Showing 30001 words to 33000 words out of 115393 words
wayar.
"Assalamu alaikum, Ummu na".
"Ameen wa'alaikassalm, yaro na tun jiya na ke nai man ka bai Shiga".
" Ummu na sharrin network ne". Fa'din Naseer.
"Abbu na ban ji da'din abunda ka aika ta ba Sam, ba ayin saki a cikin fushi, idan rai ya 'baci hankali ke ne mo shi. Kai saurare ni da kyau, wannan umarni ne, ko da wasa ka da in 'kara jin ka saki matar ka. Sannan kuma ka je ka nai min yafiyar mahaifiyar ka, domin ta na fushi da kai, kuma ka janye maganar da kan yi akan matar ta na cewar abunda ke cikin ta ba baka ba ne. Umarni na ba ka, duk da babu igiyar aure a tsakanin ku, ka kula da ita alfarmar abinda ke cikin ta, ko da kuwa ba naka ba ne. Don a addinan ce aure ya baka, ka ciyar da ita har sai ta haihu ta kuma yaye abunda ta haifa. Kaji ni ko ba ka ji ba?".
"Naji Ummu nah, zan yi abunda kika ce alfarman bakin ki da kika saka a maganar".
"Yauwa baba na Allah ma ka albarka". Daga nan suka cigaba da firar su. Sosai take 'kaunar 'dan 'yar tata, duk da tun ya na 'dan shekara takwas bai 'kara ganin ta ba har yanzu, sai dai ya ji murya ta ko kuma ya gan ta ta video call.
*KANO*
KASH NA GAJI WALLEH, MU HA'DU GOBE IDAN COMMENT SUKA RIKITANI.
*MAMAN UMMEE CE✍🏼*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 16*
*KANO*
Basu suka gama meeting 'din nan ba sai karfe 12:30pm. Kai tsaye office 'din shi ya shige ta re da shiga ba yi ya kama ruwa kana ya 'dauro alwala domin amfara kiraye kirayan sallah. Ko bi takan wayar sa ma bai yi ba. Ya na fito wa ya wuce masallaci, bayan an idar da sallah ya shiga restaurant ya ci abinci ka na ya koma office don akwai wasu aikin da yake son kammalawa.
'Karfe hu'du dai dai ya tashi. Wayar sa ya 'dauka akan teble ya jefa jaka, sannan ya 'dauki briefcase 'din sa ya fito daga office 'din ya yi office 'din manager. Minti talatin ya yi a office 'din sannan ya fito. Sai a lokacin ya fiddo wayar sa da ke cikin aljihun wandon suit 'din shi don kiran waya.
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un! Lafiya Mummy ta ke ta mun kira haka?". Naseer ya fa'da tare da dialing number mummyn. Bugu biyu ta dauka tare da fa'din,
"Duk in da kake, ko mai kake yi, ka barshi ka zo ka same ni a gida yanzu. Kuma umarni ne". Diiif ta kashe wayar.
Ciro wayar ya yi daga kunnan shi ya na kallon wayar. Mai da wayar cikin aljihu ya yi gaban sa na fa'duwa yai wajan motar shi ya shiga tare da barin companyn yai hanyar gida.
"Hajiya mun gode Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" fa'din baaba Habiba.
"Haba Baaba Habiba, na ce ku dai na min godiyar nan, ku 'dauka duk 'daya muke daku. Ni Sam ba na jin da'din yawan godiyar nan da kuke min". Fa'din haj Zulfah.
Mufeeda ma ta bu'de ba ki za tai magana haj Zulfah ta dakatar da ita tare da fa'din,
"Sam bana son jin ko mai, na San ke ma godiyar ce za ki yi. Idan ma godiyar kuke so ku mun, to ku maye shi da mun addu'ar cika wa da kalmar la'ilaha'illah muhammdur rasulullah (saw). Shine kawai bu'katata a gare ku".
"In sha Allah ko zamu kasan ce cikin masu muki addu'a da fatan cika da kalmar shahada". Fa'din baaba Habiba da Mufeeda.
"Yauwa nagode hakan kawai nake bu'kata a gare ku. Yanzu dai Baaba Habiba ta shi za ki yi mu shiga kitchen mu samawa kan mu abun da zamu ci, kin San fa ba'a son a na barin mai jego da yunwa. Musammam ma ita da take shayar da 'ya'ya har biyar".
"Haka ne kam". Baaba Habiba ta fa'da tare da mi'kewa ta nufi hanyar kitchen 'din haj Zulfah ta rufa mata baya.
********
Ya na parking kai tsaye ya nufi hanyar part 'din mahaifiyar sa. Mur'da handle 'din yai ya shiga. Gaban shi ne ya buga daaam sakamakon ganin mahaifiyar shi da ya yi fuskan nan kamar hadari, gyefan ta kuma 'yar shi ce Nazeera sai ma ka mishi harara ta ke yi. Ga kuma iyayan munafurci gyefan ta. Cak ya tsaya a tsakar 'dakin.
"Dole ka ja ka tsaya sabida kasan tsiyar da na shuka. To sai ka 'karaso ka warware mana munafurcin da kuke 'kullawa kai da 'kanwar uwar ka, wallahi tur da halin ka Naseer. A ce da kai za'a ha'dewa mahaifiyar ka kai, bayan banza kai ma ba barin ka a kai ba".
Naseer da kan shi a kulle ya ke, ya kalli yayar ta shi ta re da fa'din,
"Aunty Nazeera mai ke faruwa ne? Wallahi ni Sam ban San mai kike magana a kai ba. Wani abun ne ya faru?".
Aunty Nazeera ta hayayya'ko masa tare da fa'din,
"Uban ka ne ya faru! Mu zaka matar shashashu? Wa'dancan 'yan iskan karuwan da wancan tsinanniyar mata ta saka ka ka kwaso su har cikin gidan uban ka, ma ye ha'din ka da su? Naseer har da jarirai biyar. Hauka ka ke yi?". Aunty Nazeera ta fa'da kamar zata kife shi da mari.
"Waya sani ma ko harkar satan jarirai ta soma, kuma ta ke son tsunduma shi a harkan". Fa'din baby ta na wani juya idanu irin na 'yan shaye-shaye.
"Ke dan uwar ki ni sa'an ki ne da ana min magana zaki saka baki? Ta shi ki bar palon nan ko in zo in taka miki kai a wajan".
Da gudu baby ta bar palon don sarai ta San halin Naseer zai iya aikata abunda ya fa'da.
"Ni zaka zaga ba ita ba, ka zo ka zauna ka ma na bayanin inda ka same wa'dancan mata da jarirai har biyar. Waya San ko abunda babyn ta fa'da ma ko gaskiya ne".
Zama yai akan 1sitter ta re da fa'din,
"Aunty na fa riga da na yi wa mummy ba ya ni tun ranar da muka iso nan gidan".
"Ma'karyacin banza ma'karyacin wofi. To asirin ka tonu, domin 'kanwar uwar ta ka da kan ta ta furta babu abundan su ka ha'da da su".
Ajiyar zuciya ya sauke, domin yanzu ya tabbatar da zargin sa. Tabbasa 'dazun la'be Baby ta ke yi a windon Umman shi. Kuma ya tabbatar ita tazo ta zayyane masu duk abun da ta ji. Kuma ya 'kudurta yin maganin ta. Gyara zma yai ya fuskance su tare da fa'din,
"Mummy gaskiya na 'boye miki gaskiya da farko, ha'ki'kanin gaskiya babu abunda wa'inda na kawo jiya suka ha'da da Ummah, asalima taimakon su take yi".
Tun daga farko ya zayyane mata labarin Mufeeda tare da fatan zata ji tausayin sa.
"Sannu sarki masu taimako na duk duniya. Shikenan a duk fa'din Kaduna aka rasa wanda zai taimake ta sai kai Audu taimako ko? To bari kaji da kyau, yau ba gobe ba zasu bar gidan nan. Bari uban na ka ya dawo". Fa'din mummy kamar za ta ta shi ta rufe shi da duka.
"Wallahi mummy ka da ki sake ki yadda su zauna a gidan nan, a zamanin yanzu ana taimako ne. Yanzu yanzu zaka 'dauke mutun daka rana ka kai shi inuwa, shikuma ya mai da cikin wuta ba ma ranar da na fiddo shi daga ita ba. Saboda haka Sam ka da ki yadda da zaman su a gidan". Fa'din aunty Nazeera.
"To wai aunty ke ina ruwan ki a cikin sannan batu? Naga dai ba gidan ki na kai su ba ko? To ki kama girman ki wallahi". Fa'din Naseer ran shi a 'bace.
"Dan uban ka ta shi ka make ni kaji ko? Shege mara kunya. Ko Lukman ya isa ya fa'da min magana ba re kai da aka haife ka da wayau na. Gaskiya mummy sai kin ta shi tsaye akan Naseer idan ba haka ba shi zai nai mi yai ajalin ki". Fa'din Nazeera ta na nuna Naseer da yatsa.
"Da izinin ubangiji mahalicci bazan yi sanadiyar mutuwar mahaifiya ta ba, kuma da kin kama girman ki ba yadda za'ayi ki na fa'da ina fa'da, mai ya sa ban ta'ba yiwa aunty Saudhart haka ba".
"Sabida halin ku 'daya. Munafukai da bakwa kishin uwar ku". Fa'din Nazeera.
"A hakan ne ki ke da bakin fa'din na rai na ki, bayan ita kan ta aunty Saudhart 'din ma ba girman ta ki ke ga ni ba, ita da ta ba ki shekaru a 'kalla takwas ko tara".
Za tai magana Mummy ta katse ta da fa'din,
"Dallah ya isa haka, ban San iskanci. Kinzo nan ne ki biye masa ku tada min da hawan jini? Ku ke nan kamar ku na ganin hanjin juna ke da Naseer, sai ka ce shine sa'kon ki. To ko Lukman bakwa irin wannan fa'dace fa'dacen shi da yake sa'kon ki. Dan Allah idan bazaki kwantar min da hankali ba, ki tattara ki tafi gidan ki".
"Shikenan ai. Da ma nasan abunda za ki fa'da ke nan, Sam ba ki son laifin Naseer, kuma Gashi shi ke saka mini ciwon kai. Ina wajan aiki na ki ka kira ni akan wannan zancan. Yanzu kuma a gaban ki ya ke min rashin kunya, kuma kike goyan bayan shi". Fa'din Nazeera da ta mi'ke ta na tattara wayoyin ta tare da saka wa aja alamu ta na shirin taafiya in da ta fito.
Kwantar da murya mummy ta yi tare da fa'din,
"Ba ina goyan bayan shi ba ne Nazeera, kawai ba na son yawan fa'dan da kuke yi ne ke da 'dan uwan na ki. Shi yaro ne har yanzu. Sai ki na yi ki na kai zuciyar ki nesa".
"Hmm Naseer 'din ne yaro? Da ya yi aure ai da yanzu ya na da 'ya'ya. Yaron da ke da shekaru har ashirin da bakwai shine yaro ko? Hmm ki na nan za ki ga ni, sai ya zo maki da zancan da zai kusan tarwatsa miki zuciyar ki. Ni kin ga lafiya ta, patient's na can na jira na". Ta na gama fa'din haka ta maka wa Naseer harara tare da ficewa. Shima bayan ta ya bi da harara ya fice.
_***********_
8:30pm
"Na rantse da Allah bazan yadda in zuba idanu Zulfa'u na cutar min da 'da na ba, ka na ga ni ta saka shi kwaso wasu 'yan iska har da 'ya'ya biyar ya kawo su gidan nan kuma ka zuba masu idanu. To ni Sam ba haka nake ba. Wa'dannan mata sai sun bar gidan nan, don nasan nan gama za'a iya jifan 'dana da cikin, kuma abunda bazan lamun ta ba ke nan". Fa'din. Haj Jummai da ta tsaya akan alhj Mudassir ta na zazzaga masa masifa".
"Kin gama Inna Huwaila(Mahaifiyar sa)?". Alhj Mudassir ya fa'da.
Kumburo ba ki tai ta na harare harare.
"To idan har dai wannan gidan ba da 'darin ki a ka gina shi ba, babu in da Mufeeda da Habiba za su je, har sai Allah ya nuna na shi ikon, kuma kin san Allah, idan kika 'kara min magana akan su, to tare zaku bar gidan nan ke ki na ku gidan, tafiya ta har abada, su ma su ta fi. Ke sai dai ke ki tafi, su amma suna nan gidan, da'din abun ba mace 'daya gare ni ba". Fa'din Alhj Mudassir.
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tokare mata wuya, ji ta yi idan har ta bu'de ba ki tai magana zuciyar ta za ta iya faso kirjin ta. Ta shi ta ta hau sama fuuuu kamar kububuwa.
Kiran waya ne ya shiga a wayar alhj Mudassir. Ya a duba fuskar wayar ya ga autan shi ne Naseer.
"Hello yaro na ya akai?".
"Daddy wallahi tafiya ce ta kamani yanzu zuwa Lagos, kuma a'kallah zan yi sati biyu, yanzu haka ma bari na nan, ga ni nan ni da Mustapha da PA na zamu hau jirgi nan da 10min zai ta shi. Don Allah ka lalla'ba min mum fushi take yi da ni".
"Ka da ma da mu my son Allah ya tsare ya ki ya ye hanya".
Da "Ameen" ya amsa tare da katse wayar don an soma kiran su. Ya so ya kira Umman shi ya shaida mata, sai dai ya bari idan ya dauka ya kira ta.
*BAYAN SATI BIYU DA KWANA BIYAR*
Wata kyakkyawar farar matashiyar budurwace sanye da wani tsadaddiyar lace kalar maroon da ratson pitch colour ajikin ta, 'dinkin riga da skirt ne ya amshi jikin ta. Fara ce sol doguwa ba can ba, ta na da goguwar fuska da dogon hancin har baka, idanuwan ta dara dara farare tass irin idanun nan da ake masu la'kabi da _lulu eyes_. Gashin ta ba'ki si'dik har saman goshin ta, le'ban ta jaa da ya 'kara 'kawata kyawun fuska ta. Girar ta har ha'dewa yai kuma kamar an mata cabin. Siririyace amma ba can ba, kasan ta a bu'de ya ke. Iri matan nan ne da ake masu la'ka bi da _cocacola shape_.
Saukowa take yi data staircase 'din taa nufo parlour hannun ta ri'ke da 'dan madaidai cin cup da cokali a ciki ta juya suger da ta saka a cikin custard 'din da ta ha'da yanzu.
Architect Naseer ne ya mur'da handle 'din kofar tare da sallama, idanuwan sa ya sauka akan wannan baiwar Allah da isowar ta palon ke nan. Gaban shi ne ya bugs da wani irin karfi. Lokaci 'daya ya ji wani abu ya aiki zuciyar shi. Idanuwa ya zuba mata ko kyaftawa babu.
Cikin zuciyar ci ya ke fa'din,
"Tsarki ya tabbata ga haliccin wannan baiwar Allah. Lallai Allah ya yi halitta a nan. A ina Ummah ta samo wannan kyakkyawar halittar.
A wannan lokacin haj Zulfah ta fito saga kitchen ita ma hannunta rike da feeder da ta ha'dawa AYAAN sarkin ci madarar shi. Ta kalli wannan baiwar Allah tare da fa'din,
" Yauwa Mufeeda maza zo ki bawa AYAAN madarar nan in koma in ha'dawa IRFANA na ta, ita ma ta soma 'yan koke koke, ga baaba can na fama da ABID da SHAHIDA.
Wani irin bugawa zuciyar Naseer ya yi lokacin da haj Zulfah ta kira wannan zanka'de'diyar budurwan da MUFEEDA.
HMMMMMMM yanzu aka soma labarin
*MAMAN UMMEE CE✍🏼*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 17*
"Ahhhh! Wa na ke gani kamar 'dana Naseer?".
Saurin juyowa Mufeeda ta yi, karaf idanun su ya sar'kafe waje daya.
Wani tsadaddiyar murmushi mai kashe jiki Mufeeda ta sakar mata Wanda ya karasa kashe masa jikin sa.
"Lah! yaya na ka dawo? Mun yi kewar, sannun da zuwa."
Jin sautin muryan ta ya yi kamar kukan tsuntsaye. Sai ya ji kamar bai ta'ba jin murya mai da'di kamar na Mufeeda ba.
"Wai dan Allah Ummah ta wannan Mufeey ce mummyn quintuplets?" Naseer ya fa'di hakan ya na nuna Mufeeda.
Dariya haj Zulfah ta yi tare da fa'din,
"Dan Umman shi ka ga mummyn biyar ta canza ko? Da ma 'kuraje ne suka 'bata mata fuska, shine nai maganin su da man da ke korasu".
"Masha Allah, wallahi kam Masha Allah".
Ya fa'di hakan ne ya na sake 'karewa Mufeeda kallo. Ita kuwa Mufeeda duk kunya sai ya kamata sabida irin kallon da Naseer ya ke bin ta da shi. Haj Zulfah wani murmushi ta yi irin na su na manya tare da fa'din,
"Karaso dan Ummah ka ci abinci, nasan ka kwaso yunwa".
Sosa kai Naseer yai sannan ya ce,
"Ummah na ba ri na fara watsa ruwa tukun, don jiki na 'kai'kayi ya ke min".
"To kwa'do sarkin wanka, aje a watsa".
" bari na ga quintuplets 'dina tukun, wai ma ina baaba Habiba? Ban ji motsin ta ba". Fa'din Naseer.
"Ta na can ta na fama da 'ya'ya. Kasan su akwai ci. Must especially takwaran ka AYAAN".
"Wallahi kuwa Ummah. Tun ranar da aka ciro shina naga hakan. Bari na je na watsa lokacin sun gama sai na gan