Showing 105001 words to 108000 words out of 115393 words
suka faru. Ya yin da gyefe guda Umaymah ta ke jin tsananin tausayin da shau'kin son ganin 'Yar ta.
Duk wannan abu fake faruwa har yanzu Naseer bai lura da Aaeedah da ke gyefan baban ta ba zai yanzu da ya'dago daga haukan burgiman da take yi kamar 'karamin yaro.
Aikuwa a matu'kar firgice ya 'dago tare da nuna ta bakin shi na rawa ya furta
"Mufeedah!".
Girgiza kai Aaeedah ta yi tare da fa'din,
"Aaeedah".
Kallon gaba 'daya 'dakin yai da mamaki bayyane a fuskan shi.
Kamo hannun shi daddyn Aaeedah yai tare da fa'din,
"Y'ar uwar ka ce, 'kanwar matar ka ce Mufeeda". Abie ya nuna Umaymah ta re da fa'din,
"Ita ce ta haifi Mufeeda, ita ce asalin mahaifiyar ta. Canje aka mata a asibiti.
Mi'kewa tsaye yai rare da Zaro idanuwa Naseer ya na kallon Ummu Nah, said a lokacin ya ke 'kara karanto tsantsar kamannin matar shi Mufeeda da Ummu nah, duk da yau ne karo na farko da ya fara ganin Ummu Nah ido da ido, amma duk Wanda ya kalle ta idan har yasan Mufeeda, dole ya ce it's 'din jinin ta ce.
Wani irin jiri ne ya 'dive shi tare da fa'duwa 'ka sa a sume.
*KANO*
"Wai mai kuke tsumaye ne? Za lu fito ko said na yi la'ana tare da 'debe albarka?". Inna huwaila ta fa'da.
Gaba 'daya suka fito wa'dan'da za'ai tafiya da su.
Idan ka kalli Mufeeda da yaron ta, ko ka'ki Allah zai sun baka sha'awa. Sin yi kyau sun yi 'bul².
Kai tsaye wajan sienna su ka nufa, kowa ya shiga, baaba Habiba, haj Zulfa'u da Innah Huwaila su ke ri'ke da 'yan biyar. Ayaan ko ya na hannun Naseer takwaran sa.
Yaya Abubakar ke driving. Motar su alhj Mudassir da ban shi da alhj Aliyu da driver.
Sienna kuma su Inna Huwaila ne, da baaba Habiba, da haj Zulfah, da Mufeeda da 'yan biyar. Sai Naseer da ya Abubakar da ke driving don Inna ta ce, da tu'kin shi ta Yar da.
Kasancewar fitowar wuri su kai, karfe 'daya da rabi a Kaduna tai masu. Kai tsaye unguwar su Mufeeda su kai da taimakon Naseer da ke masu kwantance.
Parking su kai gaba 'daya su ka fito Inna Huwaila sai sababi ta ke wai Shahida ta ishe ta da kuka.
Gaba 'daya layi aka fito ana kallon su, wasu a cikin su da suka san Naseer sai nuna shi su ke suna 'yan gulmace².
Mufeeda kuwa hawaye ne su ka shiga ambaliya a idanun ta, ga gabam ta da ke wani irin duka tara².
Naseer ne yai 'karfin halin 'karisawa 'kofar gidan tare da maka sallama.
Daga ciki mal Ahmadu ya amsa, don suma dawowar su kenan a daga can gidan su Naseer, domin ba shida lafiyaa sosai. Jinin shi ya hau har 200+.
Fitowa yai tare da mi'kawa Naseer 'din hannu. Naseer kuwa mamaki ya kama shi domin bai san shi ba. Shi KALLAH kawai ya sa ni. Ganin haka su alhj Mudassir su ka 'kariso wajan.
Ita kuwa Mufeeda ganin fuskan da ko a mafarki bazata ta'ba mantata ba ta saki wani 'kara tare da fa'din,
"Babaaaaaa". Da 'karfi tare da nufar wajan shi.
Mal Ahmadu wani irin juyiwa yai tare da sauek idanun shi akan Mufeeda .
Cikin wani tsantsan farin ciki ya nufe ta, ita kum ta rungune shi tare da sumewa a jikin shi.
*BAYAN MINTI TALATIN*
Babu abunda ka ke ni a 'dakin sai gunjin kukan Mufeeda, ta ma'kal'kale Fatima ta na mai murman ganin mahaifiyar ta ta.
Inna Huwaila kuwa said la'anar KALLAH ta ke yi da matar shi *MAI ZOGALE*.
Fatima da mal Ahmadu said farin ciki suke tare da 'daukar 'yan Biyar su na mai tasbiji ga ubangij.
Mal Ahmadu ya na dogon numfashi, bayan ya gama jero godiya ga Naseer kano da mahaifan sa, ka na ya 'daura da fa'din,
"Akwai wani abu da make so ku sani, amma so na ke mu 'dugun Zuma gaba 'dayan mu muje gidan surukan Mufeeda, a can za kuji komai".
Alhj Mudassir ya ce,
"Babu komai muje".
Inna Huwaila kuwa sai yamutsa fuska take yi, domin a Cesar ta, ba ta son ganin fuskan la'anannan Naseer tsohon mijin Mufeeda.
Gaba 'day an su suka 'dugun Zuma su ka nufo SMC. Dama mal Ahmadu ya kira daddy ya shaida mass Gashi nan zuwa da ba'ki, kuma ya na son kowa ya halarta a parlour kun su 'karaso.
Mal Ahmadu shi ya fara shiga parlour, ka na matar shi, sai haj Zulfah da baaba Habiba da ke 'dauke da 'ya'ya. Ka na Inna Huwaila sai alhj Mudassir da alhj Aliyu, sai Mufeeda da Naseer kano da suka shigo a tare.
Wani irin mi'kewa Ummu Nah tai tare da nuna alhj Aliyu ta ce,
"Aliyuuu".
Inna Huwaila ce tai saurin 'dagowa ta kalli Ummu Nah tare da fa'din,
"Umaymah?".
Naseer Kaduna kuwa wani tsalle yai guda ya isa gaban Mufeeda........
*MATAR SAYYADEE*
*SORRY 4THE LATE UPDATE*
🥰❤️❤️❤️❤️😡😍😍😍😍😍😍
*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
*AKA*
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 48_*
Wani tsalle Naseer yai sai ga shi gaban Mufeeda ta re da kamo hannun ta ya na fa'din,
"Mufeey ke ce? Ke na ke ga ni a gaba na? Dan Allah ki ce ba mafarki na ke yi ba".
Wani irin fizge hannun ta Mufeeda ta yi tare da auna mashi wani irin kallon tsantsar tsana. Nu na shi tai da hannun za tai magana. Muryan Inna Huwaila ya katse ta tana fa'din,
"Umaymah ke ce ki kai 'bul'bul da ke haka? Ikon ubangiji. To sake aure ki kai ne? In ce dai wa'dannan 'ya'ya da na ke ga ni ba 'ya'yan ki ba ne? Ni Huwailah da nai wa kai na. Na saka an sake ki saboda ba ki haihuwa cikin lokaci, ga shi yanzu na ganki da zu'ka zu'kan 'ya'ya har biyu masu kama da juna. Gaskiya nai wa kai na".
Aaeedah ce ta fito daga 'dakin su Zahida ta iso nan parlour. Wani irin zaro idanu Inna Huwailah ta yi ta re da nuna ta da yatsa bakin ta har rawa ya ke yi, sai kuma tai saurin juyawa ta kalli Mufeeda da ke gyefe ta na aunawa Naseer harara don ita ba ta lura da Mommah da ke kallon small daddy ba.
"Na shiga uku, wallahi dama tun ranar da na fara ganin Nasifa na ga kamar na ta'ba sanin mai fuskar, sai yau da naga Umaymah da wannan yarinya mai kama da Nasifa na tabbatar Nasifa duk yadda akai 'kanwar Umaymah ce". Inna Huwailah ta fa'da ta na matsar hawaye.
Mommah kuwa saurin kallon in da Mufeeda ta ke ta yi ta na zaro idanu domin sai yanzu ta gan ta. Cikin sassarfa ta nufi Mufeeda ta re da rungume ta tana fashewa da kuka.
Mufeeda kuwa gaba 'daya jikin ta rawa ya ke yi. Wani matsanaicin 'kaunar Matar da taga kamannin ta a fuskan ta ya ka mata, samun kan ta tai da rungume matar ita ma.
Inna Huwailah ta kuma sakin wani kuka tare da fa'din,
"Umaymah ki yafe min, na kashe miki aure babu gaira babu dalili. To babu dalili mana, shi haihuwa ai na Allah ne, amma ban duba haka ba, saboda kawai kin jima ba ki haihu ba, lokacin da KI Ka haihun kuma, sai Allah ya 'dauke abun sa, mai makon in yi tawakkali sai na saka aka sake ki ki na cikin ra'da'din rashin 'Yar ki. Dan Allah ki yafe min Umaymah. Gashi tun ba'aje ko in ba, na soma ganin ikon ubangiji. Eh to ikon ubangiji mana, tunda gashi kin sake aure har da kyawawan 'ya'ya har uku. Dubi wa'dannan mazan yan biyu da su gwanin bam sha'awa. Don ko ba'a fa'da min ba nasan 'ya'yan ki ne. Dubi 'yar nan dai, kamar kin yi Kaki. Ga kuma 'kanwar ki (sai ta nuna Mufeesa) ita dai kamar ku 'daya, ita ma dai zuri'a ne masu yawa a jikin ta. 'Ya'ya bihar fa ta haifa, uku mata biyu maza. La'anannan mijin ta yai mata duka ta na cikin halin na'kuda ya kuma sake ta har saki uku, yace ciki ba ba shi ba ne. To in ban da shi da'ki'ki ne wa zai duki mace da ciki ta na halin na'kuda, ko da ya ke an ce nan gidan iyayan yaron ne. Ban san wani la'ana ya sa iyayan Masifa su ka kawo mu nan gidan ba. Ga dai mu mun zo, sai a YI ta ta'kare. Don billahi ban barin Kaduna sai da auran Masifa da jika na Nasuru". (ta fa'din hakan ne ta na nuna architect Naseer kano).
Tun daga kan Naseer Kd, Ummu Nah, daddy Kd, Abban Aeedah, da kuma Mommah zubawa Inna Huwailah idanuwa su kai. Mommah ce tai 'karfin halin fa'din,
"Innah Wai ki na nufin Mufeeda ce tq haifi 'ya'ya bihar a cikin ta?".
"Karya zan miki ne wai? Ai gasu nan a hannun zurfa da Habiba da Nasuru jika na, sai ki duba ki ga ni".
Mutuwar tsaye Ummah na tai ta na bin 'ya'yan da ke hannun su da idanu. Mommah kuwa rige² aka shiga yi ita da daddy da kuma Naseer wajan 'daukan 'ya'yan.
Mommah ta 'dauki Husnah da ke hannun haj Zulfah. Daddy kuma ya 'dauki Abid da ke hannun baaba Habiba, shi kuma Naseer ya kar'bi Shahida da ke goye a bayan baaba Habiba.
"Subhanallah! Masha Allah!". Shi ne abunda daddy ya ke ta maimaitawa.
Naseer kuwa wani kuka ya fashe da shi mai sauti ya na 'kara rungume Shahida kamar zai mai da ta ciki ya fa'din,
"Astagfurullah! Allah na tuba, Allah ka ya fe min. Astagfurullah Allah. Yanzu duk wa'dannan 'ya'ya na ne? Allah nagode maka. Allah na yi maka al'kawarin azumi guda goma. Ta hakan ne kawai zan iya nuna maka godiya ta a gare ka da wannan ni'ima da kai min. Allah nagode maka".
Alhj Aliyu (small) daddy kuwa ji yai jikin shi na mashi wani irin rawa, ya kuma kasa 'dauke idanun shi akan tsohuwar matar shi. Ya yin da gyefe guda Abban Aaeedah ya ke jin wani matsanaicin kishi na taso masa.
Mufeeda kuwa saboda tsabar 'bacin rai idanuwan ta har wani 'kan'kance wa su kai. Ganin ta kawai ta yi tsaye gaban Naseer tare da 'daura masa zafafan maruka har hu'du tare da fizge Shahida a hannun shi ta nu na shi da yatsa muryan ta har cracking ya ke wajan fa'din,
"Ka da ka kuskura hannun ka ya 'kara tab'a min 'ya'ya na. Wallahi tallahi, akan 'ya'ya na har kotu zan iya shiga da kai. Ba ka da ala'ka da su, ba ka san su ba, basu san ka ba. 'Ya'ya na nawa ne ni ka'dai".
Idan ka cire Mommah, Naseer kano, daddy da Inna Huwailah, babu Wanda bai yi shock da abunda Mufeeda tai ba.
"Na tsane ka! Na tsane ka!! Na tsane ka!!! Mara tausayi wanda bai da 'digon imani a zuciyar shi. Ban 'kaunar ganin fuskan ka a nan, azzalumi macuci kawai". Mufeeda ta fa'da tare da rushewa da kuka.
Inna Huwailah ta kalli Naseer da ke du'ke dafe da kunci ya na wa Mufeeda wani irin kallon tsantsan 'kauna mai nuna duk abunda ki kai bazan ji zafin ki ba.
"Au dama kai ne tsohon mijin na ta? To amma dai Allah ya la'ance ka tare da 'debe maka albarka. Du be ka kamar mutumin arziki, amma a fuska Musa a zuciya Fir'auna. Allah yai wadaran ka dai". Fa'din Inna Huwailah.
"Dan Allah Inna ki yi shuru ki zauna". Fa'din alhj Mudassir.
"Bazan yi shurun ba, na ce banyin shurun. Idan kuma suha gulu (Super glue) za'a li'ka min sai in gani. A cuci yarinyar sai ace in yi hiru dan an rainan wayo. Wallahi sai in yi la'ana yanzun nan, ko in 'debe albarka ba ruwa na".
"Allah ya ba ki ha'kuri". Fa'din alhj Mudassir.
Harara ta maka masa, ka na ta mai da duban ta izuwa mal Ahmadu ta ce,
"Kai kuma sallamamme, ka 'dauko mu ka kawo mu nan, sai kai mana bayanin dalili. Don ni na 'kosa na bar garin nan tare da auran Nasifa".
Ajiyar zuciya mal Ahmadu ya sauke tare da fa'din,
"Don Allah duk mu samu waje mu zauna. Domin magana ce mai bu'katar natsuwa".
"To ai kun ji, sai kowa ya sa mu waje ya zauna". Fa'din Inna Huwailah.
Zama kowa yai tare da zubawa mal Ahmadu idanuwa.
*___________________*
"Alhamdulillah! Da farko sai godiya zamu fara yi wa ubangiji da ya bayyana mana 'yar mu Mufeeda cikin 'koshin lafiya hakan ya nuna mana Mufeeda hannun na gari ta fa'da. Abun da ya sa na tara mu ana shine akan in warware wani nauyi da ya ke kai na shekaru kusan ashirin da uku da suka wuce".
Sunkuyar da kai mal Ahmadu yai ya na hawaye. Haka kawai Mufeeda ta ji gaban ta ya buga sosai. Kuma duk lokacin da ta 'dago kan ta, sai sun ha'da idanu da matar da ta ke tsantsar kama da ita.
Wani ajiyar zuciya mal Ahmadu ya sake jaa ka na ya cigaba,
"A ranar da mai 'daki na ta ke cikin halin na'kuda, na kai ta asibiti ina cikin tashin hankali shin Fateema za ta haye ko kuma Allah zai 'dauki abunsa, kwatsam sai aka kawo wani bawan Allah shi da matar shi cikin mawuwacin hali. Anzo wucewa ta saitin inda na ke, bawan Allahn nan yai caraf ya ri'ke min hannu da 'karfi. Tare mu ka shiga har cikin 'dakin da aka kai shi za'a duba shi.
Wata nurse ta ce min ba fita za'a du ba shi. Amma sai mutumin nan ya ri'ke min hannu ya na girgiza kan sa. Wani tari ya turni'ke sa, sai ga jini guda² yana fitowa daga bakin shi. Hannu naga yana 'ko'karin sakawa cikin aljihun shi ya mi'ko min tare da fa'din bawan Allah dan girman ubangiji ka taimake ka sauke min wannan nauyin da ke kai na. Ha'ki'ka yau Allah ya nu na min iyaka ta, ka saurare ni da kyau zan baka ta'kaitancan labari na. Da ni ri'ka'k'ken dan fashi ne. Na tara dukiya da mahaukacin yawa har nai aure. Amma shekaruna ashirin da hudu Allah bai bawa mai 'daki na haihuwa ba. Munje asibiti har 'kasar waje, an tabbatar mana daga ni har mai 'daki na lafiyar mu 'kalau. Babu irin maganin da ba mu yi ba, daga 'karshe har kauce hanya mu kai amma Allah bai kawo ba. Daga 'karshe nai deciding ni da mai 'dakii na akan muje orphanage mu yi adopting kawai. Mai 'daki na ta aminta da hakan. Amma sai dai ta ce ita idan ba jariri ko jaririya ba, ba taso, don so ta ke ta shayar da jaririn da kan ta ta yadda sha'kuwa zai shiga tsakanin su sosai. Na yi na'am da hakan. Sai dai rashin sa'ar da aka samu, duk gidan marayun da muka je a kano ba jarirai, daga 'yan shekaru uku sai saama. Mata na kuma ta ce ita jariri ta ke so. An kar'bi number mu a wajan akan idan aka samu za'a kira mu. Cikin hukuncin ubangiji wata rana muna zaune da mata na sai ga kiran waya daga orphanage akan an samu jaririya. Cike da 'doki da farin ciki mu ka tafi gidan marayu bayan gama duk wasu cike² aka dan'ka mana jaririyar da a nan cikin orphanage aka yanke mata cibi don mahaifiyar ta na haihuwar ta ta ya da ta. Tun a mota wajan dawowar mu gida yarinyar ta shiga wani irin amai ta ba ki ta hanci. Nan na karya mota muka nufi asibiti. Nurse ta kar'be ta da gaggawa su kai wani 'daki da ita. Amma cikin hukuncin ubangiji yarinyar nan ba tai cikakkan minti goma ba ta amsa kiran ubangiji. Tun da aka sanar da mu mata na ta yanke jiki ta suma. Da kyar nurse su ka shawo kan ta. Kuka kam ta'ki dai na yin da na yi lallashin har na gaji. Wata nurse ce ta kira ni waje ta kawo min tayin jaririya akan mai zai hana na 'karba ita wacce ta haihun sai a ce mata 'yar ta ta koma. Ina jin wannan tayin farin ciki ya kama ni, tuni na koma 'dakin da aka baiwa iyali na