Showing 15001 words to 18000 words out of 130717 words

Chapter 6 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

173

itace duniyar mutane nan inda kike duniyar mu ce jinn"husnah tayi shiru bata ganeba bata kumaso ta gane cikin kosawa tace "to muje"suka fito ba kowa yau kasantuwar rana tayi dik suna bacci suka fice tana waige waige tayiwa husnah umarnin ta rufe ido kamar jiya suka lula wata duniyar,


hafeez na zaune akan mota kamar an tabashi ya waiga yayi tozali da husnah yau kayan jikinta sun matukar burgesa sosai har ya kasa dauke idanuwansa daga gareta yau zaiji sunanta zai kumasan wacece a ina suke ya diro daga kan mota ya nufi inda suke tsaye tanata faraa....



daddy ya shirya tsaf momyn husnah ta rakosa ya tsaya tace "lafiya?"yayi murmushi ya gyara hula "hajiya rabi zaki kiramun bamu gaisa ba"momy tace "dama kun saba gaiswwa ne kafin ka fita?"saiga hajiya rabi kamar daga sama taga irin kallon da daddy keyi mata ya tabbatar mata da tarkomta ya kama kurciya....




karer kugiya Abraham yaji dajin yana wani irin sauti da kara wata iska na kad'awa haka kawai yaji zai koma gida jikinsa ya basa akwai matsala ya bude hannuwansa wani abu mai haske kamar hayaki yana fitowa ya haska dakin husnah daga ciki. dajin dayake Bai ganta ba ya haska kan gadonta da tafin hammunsa bai ganta ba ya haske cikin gidan baiganta ba babu ita babu narjisu.....

FREE PAGES NA GAB DA KAREWA A HANZARTA A BIYA 300 DON JIN YADDA TAFIYAR NAN ZATA CIGABA SHIN HUSNA ZATA DAWO DUNIYAR MUTANE?.....YA TURKA TURKA ABRAHAM ZATA KASANCE YA YASEER ZAI TUNO HUSNA MATARSA CE?......

*SLIMZY*✍🏻
🌑 *DUHU....*🌑
( *sark'akiya*)

©️HWA

*SLIMZY*✍🏻
Wattpad slimzy33

Daga Marubuciyar:-
🦎 *K'ADANGARUWA*🦎

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN NAIRA 300 KACAL VIP MASU BUKATAR A TURA MUSU TA PRIVATE 1000 DOMIN MALLAKAR WANAN LITTAFI TURA KUDINKI TA WANAN ACCOUNT DIN*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*3126584401*
*FIDDAUSI MUSA*
*FIRST BANK*

*SHAIDAR BIYAN KUDI TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KI TURA KATIN MTN TA NUMBER*

*GA MASU BUKATAR TALLA SU TUNTUBI WANAN NUMBER 07042277401*


*8*

narjisu ta gefen idanuwanta taga hafeez ya tunkaro su murmushi tayi tasan tabbas zaizo nemansu domin ta lura da irin kallon da yakeyiwa husnah jiya hakan yasa narjisu ta taba husnah daketa kalle kalle husnah ta juyo da sauri tace "naam iyyee menene"ta galla mata harara tace "ki natsu nafada miki saura kuma wanan idan yazo ya mana magana kiyi irin na jiya"husnah tsoro yadan kamata tace "umm narjisu inyi masa magana kikace kinsanfa inada aure kuma Abraham"narjisu tadan mata tsawa tace "saime fada masa zaki aiba cewa zaiyi yana sonkiba ai abota zaayi dashi ko kinga duniyarsu ce in mukai abota dashi zai kara nuna mana wurare"husnah najin zaa sake nuna wurin dayafi nan ta amince dai dai nan ya karaso fuskarsa dauke da murmushi yana kad'a makullin mota yacev"Assalamu alaikum yan mata sannunku dai fulanine ko hausawa"yace cikin sigar zolaya husnah bata gane mai yake nufiba dan batasan wani fulani da hausa ba tace a sanyaye muryarta mai dadin sauraro mai kamada sarewa bata bude baki sosai idan zatayi magana amma ko yaya tayi magana muryarta na dukan zukatan maza balle mata tace "Ameen waalaikumussalam"... hafeez yaji wata murya data daki zucuyarsa saida yayi shock na minti daya husnah saida ta kara kallonsa da fararen idanuwanta ido cikin ido yaji wani abu ya daki zucuyarsa sanan ya tuna da yayi sallama an amsa yacev"tabarakalla.....lallai Allah ya hore miki murya wanan muryar taki ai idan ina sauraronta babu abinda zan iya tabukawa"husnah itadai gabanta na faduwa d'arr d'arrr takeji tayi kasa da murya yadda baxaijiba tacewa narjisu '"inajin tsoro"narjisu ta tsunguleta tace "to aiko bazan sake fita dake ba"ta daga murya cikin sigar shagwaba tace "yi hakuri nadaina zaki rinka fita dani"yau ma hafeez wayarsa ya ciro ya saita camera akan husnah sosai shagwabarta da wawtarta kw burgesa yacewa narjisu "halan ke yayarta ce ko?"narjisu ta daga masa kai yace 'ya sunan naku?"narjisu ta danyi ya'ke tace"sunanta Asmau.....ni kuma sunana"sai tayi shiru ta kasa fadan narjisu dan ta tabbatar a jinsunsu na aljanu kawai ake samun wanan sunan sai kawai ta share,ganin ta share ya jinjina kai abinda yake bukata kenan yasan sunan waccen kyakkyawar yarinyar ya sake jeho musu tambaya yace "muje tacan mudan taka Naga kamar baki ne in nuna muku wurare"ba musu suke tafiya yace "ku yan wani gari ne maana a ina kuke zama?"damm gaban narjisu ya fadi tayi shiru batace komiba husnah a tsorace tace "narjisu nidai mukoma duniyarmu mu koma kar"narjisu ta tsunguleta dan tasan sunan Abraham zata kira hafeez ya maimaita a ransa yace narjisu?....sai kace sunan aljanu a zahiri kuma yace "ku koma duniyarku?akwai wata duniya ne bayan wanan?ai babu wata duniyar bayan wanan da duka muke ciki aljanu da mutane muke rayuwa....da sauri husnah ta kallesa tace "su waye aljanu su waye mutane su waye jinsi"hafeez ya kyalkyale da dariya Yana kallonta yana dariya wawtarta tayi yawa tayaya zatace batasan aljanu ba?.....wata irin kara kamar zubewar kaca narjisu taji ta girgiza ta waiga hajiya babba ta gani a kidime tace "narjisu akwai matsala najiyo sautin tafiyar Abraham yanzun haka a cikin daji najiyo tahowar iskarsa kiyi yadda zakiyi ku isa kafin ya rugaku"tana gama fadi tayi sama husnah ta hango tashin hankali wajen narjisu ta taba narjisu tana tambayarta da ido narjisu ta kalli hafeez tacev"zamu tafi amma nasan sai an kwana biyu zaka ganmu ana jiranmu yan uwanmu zamu koma ruga zamu dawo zankawo maka ita kawowa na harabada"yayi dariya dikta rude gashi bai gaji da kallon husnah ba baigaji da ganin Asmau ba dikda taki sakin jiki dashi ta fuzgi hannun husna gudu gudu sauri sauri yake kallonsu mamakine ya kashesa da baisan bacewarsu ba......


isaka ce take tashi a cikin gidan ilahirin jamaar gidan ganin yadda bishiroyi ke karyewa sunsan Abraham ya taho cikin fushi mahaifiyarsa gaba daya hankalinta ya tashi garin ne ya shiga sauyawa yana wani irin DUHU suna jiyo sautin takun kafafuwansa kamar kasa zata tsage dik wani ahalin jinn na gidan saida ya tsorata narjisu dibbbb suka dura a kofar gidan saidai yadda iska ke neman kwasarsu dik yadda taso tayi siddabarunta ta kasa Bude kacar daya rufe gidan da ita daga nesa husnah take hangensa yau baa mota ya dawoba gabanta ya fadi Irin kallon da yayi mata yasa taji kamar ta saki fitsari narjisu kuwa dauke kai tayi cikin rashin tsoro tace"sannu da zuwa yaya Abraham"bai amsaba sai cafkar hannun husnah da yayi suka shige gidan narjisu tabi bayansu dukkansu sun furgita da ganin Abraham rike da hannun husbah narjisu na biye dasu....mahaifiyar Abraham wani mawuyacin miyau ta hadiye to yaushe husnah ta fita gidan kuma waye ya fitar da ita?babu wanda zaiyi wanan aikin sai narjisu, zuhraliyya ta tsorata kanwarsa ganin yayi sashensu da ita narjisu kuwa wajen mahaifiyarta ta wuce tace "maamah wallahi nadade da sanin yaya narjis na fita da Anty husnah saboda jiya ma naga dawowarsu"ajiyar zuciya mahaifiyar Abraham tayi cikin zuciyarta tana adduar Allah ya yayyafawa wanan masifar ruwan sanyi.....

Husnah kuwa suna shiga sashensu ya wancakalar da ita gefe Daya ta fadi kasa ta dago cikin tsoro da mamaki ganin yadda idanuwan Abraham suka canja ya furgitata sosai sai kawai ta soma hawaye gumi kawai yakeyi jijiyoyin kansa dik sun fito fuskarsa tayi jajir kokarin danne fushinsa yakeyi dan yasan zai iya rikida ya koma wata halittar ganin tana hawaye yasa yaji zuciyarsa nason karaya kauda kansa yayi cikin tsananin bakin ciki a kufule yace "ina kukaje husnah?"yana kallon gefe daya yake tambayarta ta fashe da kuka tace "babu inda mukaje kawai mun fita wajene"

"karya kikeyi!!!!!"cikin tsawa da daga murya yace tayi saurin toshe kunnuwanta yadda tsawarsa ke barazana da tarwatsa mata kwakwalwa ya juyo yaga yadda take gumi ya tako a hankaki ya tsaya a gabanta yace "husnah yaushe kika koyimin karya ?waye ya koya miki karya husnah?ashe dama zakici amanata bansaniba?"ta girgiza kai tana kuka cikin tsananin soyayyarsa tace "kayi hakuri banci Amanarka ba"ya girgiza kai ya durkushe yace "kinci amanata tunda kika ketare umarnina kika fita husnah gashi kuma kinki fadamun gaskiya"ta mike ta fada bayansa ta rungumesa tana kuka tana fadin "kayi hakuri bamuje ko inaba waje kawai muka fita"gabansa na faduwa yadda yakejinta a bayansa ya juyo da ita ya rungumeta yana bubbuga bayanta baisan lokacin daya soma hawayeba saboda yadda yake matukar kaunarta yace"husnah kin dauko hanyar da zai kawo matsala a tare damu nidake kin dauko hanyar da sirrin da nake boye miki shekara da shekaru zai bayyana,matukar kika sake fita na tabbatar inaji a jikina matsala zata faru da dani dake dik zamusha wahala ko kin daina sona ne?"ya dago fuskarta ganin yana hawaye yasa ta sake burkicewa tana danasanin abinda ta aikata saidai zuciyarta ta kwadaitu da wanan duniyar ya dace ta sanar dashi hakan mai zai hana subar nan su koma can?ya tsareta da ido cikin zuciyarsa yace akwai abinda kike boyemun husnah nasan ko menene amma lokaci yayi da zakisan nidin ba mutum bane face aljan nasan zaki kaunaceni a haka saboda nayi nasara yadda nake hangen soyayyata da kaunata cikin zuciyarki ya rungumeta sosai ta makalkale a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya ya rinka lallashinta wani irin faduwar gaba yake ciki.....

dakyar ya janye jikinsa yayi murmushi ganin hakan yasa ta sauke sassanyar ajiyar zuciya yace "ina zuwa"kafin ta amsa masa ya fice cikin sauri.....


"narjisu!narjisu!!narjisu!!"yake kira cikin wata irin murya ya tsaya a tsakiyar filin daya kasance sashensu ne nan da nan suka firfito hardasu juraid mahaifiyarsa ce tayi saurin taryarsa ganin yadda jikinsa ke rawa cikin wani irin kamanni mai ban tsoro ya tsaya a gabansu "ina gargadi da babbar murya a dik inda kike kina jina kisani kindauki hanyar da zan rabaki da ranki kin dau hanyar da zan batar dake gabaki daya idan kuma kince karyane karki fasa"

"idan kafasa azabtar da narjisu ka raina Allahn daya halicceka Abraham akan meyasa kake wanan ikirarin saboda kaga ana tsoronka ka dade kayi dik abinda zakayi"....ya juyo yacev"keeeeeeew"Yana nunata da yatsansa mahaifiyar narjisu ce ke tsate rike da kwankwaso sai huci takeyi,

dukkansuxa tsorace suke ganin yadda jikinsa ke sauyawa idanuwansa suka koma ruwan roka narjisu ce ta fiti daga Inda take tana masa wani kallo cike da rashin kunya kanta yayi yaji an fuzgosa yana juyowa yaga mahaifinsa yace "idan ka kuskura ka aikata abinda kake shirinyi to ya zama dole waccen bil'adamar ta bar mana gida ta bar mana duniyar mu"

Abraham cikin fushi yace "idan zatabar nan toko tabbas kusani tare dani zatabari zakuma ku rasani harabada"ya wuce cikin fushi zuhraliyya kuka take tana fadin "mamah dan Allah ki hanasa naga ya fita banaso su tafi su barmu yaya Abraham yayi fushi zai iya aikata dik abinda yayi niyya"bacewa mahaifiyarsa tayi ta nufi sashensa ganin bakowa sai husnah zaune tasan ya tafi daji bishiyar da yake zuwa ta kurawa husnah ido tana zaune tayi tagumi wata tsanarta taji ta darsu cikin zuciyarta akanta Abraham ke wanan tsiyar to tasan maganinta ta bace .....


husnah tagumi tayi tayi zurfi cikin tunani gaskiya bazata iya rayuwa a cikin wadanda basa Sonta ba dolema Abraham yazo ya dauketa su tafi can inda suke zuwa da narjisu,hafeez ne ya fado mata a rai gabanta ya fadi tayi masa tambaya yana shirin bata amsa kuma suka taho,ta turo baki gaba tayi shiru ta hada rai tayi kicin kicin da fuska narjisu ce ta bayyana a gabanta cikin suffar aljanu narjisu wani kallo takewa husnah ta tabbatar zucuyarta ta tsunduma son komawa cikin halittarta tasan abinda zatayi....daga hannuwanta tayi ta watsa nan da nan husnah ta zabura cikin tsananin tsoro take bin ko ina da kallo kalar dakin ta sauya sai juyawa yakeyi a gabanta fitulun dakin ake kunnawa ana kashewa tanajin wani sauti ummmm ummmmm muuuuyyyyy mai ban tsoro ta mike jikinta na rawa ji tayi jiri na dibarta ganin bishiyoyi sa wasu halittu masu dogon wuya suna wucewa ta gabanta ihu ta shigayi tana fadin "Abraham!!!!!!"ta dora hannu akai ta yanke jiki ta Fadi jiyo sautin takun Abraham natahowa alamun yaji ihun husnah narjisu ta bace....

a kasa ya ganta warwas idanuwanta a rufe ya ciccibeta ya rungume "husnah husnah "yake kiran sunanta yana girgizata bata motsa ba bude baki yayi ya fesa mata wani ruwa fari karrree daga bakinsa ta bude ido ganinta rungume a jikinsa ta sake kankamesa tana fadin "nidai nagaji da nan Abraham tsoro nakeji akwai duniyar datafi wanan dadi mutafi wai shin bakace zamubar nan ba"galala ya saki baki yana kallonta hasashensa ya tabbata ya hadiyi wani mawuyacin miyau ganin rikici Karara a idon husnah ya tallabota yace "Ina kikeso muje"ta fashe da kuka 'idan bazamuje inda kace zamuba to ka kaimu wara duniyar mana ba akwai duniyar mutane ba"dammm gabansa ya fadi jikinsa ya kama rawa ya kalleta wani abu daga cikin idanuwansa suka fito suka Shiga jikinta bata sake motsawa ba bacci ya dauketa yana rungume da ita yana kallonta zuhraliyya ce ta bayyana a gabansa tace "yaya sharrin Narjisu ne nadade da sanin shirinta akan Anty husnah kuma tanada magoya baya karka kyaleta ka batar da ita ka daddaureta kayi mata azaba"ya jinjina kai kawai ya soma kuka mai ciwo.....
******

daddy na zaune ya kasa sukuni tun dawowarsa yake parlor momy batasan shigowarsa ba muryarsa taji yana kwalawa hajiya rabi kira "hajiya rabi!!"hajiya rabi daga labe a sashen ta jiyo kiransa dama ta shirya dan tasan tunda yaci naman nan baida sukuni momy ta shigo parlorn tacev"dama ka dawo daddy"baiko kalleta ba yace "ehh nadawo tun tuni ina nan zaune bansan yawan magana yasa"taji wani yarrrrr ta kalli fuskarsa babu yabo ba fallasa tacev"naji kana kiran hajiya rabi kanada wata bukata ne ayi maka"hajiya rabi ce tayi sallama parlorn tadau kwalliya ta kashe dauri "Assalamu alaikum barka da dawowa daddyn yara naji kamar kana kirana"yayi murmushi "ehh nadawo ne bangankiba bakizo kinyimun sannu da zuwa ba shiyasa"murmushi tayi tace "banji shigowarka bane "ya nuna mata geefen kujera yacev"zauna nan "ta nemi waje ta zauna momy na tsaye cike da mamaki da al'ajabi ta kalli hajiya rabi, itama kallonta tayi wani irin murmushi tayi mata mai cike da mugunta da kissa momy ta jinjina kai,

yaseer ne da muneeba sukai sallamah ummah muneeba ta washe baki daddy yace "ah ah kune tafe daddaren nan yaseer ina zuwa?"yaseer ya tsugunna kansa kasa yace "barka da dare daddy"

"barka dai yaseer kaida iyalin naka ne"yaseer ya amsa da "ehh"daddy yace "Masha Allah zama yayi kyau naji dadin biyayya da kayimun na auren muneeba dikda akwai auren husnah a tare dakai"

yaseer yace "wai daddy wacece husnah ne naga anatamun maganarta ni babu wata husnah muneeba ce matata"daddy yayi dariya bai kawo komiba ya kalli momy dake tsaye mamaki ya kasheta yace "kinji ja'irin yaro auren muneeba ya mance da husnah yana tambayar wacece to matarka ce husnah ko yanzun tazo akwai aurenta akanka"yaseer ya hada rai zaiyi magana hajiya rabi ta karbe "daddy yanzun ai bamuda tabbacin ganin husnah tunda tun tuni husnah tabarmu tun shekara biyu sabida sakaci irin na uwarta data barta tana wasa da yamma ta fice shikenan"daddy yadan bata rai ya kalli momy yace "dik kece silar batan husnah a sakacinki"momy ta fice hawaye na zubowa a idanuwanta ta fahimci komi shikenan hajiya rabi ta raba yaseer da kaunar husnah ta cusa masa soyayyar yarta gashi yabzun tana shirin shiga tsakaninta da daddy.....tana shiga daki ta rufo kofa ta fashe da kuka,

daddy ganin ta fice yayi tsaki yace "aikin banza"hajiya rabi dadi ya kasheta tace "a kawo maka abinci ne?"daddy yace "ehh injidai kinyi pepesoup din nan mai dadi?"yaseer da muneeba dariya sukai sukayi musu sallama muneeba cikin tsananin murna take alamu sun nuna daddy zai auri mahaifiyarta a kori mahaifiyar husnah yadda zasu mantar da daddy da yaseer wata husnah su soma juta dukiyar daddy da yaseer,



muneeba suna shiga daki ta zunburi baki ta zauna a two seater ta juya baya hankalin yaseer ya tashi ya zauna gefenta ya rungumota ta kwace yacev"lafiya"ta tura baki da yar kwalla tace "nidai yanzun shikenan dik ranan da husnah ta dawo mu biyu keda kai Kenan "hawaye suka zubo mata hankalin yaseer yayi kololuwar tashi wutar soyayyarta ke ruruwa cikin zucuyarsa kawai sai yasa harshensa yana lashe hawayenta yana shafa kanta yana tsotso ruwan idanuwanta ta narke masa yana shafa kanta yace "dk wanan abun da kikeyi ni bansan wata husnah ba kinzo kina tada hankalinki akanta bansanta ba bansan wani aureba ki shiru idan ma akwai auren zansamu daddy sakinta zanyi dikda bansan wata husnah ba"farin ciki ya lullube muneeba ta rungumosa numfashinsu na haduwa ya lumshe Ido kamshinta ke narkar masa da zuciya.....ya janyota ya rungumeta sosai ta dago ido ta daga masa gira tana turo masa lebe "kardai kacemun zaa kuma?baka gajiya da nan ne?"ta nuna masa kirjinta "dadin tabawa "ta Kai hannu ya tura cikin rigarta ya soma wasa da nipples dinta.....

*****
hafeez tsaye yake jingine da bangon dakinsa dare ya tsala ya kasa kwanciya tunanin asmau yakeyi so yakeyi ya amsa mata tambayarta amma baisamu dama ba ya lumshe idanuwansa fuskarta ya hasko yayi murmushi,

ummah sa ta fito daga kitchen da cup din ruwa ta hangi wutar dakinsa a kunne tace"yadai hafeez bayi bacci ba"ta nufi dakin Kila yayi bacci ne yabar globe a kunne bari ta kashe masa tana tura kofa ta gansa da waya a hannu yana zabga murmushi "Kai hafeez lafiyanka?"furgigit yayi ya kife wayar a table din karatu na dakinsa yace "ummah?baki bacci ba"cikin mamaki take kallonsa tace "na kwanta na fito naga globe din dakinka a kunne nadauka kayi bacci"yace "banyiba yabzun zanyi"ummah tace "ko akwai wata matsala ne?"ya girgiza kai ya kwanta a gadonsa ya rufe ido ummah ta kada kai kawai ta kashe wutar ta rufo masa kofa......

*****
bayan kwana biyu husnah zaune tayi tagumi ta tasa abincu a gabanta ta kasaci Yana tsaye a gabanta bata ganinsa tayi tsaki sai kawai yaga ta mike tsaye ta rike kwankwaso ta koma ta zauna ya shiga damuwa ya kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login