Showing 42001 words to 45000 words out of 115393 words
ta tare a gidan ta. Ahmad shi ya sa yi 'yar katifa da labule aka saka a ciki da palon dake gidan. Dama tuni Indo ta koma 'daki 'daya, ta ce su su zauna a ciki da palo. Bayan sati biyu mahaifin Fatima ya zo da kan shi ya kawo mata 'yan tarkacan kayan kitchen da kuma sadakin ta dubu ashirin, aiko da kyar ta kar'bi ku'din. A nan ne ta tambayi mahaifin na ta mahaifiyar ta. Mahaifin ta ya shaida mata, lafiyar mahaifiyar ta 'kalau, sannan ya 'kara da cewar mahaifiyar ba ta fushi da ita, domin ya zaunar da ita ya ma ta nasiha da kuma nuna mata shi aure rabo ne, kuma wani bai ta'ba auran matar wani.
Don ya 'kara kwantar mata da hankali ma sai da ya kira wo mahaifiyar ta ta ya ha'da su a waya. Sosai Fatima ta ji da'di domin mahaifiyar ta ta bai 'karamin addu'a tare da nasiha ta mata ba, tq kuma 'kara nuna mata mahimmancin hakkin miji da kuma ha'kuri.
Bayan auran Fatima da wata uku, mahaifiyar ta ta rasu, sakamakon fama da ta yi da cutar amai da gudawa. Aikuwa dangi sai suka juya abun akan cewa ba'kin cikin auran Fatima ne ya kashe ta. Nan dangi suka 'daura mata karan tsana da kuma tsangwama.
Ba jimawa shi ma mahaifin ta ya amsa kiran Allah. Aikuwa nan da nan magana ya ya'du a gari ai Ahmad yai asiri shi da uban shi sun kashe sirikan sa. Suka 'kara da cewar ai tun farko ma asiri Ahmad yai wa mahaifin Fatima shi ya sa ya bashi aure ba'a tare da shawarar kowa a dangi ba.
Tun daga wannan lokacin dangi su kai meeting aka haramtawa Fatima shiga dangi aka kuma cire ta a cikin dangi. Sannan aka suka 'kara da duk Wanda ya taimake ta ko da a cikin 'yan uwan ta da suke ciki 'daya ne sai an cire su a dangi suma.
Tun daga wannan lokacin duk Wanda ya ga Fatima ko da a hanya ne, sai su canza, wasu ma sai sun tsartar mata da yawu suke wucewa.
Fatima kullum cikin kuka da tashin hankali. Mijin ta da sarakuwan ta ne ke kwantar mata da hankali.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_Gare ku fans masu comments da marasa comment 'yan la'be😍 ina mai baku ha'kurin rashin ji na da ku ka yi kwanan biyu, hakan ya faru ne sakamakon fama da nai da rashin lafiya. Amma yanzu kam jiki alhamdulillah! In sha Allah zan 'daura daga in da na tsaya._*👌🏼🥰❤️
*_PAGE 22_*
*NOT EDITED*☹️
A wannan lokacin ne kuma katsam aka cintsi gawar mal Datti ya she a tsakar 'daki ya kumbura har ya fashe ya na fitar da tsutsu har ga uban wari kamar mushan jaki da ya addabi mutanan layi. Shikuma Kallah bai ma garin, domin ya aike shi Maiduguri don ya kar'bo masa wani magani a wajan wani uban gidan shi.
Mutanan unguwa sun yi cincirundo a kwar gidan, wasu matasa masu 'karfin hali ne suka fa'da gidan suka ga halin da mal Datti ya ke ciki.
Dai dai wannan lokacin ne kuma Kallah ya iso cikin taxi jibge da magunguna a boat. Hankali tashe ya fito daga motar ko kallan mai taxi 'din bai ba ya 'karaso wajan dandazon mutanan. Ana ganin shi kuwa aka dare aka bashi hanya.
A ki'dime Kallah yai saurin toshe hanci tare da kallon mutane ya ce,
"Jama'a mai ya faru? Wannan uban warin daga ina??".
Wani a cikin dandazon mutanen da dama ya jima ya na jin haushin Kallah da kuma mahaifin sa ya ce,
"Mahaifin ka ne yau Allah ya kawo mana 'karshan shi. Ga ya can ya na girbe abun da ya shuka. Kuma wallahi kai gaggawar futar da shi daga layin nan domin ya ishi bayin Allah da 'doyi ko kuma wallahi mu cinnnwa gidan wuta".
Kallah hankalin shi a matu'kar tashe ya afka gidan domin ya ga halin da mahaifin na shi ya ke ciki. Ai kuwa ba 'karamin razana yai ba, domin hatta fuskan shi fitar da tsutsa ya ke yi. Sam ba shi da kyawun ga ni. Da gudu ya fito saboda warin da mal Datti ke yi zai iya halaka shi. Wayar sa ya zaro a cikin aljihu ya danna wa wan shi Ahmadu kira tare da shaida masa halin da mahaifin na su ya ke ciki.
Hankali ta she Ahmadu ya baro wajan sana'ar sa ya taho nan unguwan su mahaifin na shi. Shi kan shi Ahmadu ba 'karamin ru'dewa ya yi ba. Jama'a kuwa suka fito suka dingi bala'i mazan su da Matan su akan lallai fa a fitar da gawan mal Datti a unguwar ko kuma su cinna masa wuta.
Da kyar da kuma to she hanci Ahmadu da Kallah su kai wa mahaifin na su wanka fatar jikin shi na zagwanyewa tsutsotsi na fita. Wajan fita da shi ma, dakyar wata ta basu hayan baro aka saka gawar shi a ciki suka gungura shi zuwa ma'kabarta domin ba by Wanda ya yadda ya sallaci gawar shi. Sai a gab da ma'kabarta su biyu kacal suka sallaci gawar shi ka na suka kai shi makwancin sa Wanda da kyar 'kasa ta amshe shi, don sai da aka saka shi sau goma sha bakwai 'kasa na bullutso shi waje.
Hakan ne ya ta da wa Kallah hankali yai rantsuwa da shi da harkan bokanci sun yi hannun riga. Ya tattara duk wani harkan tsatsuba da mahaifin shi ya koya masa ya watsar a gyefe ya tattara ya koma gidan 'dan uwan shi ya kuma nai mi yafiyar mahaifiyar sa.
Nan Ahmadu ya ba shi ciki 'daya. Shi ya na 'daya, mahaifiyar su na 'daya, shi kuma Ahmadu da matar shi Fatima suna ciki da parlour.
Shuru shuru Fatima Allah bai kawo mata haihuwa. Sai bayan shekara uku sannan dai ta samu, shi ma satin sa uku ya fita. Tun daga nan a kai a kai ta ke samu, amma da ya kai wata biyu zuwa uku ya ke fita.
*************
Kallah ya fita daga harkan tsafi kwata kwata, sai dai kuma ya fa'da harkan nai man mata. Gashi ya kasa yin sana'ar 'karfi. Kullum cikin yawo. Ahmadu ya yi fa'dan, ya yi fa'dan amma Kallah ya 'ki natsuwa. Ahmadu ya yanke shawarar yai masa aure kawai ko zai shiryu da biye biyen matan banzan da ya ke yi, don ance aure rahamaa ne ya na kuma natsar da mutum.
Bayan kwana uku da yanke shawarar Ahmadu ya yo kiran 'dan uwan na sa bayan sun yi sallar isha'i. Kallah yq so har 'daki ya same shi tare da sunkuyar da kai kamar mutumin arziki.
Ahmadu ya kalle shi har na tsawon mintuna biyu, ka na ya ce,
"Kallah kai 'dan uwa na ne na jini, wallahi ba zan so maka ta'bewa ba, Kallah ina son ka zama mutum kamar kowa. Ka natsu ka bar biye biyen mata. Shifa Zina ba shi ce, kuma wallahi duk mai yin ta da 'ya'yan shi mata ya ke biyan bashin nan. Idan har ka biya naira dubu goma kai zina da 'yar wani, to ka sa ni wallahi billahil azeem kai a kyauta za ayi da 'diyar ka. Mai ya fi wannan muni Kallah?".
Shuru Kallah ya yi kamar mutumim arziki, har da wani tankwashe 'kafa. Ya ce,
"Yaya Wallahi in sha Allah daga yau na bari, ban 'karawa. Kuma zan ri'ka bin ka wajan aikin ka".
Sosai farin ciki ya bayyana a fuskan Ahmadu. Ya ce,
"Alhamdulillah! Allah kuma ya taimake ka. Na ji da'di kwarai. Sannan akwai wata maganar bayan wannan".
Kallah ya 'kara lankwashe 'kafa tare da fa'din,
"Ina jin ka yaya".
"Akwai yarinyar da ka ke nai ma ne? Don ina son kai aure".
Sosai wani da'di ya mamaye zuciyar Kallah, dama ya na da wata budurwan da ya ke son ya aura, duk da sun da'de su na auran su a waje. Shi customer ta ne. Zogale ta ke sai da wa. Sunan ta Sakina, amma da *MAI ZOGALE* ake kiran ta. Sosa kai ya yi tare da fa'din,
"Eh yaya akwai yarinyar da muka dai dai ta da ita, dama a gidan su an mata min in tura magaba ta na".
"To babu damuwa, in sha Allah zan samu Yakubu da Idi (abokan sa na wajan aiki) sai muje".
Cike da jin da'di suka cigaba da hirar su ta zumunci.
Bayan kwana biyar, kamar yadda Ahmadu ya shaidawa Kallah zasu je nai ma mass aure hakan kuwa akai. Sunje har kuma an tsaida da rana watan mauludi, nan da wata biyu masu zuwa.
*BAYAN AURAN KALLAH*
Mai Zogale ta tare da 'zaki 'dayan da Ahmadu ya ba su. Farko ta kwantar da kan ta, daga baya ta fara shisshigewa uwar mijin na su saboda yadda ta ga soyayya da sha'kuwa tsakin Fatima (Matar Ahmadu) da sarakuwar ta su. Amma Sam sai Indo ba ta bats fuskan ba, domin ta da'de da fuskan tar halin matar 'dan na ta. Wannan ne ya hura wutar 'kiyayyar Fatima a zuciyar mai Zogale. Sannan uwa uba mijin Fatima shi ke ci da su, sannan kuma Fatima na 'daura zani mai kyau kuma ba sai shekara shekara ba. Wannan ya 'kara saka mata hassada da 'kiyayyar Fatima a zuciyar mai Zogale.
Cikin ikon ubangiji lokaci 'daya mai Zogale da Fatima suka samu ciki. Haka su kai ta rainon cikin su. Lokacin da cikin su ya shiga wata biyar Indo *sarakuwar su* ta amsa Koran ubangiji sakamakon fama da amai da gudawan da ta yi ba yi ni 'daya. Mutuwar ba 'karamin girgiza su ta yi ba. Musamman Ahmadu.
Haka suka 'dauki dangana.
Bayan wata uku, mai Zogale ce ta fara haihuwar 'diyar ta mace kamannin ta saak na mahaifiyar ta. Har akai suna yarinyar ta ci suna *Marwanatu*. Har bayan suna da sati 'daya shuru Fatima ba ta haihu ba.
Kwatsam wata rana da daddare na'kuda ya kama Fatima. Aikuwa Ahmadu ya tattara ta su kai asibiti. Dai dai lokacin aka shigo da wata mata da mijin jaga jaga cikin jini. Hatsarin mota su ka yi. An gunguro mijin akan gadon asibiti kwatsam ya cafki hannun Ahmadu da ke cikin tashin hankali matar shi na cikin na'kuda.
Ana gungura mara lafiya Ahmadu da hannun shi ke ri'ke da na mara lafiya ya na bi ye da su da gudu har 'dakin da aka kai shi.
Ita kuma Fatima na can ta na ta faman wahala haihuwa ya 'ki zuwa.
Sai bayan awa uku sannan wata nurse ta fito hannun ta ri'ke da jariri ya ta na nai man Ahmadu, shi kuma dai dai ya fito daga wannan 'dakin da aka saka wannan mutumin da yai hatsari shi da matar shi fuskan nan sharkaf da hawaye ya na kuma share zufa.
Nurse jiki a sanyaye ta mi'ka masa jaririyar ta re da fa'din,
"Bawan Allah sai dai ku yi ha'kuri ba ta so da rai ba".
Saurin kar'ban 'yar ya yi hawaye na ziraro masa.
Dai dai lokacin kuma wata nurse ta leko ta kwalowa wannan nurse kira a ru'de ta na fa'din,
"Hajara kira doctor".
A guje wacce aka kira da Hajara ta nufi wata 'kofa.
Tare suka fito da dr suka nufi labour room.
*BAYAN AWA UKU*
De ne ya fito tare da kiran Ahmadu ya zo ya same shi a office. Sun kusa minti talatin ka na Ahmadu ya fito ya na kuka.
Kai tsaye 'dakin da aka aje Fatima ya nufa, kwance ta ke ga kuma jarirai 'ya'ya mata biyu a gyefan ta, sai dai 'daya ba ta zo da rai ba
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, INA MAI BA'KIN CIKIN SANAR DA KU A PAGE 21 AKWAI MISTAKE. NA KAWO LABARIN CEWA AHMADU YA JI LABARIN KALLAH YAI WA MAI ZOGALE CIKI, DAGA BAYA KUMA YA JI LABARIN AN 'DAURA MASU AURE BA TARE DA TA HAIHU BA. A PAGE 22 KUMA NA SAKA CEWAR KALLAH BAI YI AURE BA SAI DA YA DAWO WAJAN 'DAN UWAN SA AHMADU, AHMADUN NE MA YA MASA AUREN. WANNAN KUSKURE NA NE, KASANCEWAR NA YI FIYE DA SATI BAN DA LAFIYA BA NA HAWA WHATSAPP 'DIN MA, KUMA DA ALLAH YA BA NI LAFIYA BAN BIBIYI PAGE 'DIN BAYA BA SAI NA CANZA SALON LABARIN. NASAN DA YAWA WASUN KU ZASU RU'DE. TO DAN ALLAH KU 'DAUKI SALON LABARIN PAGE 22 KAWAI IN DA NAI NUNI DA AHMADUN NE DA KAN SHI YA NAI MA WA KALLAH AUREN MAI ZOGALE. NAGODE DA FATAN ZA KUMIN AFUWA(NO body above mistake)*🙏🏼🙏🏼🙏🏼
*LOVE YOU ALL FANS Irin sosai 'din nan🥰😘😍😍🥰*
*_PAGE 23_*
Zama Ahmadu yai a gyefan ta, ya na 'karewa jariran na shi kallo. Can kuma yai wa ni dogon ajiyar zuciya ka na ya ce,
"Wannan 'kaddara ta ce, haka Allah ya so ya da ni".
"Subhanallah! Mai ya faru ka ke furta haka Allah ya so da kai?". Ba tsammani ya tsinci muryan ta a cikin kunnuwan shi. Saurin kallon ta ya yi tare da furta,
"Fa'dima ta kin tashi? Ya jikin na ki?".
"Da sauki, amma dan Allah fa'damin matsalar ka".
Hannun ta ya kawo tare da fa'din,
"Ki kwantar da hankalin ki, ki na ri ki warke tukun zan fa'da miki komai".
"A'a, dan girman Allah ka fa'damin komai yanzu. In sha Allah ko ma menene ni zan 'dauki 'kaddara ta". Fa'din Fatima tare da zuba masa idanu zuciyar ta na wani irin bugawa.
Tiryan tiryan Ahmadu ya shaida mata duk abunda dr ya fa'da masa, ya 'karashe tare da kwantar mata da hankali.
Sosai hawaye ke zuba daga idanun ta, ta 'dago wacce ta mutun kamar su 'daya saak, sai idanuwa da ta 'dauko na mahaifin ta. Aje ta ta yi ta rufe ta har fuska ka na ta 'dauki dayar da hasken fatan ta kawai ta 'dauko har ma ta kera ta a hasken fatan. Addu'a sosai ta mata sannan ta kalli mijin na ta ta ce,
"Allah shi ya San dalilin sa na 'dauke wannan ya bar ma na wannan. Allah shi ya San dalilin da ya sa mahaifa ta ta lalace bazan 'kara haihuwa ba. Ba na ba'kin ciki da hakan, sai ma godiya da na ke wa ubangiji da ya bar min wannan. Wannan ita ce jarabawa ta, Allah ubangiji ka sa na ci wannan jarabawar".
"Ameen ya Allah". Fa'din Ahmadu ya na sharar hawaye.
Zaro waya yai daga aljihu ya dannawa 'dan uwan sa kira ya shaida masa matar sa ta haihu tagwaye sai dai 'daya ba ta zo da rai ba, yazo asibiti ya same su.
Aikuwa cikin minti talatin sai ga Kallamu ya zo. Da ma tuni an basu sallama kasancewar jikin da sau'ki, sai suka kira taxi ta kwashe su sai gida. Da ma tuni Kallah kamin ya 'karaso gida ya shaida wa jama'a matar 'dan uwan shi ta haihu tagwaye sai dai 'daya ba ta zo da rai ba.
Su na zuwa akai ma ta Wanka akai jana'iza aka kai ta makwancin ta. Duk da Ahmadu shi da kan shi ya je har gidan su Fatima ya shaida masu abunda ya faru har da mutuwar, korar kare su kai masa ka na suka ce su ba su San wata Fatima ba, basu da ala'ka da ita saam, kuma kashedi na 'karshe, ka da ya 'kara tako 'kafar sa in da su ke, idan ba haka ba kuwa hukuma za ta shiga tsakanin su.
Haka nan jiki sa'bule ya taho gida, bai shaidawa Fatima abunda ya faru ba, bai ma nuna mata yq je ba. Tun Fatima na tsammanin ganin 'yan uwan na ta har da Wanda suke ciki 'daya musamman Shafa da su kai matu'kar sha'kuwa har ta cire rai. Da ma ita ka'dai ce idan tq gan ta a hanya ba ta tofar mata da yawu ko ta harare ta, kuma ba ta mata magana sai dai tai ta bin ta da kallon tausayi.
Haka rayuwar ta cigaba. Ranar suna yarinya taci suna *Mufeeda*, Fatima ta cigaba da shayar da 'yar ta, amma zuciyar ta 'kuna ya ke yi sabida tsana da kyara da dangin ta suke