Showing 102001 words to 105000 words out of 115393 words
ni, shiyasa bai iya cewa komai ba, amma da so samu ne, sai ya maka su a kotu.
Sai a sannan mal Ahmadu ya zaiya ne wa Malam da Fatima halin da ake ciki da Mufeeda. Shi Malam 'din ma sai a lokacin ya ke sanin Mufeeda ba 'diyar su ba ce. Ba 'karamin kuka Fatima tai ba da ta ji ba'asan in da 'Yar ta ta ke ba. Sai dai fa mal Ahmadu bai fa'da musu irin azabar da aka shaidawa daddy Naseer yai wa Mufeeda ba. Cewa yai kawai sa'bani ne ya shiga tsakani har suka rabu, shi kuma KALLAH ya 'ki kar'ban ta.
Sosai Malam yai addu'a akan Allah ya baiyanata sannan kama yai masu al'kawarin zai yaya su da addu'a.
Shatara ta arziki daddy yai wa Malam tare da kyautar dubu ashirin ka na yai masa shatar mota dan Malam 'din ya turje akan ba zai kwana Kaduna ba.
Mommah ta jawo Fatima a jiki sosai. Don Mommah ta girmi Fatima sosai, ita 'din ba za ta wuce shekaru 38 zuwa da 39 ba, Mommah kuma ta fi arba'in da hudu.
Nan 'dakin da aka baiwa mal Ahmadu Fatima ta tare, duk da mal Ahmadu ma ya ce shi gidan sa zai koma gobe. Kuma daddy bai musa masa ba.
*MARWANATU*
Tunda ta bar gida ba ta tsaya a ko ina ba sai wajan 'kawar ta suka 'dugun Zuma su kai TAFA, dama 'kawar tata ta na da 'daki a can. Tu ni ta soma harkan karuwan ci kuma ta shiga da 'kafar dama. Domin tun da taje can customomi da dama su ka juyo kan ta. Sosai ta ke samun ku'din, domin duk wanda yai masha'a da ita, 'yar 'dari biyar zuwa 'dari takwas ake ba ta duk mutum 'daya. Har ta samu ta kama 'dakin ta ta bar squatting da 'kawar ta da ta kawo ta bariki. Likafa ta ci gaba, yanzu har lesbian ta ke yi. Ta yi 'bulin hanci har biyu ta saka barima. Ga 'bulin kunne tun daga farko har karshan kunne duk ta saka barima. 'Kafarta kuwa, chain ne ma'kale da kuma zobe a yatsun 'kafar na uku. Hatta cibiyar ta sai da ta sakawa barima da harshan ta. Ka na ganin ta ka ga ri'ka'k'kiyar karuwa 'yar lesbian. Yanzu haka ma wani alhaji ne ya 'dauke ta tazama daduron sa, duk da ta na cin amanar shi a bayan idanun shi, domin ta na kawo maza da mata har gidan da ya ajiye ta su na masha'a da shaye². Duk da matan ba damun sa su kai ba, don har ku'di ya ke biyan su su yi a gaban shi ya na masu video.
*MAI ZOGALE*
Tunda Marwanatu ta tsallake tai tafiyar ta karuwan ci, abubuwa su ka 'kara ta'bar'barewa. Domin hatta ma'kota sun fara takura da warin da ke shigo masu gida. Ga zarnin fitsari da warin kashi. Ga uban yunwa da ''kishirwa da ke addabar ta. Kwanan Marwanatu biyu da tafiya *MAI ZOGALE* ta amsa kiran ubangiji bayan ihu da fizge fizgen da ta ke ta yi har rai ya fita.
Kwana biyu babu Wanda yaa duba ta balls a San ta mutu. Gashi ta kumbura ta yi suntumm har ta fashe tsutsa na fita daga jikin ta.
Washa gari ne da mal Ahmadu da matar shi da kuma su daddy da Mommah har da twins. Tun daga bakin 'kofar gidan su ka to she hancin su saboda azabar wari. Dakyar daddy da mal Ahmadu su ka shiga suka ga halin da *MAI ZOGALE* ta ke ciki. Da kyar da ro'ko makota suka shiga aka mata wanka tare da sallah aka kai ta makwancin ta kana suka tsaftace gidan yai fasali. Tuni kowa ya watse, dama ba gaisuwa ake zuwa yi ba, da yawan mutane ma barka su ka zo yi wa mal Ahmadu da Fatima.
Washa gari daddy ya saka aka kawo uban su furnitures aka jera a ciki da parlour dake gidan, kana aka saka labulayya masu tsada har electronic, plasma 'katoto da home theatre kamar 'dakin amarya.
Tuni mal Ahmadu da Fatima aka tuna da. Soyayya su ka shiga zubawa Wanda basu samu damar yin ta da ba. A gyefe 'daya kuma su na addu'a da ro'kan Allah ya bayyana masu Mufeedan su a duk inda ta ke.
*KALLAH*
Kwanan shi biyu a station. Washa gari da za'a mi'ka shi kotu, ya tashi da gagarumar hauka. Domin tsirara ya yi yana ta ihu tare da fizge². Gaba 'daya station 'din nan sun kasa controlling 'din shi. DPO ne ya ce su sake shi kawai. Aiko ba b'ata lokaci suka sake shi ya nausa titi da gudu tumbur sai soshe² ya ke yi tare kyalkyalewa da dariya. Can kuma sai ya hau rawa ba ki'da.
Tuni yara sun yanyame shi suna tsokalar shi ya na bin su da gudu. Wasu har dutsi su ke 'dauka su na kwa'da masa aka. Jini sai bin jikin shi ya ke. A kan bola ya ke kwana tare tsince tsince kayan bola ya zuba a 'katuwar jaka wai shi ya na SAI da kaya.
*GA SHI NAN NA 'KARA MAKU, NA GOBE NE DON BA ZAKU SAMU BA GOBE SABIDA HALIN NETWORK*
*MATAR SAYYADEE*
*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
*AKA*
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 47_*
Ko da mal Ahmadu ya ga 'dan uwan shi cikin hauka, ba 'karamin tashi hankalin shi yai ba. Sawa yai aka kamashi tare da kai shi gidan mahaukata (psychiatric) aka rufe shi a can.
*KANO*
Naina tsabar farin ciki har rasa in da zata saka kan ta ta yi, lokacin da Jawad ya sanar da ita ta kasance a cikin shiri don cikin satin gaba za su koma *Germany*.
Lukman kuwa ya daddage ya na ta baiwa Baby kula da soyayyar dole da mummy ta saka ya ke nuna mata. Sosai ya jawo ta a jiki tare da nuna mata illar shaye². Alhamdulillah kuma ta gamsu, domin 'dan kulawar da Lukman 'din ya ke bata ba 'karamin sata farin ciki da kuma canza ta yai ba.
'Bangaran Mufeeda kuwa, hankalin ta a tashe yake, domin har ga Allah idan ta ce ba ta son Naseer, to ta yi 'karya. Sai dai wani zuciyar na garga'din ta akan ta rufawa kan ta asiri ta ce masa yai ha'kuri. Don gaskiya idan ta amince ba'karamin Marsala za'a samj ba. saboda mahaifiyar sa ba 'kaunar ta ta ke ba, ga kuma 'yan uwa da take son ha'dawa fa'da ta dalilin son da suke mata.
Wayar ta ma kashe sa tai gaba 'daya don ka da Naseer 'din ya takura mata da kira. Gashi Innah Huwaila ta kanainaye ta mai da ta 'dakin ta da zama. Shikuma Naseer nan ya ke wuni duk weekend.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Alhaji Aliyu ya sauka a 'kasar sa bayan kusan shekaru goma. Sosai ya ga canje² a garin nasa. Alhj Mudassir ne da kan shi yaje airport ya 'dauko 'dan uwan nasa ya na mai tsananin farin cikin ganin sa. Kai tsaye gida suka nufo, gaba 'daya zuri'ar Inna Huwaila da ita kan ta Innar su ka yo waje domin tarban alhaj Aliyu. Inna Huwaila sai washe baki ta ke yi ta re da fa'din,
"Maraba 'dan gudun hijira. Ka da ba din danne zuciya ta da na ke ba, ai da tuni nai 'batanci da la'ana. Ace don kawai na maka gata, sai ka guje ni ka koma 'kasar arna da zama. Ni dai Allah ya sa ma baka kwaso 'dabi'ar su ba".
Murmushi kawai alhj Aliyu ya ke yi. Dur'kusawa yai tare da fa'din
"Ina wuni Innah? Mun same ku lafiya?".
"Eh to, lafiya ba lafiya ba. Amma dai ka shigo ka huta tukun kamin na kora maka baya ni"
Murmushi ya 'kara yi tare da amsa gaisuwar da yara ke ta jero masa.
Idanuwan sa ne ya sauka akan Mufeeda. Gaban shi ne yaji ya buga da 'karfi. Ita kuma hakanan taji ta kasa 'dauke idanun ta a kan shi ita ma zuciyar ta na tsinkewa.
Alhj Aliyu ya mai da kallon shi izuwa ga alhj Mudassir tare da fa'din,
"Yaya wannan kuma 'yar wacece?".
Hannun shi alhj Mudassir ya kama tare da fa'din,
"Mu shiga ciki ka kimtsa, sai muyi maka baya ni a nutse"
*BAYAN AWA BIYU*
Gaba 'daya hankalin alhj Aliyu bai jikin sa, ya 'kosa a fa'da masa matsayin 'yarinyar da ya ga kamannin matar da bazai ta'ba iya manta ta ba iya tsayin rayuwar shi ba a fuskan ta.
Gyaran murya alhj Mudassir yai tare da fara korawa 'dan uwan nashi baya ni.
Sosai alhj Aliyu ya nutsu ya na sauraran shi har ya kai aya.
Sosai tausayin Mufeeda ya kama alhj Aliyu. Ya ce,
"Amma ni kuma Naina ta kira ni ta shaida min yarinyar Jawad ya ke so, shiyasa ma ya ce ba zai koma Germany ba, Wai ya dawo 'kasar sa kenan".
Da mamaki alhj Mudassir ya kalle shi tare da fa'din,
"Wannan zance ba haka ya ke ba, Lukman ne ma ya nuna shima ya na son ita yarinyar har haka kai su ga doke². To amma yanzu komai ya dai² ta, shi Lukman 'din yanzu kuma 'yar uwar sa ya ke so *JALILA*(BABY). Sun dai² ta kan su. Ina ga in sha Allah idan munje Kaduna abu ya dai² ta, ha'da bikin za'ai duka".
"Allah ya a dace. Idan abun ya tabbata kuma Allah ya ba da zaman lafiya ya kuma ka'de fitina". Fa'din alhj Aliyu.
Mufeeda kuwa tunda ta koma 'daki gaban ta ke wani irin fa'duwa. Sai ta ke ji kamar wani al'amari zai faru da ita.
Haj Jummai kuwa, al'kawari ta 'daukar wa kanta, ba zata ta'ba barin Mufeeda tai zaman lafiya a gidan 'dan ta ba. Ba dai aure ba, suje suyi, amma sai ta 'dan 'dana mata ba'kin cikin da bazata manta da shi ba.
Baby kuwa ta kwantar da hankalin ta, soyayyar sosai suke zubawa ita da Lukman 'din ta, sai taji ma tafi son shi da Naseer 'din da da take matu'kar 'kauna.
Tuni Inna Huwaila har ta saka ranar tafiya nan da kwanan hu'du masu zuwa. Ta kuma za'bi wa'danda za'a tafi dasu. Alhj Mudassir, alhj Aliyu, ita, Mufeeda, baaba Habiba, haj Zulfah, Naseer da ya Abubakar.
*KADUNA*
Sosai Umaymah ke kuka kamar ran ta zai fita, Aaeedah da ke gyefan ta ta na taya ta. Idan ka ga Aaeedah zaka rantse da ubangiji ita da Mufeeda 'yan biyu ne. Domin babu abunda ta baro na Mufeeda, kuma duk mahaifiyar su suka biyo har da hasken fatan. Sai mazan uku da suke 'kannan Aaeedah, su kamannin mahaifin su suka 'dauko kuma triplet ne su identical don ba'a banbance su.
"Ashe 'ya ta tana da rai, ashe ba ta mutu ba. Tsawon shekaru ashirin da uku". Sai ta kuma fashewa da kuka.
Mijin ta ne ya dafa ta tare da fa'din,
"Godiya ya kamata muyiwa ubangiji da ya baiyanar mana da ita ba kuka ba. Ummu Aaeedah godiya ya kama ta muyi".
Aaeedah ta koma wajan mahaifin ta tare da fa'din
"Abie yayar mu ta na nan da rai. Ashe zan gan ta". Ita ma ta fashe da kuka.
'Yan uku masu shekaru goma sha biyu ma kukan su ke yi.
Daddy ya ce,
"Yanzu ba lokacin koke² ba ne, lokaci ne na naimo Mufeeda a duk in da ta ke".
Kallon shi Umaymah ta yi tare da fa'din,
"Ku kai ni wajan iyayan ru'kon ta. Ina son jin yadda aka canza min 'yata a asibiti".
"Kwantar da hankalin ki, shi mal Ahmadu da matar sa Fatima ma suna hanyar zuwa nan gidan. Tun jiya muka sanar da su dawowan ku daga Saudi Arabian".
Daddy bai gama rufe baki ba, mal Ahmadu da matar shi Fatima su kai sallama su ka shigo.
"Yauwa ga sunan 'yan halak".
Da sauri Umaymah ta mi'ke ta rungume Fatima tare da fashewa da kuka. Fatiman ma kukan ta ke yi tare da fa'din,
"Wallahi ko makaho ya shafa yasan ke ce mahaifiyar Mufeeda".
Sa'bewa Zaheeda tai tare kiran Naseer a waya.
*NASEER*
Mama ce du'ke guiwowi a 'ka sa ta na rok'on Naseer,
"Naseer na san Mashkura ta cutar da kai matu'kar, don girman Allah ka yi ha'kuri ka sake ta in tafi da ita, wallahi ta cigaba da zama a haka hannun ta ru'bewa zai yi. Ba dan halin ta ba, dan girman ubangijin halitta ka yi ha'kuri".
Naseer kuwa ji yai zuciyar na wani irin tafasa, ya nuna Mashkura da tai wani irin ramewa, hannun ta kuwa har 'kashin sai da ya bullu'ko le'ban 'kasan bakin ta da ya rave biyu, don said an mata 'dinki a wajan, ya ce,
"Wallahi ba ta ga komai ba a irin azabar da zan gwada mata, kamar yadda na ke 'dan'danar ba'kin ciki ita ma sai ta yi shi. Sai na mai da ta abun kwatance".
Fashewa da kuka mama tayi tare da kamo 'kafar shi ta ce,
"Dan alfarman ubangijin halitta ka sauwa'ke mata, wallahi ko a haka ka bar ta ita 'din abun kwatance. No ro'keka dan son da Allah kewa annabin su (saw) ka yi hakuri ka sauwa'ke mata".
"Zan sake ta, amma da shara'di".
Mama ta ce, "fa'din shara'din ka na in sha Allah zan yi shi".
Naseer ya ce,
"Za mu tafi can gidan iyaye na tai masu bayanin abunda ta yi da bakin ta".
Kamin mama ta ce wani abu, Mashkura ta ce,
"Wallahi na amince zan fa'di komai. Duk abunda nai zan fa'di wallahi".
" To je na sake ta saki uku, ku tashi muje can gidan na mu". Ya na gama fa'din hakan ya mi'ke dai² lokacin wayar shi ta hau ruri.
Fito da wayar yai daga aljihu ya ga Zaheeda ke kiran sa, cikin sauri ya 'daga tare da karawa a kunne.
"Yaya kazo gida yanzu, wallahi akwai babbar al'amari. Kuma Ummu na sun dawo daga Saudiya tun shekaran jiya".
"Ga ni nan yanzu nan". Naseer ya fa'da out of excited.
"Ku tashi muje". Naseer ya fa'da tare da fita waje. Mama ta kamo Mashkura su ma suka fito.
Ko kamin su fito har Naseer ya tsaida 'dan sahu. Suna fitowa ya shiga suma suka shiga su kai SMC.
'Dan sahu na sauke su ya biya ku'din tare da shiga gidan, su na biye da shi a baya.
Ba tare da sallama ba ya shiga 'dakin, kai tsaye wajan Ummu na ya nufa tare da rushewa da kuka kamar yaron goye.
Hannun ta ta 'daura a kan shi tare da shafa ta na fa'din,
"Bar kuka Abie, bar kuka kaji son". Duk da an fa'dawa Ummu Nah shine ya auri 'Yar ta Mufeeda ta re da bakin ta bayan ya wulakanta ba, ba ta ki ta tsane shi ba, ko ta ji zafi shi ba.
Daddy ne ya ce,
"Ta shi ka fitar min a gida, ni tuni na tsame ka a cikin 'ya'ya na".
"Yaya ba za ai haka ba, dama Allah ya riga ya rubuta hakan a cikin kaddarar Mufeeda, 'dan uwan ta zai aure ta, ku ma zasu rabu".
"Wallahi rabuwar su ba na Allah ba ne, duk da ya na cikin kaddarar su, amma wannan ita ce sila". Mama ta fa'da tare da nuna Mashkura.
Mashkura na tsiyayar da hawaye ta soma basu LABARI kamar yadda ta bai wa Naseer labari, ta na yi ta na kuka.
Wani irin wuta ne ya 'dauke a 'dakin na kusan mintu biyar. Kowa a wajan jikin shi ya mutu.
Naseer kuwa ji yai abun ya dawo mass sabo, yai wani irin tsalle tare dam'kar hannun ta mai ciwo da 'karfi.
Aikuwa Mashkura ta saki 'kara tare da fitsarin azaba, gumi tuni ya tsatstsafo mata. Fa'di ta,
"Shikenan mutuwa ta tazo".
Daddyn Aaeedah da daddy har rige² su ki wajan janye Naseer don zai iya kisa.
"D'auki 'yarki ku fice daga gidan nan tun kamin n h'da ku da hukuma". Daddy ya fa'da a fusace .
Jiki na raw mama ta kama Mashkura su ka fice.
Nan Naseer yai ta kuka har da birgima akan duk India matar shi take sai an nemo masa ita.
Nan dai akai ta jimami abubwan da