso wajan Mufeeda ta re da dafa ta, ta ce,
"Lafiya 'kalau 'yata. Ya gajiyan jiya da kuma ba'kon waje".
Kai a 'kasa, Mufeeda ta furta,
"Lafiya 'kalau aunty".
*******
Zuwan su aunty Nafeesa, ai kamar dama ya bu'dewa mutane. Daga 'yan uwa da abokan arziki, har mutanan unguwa cincirundon zuwa ganin amarya ake, ko in ce cin cin².
Tuni Aunty Nafeesa ita da su twins da su ma su ka iso, su ka shiga kitchen tare da sake gyara shi tsaf, su killace komai a muhallin sa.
Naseer kasa zama yai a gidan, domin ko ya d'aga waya ya kira Mufeeda akan tazo, kasa zuwa ta ke yin saboda idanun 'kanwar mahaifiyar sa da kuma jama'a da ke ta cincirundon shigowa. Kun san ance amarya ko ta buzuzu ne, farin jini gare ta. Balle kuma ga maganar cin², kun san mutanan mu da son banza. Yar layi ce za ta zo, sai ta taho da 'kawar ta. Idan sun koma gida, sai 'kawar ita ma ta kintsawa 'kawar ta, ita ma 'kawar sai ta fa'dawa 'kawar ta, sai ki ga sun ha'da kai sun sake zuwa duka tare. To amarya kai ya 'dau zafi, ko ga ne su ma ba yi za tai ba. 🤣🤣
Naseer ba by yadda ya iya, haka ya tattara ya bar masu gidan ya na 'kun'ku nai cikin zuciya. Amma a zahiri sai washe baki ya ke ya na gaida mutane.
Mashkura kuwa, ta na gida yau ba ta samu damar dawowa gidan 'kawar tata ba. Sakamakon zazzafar zazza'bin da ke damun ta saboda kukan da ta sha jiya da ya haifar mata da ciwon kai na 'bari d'aya.
💜💙💚❤️
Sai gab magriba kowa ya watse bayan sun gyara mata gida, da kuma wanke kayan abinci da aka 'bata, ka na suka saka turarun ka wuta, 'daki ya game da 'kamshi.
A na idar da isha'i, Naseer ya dawo gida.
Key ya sa ya bu'de. Ba bu kowa a parlour. Sama ya hau, kai tsaye ya nufi 'dakin ta da san'da. A hankali ya turo 'kofar, kasancewar 'kofar ba ta da 'kara, Mufeeda ba ta ji 'kara ba, sai ji ta yi an 'daga ta caak.
Wani irin zabura ta yi za ta kwalla 'kara. Yai saurin juyo da ita tare da ha'de bakin su.
Zaro idanu Mufeeda ta yi lokacin da tai arba da fuskan shi.
Rufe idanun ta tai ta bu'de. Sai hakan ya ba da wani irin style tare da 'karisa kashewa Naseer jiki. 'Kafafuwan su bai iya 'daukan su ba, sai da suka zu'be a kan gado. Da kyar ya tsagaita tare sauke numfashi, ya furta a cikin kunnan ta,
"I really miss you Habibaty. Su KB sai zaulaya ta su ke su na min dariya, Allah ji nai.....". Wayar shi da ke ringing ta katse shi. 'Dauko ta daga cikin aljihun wandon shaddar da ke jikin shi da a yanzu duk ta yamutse. Wani irin zaro idanu ya yi yana kuma rufe bakin shi. Bai 'dauka ba, sai da wayar ta gama ringing, ka na ya bi bayan kiran. Bugu biyu ta 'daga ta na wani murmushin da ya ke jin sautin sa har cikin kunnan shi.
"Ummu na I'm....".
"Not a word". Ummu na ta katse shi ta na dariya.
"Da ma ai na fa'da maka Abie, duk lokacin da kai aure za ka manta da Ummun ka. Gashi yau dai tsawon kwanaki hu'du, rabon da kai waya da Ummun ka, da ai a yini muna wayar a 'kalla sau uku".
'Kasa cewa komai Naseer yai, sai 'yan dumi² ya ke yi na borin kunya.
Sosai Ummu ke dariya, ta ce,
"Ni ba ni 'diya ta mu gaisa, mun b'ata daga yau. Na canza ka, nai sabuwar d'iya yanzu".
"Ummu nah kar mu yi haka da ke, afwan Ummuuu".
"Apology accepted. Ai nasan hidimar bikin ce tai yawa. Shiyasa ni ma ban takura ka ba. Amma ai nasan Ummun ka na nan a zuciyar ka".
"Wannan haka yake Ummu Nah". Fa'din Naseer ya na dariya, farin ciki kwance a fuskan shi.
"A ba ni 'yata mu gaisa". Fa'din Ummu.
"To ummu, ai ga ta nan". Fa'din Naseer tare da mi'kawa Mufeeda wayar.
"Assalamu alaikum, Ummu nah ina wuni?". Mufeeda ta fa'da kamar yadda ta ji Naseer na kiran ta.
Ummu nah ta ce,
"Lafiya 'kalau 'diya ta, Allah ya yi, ni bazan halarci bikin ba, ni da 'ya'ya. Kin san ni a saudiya na ke da zama, amma in sha Allah, saura shekara biyu, mu tattaro mu dawo gida gaba 'daya. Zan zo na gan ki in sha Allah".
"To Ummu nah, Allah ya dawo da Ku lafiya, ya sa kuma muna da rai". Fira sosai Ummu nah su kai da Naseer, ka na su kai sallama ya yanke wayar ya na mai jin da'din Ummun shi ta kuwa dawowa.
Naseer ya kalli Mufeeda da tai tagumi ta na kallon sa.
Kallon ta yai shi ma tare da hura mata iska a idanu, ya 'dage mata gira 'daya kamar yadda ta ke masa idan ya na kallon ta tare da fa'din,
"Ya dai kallon fa?".
Murmushi ta sakar masa tare da fa'din,
"Ina kallon kyakkyawar fuskan miji na ne".
"Iyeen ba, dan Allah dagaske mijin ki ne? Anjima ka'dan zan ga ne hakan". Naseer ya fa'da ya na 'dage mata gira.
Kauda maganar ta yi tare da fa'din,
"Mu je dinning ka ci abinci. Na shirya maka girki mai da'di".
"Me sona, wai girki ki ka yi? Ni fa wallahi har ga Allah ban so ki aiki wahala. Yau ma ba ki ji haushin da na ji ba, da ba'ki su kai ta zuwa, za su gajiyar min da ke".
"Ha'kuri za kai, na 'yan kwanaki ne".
Zaro idanuwa yai tare da fa'din,
"Ki ce ma ba na yau ba ne kawai, lallai ashe gobe mai gadi zan wa kashe di akan duk wanda yazo gobe, ya ce masu mutanan gidan ba su nan, sun tafi honeymoon".
Zaro idanu Mufeeda ita ma ta yi tare da fa'din,
"Yallab'ai dan Allah ka rufa mana asiri ka da kasa a tafi damu a baki".
"Idan ma a hanci ne, an da'de ba'a tafi ba". Naseer ya fa'da tare da saukowa a kan gadon ya 'dauke ta caak su ka nufo palon, bai aje ta ba, SAI da ya kai ta har dinning ka na ya aje ta a kan kujera ka na shi ma ya jaa ya zauna.
Bu'de kulan yai, sai yai arba da jolof 'din shinkafa da yaji kayan lambu, sai da ya lumshe ido.
Mi'kewa tai za tai serving 'din shi ya dakatar da ita. Shi da kan shi ya zuba masu a plate tare da cokali 'daya.
Ita ya soma ba, ka na shi ma ya 'debo ya saka a baki.
"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka ni'imta ni da mata wacce ta iya girki".
Sosai Mufeeda ta ji da'din yabon girkin ta da yai.
Haka su kai ta ciyar da kan su, domin kama² su kai ta yi. Idan ya ba ta, sai ta kar'ba ta ba shi.
Bayan su gama, tare su ka tattare wajan, ka na ya 'dauke ta caak su kai 'daki ya aje ta akan gado.
"Ina zuwa". Naseer ya fa'da tare da fita.
Ita kuma tai saurin shiga ba yi domin tai wanka. Har ta fito ta kimtsa cikin tattausan kayan bacci ta kuma feshe jikin ta da turare bai shigo ba.
Gashin ta, ta warware sai da ya sauko tsakiyan bayan ta. Ka na ta 'dau cumb ta na tajewa.
Lokacin Naseer ya turo 'kofa ya shigo, da alama shi ma wankan ya je ya yi. Domin sanye ya ke cikin kayan bacci.
'Karasawa yai wajan madubin tare da 'karban cumb 'din da ke hannun ta ya shiga taje mata kan na ta tare da 'daure mata shi, bayan ya shafa mayuwa da kuma turaran gashi.
"Ya yi kyau, kamar ka yi aiki a shagon saloon". Mufeeda ta fa'da.
Juyo da ita yai tare da rungume ta, ya furta mata cikin kunnan ta,
"To a kan ki meye bazan iya koya ba".
Tun daga nan Naseer ya soma hawa titin da'din kowa. (Tuni na ja sandar 'kafa ta tare da jawo masu 'kofa).
💓💘💓💘
Washa gari da safe, Naseer an yi 'banna, sai nan² da Mufeeda ya ke yi. Ita kuwa sai kuka ta ke masa tare da shagwa'ba da kuma narke ma sa (Ai ko na ce yarinya ki yi, lokacin ki ne)🤣🤣🤣
Allah kuma ya taimake su, yau mutane ba su tashi takura masu ba, sai karfe biyu.
Nan ma dai Naseer ba yadda ya iya, haka ya kuma barin masu gidan.
*KURA* ma ta zo, sai da kallo 'daya tai wa Mufeeda ta ga ne an kashe boss. Aikuwa ji ta yi kamar ta caka mata wu'ka tsabar kishi.
'Daki su ka haura su biyu, *KURAN* ta kalli Mufeeda ta re da Fad'in,
"Aminiya ki ce har an kashe boss?".
"A wani film ke nan?". Mufeeda ta tambaye ta kamar ba ta ga ne mai ta ke nufi ba.
"Ban san WULA'KANCI fa, ai kin ga ne abunda na ke nufi". Fad'in Mashkura.
"Ni ban ga ne ko mai ba".
Mashkura tai dabaran amma fir Mufeeda ta 'ki ce mata komai, don ita ba jahila ba ce, da za ta zauna na furta sirrin mijin ta wa 'kawa, wanda ta san haramun ne".
*BAYAN SATI BIYU*
Ba'karamin soyayya ake zubawa ba a gidan Naseer. Naseer na matu'kar kulawa da Mufeeda. Ko mai tare su ke yi, girki, gyaran 'daki, wanka, da duk wasu aika ce aika cen gida kasancewar har yanzu hutun amarcin na shi bai 'kare ba.
Sun je gida wajan Mommah sun gaishe ta, Mommah sai 'kara Japan Mufeeda ta ke a jiki. Kasancewar lahadi ne, Daddy ma na gida, aiko shi ma ya ware ya na ta jaan Mufeedan a jiki. Har yau kuwa bincike ya ke akan ta.
Sai bayan isha'i su ka bar gidan su Momman ka na su 'day hanyar gidan Kallah.
Lokacin da *MAI ZOGALE* tai arba da Mufeeda kusan ha'diye zuciyar ta ta kusa yi, domin Mufeeda tai wani kyau da 'kara haske da kuma 'kiba. Ki na kallon ta kinga wacce hutu ya ratsa ta.
Lokacin da za su tafi, Mufeeda ta zuge jaka, ta fiddo dubo goma, ta bai wa kallah biyar, *MAI ZOGALE* biyar.
Ba'kin ciki kamar zai kashe *MAI ZOGALE*, ta zo a ce Marwa ce ke wannan kyautar a layi.
Haka Mufeeda ta baro su ba'kin ciki faal ran su.
💚💚💚💚💚
Sai ta mi'ka masa briefcase 'din, shi kuma ya mi'ko hannu zai karb'a, sai ta janye tare da fad'in,
"Yallab'ai, yanzu tafiya za kai ka bar ni?? Wallahi I'm going to miss you a lot". Ta 'karishe maganar ta re da narke fuska.
Jawo ta yai sai da ta fa'da jikin sa, ya ce,
"Allah idan ki na maganar nan, zan aje aikin in dawo in zauna da ke a gida".
"Ahhh ba haka na ke tufi ba, kawai dai zan yi kewar ka ne".
"Ni ma zan yi kewar ki". Naseer ya fa'da tare da manna mata kiss a goshi.
Briefcase 'din ya kar'ba tare da fa'din,
"Mai zan samu anjima?".
Kashe masa idanu tai tare da fa'din,
"Abun da'di har saika ture". Mufeeda ta fa'da tare da kuma ra'da masa wani magana a kunne.
Hannu ya ba ta su ka kashe tare da fa'din,
"Yauwa 'yar garin".
Dariya ta yi tare da fa'din,
"Allah ya tsare, Allah ya ki ya ye ka da sharrin 'karfe".
"Ameen² habibty. Mai zan taho miki da shi?".
"Kai". Fa'din Mufeeda.
"Eh kai na ke so ka dawo min cikin 'koshin lafiya".
"To an gama. In sha Allah zan dawo lafiya. Ke dai ki ta min addu'a".
"In sha Allah yallab'ai". Fad'in Mufeeda.
Key ya wa motar tare da yin reverse. Dama tuni mai gadi ya wangale masa gate.
Bye bye Mufeeda ta masa tare da hura masa kiss. Cafkewa yai tare da dafe sai tin zuciyar shi, ka na ya huro mata shi ma.
Ya na fita, ko minti biyar ba'ai ba, Mashkura ta shigo.
Lokacin da ta danna abun da ke nuna cewar akwai mutum a 'kofar 'daki, Mufeeda ta zo ta bu'de. Ta na arba da ita sa saki ihun murna tare da rungume ta.
Mashkura ko ya'ke kawai ta ke ta yi, na ciki na ciki. Don ga ni ma ta yi Mufeedan ta 'kara mata wani uban kyau da haske kamar me yaron ciki.
"Mufeeda ko dai ciki gare ki? Wannan irin 'kiba haka da kyau. Kin ga yadda ki ka 'kara haske".
Juya idanu Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Ba ni da komai, kawai tsabar kulawa ne da nake samu daga yalla'bai. *KURA*, wallahi Naseer *HEAVEN SENT* ne a gare ni. Ji na nake cikin aljannar duniya. Hmm *KURA* aure akwai dad'i idan ki kai da ce da miji irin yallab'ai".
"Ke! To ki kiyayi kan ki. Na miji ne fa, *MAN* ne faah. To ba 'dan goyo ba ne. Idan kuma ki ka goya shi, to wallahi ina mai tabbatar mi ki da sai kuna tsakiyar kasuwa zai 'balle".
*MAMAN UMMEE*✍🏼
*AKA*
*MATAR SAYYADEE*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 38_*
Dariya Mufeeda ta yi sosai, ka na ta ce,
"Wannan magana duk shirme ce wallahi. Ke ina ki ka san hakan bayan ba ki ta'ba aure ba? A titi kawai fa ki ka tsinci maganar shine ke ma ki ke amfani da ita. To ni dai na goya abunda har da saka zani wallahi. I'm sooo much in love wallahi. Wallahi ina wa yallab'ai wani irin 'kaunar da ni kai na bazan iya kwatanta shi ba. Kuma in sha Allah zan yi matu'kar k'o'kari wajan yi masa biyayya. Domin ita ka'dai ce sakayya ta agare shi".
Ta'be baki Mashkura ta yi, tare da fa'din,
"Lallai kin yanka wa kan ki kazar wahala".
"Naji d'in". Fad'in Mufeeda tare da mi'kewa ta nufi kitchen don kawo wa Mashkura abun kari, don ko takwas na safe ba ta yi ba.
Mashkura kuwa bin ta tayi da wani kallon tsana tare da furta magana cikin zuciyar ta,
"Wannan hanyar ba ta yi ba kenan. Lallai dole na canza sabon salo".
Daga tafiyar Naseer aiki, zuwa wucewar Mashkura, ya kira Mufeeda don jin lafiyar ta kusan sau bakwai. Abunda ya 'kara ba'kan ta zuciyar Mashkura ke nan da ganin irin kulawar da Mufeeda ta ke samu wajan Naseer 'din.
Mashkura ba ita ta koma gida ba, sai biyar na yamma, lokacin Naseer ya na gab da dawowa. Dama ita Mufeeda addu'a ta ke ta yi akan Allah ya sa ta tafi