Showing 24001 words to 27000 words out of 115393 words
```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 14*
*_______________________*
*CIGABAN LABARI*
*_______________________*
Ya na fitowa kai tsaye ya nufi 'dakin haj Zulfah. Knocking yai tare da sallama ka na ya mur'da handle 'din kofar ya kutsa ciki. Babu kowa a palour sai dai kan dinning an jera manyan kulolin abinci da plates.
Zama ya yi a kan kujera tare da fa'din,
"wash Allah na". Mi'ka hannu ya yi ya 'dauki remote ya sauya tasha zuwa Bollywood don shi ma'abocin kallon fina-finan India ne. Sai kuma yai da ce suna haska film 'din da bai gajiya da kallon shi mai suna *KALHO NA HO*. Gyara zama yai tare da murmushi. Preety ta na matu'kar birgeshi. Sanyin ta da kuma yanayin acting 'din sa ya na matu'kar birge shi, must especially dimples 'din ta Wanda ko magana take yi suke lo'bawa. Sosai ya mai da hankali ya na kallo har ya manta da yunwar da take kwakwular sa.
A can sama kuwa, haj Zulfah ta yi wa quintuplets wanka ta shafe su da mai ta saka masu overall irin wanda suke zuwa mai saitin nan. Duka matan masu kalar white da 'digon red colour wanda aka 'kawata su da butterfly flowers. Ma zan kuma plane blue. Sun yi matu'kar kyau.
A can da'kin Mufeeda kuwa, ta kimtsa ta kuma saka wata dohuwar riga mai stones daga zama har 'kasa kalar ta red colour ce, sai stones 'din ne silver da golden. Rigar ta amshi jikin ta, gashin kan ta ta warware mai uban cika da kuma tsayi, cumb ta 'dauka a kan dressing mirror ta soma tajewa, wani uban zafi taji har kwakwalwar kan ta, saboda kan ya cushe ya dan'kare, don baza ta iya tuna last da ta taje kan ba. Ta na dai wanke wa da oma, idan ya bushe ta tubke ta mai da hula ko 'dan kwali ta a kan. Bu'de wardrobe ta yi ta 'dauki wani ba'kin hula da gaban shi ya sha stones ta 'daura a kan ta.
Dai dai lokacin haj Zulfah ta turo kofar *SHAHIDA* sa'be a kafadar ta, don rigima take yi, alamun ta na jin yunwa.
"Yau 'diya ta kin kimtsa ko, to fito muje ku ci abinci. Baaba Habiba ma ta gama, har ta sauka parlour ma". Haj Zulfah ta fa'da tare da kamo hannun Mufeeda suka fito.
*PARLOUR*
Baaba Habiba ce tsaye sai jijjiga Ayaan ta ke yi yana kuka. Architect kuma dauke Abid shi ma ya na nashi. Irfana da Husna ne kawai ke bacci har yanzu.
"Yauwa Alhamdulillah. Don Allah Mufeey ki zo ki ba su abincin su". Fa'din Naseer.
'Dan turo baki gaba ta yi sannan ta 'karaso parlourn ta zauna sai wani tutturo baki ta ke yi. Shi Naseer abun ma dariya ya ba shi. Baaba Habiba kuwa sai da ta murmusa. Haj Zulfah ne ta ce,
"Wai! To da wanne kuma zata ji, gaskiya rigimar kuma tai yawa wa'dannan jikoki nawa."
Kamar jira dama ta ke sai ta ce,
"Wallahi kuwa Ummie tun a mota suke zu'ke ni, su basu 'koshi wallahi. Da na 'dan ci abinci, da sun zu'ke shi".
"Yi hakuri 'diya ta, zauna ki ba su ko yaya ne, sai ke ma ki ci abinci".
" To" ta ce, tare da turo ba ki. Haj Zulfah ta 'daura mata Shahida a kan cinyar ta tare da fa'din,
"Fara ba ta, ai an ce ladies first."
'Karban Shahida ta yi, amma sai ta rasa ta inda zata fara kasancewar architect na parlour kuma ya na kallon ta. Shi kuma da ya fahimci kunyar shi ta ke ji, ba za ta iya shayarwa a gaban shi ba, sai ya mi'kawa haj Zulfah Abid ta re da fa'din,
"Ni dai ban jiran ku, bari na je na fara cika ciki na".
Baaba Habiba ta ce,
"Ai kuwa dai gwara ka fara ci, don nasan ka na jin yunwa".
Kai tsaye dinning 'din ya nufa ba tare da ya waiwayo ba, da ya isa ba sai ya zauna a kujeran da ke kallon gaba ya juya masu baya.
Ajiyar zuciya Mufeeda ta saki tare da dan Jan zip 'din ta ta baya, sannan ta soma shayar da Shadida. Haka duk ta bi ta shayar da su, sannan ta shimfi'dar da su. Saukin ta m da sun koshi suke fara bacci.
" Alhamdulillah tun da sunyi barci, ku taso muje muci abinci". Fa'din haj Zulfah.
Gaba 'daya suka mi'ke suka nufi dinning 'din.
Lafiyayar shinkafa da wake da miyan stew da kuma salat ta dafa, a gyefa a coconut juice da ta hada. Sannan ga kuma pepe chicken. Ita da kan (haj Zulfah) ta tai serving 'din su, sannan ita ma tai serving kan ta. Babu abunda kake ji sai 'karan cokula. Naseer ya riga su gamawa. Ya goge bakin shi da tissue ya masu sai da safe tare da ficewa.
Suma bayan sun gama, haj Zulfah da Baaba Habiba suka kwashi 'yan biyar su ka aje su a 'dakin Mufeeda. Nan 'dakin Mufeedan Baaba Habiba ta dawo zata kwana sabida yaran suna ta shi rigimar dare.
Kasancewar tara har ta wuce, wani masifaffan bacci yai awon gaba da su, gashi dama sun sha hanya.
Bayan sun wuce 'daki ne alhj Mudassir ya shigo duba matarsa ya mata sallama, da ma ya fita tun la'asar, dawowan shi ke nan, kuma ba a 'dakin haj Zulfah ya ke ba. Sai alokacin ma haj Zulfan ta ke shaida masa da isowar Mufeeda da baaba Habiba.
Sosai yaji da'di, sannan kuma ya ce in sha Allah da safe zai shigo ya duba su.
***********
Kwalaban cordine ne a gaban ta har uku. Ga kuma wasu uban kwayoyi a gyefe. A kan tebur kuma cocaine ne a cikin wata 'yar farar takarda.
Matsawa tai gaban teburin, ta saka rami haancin ta daya akan takardar ta toshe dayan ramin tare da zu'ko cocaine 'din. Sai da ya shiga har kwakwalwar kan ta. Wani irin gigicewa tai tare da zazzaro idanunwa, can kuma ta soma bubbuga kan ta da hannayan ta biyu. Bayan minti biyu, ta kuma kara kanga hancin ta ta zu'ko cocaine 'din. Wannan karan sai da tai wani irin mi'kewa ta tafi luuuuu ta fa'da kan gado. Sai da tai minti sha biyar sannan ta sauko daga gadon ta rarrafo ta 'dauki kwalbar cordine ta 'da'd'dake sannan ta kwana rub da ciki a wajan. (Hmm su baby kenan).
*WASHA GARI*
Allah ya rufa mata asiri, sau 'daya kawai quintuplets suka farka daga bacci. Da ya ke ma ba sallah ta ke ba, sai baaba Habiba ba ta tashe ta da asuba ba, sai karfe takwas ta ta shi, lokacin tuni har baaba Habiba da haj Zulfah sun gama ha'da breakfast har sun yi wa quintuplets Wanka.
Bayi ta shiga tai wanka tare da tsaftace jikin ta. Bayan ta fito ta saka pad ta gyara jikin ta, sannan ta dauki wata doguwar rigar material kalar blue black da kwalliyar flowers fari a jiki ta saka. Kayan sun mata 'daas, bazaka ta'ba cewa ita ce ta haifi 'ya'ya biyar ba.
Fitowa tayi ta nufi parlour, tsaf palon ya ke sai ta shin kamshi turaran wuta mai sanyin da'di yake yi. Ga 'yan biyar 'din ta kwance reras a kan makeken royar 3sittern dake palon.
Haj Zulfah ce ta fito daga kitchin sanye da apron hannun ta rike da wati tire mai 'dan zurfi kusan cike da panke sai shinning suke yi, ka na kallon dole miyan ka ya tsinke. An rufe shi da white raping paper.
"Aaa'ah 'diya ta har kin tashi?". Fa'din haj Zulfah tare da aje wannan farantin akan dinning table.
"Eh Ummie na tashi, saukowa ta ke nan" fa'din Mufeeda.
"To maza je ki zauna a dinning ga munan ni da baaba Habiba sai mu 'karya. Nasan yunwa kike ji, jikoki na sun tsotse abincin ko?".
Dariya tai cike da kunya tare da fa'din,
"A'a Ummie ba ri nazo kitchen 'din na 'karasa aikin".
"Kul kar k kuma min musu. Waya fa'da miki mai jego wacce ma aka wa aiki ta na yin wasu ayyukan gida? Maza je ki zauna a kan dinning ki tsumaye mu".
Da "To" ta amsa cike da jin da'din yadda haj Zulfah ta ke nuna mata kulawa kamar ita ce ta tsugunna ta haife ta.
Dinning 'din ta je ta zauna. Minti biyar haj Zulfah da baaba Habiba suka fito daga kitchen 'din, hannun baaba Habiba ri'ke da flasks suka 'karaso dinning 'din.
Zama suka yi, haj Zulfah ta mi'ke ta dauki cups 3 ta zufa tafashashshan ruwan lipton 'din da ya ji kayan 'kashi a ciki, ka na ta zuba milo da madara, sai da ta ga tea 'din ya mata kauri sosai kamar koko, sannan ta saka suger dai dai misali, don ita Sam ba ta shan suger da yawa, haka ma duk Wanda ya zauna da ita ta ke 'ko'karin mai da shi hakan don shan too much suger na da matsa ga lafiyar 'dan Adam.
Bayan ta tura aje masu cups 'din a gaban su, sannan ta dauki plates ta zuba wannan panken ta turawa ko wacce a gaban ta da kuma soyayyar kwai da yaji albasa da kayan miya. Ga kuma bredin da ita da kan ta ta ha'da shi mai 'dan karan da'di da kuma laushi. Sai da ta gama serving 'din su kana tai wa kan ta.
Tunda Mufeeda ta 'dauki wannan abun da take masa kallon panke ta saka a bakin ta kunnuwan ta suke wani irin rawaaan da'di. Don har wani chocolate da wani madara madara take ji a ciki. Haka tea 'din ma duk 'kur'ba daya sai ta ji wani da'di har 'ko'kon zuciyar ta. Baaba Habiba kuwa sai rawa take yi da kai, domin a rayuwar ta na ta ta'ba shan shayi da kuma panken turawa mai da'din wannan da take ci ba.
Mur'da kofa aka yi tare da fa'din,
"Assalamu alaikum".
Gaba dayan su suka juya suka kalli 'kofar 'dakin.
Ka na ganin shi ka ga baban Naseer, domin ko mai nasu iri daya ne sai dai tsufa kawai da baban na shi ya fara.
Amma mashi sallama suka yi.
Ita kuwa Mufeeda ta na 'dagowa idanun su ya shiga na juna, gaban ta ne ta ji ya buga da 'karfi.
Shikuwa alhj Mudassir bai San sadda ya furta U... May.... mah a rarrabe akan la'b'ban shi ba.
Hmmmmm mu dai je zuwa.
Taku ce
*MAMAN UMMEE*
idan na ga ruwan comment kuga update gobe.
✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 15*
"Lallai na yadda da aka ce ko wani mutun akwai irin sa guda biyar, wannan kamanni ai ya yi yawa". Fa'din alhj Mudassir a cikin zuciyar sa. Murmushi shimfi'de a fuskar ka ya 'karaso dinning 'din tare da fa'din,
"Maraba lale, sannu da zuwa 'diya ta. Ya jiki da kuma gajiyar hanya?".
'Dan zamowa Mufeeda ta yi tare da du'kawa ta ce,
"Lafiya qalau" sannan ta 'kara da fa'din,
"Ina kwana daddy, mun sa me ku lafiya?".
" lafiya qalau 'diyar albarka, ki saki jikin ki anan gidan, ki 'dauke mu kamar mahaifan ki. In sha Allah zan ri'ke ki ke da 'ya'yan ki tamkar 'ya'yan ciki na. Allah ya miki albarka".
Da ameen ta amsa wasu zafafan hawaye na zirarowa daga idanun ta.
"Alhj ina kwana?"
Baaba Habiba ta katse masa tunanin da ya lula akan Mufeeda. Mai da duban sa dai izuwa ga baaba Habiba ya ce,
"Lafiya qalau, ya ba'kunta?".
"Alhamdulillah ai an zama 'daya. Mun gode Allah ya saka da alkhairi, ya kuma kare ka daga ma'kiya".
Da "Ameen" ya amsa tare da fa'din,
"Ina jikokin nawa?"
Haj Zulfah tai masa nuni da 3sitter. Shi kuma ya jefe ta da wani 'kallon 'kasa 'kasa irin na dattawan masoya. Wani sanyayyar murmushin ta sakar masa. Domin magana ya mata da na su kalan yaran masoya.
"Masha Allah! Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wa'dannan 'ya'ya". Fa'din alhj Mudassir ta re da fiddo waya ya na 'daukar su photo, don ba 'karamin birge shi 'ya'yan su kai ba. Shi da zai fita saboda muhimmiyar kiran da aka masa, sai gashi ya shagala da kallon 'yan uku. Ya 'dauki wannan ya aje, sai ya koma ya 'dauki wancan.
Har suka gama cin abinci suka tattara komai su ka kai kitchen alhj Mudassir bai fita ba. Ji ya ke kamar ya kwashi 'ya'yan ya tafi da su.
(Masu karatu ba fa alhj Mudassir ka'dai ba ne ya ru'de akan 'yan biyar. Hatta pinky da Sa'ardha sun rikice lokacin da suka ji labarin an haifi 'yan biyar a MANAAL HOSPITAL, don har ha'da baki su kai akan su sace matan, sai Allah ya sa wata nurse ta ji su ta fatattake su. Lol🤣)
"Ohh Daddyn Naseer wai ba fita zaka yi ba ne? Idan an bibiya ma jiran ka ake yi". Fa'din haj Zulfah da ta zauna a gyefan sa.
"Wallahi kam jira na ake yi, yaran ne sai in ga kamar idan na fita bazan dawo in same su ba". Fa'din alhj Mudassir.
"Babu in da zasu, dan Allah ka je in da ake jiran ka, ba da'di ka aje mutum yai ta jiran ka".
"Hakane kuma matar arziki, bari na hanzar ta naje".
"Yauwa dan Allah ina son in 'dan fita in yo wa Mufeeda da 'ya'yan ta da kuma baaba Habiba shopping, don suna bu'katar abubuwa da dama".
"Babu damuwa kuke. Da akwai lokaci ma da tare zamu ai. Amma du da haka ga ATM card 'dina nan, kuyi amfani da shi wajan sayayyar kayar". Fa'din alhj Mudassir.
" Haba daddyn Nasser, ni ma ka bari ri in sa mu ladar mana, akwai ku'di a waje na ai".
"Na San akwai ku'di a wajan ki, amma ki ba ri ni ma na samu ladar".
"To ba bu damuwa, duka da na ka da nawan zan yi amfani da shi". Haj Zulfah ta fa'da.
"To shi ke nan, kin raba gardama, ki yi wa Lado driver magana ya kai ku, ban cika son ki na uawan driving da kan ki ba, kin ga ki na da 'dan matsalar idanu".
"Ba matsala duk yadda ka ce haka za'ayi. Fatana Allah ya ba mu ikon ri'ke wannan baiwar Allah da bamu ha'da ko mai da ita ba da amana. Wallahi bazan 'boye ma ka ba, ina jin ta har cikin jina, tam'kar ni na haife ta". Fa'din haj Zulfah.
"Wallahi ni kai na da na kalle ta ma sai da gaba na ya fa'di, don sai ta ke min kama da wata da'da'd'diyar fuska da na ta'ba sani". Fa'din alhj Mudassir
"Hakane, kasan ance ko wani mutum da akwai kalar shi". Haj Zulfah ta fa'da.
"Ba ri na je ana jira na, sai na dawo".
"Allah ya kiyaye hanya kuma Allah ya tsare". Haj Zulfah ta fa'da tare da 'daukar wayar sa akan hannun kujera ta mi'ka masa. Shikuma ya 'karba ya fice.
Bazaka ta'ba tunanin akwai halitta a wajan ba, yadda ta lafe cikin flower red&yellow dake jikin windown palourn. Ka na kallon idanun ta idan har ka San mai shaye-shaye zaka tabbatar ta sha wani abu jiya. Ba ta ma gama dawowa sosai ba.
"Ke!" Wani tsawa ya daka mata sai da cikin ta ya ba da sautin 'kulululuuu tare da zazzaro idanuna ta na kuma yarfa hannu don ta San yau kashin ta ya bushe.
"Ba dake nake magana ba kin tsasstsareni da idanuwa? Munafuka annamimiya". Naseer ya fa'da tare da nufo ta.
Ja da baya ta yi tare nuna masa 'dan kunne guda 'daya ta ce wallahi yaya ka ga abunda nazo nai ma". Ta fa'da jikin ta na rawa.
"To 'bace a wajan kamin na karya 'kashin bayan ki". Naseer ya fa'da ya na 'kara nufo wajan.
Da gudu ta kwasa ta part din haj Jummai.
Shikuma kwafa yai ya nufo in da ta lafe, don haka