Showing 99001 words to 102000 words out of 115393 words
"Ban aure ki don ina son ki ba. Deal mu ka yi da ke. Kuma kin amince da hakan. Babu soyayyar wata 'diya mace a zuciya ta. Kuma ba na tunanin zan 'kara son wata 'diya mace. Na fa'da miki, idan kin gaji ki fa'da in sauwa'ke miki".
"Wallahi Naseer zan iya zama da kai koda kashi ne zai kasance abincin mu I'm dai zaka 'kauna ce NI".
Dogon tsaki Naseer yaja tare da fa'din,
"Ki soma ha'da kayan ki, gobe zamu tashi daga wannan gidan mu koma in da na kama. Ciki 'daya ne". Ya na gama fa'din haka yai ficewar sa.
Hannu biyu Mashkura ta 'daura a kai tare da kurma ihuu ta shiga birgima a 'kasa kamar mahaukaciya.
Mama ne ta shigo gidan ta taras Mashkura na wannan haukan. Cikin sauri ta 'karisa wajan ta tare da fa'din,
"Mashkura mai ya same ki?".
"Na shiga uku mama, na lalace. Naseer ba zai ta'ba so na ba duk abun da zan yi masa. Wani irin tuggu ne ban yi ba wajan rabashi da matar shi, amma hakan bai saka na samu soyayyar shi ba. Mama yanzu haka gobe zamu bar gidan nan mu koma gidan haya ciki 'daya kawai. Yanzu fa tuwan masara da koko na ke ci a gidan nan. Rayuwar ba da'di ga kuma rashin 'kauna daga wajan miji"
"Mai na fa'da miki Mashkura? Wani irin baki baki ne ban yi ba. Dama duk daran da'dewa nasan haka zai faru. Gashi tun ba'aje ko ina ba, kina ganin abunda kika shuka. Kin raba aminiyar ki da mijin ta, sannan ki na tunanin zaki aure shi ki samu farin ciki. Hmm Mashkura kiji tsoran Allah. Kin fa'da harkan bin malamam 'yan tsubbu duk akan raba aminiyar ki da mijin ta. Ki na tunanin 'hakkin ta zai barki? Wallahi ki tuba tun ka min lokaci ya 'kure miki".
"Mama duk abunda na yi, wallahi 'kaunar Naseer ce ta jawo haka. Ki na gani duk wani abu da na ke so, Mufeeda ke samun shi. Ai ni ma na sota tsakani da Allah. Amma tun muna 'kanana ta ke 'kwace abunda ya kamata ya zama nawa. Kyawu, kwarjini, farin zini, 'kawaye na, samarin da na ke so, komai da na ke da burin samu. Sai in barta tai nasara. Sam bazai yu ba".
Naseer da ke bakin 'kofa, ya soma ganin wani duhu² da ba'kin ciki a zuciyar shi. Addu'a ya ke Allah yasa mafarki ya ke yi.
Rufe idanun shi yai tare da bu'dewa. Idanun sun yi jazuur. Handle 'din kofar ya mur'da tare da shiga ciki.
Saurin 'dagowa Mama tai ta kalle shi tare da fa'din,
"Yauwa Naseer, gwara da ka shigo. Ga ta nan ta maka bayanin abunda tai da bakin ta. Domin bazan bari ta cigaba da fa'dawa halaka ba. Ni na wuce". Mama na gama fa'din haka ta fita daga d'akin da sauri ta na hawaye.
Jikin Naseer na wani irin rawa ya du'ka a gaban ta tare da fa'din,
"Ki min bayani tun ka min na 'dauke numfashin ki a 'dakin nan. Ke ki ka raba ni da matata abun 'kauna ta? Ke ki ka min message? Ke kika ha'da duk abunda na ga ni a wayar Mufeey?". Naseer ya karisa maganar da wani irin gigicaccan tsawar da amsa 'dakin tare saka hantar cikin Mashkura kartawa tare da yamutsewa.
"Dake nake magana ki ba ni amsa". Naseer ya sake fa'da sai da 'dakin ya amsa.
Mashkura na tsiyayar da hawaye ta kalle shi idanu jazir tare da fa'din,
"Kwarai ni ce. Ni ce na ha'da ko mai, Mufeeda ba ta San komai game da group 'din da ka gani ba a wayar ta. Sannan ni ce wacce ke zubar mata da ciki duk lokacin da ta samu. Domin boka ya ce min asiri bazai ta'ba tasiri a kan ka ba har sai kana cikin 'kololuwar rashin hankali da 'bacin rai. Da wannan group 'din nai amfani wajan kai ka 'kololuwar ba'cin rai har na samu boka ya cusa maka tsana da rashin tausayin Mufeeda a zuciyar ka har ka ke dukan ta tare da wula'kantata. Kuma ba komai ya jawo hakan ba, sai tsananin kaunar ka da na k............".
Naseer bai bari ta 'karishe maganar ba ya 'dauke ta da gigicaccan maruka hagu da dama.
Wani irin ba'kin ciki da danasani da haushin kan shi ya kamashi lukaci guda sakamakon tariyo irin azaba da wula'kancin da yai ta wa Mufeeda ba tare da ta aika ta komai ba.
Kuka ya ke yi sosai tare da buga kan shi da bango. Kan shi ya fashe ya na tsiyayar da jini amma bai bar buga kan shi da bango ba ya na tur da halin shi saboda tariyo azabar da ya ganawa Mufeedan da tsohon cikin shi a jikin ta.
Mashkura ba 'karamin tsorata tai ba da ta ga yadda yake buga kan shi a bango jini na zuba a kan nashi.
Saboda da'ki'kiya ce sai ta nufu kan shi tare da ru'ko hannun shi.
Wani irin zabura yai tare da ri'ke hannun ya buga da bango ka na ya ta'diyo ta ta fa'da ya taka hannun ji kake 'kasss.
Wani irin 'karan azaba ta saka tare da kurma ihuuu ta na fa'din,
"Wayyooooo Alllaaahh na shiga uku hannu na".
Naseer bai bar ta haka ba, ya dunga buga mata Kai da tiles ya na kuka ita ma tana gurnanin azaba domin kukan ma ya'ki zuwa mata.
Naseer dukan ta ya shiga yi tare da kwallo da ita kan ta na buguwa da kujerun 'dakin. Ha'koran ta na gaba huda hu'du suka zube saboda azabar duka.
Sakin ta yai ana kasa ko motsi ba ta iya wa, ga hannun ta da ya kumbura yai suntum. Fuskan ta ma ya canza kamanni saboda azabar naushi da yake auna mata a fuska.
Kitchen ya nufa da gudu ya dauko wuka ya nufo inda ta ke da ko bu'de idanu ba ta iya yi.
Da wu'ka ya dunga yanke gashin kan ta, wu'kan ya yar 'kasa tare da saka hannun shi ya dunga fizgan gashin kan ta.
Wani irin nishi ta shiga yi, can sai ga aman wahala. Aikuwa ya danna bakin ta akan aman nan ya dunga gogawa. Sai da yaga numfashin ta kamar zai 'dauke sannan ya 'daga ta tare da tu'beta tasss tare da 'dauko bulalar *AUX* ya shiga zumbu'da mata a ko ina a fatar jikin ta.
Sai da ya gaji dan kan shi, kana ya koma kitchen 'din ya 'debo ruwa a baho ya kawo parlour. Kan ta ya 'dago tare da dannawa a cikin bahon, sai ta da'de sannan ya cire tare da 'kara dannawa a ciki. Sai da yaga jikin ta ya saki, kana ya yashar da ita a nan parlour tare da rushewa da kukan 'bakin cikin rabuwa da Mufeeda.
*MATAR SAYYADEE*
سم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*WANNAN PAGE 'DIN TUKUICI NE A GARE KU SABODA JAJIRCEWA WAJAN YIN COMMENT*
*DARMA*
*HALEEMATOU*
*FARIDA HARUNA*
*FATIMA UNAR*
Da sauran da ban kira sunan ku ba. Allah ya maku albarka.
Ina muku son so irin sosai 'din nan
*_PAGE 46_*
Sosai Naseer ke kuka, ji yake kamar ya tashi ya sha'ke Mashkura ta mutu ya huta da ba'kin cikin da ta 'kunsa masa. Kallon ta yai tare da fa'din,
"Wallahi sai na 'dan'dana miki ninkin² azabar da ki ka sa naiwa yarinyar da nake 'kauna fiye da yadda na ke son kai na. Bazan sake ki ba, sai na tabbatar kin zama abun kwatance ga mutane azzalumai masu irin halin ki. Sai na miki azaba mafi muni a rayuwar ki yadda ko sunan namiji idan aka kira sai gaban ki ya fa'din".
Inaah ita Mashkura ma a sume ta ke, ba ta jin mai ya ke fa'di. Ga hannun ta da ya kumbura yai suntum. Jikin nan na ta ko ina shatin bulala ne.
Ruwan bahon da ya 'debo ya 'daga tare da she'ka mata. Aikuwa a gigice ta farfa'do ta na fa'din,
"Na tuba, wallahi ban 'karawa. Na dai na sonka wallahi. Dan Allah ka yi ha'kuri".
Wani gigitaccan tsawa ya daka mata tare da fa'din,
"Ta shi ki tsaftace min parlour ko in kusa karshe ki. Sanadiyar ki na rasa abubuwa masu mahimmanci a rayuwa ta. Na rasa mama ta abun 'kauna ta, na rasa aiki na, na rasa tausayi da soyayyar mahaifa na. Allah ya isa tsakani na da ke. Shegiya tsinanniya. Wallahi sai kin 'dan'dana ku'dar ki. Mi'ke ki rufe wannan tsinannar jikin na ki da mazan titi duk suka gama ga ni ki kuma tsaftace min parlour na".
Mashkura kamar za ta mutu, don ko kukan ma yanzu ba ta iya wa sai ajiyar zuciya akai². Da kyar ta iya 'daukar zanin ta da hannu 'daya ta 'dan yafa a jikin ta. Ka na tai kitchen 'din ta 'dauko mopa da hannun da ke da lafiya ta soma goge ruwan da kyar.
"Ki saka hannu biyu ki goge 'dakin nan da kyau". Naseer ya fa'da da 'karfin.
Bakin ta na kakkarwa ta ce,
"Wallahi bazan iya saka hannu biyu ba, wannan hannun ko 'daga shi bazan iya ba wallahi. Ciwo ya ke min sosai".
Wani irin mi'kewa yai tare da mur'da hannun da ke ciwon. Aikuwa ta saki gigitaccan 'kara tare da sakin zawon azaba. Caaan kuma ta tafi luuuuu ta sake sumewa a wajan.
"Wallahi Hajjo ba 'karamin tujara zan miki ba, idan muka isa Kaduna na ji sa'banin abunda kuka hi'di min ke da sauran 'yan uwan ki. Yo in ban da iskanci, ku rabo 'diya da mijin ta, saboda tsabar shashanci da rashin hankali irin na ku na mazan shanu, yaushe aka ta'ba irin haka".
Shuru dai wacce aka kira da Hajjo ta yi, SAI zufa ta ke yi domin tasan su na isa Kaduna kashin ta ya bushe. Sau'kin ta 'daya ma da aka tabbatar mata da shi Ahmadu 'dan boka an da'de da rataye shi sakamakon shimnafin(Kidnapping) d'in da yake yi.
'Karfe biyu suka iso Kaduna. A unguwan kanawa aka sauke su, haka kawai Fatima ta tsinci kan ta a matsanaicin farin ciki. rabon ta da Kaduna yau shekaru goma sha biyar. Gaba 'daya SAI ta ga garin ya canza mata. Shatar keke napep su kai har badarawa can ainahin gidan iyayan Fatima.
Kowa na gidan da ya gan su, sai ruwan jikin shi ya tsaya, musamman ma da sukaga da mallam aka zo. Sun tabbatar yau asirin su ya toni.
Ko saurarar abinci mallam bai yi ba, ya ce shi abun da ya kawo shi Kaduna, so ya ke yaji dalilin barowar Fatima nan garin. Shin dagaske ne sanadiyar mutuwar mijin ta ne da hakan ya jawo mata ta'bin hankali? Ko kuwa son zuciyoyin su ne ya sa su ka karshe mata aure.
Ai kuwa duk su kai tsuru, don hatta mazan gidan da ha'din bakin su a kai komai, idan ka cire 'kanwar Fatima. Ita ce ma a wajan tai 'karfin halin zayyanewa malam 'din komai tun daga rigimar aurar da cire Fatiman da akai cikin dangi har izuwa ranar da su ka 'kulla makirci akan Fatima ta fara ha'da zuri'a da dangin boka ya ka mata ai tufkar hanci. Shine su kai 'kulla² akan su 'dauke Fatiman su mai da ta can kauye bayan sun shaida maku mijin ta ya mutu. Idan ya su said ta sake wani auran a can. Shikuma Ahmadu aka turo aka fa'da masa ai su Fatima sun yi hatsari babu Wanda yai rai cikin motar.
Salati da sallallami Malam ya shiga maimaitawa tare da fa'din,
"Tur da hali irin na ku, yanzu da badun Allah ya tsare ba, da so ku kai Fatsima tai aure bi sa kan aure? Ku yanzu abunda ku kai kun kyauta? Kun rabo mace da mijin ta tsayin shekaru coma sha biyar. To wallahi ubangiji ba zai ta'ba barin ku ba akan abunda ku ka aikata".
Hajjo ta bu'de baki tare da fa'din,
"Malam ai shi Ahmadu ya da'de da mutuwa domin an kamashi da sana'ar garkuwa da mutane shine aka yanke masa hukuncin kisa".
"Za ki min shuru da wannan 'dumin na ki ko sai na miki duka nan wajan? Ai ni ban 'kara yadda da zancan ku, ni da kai na zan 'dau Fatsima har gidan Ahmadu in ji komai da kunne na".
Tsit akai a wajan, kowa na zufa tare da zazzaro idanuwa. Don sun san yanzu kashin su ya bushes. Har abada Malam ya bar amin ta da maganar su kuma.
"Ta shi Fatsima muje can gidan mijin na ki". Malam ya fa'da tare da mi'kewa.
"Malam ai da kun 'dan tsaya kun huta kun ci abinci".
"Baza'a ci abinci na ku ba. Kuma ku sani, idan na sasanta komai, bazan dawo wannan gidan makaryata ba. 'Kauyan mu na yi. Kuma ka da na sake na 'kara ganin 'kafar 'daya daga cikin ku a 'kauye da sunan ya zo waje na". Malam na gama fa'din haka ya mi'ke. Fatsima ma ta mi'ke ta bi bayan shi.
Ko da su ka isa can gidan Malam Ahmadu, ma'kota kowa cike ya ke da mamaki tare da al'ajabin ganin wannan ikon Allah. Malam ne ya masu baya ni ko mai tare da tambayan su shin mai gidan na ta dagske ne ya mutu.
Wannan bawan Allah da yai wa mal Ahmadu al'kawarin zai ta ya shi nai man Mufeeda da dukiyar shi da kuma 'karfin shi, shi ya zayyanewa mallam da Fatima ko mai har da rayuwar da Mufeeda tai a gidan da kuma irin korar karen da KALLAH yai ma ta da tsohon ciki jikin ta.
Sosai Fatima ke kuka mal na bata baki tare da wannan bawan Allah. Malam ya ce,
"To yanzu bawan Allah dan Allah ina zamu samu shi mal Ahmadun?".
"Wannan mai sau'ki ne, domin ya na wajan wani bawan Allah mutumin arziki, domin shi ya fiddo shi daga prison 'din, kuma shi sanannan mutum ne. A nan Kusa ma ya ke. Muje na kai Ku".
Sosai Malam yai masa godiya tare da saka masa albarka. Tsallaka titi su kai su ka hau adaidaita ya kai su SMC.
Bawan Allahn nan mai suna Tasu'u ya kwankwasa gate 'din. Mai gadi ya le'ko tare da tambayan su wa suke nai ma. Tasu'u ya ce masa mai gidan su me son gani. Mao gadi ya ce ya na zuwa bara ai sallama da shi.
Minti biyar sai ga mai gadi tare da Daddy. Ya na ganin su, duk da nai shaida su, ya kar'be su cikin mutunci tare da basu izinin shigowa. Parlour ba'ki ya kai su. Ka na ya koma ciki tare da aiko twins su ka kai masu ruwa da abinci.
Bayan sun ci abinci sun sha ruwa, ka na Malam ya korawa daddy bayanin da ya je tafe da shi. Sosai daddy ya ke al'ajabi tare da tsantsan farin ciki. Aikuwa ya ce masa su jira sa ya na zuwa.
Kai tsaye daddy ya nufi boys quarter wajan mal Ahmadu. Sallama yai ka na ya shiga farin cikin shi ya kasa 'biyuwa.
Mal Ahmadu da ke kwance ya fa'da kogin tunani 'diyar shi Mufeeda da kuma matar shi. Wai da daddy ya ta'bashi ka na ya firgigit tare da zama.
Daddy ya kamo hannun shi ya ri'ke tare da fa'din,
"Mal Ahmadu kai ma yau za kai farin cikin da ma da'de ba ka yi shi ba. Biyo ni muje parlour ba'ki".
Ba tare da musu ba mal Ahmadu ya bishi. Haka kawai ya sa mu kan shi da fa'duwar gaba, tare da jin jikin shi yana masa wani zum² kamar Mayan 'karfe ya ga 'karfe.
Daddy ne ya fara shiga parlour ka na mal Ahmadu. Babu in da idanuwan shi suka hara dauka sai akan Matar shi Fatima. Wani irin waro idanu yai tare da fa'din,
"Fatima! Ke ce ko idanuwa ne me min gizo kamar yadda na ke gani a 'yan kwanakin nan?".
Tsaye Fatima ta mi'ke ta na mai jin wani irin farin ciki mara misaltuwa, hawayan da'di na kwaranyo mata ta ce,
"Baban Mufeeda ni ce, ban mutu ba, ina nan da rai na".
Zubewa mal Ahmadu yai tare da yi wa Allah sujada. Ka na ya 'dago tare da fashewa da kuka. Ba bu Wanda ya hana shi sai da yai mai Isar sa. Ka na Malam ya shiga ba shi ha'kuri bi sa abunda 'yan uwan Fatsima su ka yi. Sannan ya ce mass,
"Ga matar ka nan na dawo maka da ita. Wallahi ban san komai game da abunda suka 'kulla ba, da babu yadda za'ai hakan ta faru".
Girman Malam 'din ya ga