Showing 57001 words to 60000 words out of 115393 words
bacci ta ke yi tun bayan sallar asubha. Na yi² da ita akan ta dai na bacci bayan asubhan nan, amma wallahi ta 'ki ji. Sannan wannan yaro Jamilu, ba ki ga yadda ya ke 'kaunar yarinyar nan ba, kullum cikin sintirin zuwa wajan ta ya ke ta na wula'kan ta sa, amma wallahi yaro bai yi zuciya ya dai na zuwa ba. Ban san mai ke damun Mashkura ba, ni na ce ko namijin dare ne ya aure ta. Ta'ki ta tsaya da kowa. Ita kenan gare ni. Wallahi ina so tai aure na ga jika na". Mama ta fa'di hakan kamar za ta yi kuka.
"Mama ki kwantar da hankalin ki, ina sha Allah Mashkura za ta yi aure. Kuma za ki ga jikan ta da izinin ubangiji mai rahama. Addu'a za ki ma ta. Kuma ni na zan taya ta da addu'a. In sha Allah babu wani namijin dare da ya aure ta". Fa'din Mufeeda cikin tattausar harshe.
"Allah ya muku albarka Mufeeda. Ke ma Allah ya kawo miki Wanda ya fi Musan. Jiya Mashkura ta sanar min komai. Ki yi ta ha'kuri kinji".
"In sha Allah Mama". Fa'din Mufeeda zuciyar na soyuwa saboda tuna mata da akai da Musan.
Bayan sun gama shanyar ta nufo 'dakin Mashkura da tai 'dai² akan 'katuwar katifar ta.
Bubbuga katifar Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"To kasa tashi, baccin ya isa haka".
Idanun ta cike da bacci ta bu'de su jaazur ta re da fa'din,
"Naaaa amm". Cikin magagin baccin.
"Dallah malama ta shi bacci nan ya isa haka ko in yi tafiya ta. 'Karfe sha 'daya fa".
"Kaaaaaaaiiiiii! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Wallahi ke kill joy ce. Da kin ba ri ya furta min ai". Fa'din Mashkura ta na bugun filo.
Galala Mufeeda ta saki baki ta na kallon Mashkuran. Cikin zuciyar ta ta ce,
"To ko dai maganar Mama gaskiya ne aljanin dare ya auri *KURA*".
"Kai amma wallahi kin cuce ni Feedy". Mashkura ta katse mata maganar zucin ta.
"Lafiyar ki 'kalau kuwa *KURA*? Mafarkin wa ki ke yi?".
"Share kawai". Mashkura ta ba ta amsa.
"To Allah ya kyauta". Fa'din Mufeeda.
"Na gaba". Mashkura ta ba ta amsa tare da mi'kewa ta shige bayin da ke cikin 'dakin. Kasancewar 'dakin ta ciki 'daya ne da ba yi a ciki.
Nan ta bar Mufeeda zaune da tunanin yadda za tai ta raba Mashkura da aljanin daren da ya shiga jikin ta.
Minti goma Mashkura ta fito sanye bathtub a jikin ta. Zama ta yi akan katifar tare da jawo wani 'dan basket da ta zuba kayan shafan ta a ciki. Mai ta shafa tare da yin simple makeup. Ka na ta mi'ke ta 'dauko doguwar riga ta saka bayan ta saka na ciki.
Mufeeda ko sai bin ta tq ke da idanu cike da tausayin da kuma tunanin yadda za ta rabata da aljanin dare.
"Wai wannan kallon fa kamar ba ki ta'ba ga ni na ba". Fa'din Mashkura.
"Ba komai kawai kin min kyau ne". Fa'din Mufeeda.
Wani farr ta yi da idanu na jin da'din yaba kyawun ta da Mufeeda ta yi. Don ita ta na bala'in son a yabe ta.
"Mamaaaaaa! Ina abinci na?". Mashkura ta ware ba ki ta na tambayan Mama abincin ta lamar wata 'kanwar ta ko sa'ar ta.
"Jira ni na zo na baki a baki". Mama ta jefo mata ba'kar magana.
"Kin yi min dai dai Mama". Fa'din Mufeeda ta na hararar Mashkura.
Harara ita ma Mashkura ta watsa mata tare da fita daga 'dakin ta na 'kun'kunai.
Can ta dawo 'dauke da 'kak'kauran tea cup biyu da soyayyar Irish da kwai.
Ajewa Mufeeda cup 'daya tai a gaban ta, sannan ta zauna ta aje masu plate 'din Irish a tsakiyar su tare da fa'din,
"Ban son inji komai, kawai 'dauka ki fara sha. Don naga a wajan ki har yanzu ba mu zama 'daya ba".
Murmushi Mufeeda ta yi tare da fa'din,
"Ke dai ki ka sa ni". Tare da 'daukar cup 'din ta kai bakin ta. Duk da matsanaiciyar yunwar da ta ke ji, haka take shan tea 'din a tsanake.
Bayan sun gama karyawa, Mufeeda ta kalli Mashkura tare da fa'din,
" *KURA* akwai matsala fa?".
Mashkura ta zuba mata idanu tare da fa'din,
"Matsalar me fa?".
"Inna ta kunno min wuta jiya da daddare. Sai da ta gama zage ni kaf akan abunda ya faru jiyam tsakanin ki da Marwa, sannan ta saka na je na ba ta ha'kuri. To bayan na je ba bata ha'kuri na dawo. Shine ta ke ce min wai yau zan fara fita tallah da daddare, wai zan fara tallar gya'da da ri'di don ta samu ta sayawa Marwa kayan kwalliyar 'daki".
"Kan bura uban nan! Kuma ke ki ka ce me?". Fa'din Mashkura rai 'bace.
"To me zan ce *KURA*? Ya zan yi? Ai dole ko na 'ki, ko na so, dole na yi". Fa'din Mufeeda.
"Ni wallahi yanzu ke ke ba ni haushi ba su ba. Ta yaya bazan kar'bi 'yanci na ba a gidan uba na. Wallahi idan ki kai Tallar nan, ke kill ka so. Mtsww".
Shuru Mufeeda ta yi ba ta 'kara cewa ko mai ba. Don ba zata ta'ba fahimta baa.
****
Ko da Mufeeda ta dawo gida, ta Tara's *MAI ZOGALE* na ta aikin ri'di. Ikon Allah kuma, ba ta tanka ta ba balle ma ta tambaye ta daga Ina ta ke. Kuma ba ta ce mata tazo tai aikin ri'di ba.
Ta samu ma, har girkin rana ta yi. Babu abunda ya ba ta mamaki, sai kallon ta da *MAI ZOGALEN* ta yi tare da fa'din,
"Ki je ki 'diba abinci ki ci".
"Iye, na'am". Shine abunda Mufeeda ta ce.
"Cewa nai ki je ki 'dibi abinci ki ci". *MAI ZOGALE* ta 'kara maimaita mata.
*ALLAH WALLAHI IDAN BAN GA RUWAN COMMENT BA, ZAN BAR TYPING NI DA SHI ABU 'DAYA NE DAGA YAU*
🤷🏼♀️🤷🏼♀️🤷🏼♀️🤷🏼♀️🤷🏼♀️
*MATAR SAYYADEE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*This page is for u Salis😍 ina matu'kar godiya da addu'ar ka a gare ni. Allah ya kawo maka mata ta bari wacce ta iya girki mai 'dan karan da'di*👌🏼👌🏼
*_PAGE 31_*
Sosai Mufeeda ke mamakin wannan sauyi na *MAI ZOGALE*.
Jiki ba kwari ta shiga kitchen 'din. Lafiyayyar shinkafa ce da wake da miya. Gyefe kuma ga salat. Zubawa tai a plate dai dai yadda za ta iya ci sannan ta fito daga kitchen 'din tare da kallon *MAI ZOGALE* ta ce,
"Nagode Inna".
Ko kallon ta *MAI ZOGALE* ba ta yi ba. Ita kuma ta shige 'daki tare da bararrajewa ta ci abinci ta sha ruwa.
*KARFE TAKWAS*
"Sai ki fito ki 'dauki gya'da da ri'din ki tafi tallah. Kuma wallahi na 'kirga duka. Sittin ta ubangiji gya'da ta dubu da 'dari takwas, ri'di kuma na 'dari shidda. Kuma ki sayar duka, ka da ki sake ki dawo min gidan nan da sauran gya'da ko ri'di. Ehe". Fa'din *MAI ZOGALE*.
Idanun Mufeeda cike da hawaye ta 'dauki 'katon faranti ta 'daura a kai da kuma robar fallasa cike da ri'di ta ri'ke a hannu".
Ko kallon *MAI ZOGALE* ba ta yi ba, tai hanyar waje. Marwanatu da ke zaune gyefan *MAI ZOGALE* ta na daddana waya ta bushe da dariya tare da fa'din,
"Mai kyawu irin na India an tafi tallah. To a dai sayar duka ko jiki yai tsami".
Kallon in da ta ke Mufeeda ba tai ba ta fice daga gidan.
Can Kusa da bakin titi ta aje kayan in da ta ga mai suyar wara da wainar rogo suna sana'ar su.
Gaishe su ta yi. Gaba 'dayan su da kallon mamaki su ke bin ta. Kasancewar sun san ta, kaf Fulani road ma 'dai² ku ne ba su san ta ba.
"Wai tallah ki ka fara yi ne Mufeeda". Mai awara ta jefa mata tambaya.
Murmushi kawai Mufeeda tai mata, don ita ba son yawan tambaya tai ba, musamman akan abunda bai shafe ka ba.
Ganin haka mai awara ba ta 'kara cewa komai ba.
"Ke! Na wa ne gya'da gwagwani?". Wani 'dan matashin saurayi, irin masu ji da tashan balagar nan ya jeho mata tambaya.
Wani tsoro ne ya dirar mata. Saboda yadda ya tsaya mata akai 'dangangan haka.
"Gwangwani talatin". Mufeeda ta ba shi amsa.
"Biyu hamsin idan kin sayar". Yaron ya fa'di hakan ya na wani ciccijewa.
Allah² ta ke ya bar wajan, domin wani tsamin wiwi ya ke yi. Sai ta ce masa,
"Kawo ku'din".
"To zuba min ma na. Ko guduwa zan yi ne". A wani ciccije ya fa'di hakan.
Gwangwanin awon ta kwance a cikin leda tare da soma aunawa.
"Ke kifa yi min awo mai kyau. Na ga ba ki son cika gwangwanin ne".
'Kala ba ta ce masa ba, sai ma 'kara debowa da ta yi ta zuba masa tare da mi'ka masa.
Kar'ba ya yai tare da ce ma ta,
"Shi ma ri'din samun na hamsin, ki kuma samun gyara 'daya".
"Ka yi ha'kuri ba'a saka gyara, domin komai anan a 'kirge ya ke". Fa'din Mufeeda.
"Saka min ri'din to, tunda baza ki saka min gyarar ba". Fa'din yaron.
Ri'din ta saka mata tare da mi'ka masa. Kar'ba yai tare da fa'din,
"Yauwa. Ma jame gobe idan ta fito. Don ban fito da ko sisi ba". Ya na fa'din hakan ya karkace ta re da yin tafiya irin na 'kauraye. Sannun daman shi kamar zai ta'bo 'kasa.
Kirjin Mufeeda ne ya fara wani lugu'den tashin hankali.
"Hmm haka su ke faa, Sai kin yi hakuri. Ko ji ma da ki ke gani na a nan, kullum akwai mai zuwa cin warar 'dari ba sisi, ida. Ki kai rashin kunya kuma a ne mi keta miki mutuncin ki. Ko wallahi ba bu abunda zai faru. Kawai ha'kuri za ki yi. A hankali za ki saba". Fa'din mai awara.
"Ko ma ka biya ta ku'din ta". Naseer ya fa'da tare da tura kyeyar wannan yaron.
"Haba Oga, haba. Ya za ka min haka ne. Wannan abu fa bashi na ci. Kuma gobe zan kawo mata ku'din billahil lazee". Fa'din wannan yaron.
"Da ma haka ake kar'ban ba shi da gadara? Ke Jazuga ka san ni, wannan zan gyara maka zama a layin nan. Ka je ka tambayi iyayan gidan ka su Mai dula da Faisal. Ko su zan ci uban su ba re kai 'karamin kwaro. Dan iska kawai. Ko je ku nutsu ku kama sana'a ku ciyar da kan ku da iyayan ku, amma kun 'ki. Kun gwammace ku zauna kuna shaye² a layi tare da sace² kayan al'umma. Tir da halin ku wallahi. Dallah wuce ka ba ta ku'din ko ka aje mata kayan ta". Naseer ya fa'da a fusace.
"Lafiya dai Oga, ai min afuwa dan rahamanu". Yaron ya fa'da tare da 'daga hannun shi ya ha'de biyu alamar nai man afuwa, ka na ya je ya aje gya'dar da ri'din akan farantin gyadar ya wuce".
Dogon tsaki Naseer yaja tare da 'karasowa wajan da Mufeeda ta ke zaune akan dutse.
"Meye ma'anar hakan? Tallah, tallah kuma Mufeeda? Tallar ma da daddare, bayan kin san unguwar nan ba ta da tsaro. Why? Me ya sa?".
Shuru tai masa. Don haushin shi ma ta ke ji.
"Ba da ke na ke magana ba". A tsawace ya fa'di hakan tare da dukan farantin gya'dar Sai da ya watse gaba daya.
Sosai ta razana, ba ita ba hatta mai awara da mai kosan rogo Sai da suka razana.
Hannun ta ta fara yarfawa tare da fa'din,
"Na Shiga uku! Na shiga uku!! Na shiga uku na!!!".
"Ina miki magana ki na kin shiga uku? Wato Mufeeda so ki ke a keta min mutuncin na ko? So ki ke wani ya fara shiga gona ta ko? Gonar da ko ni ban fara shuka a cikin sa ba ko?".
Inaaa Mufeeda Sam ba ta sauraran shi, domin gaba 'daya hankalin ta ya koma gida. Tunani ta ke ba ta can *MAI ZOGALE* ta na kir'ba ta a turmi.
Saurin 'daukar faranti tai ta fara tattaro gya'dar ta na sakawa a faranti hawaye kuma na zuba daga idanun ta.
Ko mai Naseer ya tuna kuma oho, Sai ya tsugunna ya so ma taya ta tattaro gya'dar da ya watse.
Bayan sun gama tattarawa, sai ya kar'bi tiran ta re da kiran wasu gungun almajirai da ke zaune can gyefe guda ya ba su. Aikuwa suka hau wawa.
Mufeeda na nan tsaye kamar an dasa ta. Jikin ta sai rawa ya ke yi. Don ta tabbatar yau kam *MAI ZOGALE* ba za ta bar ta da rai ba.
"Kai kuzo ga wannan ri'din ma ku raba".
Aikuwa nan suka kara rantamowa suka wawushe ri'din.
Mi'ka mata bokitin ya yi. Amsa tai jikin ta na rawa.
Hanya ya nuna mata tare da fa'din,
"Wuce mu tafi".
Yadda ka kan yai mata asiri ta soma gaba ya na bin ta a baya.
"Tsaya". Naseer ya fa'da.
Cak kuwa ta tsaya idanun ta na tsiyayar da hawaye.
"Meyasa kike kuka?". Ya jeho mata tambayar rai nin wayau.
Harara ta ma ka masa tare da share hawayan da ke zubo mata a idanun ta.
"Don na yi kyauta da gya'dar ki? To ki kwantar da hankalin ki, zan biya ki ai".
Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, sai da ya jiyo ta.
Duk da ya yi bincike a kan ta, ya ji labarin ta da u'kubar da ta ke sha wajan matar 'kanin mahaifin ta da shi kan shi kanin mahaifin na ta da kuma 'Yar su. Zai zo ya ji labarin ta a bakin ta da kan ta.
Wani 'dan dandamali ya nuna mata tare da fa'din,
"Zauna mu yi magana". Kamar bazata zauna ba, sai kuma ta zauna a in da ya nuna mata 'din. Shi ma zama yai 'dan ne sa da ita ka'dan tare da fa'din,
"Mufeeeedat".
Sai da tsikar jikin ta ya fa'di saboda yadda ya jaa sunan na ta. Ba ta amsa ba, shikuma ya cigaba,
"Ha'ki'ka na da'de ina son ki da 'kaunar ki a cikin zuciya ta. Na rasa ta yadda zan sanar da ke, shiyasa na 'bullo miki da da yawan tsokana da kuma harare harare idan na gan ki. Kin gan ni nan. A SMC quarter mu ke da zama. Amma saboda ke, sai in zo Fulani road wajan mahaifiyar baba na tai sati don in ri'ka ganin ki kawai. Wanda da ni samm said an matsamin sosai ma na ke zuwa wajan ta na gaishe da ta. Kin ga dai ba wani nisa gare mu ba. Ina SMC ina Fulani road. Ai ba wani ni da. Wallahi Mufeeda INA son ki har cikin zuciya ta, kuma auran ki na ke so na yi nan Kusa idan har za ki ba ni dama".
Shuru Mufeeda ta yi. Cikin zuciyar ta kuwa cewa tai,
"Ha'ki'ka kai 'din ba namijin da za'a ki amsa tayin sa ba ne, ko don fitinar gidan mu ma, ai na amince ma ka nie ma na tafi wana 'dakin ko zan huta". Amma a zahiri sai tai shuru.
"Feedat kin yi shuru ba ki ce komai ba".
Kamar ba za tai magana ba, sai kuma ta ce,
"Ka bari in yi tunani tukun".
"Na ba ki ishashshan lokaci Feeda. Take your time".
Shuru ya ratsa wajan na wasu 'yan sakwanni. Naseer ya katse shurun da fa'din,
"Dan Allah ina nai man wata alfarma".
Kallon shi ta yi na sakon biyu tare da mai da idanun ta 'kasa.
"Dan Allah ka da KI 'kara fitowa tallah". Naseer ya fa'da ya na kallon ta.
"Ka yi hakuri, bazai yu ba. Dole ne na fita tallah".
Shuru yai kamar bazai ce komai ba. Can kuma yai ajiyar zuciya tare da fa'din,
"To na ji. Amma ki sa ni, kullum idan ki ka fito, zamu ha'du a nan. Ni zan miki jute sai ki koma gida. Don wurin na wallahi ba tsaro, 'yan iskan unguwa sun yi yawa a wajan".