Showing 21001 words to 24000 words out of 115393 words

Chapter 8 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22936

bi ye da ita a baya.
Turus, ta tsaya sabida ganin shi da tai ya na sallah.
"Ka idar ina nan ina jiran ka".
Baby dake gyefe sai zare idanu ta ke yi ta na 'karewa 'dakin kallo, don shigowar ta na farko kenan bedroom 'din sa. Don ko gyara ya saka ta zai kulle bedroom 'din sa, iya ka cin ta parlour.


Sai da ya idar da sallar sa a natse yai addu'a ya shafa, sannan ya juyo ya fuskan ci mahaifiyar shi tare da fa'din,
"Mummy ina wuni? Sai kawai kika ganni na dawo ko? Wani aikin ne ya mai do ni."
Harara ta maka masa, tare da fa'din,
"Dallah rufe min baki! Da ma can ba aiki ka je dubawa ba, da inda munafukar can (haj Zulfah) ta aike ka, kuma an fa'da min tare kake da mata biyu da jarirai biyar, daga gidan uwar wa ka samo su?".

Mai da kallon sa yai izuwa ga Baby tare sa maka mata wata uwar harara ka na ya mai da kallon sa ga mummy ya ce,
"Ohhh Allah mummy! Ki ri'ka kwa'bawa wannan yarinya. Ba ko mai za ta kawo miki, ki kuma hau ki zauna ba".

" zaka amsa min tambaya ko kuwa??" A tsawace ta fa'da hakan.

"Tabbas idan har mummy ta San gaskiyar al'amarin Mufeeda ya San gidan nan ba zai ta'ba mata da'din zama ba, ahakan idan ma ba ta an yadda ta yi ta Kore ta ba ke nan. Ya zama dole na nai mo wata dabaran.". Naseer ya da'di hakan a zuciyar shi. A zahiri kuma sai ya ce,
"Mummy na je Kaduna sai kuma daga nan aka yo kira na akan kawai wata 'yar matsala a can *COMPANY* shi ne na kira daddy don in sanar da shi ya fara zuwa kamin ni na 'karaso, to bayan mun gama magana ne ya ke cemin gashi a gida, Ummah ta ce, don Allah a kai wata 'yar 'kanin mahaifin ta zata zo kano, kuma 'ya'ya biyar ne da ita, kuma daga ita sai mai aikin ta, shi ne ta ce na taimake ta na tawo mata da'ita".
"Saboda ta mai da ka driver ko? Sha-sha-sha kawai. Wallahi Naseer ka fita harkan wancan matar tun kafin na sa'ba mana. Tom".
"To mummy ta ki yi hakuri, 'dan ki mai kadaran million dubu goma, wa ya isa ya mai da sa driver? Ki kwantar da hankalin ki, a hankalce na ke da kowa, wani lokacin sai ka shigewa mutum ka mai da kan ka wawa kake gane takun sa".
Washe baki ta yi tare da fa'din,
" kuma fa hakane, amma duk da hakan dai ka dai na yawan shige mata, kuma wannan kadaran da ka ke da shi, ita take saka ake nani'ke da kai, kuma ake son rabani da kai."
"Babu Wanda ya isa ya raba ni da mahaifiya ta, sanyin idaniya ta". Duk abun da Naseer ya fa'da, ya fa'de shi ne don kauda zargi a wajan mummyn na shi, amma ya 'kudirin niyyar cin uban Jalila (Baby).
"SON ba ka fa'da min zaka dawo ba, da na ha'da maka abinci, amma duk da hakan ma bari na je kitchen 'din na ga ni, sai in samu abu mai sauki in dafa maka"
"Noo mummy ki bar shi ka wai, ba sai kin wahalar min da kan ki ba, Fifa ma zan yi yanzu, kuma ba lallai in dawo da wuri ba, idan na fita zan je restaurant na ci". Fa'din Naseer.
Mummy ta ce,
" To shi ke nan, amma ka tabbata ka ci fa, don ban so ka na zama da yunwa".
"To mumcy na, ki na ji da autares 'din ki".
Shafa kan shi ta yi tare da fa'din,
"Maza ka tashi kai haramar fita, ka da kai dare a waje".
Da "to" ya amsa ma ta tare da mi'kewa. Ita kuma ta fice, Baby tai saurin bin ta a baya, don ka da ta samu tsarabar mari.



*___________________________________*

_WAYE ARCHITECT NASEER?_

Alhaji Mudassir Abubakar shi ne mahaifin shi, su haifaffun *KANO* ne. Alh Mudassir su biyar ne a wajan mahaifiyar su _Inna Huwailah_ ( *Tsohuwa da ba ta 'daukar raini*) Mariya ita ce babba, ta na aure a Jigawa, 'ya'ya biyu kawai ta haifa a duniya, Jabir da Maimunatu. Jabir ke auran 'yar gidan Mudassir (Nazeera) auran zumunci aka musu, amma su suka dai dai ta kan su, ba dole aka musu ba. Daga Mariya sai Abdul shakur, shi ma dai 'ya'yan sa biyu, Mu'azzam da Muzakkir. Sai Mudassir wanda shine na uku, kuma shi ka'dai ke da mata biyu a cikin su duk ya fisu zuri'a domin 'ya'yan shi bakwai, 'Dan shi na fari Abubakar, takwara ya wa mahaifin su, sai Jawad, Abdulmalik, Saudart, Nazeera, Lukman sai auta Naseer, Wanda data shi haj Jummai ba ta 'kara haihuwa ba. Don ba 'karamar wuya ta ci ba, dalilin cikin shi ta kamu da hawan jini, Wanda har yau bai bar ta ba. Daga Mudassir sai Shafa'atu, ita ma tai aure da 'ya'yan ta uku. Abida, Hauwah, da Suhail sai autan su Aliyuu, yai aure tsawon shekara ashirin, 'ya daya kawai ya haifa, ita ma ta na kuka Allah ya 'dauki ran ta, tun daga wannan lokacin ba ta kuma haihuwa ba. Ya na tsananin 'kaunar matarshi, amma haka nan Inna Huwaila ta sa ya mata saki 'daya. Shi kuma tun daga wannan lokacin bai 'kara aure ba, yanzu haka ma ya na 'kasar *GERMANY* shi likita ne, a can dama ya ha'da degrees na daya da ba biyu. Da ma sun yi sunyi ya zauna can ya masu aiki, shikuma ya ce 'kasar shi zai wa aiki. To da wannan abun ya faru, said ya tattara ya koma, dama kuma mai man sa suke yi.
Mahaifin su ya da'de da rasuwa, tun inna Huwailah na da saurin 'kuruciyar ta, dama kuma mace kyakkyawar gaske, sai dai ba'ka ce. Idan ka gan ta sak architect, sai dai tsufa da ya ka ma ta yanzu. hakan ne ma ya sa bayan ta gama takaba, maza suka dinga mata tururuwa, a wannan lokacin ne sam ita kuma ta ce ta gama aure. Sai da mahaifin ta yai kamar zai ha'diye ta da fa'da, shine ta bawa wani tsohon saurayin ta dama, matar shi 'daya da 'ya'ya takwas. 'Ya'ya biyu suka haifa da shi, kuma duk maza Muhammad Aasim da Sha'aban.
Kawunan 'ya'yan kaf a ha'de ya ke dukkan su, sannan duk abun da ta tsara babu Wanda ya isa ya tsallake shi, bata 'daukar raini ko ka'dan, ta na kuma matu'kar 'kaunar jikokin ta, musammam *Naseer*.


Alh Mudassir sun ha'du da haj Jummai wacce asalin sunan ta *Asma'u*, ranar jumma'a aka haife ta, wannan shi ne ya sa ake kiran ta da Jummai, gidan su talakawa ba ne, sannan kuma ba masu mugun ku'din nan ba ne, tsaka-tsakiya ne su, makarnata 'daya su kai yi da alhj Mudassir, ya na 300lv ita kuma ta 100lv, farko tafiyar nasu daga koya mata karatu ya soma, daga baya kuma ya juye zazzafar soyayya. Wannan lokacin saura mashi shekara daya ya kammala, kuma ko mai sun tsara, akan lokacin da zai kammala ita kuma ta na 200lv, ya ga gama bautar 'kasarci, zai fa'da harkan kasuwanci, Wanda ya tashi yaga mahaifin shi a ciki, don abunda ya karanta ma ke nan. Bayan ya fara kasuwanci sai su yi auran su, idan yaso ta cigaba da karatun ta a gidan shi.
Hakan 'din ce kuwa ta faru, sai dai fa ansha daga da Inna Huwailah, domin da kyar aka shawo kan ta ta amince, don cewa tai an mata bincike akan Asma'u (haj Jummai) kuma an tabbatar mata yarinya ce mai 'dagawa da kuma tsiwa, kuma ba ta da mutunci saam. Shikuwa alhj Mudassir Allah ya 'daura masa 'kauna ta, haka yai ta wa 'yan uwan shi magiya akan su taimaka su shawo mashi kan Innar ta su don ta amince. To a 'karshe dai ta amince da kyar, an yi aure, amaryar ta tare, wata daya ta koma makaranta.
Farkon matsalar da suka fara samu shi da haj Jummai a kan ciki ne, domin kuwa ba ta rufa wata uku ba ta samu ciki, aikuwa tai tsalle ta dire akan ita lallai baza ta haihu yanzu ba, sai ta gama makaranta. Alhj Mudassir yai lallashin, yai lallashin amma Sam ta shafawa idanun ta toka, ita a tafau sai ta zubda shi. Ta kai ta kawo har alhj Mudassir yai fushi ya bar mata gidan ya koma kwana a gidan gona.
Labari ya kai kunnan Inna Huwaila, aikuwa takanas tun daga Jigawa ta wanko 'kafafun ta ta zo Kano ta wanke haj Jummai tass, kuma tawo kiran alhj Mudassir ta ce masa ya dawo gida yanzu yanzu ga ta tazo. Gaban sa sai da ya fa'di, don ya san Inna ta riga ta ji komai, aikuwa ya na zuwa ta hau shi da mafisa, kuma ta ce masa, idan har Asma'u (haj Jummai) ta 'kara cewa zata zubda ciki wallahi wata biyu ta bashi ya fiddo mata ya 'kara aure idan ba haka ba kuma sai ta masa baki, kuma dole ya saki Asma'u (haj Jummai).
Aikuwa wannan maganar ta shigi haj Jummai, don a rayuwar ta idan akwai wacce ta tsana a rayuwar ta fi ye da mutuwar ta to kishiya ce. Wannan magana da Inna ta yi shi ya sa haj Jummai ta sadudu, har ta haifi Abubakar Wanda suke kira da (Abba) sai shekarar Abba daya ta kuma samun ciki. Ba 'karamin gigicewa ta yi ba, musamman da ta samu wata 'kawa mai sunan Khausar ta na 'daura ta a gur'batacciyar hanya. Ita tai ta zuga ta akan wai ta 'dau mataki akan haihuwa idan ba haka ba, lalacewa za ta yi, kuma Mudassir 'kara sure zai yi ba ruwan shi. Ba 'karamin ru'dewa ta yi ba da jin wannan maganar, ta nufi asibiti ba tare da sanin Mudassir ba, tai tsarin haihuwa har na shekara bakwai. Allah kuma da ya tashi kama ta, shekarar Abba daya ta kuma samun wani cikin.
Wannan karan ma ba 'karamin rikici a kai ba, sai da ya rantse mata idan ta 'kara maganar, goben nan za taji gu'da a cikin gida. Wannan shine rana zafi inuwa 'kuna.
Wannan karan ba 'karamin dauriya tai ba wajan barin ciki. Aikuwa Inna Huwailah na samun labari ta zo ta 'dauke Abba, tun daga nan ya koma 'dan wajan ta.
Arzikin alhj Mudassir sai da'da ha'b'baka ya ke yi, domin kaya har saga China, India, etc ake kawo masa, ka kiwo da ya ke yi, su dokuna, Kifi, zabbi, kazi, akuyoyi, shanaye, kai har da ra'kuma. Duk 'yan uwan sa ya 'daura akan harkan, kasancewar su ma duk business 'din suka karanta.
Allah ya sauki haj Jummai lafiya ta 'kara sumun 'da namiji aka saka masa suna Jawad. Jawad sai da ya shekara uku sannan ta kuma sun haihuwa, kasancewar ta na final year 'din ta ne, sai ba ta wani damu ba, shi ma ta haife sa lafiya an samu Abdulmalik. Daga nan ta samu ciki sau biyu, ta zubda ba tare da sanin alhj Mudassir ba.
Allah ya wa haj Jummai kwayoyi halitta, don haka duk tsarin haihuwar da ta yi, bai yi tasiri a jikin ta. Duk da zubda cikin da take yi dai bayan Abdulmalik sai da ta haifi Saudart da Nazeera, akan Nazeera ne ma, haihuwar ta zo da 'dan gardama, kuma sai akai sa'a Inna Huwailah ta zo daga Jigawa, tare da ita a kaje asibiti. Bayan wahalar da ta sha, ta haifi Nazeeran, kuma doctor ya shaidawa alhj Mudassir matar shi na shan kwayoyi kuma ta na zubda ciki, kuma wannan magana da Dr ya yi a gaban Inna Huwailah a ka yi, aikuwa ba 'karamin 'dagawa kowa hankali ta yi ba, kuma ta ce wallahi ta bawa alhj Mudassir wata 2 ya sake aure, idan ba haka ba, ya biya ta nonon ta da ya sha.
Aikuwa maganar ya 'daga masa hankali. Ita kuwa haj Jummai, suma tai ta yi.
Ran alhj Mudassir bai ta'ba 'baci da haj Jummai ba sai yau da yaji abunda ta ke yi ba tare da ya sa ni ba, kuma ya 'dau wa kan shi al'kawari sai ya cika mahaifiyar sa burin ta, sai ya 'kara aure ko dan ya 'kuntatawa haj Jummai kamar yadda ita ma ta bata ransa da na mahaifiyar sa. Don ita so tai ma a sake ta, sai kuma tai wani tunani ta ce ka wai a mata kishiyar.
Aikuwa wata biyu bai cika ba ya auro wata 'yar gidan mutunci mai suna *ZULFAH*.
Aikuwa haj Jummai kusan haukacewa ta kusa yi, gashi abun ya ha'de mata biyu, ga ta shin hankalin kishiya, ga kuma na juya mata baya da mijin ta ya yi.
Zulfah irin matan nan ne wa'yan da suka iya kula da tarairayan miji, da wannan da barun na ta, ta samu babbar fa'da a cikin zuciyar alhj Mudassir. Domin ba 'karamin natsuwa ya ke samu tattare da ita ba.

Kullum cikin nai man tashin hankali haj Jummai ta ke da haj Zulfah, amma Sam haj Zulfah ta 'ki kula ta, domin ta iya takun ta, kuma ba ta ta'ba kai 'karanta ta wajan mijin su ba, ita kuwa haj Jummai kullum ciki 'korafi ta ke.
Wannan ne ya 'kara sa tauraron haj Jummai ya 'dan rage haske a zuciyar alhj Mudassir.

Har Nazeera ta shiga shekara biyu, ko 'bari haj Zulfah ba ta ta'ba yi ba. Wannan shi ya 'kara sanyaya zuciyar haj Jummai har ta ke jin idan duniya ne ma yanzu a shirye take ta haifa.
Wani cikin ta 'kara samu, ya yin da haj Zulfah har yanzu shuru, sunje asibiti kuma an tabbatar da lafiyar ta 'kalau, ka wai lokaci ne bai yi ba.
Wannan ciki da haj Jummai ta samu ya zo mata da matsala, domin laulayi ta sha mai uban wahala, ga hawan jini, duk ta kumbura. Haj Zulfah ke kula da ita tsakani da Allah kuma. Hakan kuma ya da'da 'kara 'Kimar ta a idanun alhj Mudassir. Ita kuwa uwar gayyar ko a ha'ban zanin ta, don wani zafin haj Zulfah ma ta ke yi, ganin ta ke duk sani bariki ne.
Ta sauka, ta samu 'da na namiji, Wanda da kyar ta haye, ba Wanda ma bai yi tunanin lokaci ka wai take kira ba. Kulawar Naseer gaba daya ya dawo wajan haj Zulfah. Wannan shine sanadiyar 'kauna da ta shiga tsakanin haj Zulfah da Naseer.
Bayan haj Jummai ta warware, sai Sam Naseer ya 'ki zuwa wajan mahaifiyar ta sa, Wanda hakan ta ta da hankalin ta, har ta ke tunanin haj Zulfah ta asirce mata miji da kuma 'ya'yan ta. Musamman Saudart da Naseer. Ba 'karamin rikici a kai ba, Wanda ya fusata alhj Mudassir har ya kwashe kayan Naseer kaf ya kai wa haj Zulfah tare fa'din ya ba ta shi halak malak. Da ma ba nono yake sha ba. Wannan ne ya 'kara hassasa wutar 'kiyayya da tsanar haj Zulfah a zuciyar. Tun daga wannan lokacin kuma haihuwa ya tsayawa haj Jummai.

Lokacin da Naseer ya cika shekara 10 ne 'kanwar haj Jummai ta rasu bayan ta haifi 'yar ta mace, kyakkyawa da ita. Haj Jummai ba 'karamin ru'dewa ta yi ba, don suman ta uku, bata ma san lokacin da aka kai ta gidan ta na gaskiya ba.


_Bayan kwana bakwai_
Bayan kwana bakwai da rasuwar kanwar ta ta, haj Jummai ta matsa akan sai an bata Jalila (Sunan mahaifiyar ta aka mayar mata) shi ya sa take kiran ta Baby. Sai da alhj Mudassir ya saka ba ki sannan aka bai wa haj Jummai Baby (Jalila).
Baby ta taso wajan haj Jummai a sangarce, domin ba ta kwa'ba mata, sannan ba ta koya mata aiki irin wacce ko wace mace ya kama ta ta koya. Ga gulma a wajan baby tun ta na da shekara biyar. Sannan ta tura mata 'kiyayyar haj Zulfah a cikin zuciyar. A ta'kaice dai Baby gumtsi fesa ce. Don hatta ita kan ta mummy, baby ba ta kyale ba, don duk lokacin da suka kye'be da alhj Mudassir sai ta musu la'be. Ga wata muguwar 'dabi'a da ta koya a wajan 'kawayan ta, ( *_Shaye-shaye_*).
Da ya ke Naseer dodan ta, ba a kasar ya yi UNI 'din shi ba, shi ya sa take cin karan ta ba babbaka, dama shi ke taka mata birki.
A kasar Spain ya yi karatun sa a fannin architecture, anan suka ha'du da aminin shi Dr Haroon, sai dai shi Medicine ya ke karanta. Sosai suka sha'ku da Dr, Wanda da da farko da rigima suka soma.
Bayan kammala degree 'din sa ne, ya dawo gida ya tamfatsa companyn sa da taimakon mahaifin sa, shi da kan sa ya zana companyn, sannan ya 'dauki ma'aika ta a ka hau aiki. Kuma alhamdulillah company ya na cigaba, don mutane kusan arba'in suna da shares a companyn.
Tun da Baby ta kyallara idanun ta ta ga 'dan uwan na ta, ta ji duk duniya baza ta ta'ba aure ba idan ba wan ta zata aura ba, kuma mummy ta goya mata baya a kan haka. Domin ita ma haka ne burin ta, don ta na tsananin 'kaunar 'yar 'kanwar ta ta.

*WANNAN SHI NE LABARIN ASALIN NASEER*


*_CIGABAN LABARI_*




_SAI KUN BI NI A SANNU, DON NA SAN DA YAWAN CIN KU, A NA ZIRYA A HANYAR KE WAYE, SABIDA YADDA AKA YI WA NAMAN YANKAN 'KAUNA_

🤪🤪🤪🤐🤐🤐


*MAMAN UMMEE CE*✍🏼

*بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login