Showing 12001 words to 15000 words out of 115393 words

Chapter 5 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22939

"Lafiya 'kalau my boy. Ya ka baro Haruna da iyalan shi??" Daddy ya tambaye shi.
"Alhamdulillah, sun ce a gaishe ka".
"Masha Allah Ina amsawa. To ya wajan aikin? Zane ya fita yadda ka ke so?"
"Eh daddy har ma an fara aikin wajan. Nan da kwana biyu zuwa uku ma Zan koma".
"To masha Allah. Allah ya taimaka ya kuma maku albarka".
"Ameen daddy nagode". Sai kuma yai shuru ya sunkuyar da Kai, shi bai tashi ya tafi ba, kuma shi bai ce komai ba.
Murmushi daddy ya yi, don tunda yaga hakan yasan akwai magana a bakin 'dan nashi. Gyaran murya ya yi tare da fa'din,
"Nasser akwai magana a bakin ka, mai ke faruwa? Ina jin ka. Fa'damin damuwar ka 'da na".
Haj Zulfah na jin hakan, ta mi'ke za ta bar wajan domin ta bawa 'da da uba waje su ga na. Amma sai ya Mata alama da ido alamar ta koma ta zauna. Ba musu ta dawo ta zauna.
Gaban shi na fa'duwa, bai San ta yaya daddy zai 'dauki zancan nashi ba. Amma haka ya tattaro kwarin guiwar shi ya soma bawa mahaifin nashi labari tun daga lokacin da ya taimaki Mufeeda har aikin da aka Mata da kuma zuwa gidan su wajan 'kanin mahaifin ta da ya yi. Sannan ya 'karasa maganar da fa'din,
"Daddy idan har ka aminci Zan 'dauko Mufeeda da 'ya'yan ta zuwan nan gidan, sai ta zauna anan shashan wajam Ummah".
Mi'kewa zaune daddy ya yi tare da.......



*SHARE AND COMMENT*

*_MAMAN UMMEE CE_*✍🏼
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*


🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.

*STORY AND WRITTEN BY* *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* ( _Maman Ummee_)


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )

*PAGE 9*


"Ban fahimci mai ka ke fa'damin ba son. Ka na nufin yarinya ta haifi 'ya'ya har biyar, sannan kuma iyayan ta sun'ki yarda ta zauna tare da su saboda mijin ta ya sake ta har Saki uku saboda ya na zargin ba 'ya'yan shi ba me?
"Kwarai haka maganar yake daddy" architect ya ba shi amsa.
"OK na ji, amma ka ba ni lokaci zanyi bincike a Kai tukun ina da mutane a Kadunar ai.
"Nagode daddy Allah ya 'Kara girma". Naseer ya fa'di hakan.
"Ba komai Naseer, ai 'da na kowa ne, haka ake so ka cigaba da taimako, Kai ma Allah zai taimake ka".
"Wannan haka ya ke" haj Zulfah ta fa'da.
Mi'kewa ya yi tare da fa'din
"daddy ba ri na duba company'.
"Ok Allah ya kiyaye, sai ka dawo"
Da ameen ya amsa tare da yi musu sallama ya fice.

ѧsıɞıţı
Ayaan ne ke ta 'barka kukan nai man abinci, Abid na hannun Baaba Habiba shi ma ya na nashi sai faman jijjigashi ta ke yi. Irfana, Shahad da Husna kuma suna bacci.
"Baaba Habiba wallahi Allah Ayaan akwai ci ga rashin hakuri, dama dama ma Abid idan na bashi ya sha yana barin rigimar" Mufida ta fa'da.
"Haka nan zaki ta hakuri, amma dai kam wa'dannan 'ya'ya akwai cin tubarkallah." Baaba Habiba ta ba ta amsa.
"Aikam suna yin shekara Zan ya ye su ne" ta fa'di hakan ne ta na yamutsa fuska. Ita tasha ganin matan da suka haihu, kirjin su yayi ha'ke ha'ke har suyi ta 'korafi ya na masu ciwo, amma ita Sam ba haka ba ne a wajan ta saboda wa'dannan 'ya'ya masu bala'in tsotso KO bacci bata samun yi, don ma watarana juya masu baya take yi ta kyalesu da baaba Habiba.
Dakyar ta samu suka nutsu su Kai barci ta kwantar dashi ta na ajiyar zuciya. Wayar da Architect ya bai wa baaba Habiba ne yai 'kara. 'Dan kwance zanin ta tai tare da saka hannu cikin lalita ta zaro wayar. Duk da ba ta duba wayar ba tasan mai kiran wayar, don tunda ya ba ta wayar shi ka'dai ke kiran wayar. Ita ma Mufeeda ta san shi ke kiran wayar, wani sanyi taji cikin ranta, don tun da ya tafi sau 'daya ya kira su. Hakan sai ya dame ta. Wanda ya taimake ka ai Kai ma dole ka damu da shi.
Mi'ko mata wayar Baaba Habiba ta yi, tare da fa'din
"gashi Mufeeda 'dauki kamin ya tsinke, kin San ni ba sanin kan wayar nan na yi ba". Kar'bar wayar ta yi kamin ta 'daga kiran ya tsinke.
"Laah kin ga kuwa har Kiran ta tsince". Kamin baaba Habiba ta ce wani abu, wani kiran ya 'Kara shigowa. 'Dagawa tai ta Kara a kunnan ta tare da fa'din,
"Assalamu alaikum."
"Ameen wa'alaikissalam, ya 'karfin jiki maman quintuplets ?"
Siririyar dariya ta yi tare da fa'din,
"Alhamdulillah. Ya gajiyar hanya?"
"Wai sau nawa za ki tambayi gajiyar hanyar nan ne? Ai nan riga na Saba zirya tsakanin kano da Kaduna, gajiya ai ta bi lafiya. Ina babies 'dina?".
"Ga sunan sun gama rigima suna barci". Ta ba shi amsa.
"Ana dai basu abinci suci su 'koshi ko???"
"Uhmm" kawai ta ce masa.
"Yaya da uhmm kuma? Ki yi magana ma na. Idan fa ba ki basu abincin su suci su 'koshi zamu samu matsala da ke faaaah, tom".
Murmushi kawai ta yi. Sosai Mufeeda ta bawa Naseer babban matsayi a rayuwar ta, jin shi take yi kamar wani 'dan uwa, Kai ko a cikin 'yan uwan ma samun irin shi sai an tona, shi mutum ne mai zuciyar zinari, tabbas Mufeeda ta San akwai mutanan arziki a cikin al'ummah, kuma al'kawari ta 'daukar wa kan ta akan bayan iyayan ta to sai wannan bawan Allah a cikin addu'ar ta. Tabbas ya taimaka mata a dai dai lokacin da take ga'bar mutuwa.
Katse mata tunanin ta ya yi da fa'din,
"Kin yi shuru. Ina baaba Habiba ta ke?" Amsa ta bashi da,
"Ga ta can"
"Ni ma in sha Allah jibi Zan dawo, don doctor Haroon ya fa'damin jibin za'a baku sallama, don't duk kuna cikin 'koshin lafiya."
Gaban ta ne ya bada sautin daam don tunawa da ta yi zata bar asibiti, kuma tasan cewa baba Kalla bazai ta'ba Bari ta sauna masa a gida ba. Kai ko da ma ya bari, baaba mai zogale baza,ta Bari ba. To yanzu ina za ta nufa da 'ya'ya har biyar??
"Hello ko ba kiji abunda ba ce ba ne??" Ya katse Mata tunanin ta.
" haka ne naji sauki, muna cikin koshin lafiya. Allah kuma ya dawo da kai lafiya".
"Ameen ameen, sai nazo in sha Allah ko mai zai dai dai ta, ni bawa baaba Habiba wayar"
Mi'kawa baba Habiba wayar ta yi tare da fa'dawa dogon tunani inda zata samu matsuguni ita da 'ya'yan ta biyar. Hawaye ne suka gangaro Mata, tai saurin sharewa don ka da baaba Habiba da ke waya da architect ta Gan ta tare da jifan tsohon mijin ta da Allah ya isa, don shi ya jefa ta a halin da take ciki yanzu.

"Muje mana 'yalla'bai, favorite 'din ka ne fa, Avocado juice ne na ha'da maka da pancake, Allah idan ba ka tashi ba zan yi fushi in wuce Abu na ni ka dai inyi lunch 'din"
Sanye take da wando jeans pitch color pencil ne, sai wata arniyar riga kalar ta ba'ka mai shape 'din love ♥ ta gaban rigar, kalar rigar ba'ka, a gaban rigar anyi rubutun cool baby a jiki, sai wasu siraran igiya guda biyi ta bayan wuyar rigar, bayan rigar a fafare ya ke. Fuskan ta simple makeup ne, amma ba 'karamin kyau ta yi ba, kasancewar ta farar mace.
Shikuma zaune ya ke akan kujera 2sitter, cinyar shi kuma laptop ne a kai yana tura sako ta email. Aje laptop 'din ya yi a gyefe tare da fa'din,
"Ooh my princess, wannan wankan na ni kawai ya isa ya rikita ni, na kasa aikin da nake yi" ya fa'di hakan ne tare da janyo ta ta zauna akan cinyar shi, sannan ya zagaye hannun shi ya rungume ta, tare da ha'de goshin su.
Ashagwa'be ta ce,
"Pleaseee ka tashi muje dinning. I'm hungry. Your unborn child is also hungry. Do you want him/her to die?"
"Oh no no no, please stop saying that, you and you child are my world, my joy and My happiness. I can't live without you."
"Really then let go and eat".
"OK babe as you wish, cus ur wishes are my command". Ya na gama fa'din haka ya 'daga ta cak, bai aje ta ko ina ba sai dinning. Za ta mi'ke ya mai da ya zaunar ta re da fa'din,
"Ohh please just sit there, i'm going to serve you today".
Plate ya 'dauko ya zuba fried superghetti da yaji naman kaza sai tururi ya ke ya zuba. Kallon ta ya yi tare DA fa'din,
"Zaki sani, ki ka ce kinyi pancake da avocado juice ko"
Dariya ta yi tare DA fa'din,
"To Kai ne ai tun tuni nake magiya ka taso muci abinci amma ka'ki sai faman aiki ka ke yi sai ka ce agogo"
Aje plate 'din ya yi a kusa DA ita sannan ya zagaya ya 'daga ta akan kujeran ya zauna sannan ya zaunar fa ita akan cinyar shi. Fork 'din ya saka ya 'debo taliyar tare DA fa'din,
"Oya open your mouth".
Bu'de bakin ta yi shikuma ya saka mata taliyar, haka ya dinga 'debowa yai ta ba ta ita kuma ta na ci. Kar'ban fork 'din ta yi a hannun shi ta 'debo taliyar ta Kai baking shi, ya bu'de baki sai ta saka a bakin ta. Cakulkuli ya soma Mata, sai zillewa take yi ta na dariya. Taliyar ta 'Kara debowa, ya kuma bu'de bakin shi, wannan karan ma ta saka a bakin ta, aikuwa ya Kai bakin shi zai tsotse na bakin ta, ta 'kumshe bakin ta GAM.
"Ina wasa dake? Kin San Allah KO ki bude bakin ko Kuma haahahaa yarinya"
Hannun ta ke karka'da masa, tana yin baya shikuma yana 'Kara ri'ko ta.
Naseer! Naseer!! Naseeer!!!
A furgice ya mi'ke ya na rarraba idanu, caan kuma ya saki mugun tsaki tare DA fa'din,
"Wannna wani irin iskanci ne haka KB? Kafi kowa sanin yadda na tsani ina bacci a tada ni. Kai banza ne wallahi".
"KO kuma Kai ne banzan ba. Ka Saki har mutane kazo abun na damun ka, tunda gashi har mafarkin ta kake yi sai sakin murmushi ka ke yi, ai wallahi Nas ka na DA mugun matsala, ba irin shawarar da ban baka ba, amma Kai kunnan uwar shegu da ni. Ai gashi nan tun ba'a jeko'ina ba ka na da na sa ni, wallahi Naseer ka cutar da Mufeeda, kuma wallahi samun irin da wuya a wannan zamanin. Wani iron hakuri ne wannan baiwar Allahn ba ta yi da Kai ba".





*COMMENT AND SHARE*


*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
[7/17, 3:10 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*



🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)

ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*PAGE 10*


"Allahu Akbar ya akrami Kabiru. To uban wa ya ce maka mafarkin ta na ke yi? Kuma da ka ke maganar bazan samu kamar ta ba, ai shika uku na yi Mata, ka ga kenan kana iya bin layin zaurawan ta, wata'kila sai Kai DA ce. Wallahi KB ka fita daga idanuwa nan in kulle, ka DA ka sake zuwa min DA maganar wannan shai'daniyar yarinyar a inda na ke. Tunda Ku bakwa ganin abunda ta min sai Wanda ni na Mata. To wallahi idan har ka na 'kaunar tarayyar mu to ka dai na kawo min maganar ta, tom".
"Hmmm haka dai ka ce koh" KB ya ba shi amsa.
"Kwarai haka na ce" shi ma ya mayar masa a harzu'ke.
"To ai shikenan, amma ni ma Ina DA magawa, wallahi duk ranar da Kai na NADAMA ka DA ka sake ka tuna cewa ka na DA wani aboki mai suna Kabiru, domain wallahi babu abunda Zan iya mama. Kuma ma ba wannan ya kawo ni wajan ka ba, Abba ne ke Neman ka, an Kira wayoyin ka duka a kashe. Nagama" ya na gama fa'din haka ya mi'ke ya fice daga dakin.
Tsaki Nasser yaja yare DA shigewa ba yi, shower ya sakarwa kanki, mafarkin DA ya yi ne ya dawo mashi a kwakwalwa. Tabbas duk abunda ya ga ni a cikin mafarkin shi, hakan ya faru lokacin DA suke zaman lafiya DA Mufeeda, soyayyar su ya Fara tariyowa tun daga ranar DA suka Fara ha'duwa. Dogon tsaki yaja tare DA dukan bango.
"Sam ni ba ta raina yanzu",ya furta DA 'karfi.


ⓚⓐⓝⓞ ⓢⓣⓐⓣⓔ
Architect Naseer ne dur'kushe a gaban mahaifin shi ya na sauraron abunda ya ke fa'da.
"Naseer an gama min bincike akan wannan yarinyar DA kake son taimaka wa, gaskiya bata tare DA mutanan kirki, kama ta task cikin 'kuncin rayuwa. Marainiya ce amma ba ta samu iyayan ri'ko na arziki ba. Na amince maka ka taho DA ita idan har ta amince, amma ka Fara 'daukar ta kamar yadda ka ce idan an bash sallama a asibitin, sai ka Kai ta can gidan nasu wajan 'kanin mahaifin na ta, idan har ya'ki kar'bar ta, ka taho DA it's kano kawai."
Sosai yaji farin cikin amincewar DA mahaifin shi ya yi, duk DA has an damage mahaifin nashi mai taimako ne.
"Nagode kwarai daddy, Allah ya 'Kara girma da lafiya. Ya kuma sa ka cika DA kyau DA imani". Naseer ya fa'da.
"Ameen son, yaushe zaka wuce kenan?"
"Yanzu na ke so na Kama hanya daddy" Nasser ya ba shi amsa
"To Naseer Allah ya kiyaye hanyar". Da ameen ya amsa tare da mi'kewa ya fice daga 'dakin na nufa 'dakin mom 'din shi tare da sallama ha'de da knocking. Daga ciki mom ta bashi izinin shiga.
"Ba dai har ka fito ba?" Mom da ke take wa baby kai ta jeho masa tambayaa. Mai makon ya ba ta amsa sai ya ce,
"Haba mom, wannan yarinyar fa wata rana gidan miji zataje amma har yanzu bata San kan ta na, dubi fa! Babu abunda ta iya sai dai ta kwanta ta karanta novel sai kuma kallon series film. Wallahi akwai gyara a lamarin yarinyar nan".
"Na ce uban ka kaji ko? Ya zaka shigo min 'daki haka kawai ka hau masifa. Kafa kiyaye ni Nasser. Kuma da lake maganar banza ka ai kai ne mijin na ta na gobe".
"Ni 'din?" Ya nuns kan shi tare da tambaya.
"Ah'a ni". Mom ta bashi amsa tare da mama mass harara.
"Ohh mom please don't even dream about that".
" Really" mom ta tambaye shi.
"I can't marry this little spoil brat, and I'm saying the fact."
"Zan gani ni da kai wa ya haifi wani. Get out of my room. Nonsense!!" Sassautar da murya ya yi tare da fa'din,
"I'm really sorry mom. I don't mean to upset you, kawai dai ki dai na magana a gaban ta kin San ban San rai ni. By the way, I'm going now. Need ur prayer".
"Allah ya kiyaye, kuma idan har sai ka na sin my shirya da kai wallahi Naseer sai ka amince da Baby a matsayin matar aure".
"Mom sai na dawo" peck ya ba ta a forehead tare da wuce wa.
Ita kuwa Baby tuni dama ta fara hawaye. Ya ba fucewa ta saki kuma mai sauti har da shasshe'ka.
"Will u stop that nonsense! Ai duk laifin ki ne. Sau nawa nake zaunar fake ina karanta miki abunda yayan ki Naseer ke so, amma nan kike watsar dashii, kuma idan har haka saki cigaba ki na ji ki na ga ni wata zata kwace miki shi, sai dai ki zama 'yar kallo, kuma babu abunda zan iya miki. Ke ya kamata ki wa kanki fighting, ki shisshige masa, ki koyo dabarukan da zaki sake zuciyar shi. Amma kin zauna sai kuka. To ki zauna nan garin kallon ruwa kwado ya miki 'kafa". Ta na gama fa'din haka ta fice ta bar ta a 'dakin.
"baby kuwa ha'da kai ta yi da 'gado ta saki kuka tare da jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login