Showing 36001 words to 39000 words out of 115393 words
ta kamo tare da fa'din,
"Ai kai fushi na ke yi da kai, ace ko kiran wayar nan ma ba ka yi wa mutane. Hatta daddyn ka ma 'korafi ya ke yi ba ka kiran sa ka gaida shi. Kuma idan 'da na nai man albarka ai dole ya kira iyayan sa".
"Auuuuuch! Wayyo kunne na, Ummah za ta tsinka min kunne. Na tuba ban kuma wa, zan ri'ka kiran ku a kai a kai". Fa'din Lukman.
"Ai Zulfah tsinke kunnan kawai. Idan dai Lukman ne ba canza zai ba. Always busy. Bai kira, idan kuma aka kira shi, sai ya ga dama zai 'daga. Kullum da excuses 'din da ya ke kawowa". Fa'din alhj Mudassir tare da 'karasowa parlour 'din ya zauna a kusa da Naseer.
Gaba 'daya suka zamo tare da gaida mahaifin na su har da Naina cike da jin da'din ganin shi.
Shima alhj Mudassir cike da farin ciki ya amsa musu tare da tambaya su yadda suka baro mahaifin na su (Dr Aliyu(small daddy)). Su ka amsa mishi ya na nan lafiya. Nan ma suka kira shi video call suka sha hira sosai. A nan ne ma architect Naseer ya ji wani 'bangare daka cikin damuwan shi ya ragu.
"Bari mu shiga wajan Mummy, don zuwan kenan muka yo nan". Fa'din Naseer.
"Ahhh to muje dinning kuci abinci tukun mana". Fa'din haj Zulfah.
"Ummah ba ri dai mu fara zuwa mu gaida da mom sai mu dawo, bata san ma mun iso ba". Fa'din Lukman.
Haj Zulfah ta ce,
"To shikenan, ku shiga idan kun kimtsa, sai ku zo kuci abincin. Ko kuma na aiko muku da shi part 'din yayan".
Gaba daya suka mi'ke suka fice daga 'dakin sukai part 'din mahaifiyar su.
Da guda baby dake charting tai wurgi da wayar ta ta nufe su. Rungume Lukman tai, sannan ta sake ki ta nufa Jawad. Ai ka min ma ta isa Naina tai saurin taran ta tare da rungume ta saboda bata so ta ha'da jikin ta da na mijin ta. Duk da Nainan ba ta ta'ba zuwa Nigeria ba, amma sun san juna da Baby saboda suna yawan yin video call. Baby ba ta kawo komai a ran ta ba. Ta 'kara ma'kal'kale Nainan 'din. Shikuma Jawad da ya san halin matar tashi. Gaba ya yi ya je ya zauna a kujera.
Harara Naseer ya watsawa Baby ta re da fa'din ke ba ki iya gaisuwa ba sai rungume rungume da iface iface ko?".
"Ni wallahi mamakin girman ta ma na ke yi". Fa'din Lukman.
"Kasan girman mace ba wuya ne da shi bai". Fa'din Naseer.
Dai dai lokacin haj Jummai ke saukowa daga step fuskan nan na ta kamar gonar auduga.
Mi'kewa Naina ta yi ta nufe ta tare da rungume. Ita ma mummyn rumgume ta ta yi tare da fa'din,
"Welcome my daughter".
Hannun Ahmad ta ru'ko ta na shafa fuskar shi. Sam bai jin Hausa. Don iyayan nashi ba yo mashi suke ba. Da turanci ta gaida shi. Kasancewar ba'a uwar tashi ba ta koya mashi gaida mutane ba. Kuma babu kunya Ahmad ya amsa gaisuwan da haj Jummai ta masa. Haj Jummai na matu'kar 'kaunar 'ya'yan ta, kamar ba ita ce wacce aka dunga daga da ita ba akan haihuwar.
Sosai fira ya 'barke tsakanin uwa da 'ya'yan ta. Kan ka ce kwabo sai ga Nazeera, Saudhart, babban wan su Abubakar (Inna Huwailah ce ta raine shi, a can Jigawa yai makarantar shi yai aure har da 'ya'ya uku duka maza) Abdulmalik ma ya zo, shima dai ya yi aure da 'ya 'daya Husna takwara yai wa mahaifiyar shi. Shi a nan cikin kano ya ke aiki (banker ne). Gaba 'daya 'ya'yan haj Jummai sun ha'du sai hiran zumunci a ke yi. Ko ina haj Jummai ta waiga jikoki ne da 'ya'ya. Haj Zulfah ma da daddy nan suka zo a kai ta hirar da su. Sai dai cikin magana haj Jummai ta ke watsowa haj Zulfah habaicin ita fa ita ce da gida saboda ita ce da 'ya'ya. Ita kuwa baiwar Allah Zulfah yi take ma kamar bata fahimci in da maganar ta ta ta dosa ba.
*BAYAN KWANA UKU*
Matan ne kawai suka koma gidan mazajan su, ita kuwa Nazeera da ya ke 'dan uwan ta JABIR ta ke aure 'dan wajan babbar yayar su daddyn su (Inna Mariya). Kusan kullum ta na gida wajan 'yan uwan ta. Don sauran 'yan uwan ta maza. Gyara part 'din baya su kai kowanne ya tare da matar shi har sai JAWAD da LUKMAN sun koma 'kasar da suke aiki. Saboda su ma kwasar shekaru ba su zo ba.
Jawad dai da Lukman sun zama 'yan 'dakin haj Zulfah, don dai ma shi Jawad Nainan shi ta na saka masa idanu. Don ba 'karamin uwar watsi a kai ba lokacin da su ka ke'be ta ce masa taga soyayyar Mufeeda a cikin idanun shi. Shi kuma ya dage mata saam ba haka ba ne.
Ita kuwa Mufeeda, ta na ganin sun shigo 'dakin ta ke komawa sama. Kuma har yau Allah bai ta'ba sa sun ga 'yan biyar ba. Don duk lokacin da za su shigo, 'yan biyar na sama wajan baaba Habiba ko kuma wajan Daddy. Don yanzu sun 'kara wayau sun yi 'bul 'bul abun su. Matan gaba 'daya kamannin ta suka biyo. Ya yin da mazan kuma suka 'dauko kamamnin Naseer har da wani 'dan 'digo fake gyefan kuma tun sa.
***************
"Baby ina so na tambaye ki". Fa'din Naina da ke zaune kan 1sitter tare da fuskan tar Baby.
Baby iyayan gulma ta ce,
"Ina jin ki aunty. Tambaye ni, ni kuma Idan har na sa ni zan gaya miki taasss wallahi". Fa'din baby tare da barin in da ta ke ta dawo kusa da Naina.
Naina ta ce,
"Akan wancan yarinyar ne da ke zaune a wajan wancan matar. Wacece ita? Ita ma family ce?".
Girgiza kai Baby ta yi da sauri ta re da da'din,
"Allahu ya sawa'ke ta zama familyn mu. Karuwa ce fah."
Zaro idanu Naina ta yi tare da fa'din,
"What? kin san me like cewa kuwa?".
"To bu'de kunne kiji ni da kyau. Wannan yarinya dai da ki ka ga ni karuwq ce, domin har 'ya'ya gare ta guda biyar. A wajan karuwancin ta taje wani ya 'dura mata ciki ta haifi quintuplets".
"What! Quintuplets? Impossible. Wannan 'karamar yarinyar ce ta haifi 'yan biyar? Ai da ta mutu. Ko ni na kusa mutuwa wajan haihuwar Ahmad da ya ke bakwaini bare wannan 'karamar yarinyar".
"Aunty Naina kenan. To wallahi wannan yarinya dai da kika ga ni, ita ta ta haifi 'ya'ya biyar. Ko da ya ke naji ya Nas ya ce CS aka mata".
"Yauwa yanzu naji magana. Kuma duka 'ya'yan su na da rai?". Fa'din Naina.
"Su na nan wallahi. Idan ma ki na so ki ga ni, yanzu ta shi muje 'dakin munafukar matan can, zaki gan su". Fa'din Baby har miyau na zubowa daga bakin ta.
"To ya akai tazo gidan nan?. Naina ta tambaye ta.
"Hmm iyayi irin na yaya Nas mana. Wai shi mai taimako. Wai nan taimakon ta yai ya kawo ta gidan nan, Wai iyayan ta sun 'ki kar'ban ta saboda abun kunyar da ta yi". Fa'din baby ta na ta'be ba ki.
Shuru Naina ta yi, can kuma ta ce,
"Kai can't believe. Ta shi mu je in ga ni da ido na".
*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*PAGE 19*
Fita ta yi ba tare da ta jira cewar Babyn ba, ita kuma Baby da ma abunda ta ke jira ke nan tai saurin bin bayan ta.
Kai tsaye part 'din haj Zulfah ta nufa cikin zuciyar ta ta na mamakin anya dagaske ne duk abun da Babyn ta fa'da mata kuwa.
Ko knocking ba ta yi ba, mur'da handle 'din kawai ta yi ta kutsa.
Sai da gaban Mufeeda da ke shayar da Abid ya fa'di, don ita duk a zaton ta ya Lukman ne, ko ya Jawad. Don su ne kwanan biyun nan suke kusan wuni a nan, must especially ma ya Lukman.
Aikuwa su Naina da Baby dai sun ta ki sa'a, domin 'yan biyar dai gaba daya suna parlour, Ayaan sarkin ci da Husna su na kwance a 3sitter kuma ba bacci suke ba. Irfana na hannun Baaba Habiba ya yin da Shahida ke hannun haj Zulfah ta na mata rawa. Abid kuma na hannun Mufeeda ta na shayar da shi.
"Unbelievable!" Naina ta fa'da cike da mamaki a fuskan ta. Don ita iya tsayin rayuwar da ta yi baya, ba ta ta'ba ganin ko 'yan hudu ma ba re biyar. Ha na rantsuwa ta ta'ba ganin triplet ('yan uku) wata ma'kociyar ta ce ma a can *GERMANY* ta haife su duka mata.
Abun ka da tagwaye akwai farin jini. Ai tuni har Naina ta 'karisa wajan da aka kwantar da Ayaan da Husna ta na kallon cike da sha'awa. Can kuma ta 'karbi Shahida a hannun haj Zulfah, can kuma ta koma wajan Baaba Habiba ta na 'karewa Irfana kallo.
"Wallahi wa'dannan matan identical triplet ne. Ki gan su faah baby, wallahi ba ki iya banbance su". Naina ne ta fa'di hakan ta na nuna wa Baby Shahida da ke hannun ta.
Ta'be baki Baby ta yi. Haj Zulfah da baaba Habiba kuwa sai bin Naina suke da idanu tare da murmushi. Don sun San ko waye yaga wa'dannan 'ya'ya sai ya ru'de. Ga su farare, kyawawa, 'yan bul bul gwanin sha'awa.
"Unbelievable!" Naina ta sake fa'da. Sai kuma ta mai da kallon ta izuwa ga haj Zulfah ta ce,
"Ummah please to be sincere, wannan 'yar yarinyar ce ta haifi wa'dannan very cute yaran?".
Dariya sosai haj Zulfah ta yi, sannan ta ce,
"Naina 'ya'yan ta ne. Ita ce ta haife su. Ba ki ga ma shayar da su ta ke yi ba".
Still dai Naina mamaki bai bar fuskan ta ba. Can kuma ta kalli Mufeedan ta re da fa'din,
"Imagine! Kuma ba ki mutu ba, ina nufin kuma 'ya'yan duka suna da rai babu wanda 'ya mutu?".
"To gasu nan dai reras ki na kallon su, babu Wanda ya mutu a cikin su. Kuma in sha Allah za su yi tsawon rai mai cike da albarka". Fa'din Baaba Habiba.
Shuru Naina ta yi, can kuma ta ce cikin zuciyar ta,
"Dole Jawad ya ru'de, na farko ya ga kyakkyawar yarinya. Na biyu kuma sabida ya ga ta na haihuwar quintuplets shi ya sa ya kamu da son ta don shima ta haifa masa 'yan biyar 'din ko. To zan ga ta yadda hakan zai faru". Kawai sai ta aje Shahida akan cinyar haj Zulfah tare da kama hannun Baby ta ja ta fuuuuu suka fice daga 'dakin.
Cike da mamaki haj Zulfah da baaba Habiba suka bi ta da idanu.
"Tooooh! Mai hakan ya ke nufi". Fa'din baaba Habiba.
"Hmmm lallai akwai abunda ya ke tun karo gidan nan". Fa'din haj Zulfah a cikin zuciyar ta. Amma a zahiri sai ta ce,
"Ko ma menene, aniyar ta ta bi ta".
Ita kuwa Mufeeda ba ta ma San su na yi ba, tuni hankalin ta ya tafi can wata duniyar. Idan har ba ta manta lissafi ba, yau kwana uku rabon da ta saka *katangar ta* (Ya Naseer) a idanun ta. Duk sai ta ke jin ta wani iri.
"Mufeeda! Mufeeda!! Ke Mufeeda!!!". Firgigit sai ta dawo cikin nutsuwar ta.
"Tunanin mai kike yi hakan? Ba dai wannan abun da yarinyar nan ta yi ba ne har ya jefa ki cikin tunani? To wallahi idan har kika bari aka gano lagwan ki a gidan nan kin shiga uku".
"Wallahi Ummie ni ban ma San mai ta yi ba". Fa'din Mufeeda.
"To tunanin mai kike yi?". Haj Zulfah ta jefe ta da tambaya.
"Ummie yau kusan kwana uku ban ga yaa Nas ba, shi ne na ce ko jikin ne ya ta shi?".
Haj Zulfah kafe ta ta yi da idanu, can kuma ta saki wani murmushi da ita ka'dai ta San ma'anar shi. Sai kuma ta ce,
"Ya na shigowa kullum da safe ya na gaishe ni, duk lokacin da zai shigo ku kuna sama, amma ai suna ha'du ba baaba Habiba".
"Kwarai kuwa, ko jiya ma mun ha'du, har ya ke tambaya na ke da kuma yara". Fa'din Baaba Habiba.
"Ai ya na nan, kije ki dubo sa, sai ki gaida shi". Fa'din haj Zulfah.
Shuru Mufeeda ta yi. Haj Zulfah ta kwantar da Shahida a inda ta mi'ke, ta 'karaso ta kar'bi Ayaan a hannun Mufeeda tare da fa'din,
"Maza ta shi kije ki dubo sa sai ki dawo".
Hakanan wani kunya ya lullu'be ta said ta ji kuma ta ka sa ta shi.
"Ta shi ma na ki je". Haj Zulfah ta 'kara fa'da.
"A'a Ummie ki barshi kawai, ba sai na je ba, idan ya shigo ha'du".
"A'a ba za ai haka ba, ta shi dai ki je ki dubo sa". Fa'di. Haj Zulfah.
"Ummie kin ga tunda nazo gidan nan, ban ta'ba fita daga 'dakin nan ba sai ranar da muka je shopping da ke, ban San part 'din shi ba". Fa'din Mufeeda.
"Wannan kam ai mai sau'ki ne. Yanzu ki na fita daga nan, ki yi hannun dan ki kamar za ki ga wani get na kallon ki, to sai ki hannun hagun ki, part 'din shi ne na farko.
Da "To" ta amsa ma ta tare da mi'kewa. Atampa ce a jikin kalar yellow da ratsin purple. 'Dinkin riga da skirt irin open shoulder 'din nan, kayan ya amshi jikin ta. 'Daurin Aysha buhari ne a kan ta. Wani purple 'din gyele ta 'dauka dake gyefan ta ta yafa tare da rufe kafa'dar ta. Ba 'karamin kyau ta yi ba. Da ma akwai flat shoe a 'kafarta kalar purple, kasancewar dukan su ba sa yawo ba takalmi a 'kafar su sabida sanyin tiles, dan sanyi ta 'kafa yake fara yiwa mace illa, shiyasa ba'a so mace ta na yawo ba takalmi, rage darajar 'ya mace yake yi.
Fita tai daga 'dakin ta nufi in da haj Zulfah ta ma ta kwatance. Tsaye ta ke a bakin kofar da'kin, sai ta kai hannun zata kwankwasa sai kuma ta janye. Can dai tai 'karfin halin kwankwasawa. Shuru daga cika ba amsa. Sai da ta 'kara har sai uku, sannan ta ji alamun ana murza key zata bu'de 'kofar.
Saurin 'dan ja baya ta yi ta na 'kara gyara gyalan ta.
Gaban shi ne yai wani irin bugawa da 'karfi sakamakon arba da ya yi da idanun ta. Saurin ba ta hanya ya yi tare da fa'din,
"Bismillah shigo mana".
Shiga ta yi tare da zama akan center carpet 'din da ke shimfi'de a tsakiyar 'dakin.
"Miye haka kuma? Dan Allah ta shi ki zauna a kan kujera ka da rai na ya 'baci". Naseer ya fa'di hakan.
Ta shi ta yi ta zauna ta re da furta,
"Ina kwana yaa'aya". Sai da ta wani jaa yayan.
"Hasbunallahi wa'ni'imal wakeel! Yarinyar za ta kashe ni wallahi". Naseer ya fa'da a can cikin ma'koshin shi.
"Lafiya 'kalau Mufeey". Da kyar ya iya fizgo maganar.
Shuru ta yi ta na wasa da 'yam yatsun hannun ta. Da'kin ya 'dauki shuru. Shikuma zama ya yi ya na fuskantar ta tare da zuwa mata idanu ya na 'karajin wutar 'kaunar ta na ruruwa a zuciyar shi.
Katse shurin ya yi dda fa'din,
"Mufeey akwai wata damuwa ne?".
Girgiza ma shi kai ta yi tare da fa'din,
"Kwana biyu ne ban gan ka ba, shine na ce bari nazo na duba ka ko jikin ne". Fa'din Mufeeda.
"Ashe kema kin da mu da ni kamar yadda ni ma na ke kwana kuma na ke tashi da ke". Bai San maganar ta su'buto daga bakin shi ba.
Sunkuyar da kai ta yi ta na murmushi tare da fa'din,
"Ya za'ai bazan damu da wanda ya zame ma no garkuwa ba. Ya za'a yi bazan damu da Wanda ya fiddo ni daga cikin wahala ba. Kai ne fa ka taimake ni a lokacin da 'kafa na 'daya ya ke duniya, 'daya kuma a lahira. Ha'ki'ka kai 'din ka na da wani babban matsayi da kuma daraja a waje na. Dole idan ban gan ka ba, hankali na ya ta shi, musaman ma da na San cewa ba ka da lafiya. Na, ka 'dauko ni ka ba ni muhalli, ka ba in mahifiya, ka kula da 'ya'ya tamkar kai ne mahaifin su. Ya zama mini dole na so na duba garkuwa na, ni da 'ya'ya na". Duk maganganun da Mufeeda ta fa'da kan ta na 'kasa ta na tsirarar da hawaye.
Ba 'karamin da'di