Showing 72001 words to 75000 words out of 130717 words

Chapter 25 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

209

tana kallon momy jinjina mata kai tayi tace"ki kwantar da hankalinki kinji?zaki dawo nan din idan angama komi na aurenki da yaseer "husnah ta zabura tace "momy aurena da yaseer kuma?"sai kuma tayi shiru tanajin bugun zuciyarta na karuwa momy ta dauko kayanta tace "momy banasom wadanan kayan "momy na kallonta tace "don me?"ta girgiza kai tace "Abraham ne ya siyamun su"momy ta jinjina kai kenan ranan da suka fita da yaseer ashebada yaseer bane da aljani ne?"dire kayan momy tayi yana juyawa ta waigo taga kayan sun bace husnah tana kallonsa ya dauka ya rungume momy ta kalli wajen ta kalli husnah,"ina kayan?"husnah ta muskuta ta sauko tace"maishi ya dauka"momy ta waiga bataga kowa ba ta ruko hannunta suka fice....

yaseer mikewa yayi yace "muje momy in rakaku gate"hajiya saude tace"kamata yayi kaje can ka kwanta a sashen muneeba kayi wanka ka sauya kayan jikinka kaga jikinka dik jini"ya gyada mata kai muneeba tayi saurin rukosa tace"muje"ya kalleta ta gefen ido momy na tafe husnah na biye da ita tana satar kallon yaseer shima satar kallonta yayi ta Shiga mota momy ta shiga su innah nan aka barsu suka wuce....


muneeba ta taimakawa yaseer ya tube ringarsa ta shige kirjinsa ta kwantar da kai tace"yanzun nasan shi kenan munkoma mu biyu muke da kai ko?'ya shafa kanta kawai bayason magana ya janyeta ya shige toilet ta fita ta nufi kitchen cikin takaici take da tsananin kishi tabbas zata nunawa husnah ita rainon mutane ce dan tasan husnah batasan komiba kuma husnah zuciyarta na wajen aljanin mijinta zata kwace yaseer ta rabata dashi kota wani haliz

daure da towel ya fito yana goge jikinsa yayi tozali da Abraham a tsaye cikin dakin yayi wani juyi ya kallesa ya gifta ta gefensa yana zagayesa yacw"kayi nasarar mallakar husnah amma kasani mu biyu zamuyi zaman aure da ita dan bazan taba barinka da ita ba bazaku taba zaman lafiya ba"yaseer ya kallesa ya kauda kai tsoro ya basa yadda fuskarsa ke juyawa yana canja kamanni. daga fari ya koma baki idanuwansa kuwa jujjiyawa sukeyi idan ka kallesa idanuwansa guda shida suka koma zaiyi magana Abraham ya bace....yaseee ya jujjuya bai gansa ba muneeba ta turo kofar da tray a hannunta ta doro flask tana kokarin zubawa ta mika masa taji an fuzge daga hannunsa an watsawa yaseer a jikinsa tafadasshen ruwa ta ware idanuwa tana kallom. yaseer shima ita yake kallo jikinta na rawa tace"bani bace wallahi naji kamar an kwance an karba daga hannuna ne kaji?"ya jinjina mata kai yace"nasani"ta mike ta dauki tray din ya dauki magungunansa ya wetsa ya zura jallabiya ya shimfida dadduma ya tada sallah.....

******
husnah na zaune kan carpet din dakin taji tanajin fitsari ta kalli kofar dake manne jikin bango jikinta ya bata toilet ne ta shiga,

Abraham ne ya fito ta jikin bango ya sauya kamanninsa zuwa yusrah kanwar yaseer ya kalli carpet din take tray na abinci lafiyayye da madarar hollandia ya bayyana ya zauna ta fito sukai ido hudu da yusrah tayi murmushi dikda tasanta tunda sunzo gida sau biyu tace"ga abinci nan nakawo miki kici ki koshi idan ma bazakiciba ni zan zauna muci tare inbaki aike matar yayana ce"Abraham yace cikin suffar yusrah tayi murmushi tace"zauna mucu"a sanyaye yusrah ta zauna husnah nata kallonta sam jikinta ya kasa natsuwa tace"mucu"Abraham ya dibo yakai bakinsa husnah bata ganin tauna bakin yusrah take cinyewa tare sukaci yusrah tace"umm Bari kiga yanzun zan fita yaya yaseer ya kasa sukuni yace zaizo yanzun ya ganki"husnah tayi murmushi tace"nima inaso ingansa kodan insan ya jikinsa"Abraham ya kada kai yadau tray din ya fice yana fita ya bace....

bayan fitar yusrah da minti talatin taji an turo kofar da sauri ta zabura cikin tsoro tana ganin yaseer taji hankalinta ya kwanta cikin shagwabarta data zame mata nature tace"saida kazo ko?ya jikin naka?"zama yayi gefen gado yace"da sauki tayaya zan iya zama can bayan kina nan?"husnah tayi murmushi sam batajin sonsa ko kadan a zuciyarta saidai idan suna tare tanajin faduwar gaba miko hannu Abraham yayi yace"taho nan muyi wata magana"wani yarrr taji ta yaya yaseer zaice ta kawo hannunta?daga zuwansa dikda ance an maida aurensu?"ya tsareta da ido wani abu ne ya fito daga idonsa ya shiga jikinta ji tayi ta gagara yi masa musu ta tako ta taho a hankali ya dorata a cinyarsa ya rungumeta yana sauke numfashi yana shakar kamshin jikinta yace "ummm inason kamshin jikinki koba turare"take maganar Abraham ta fado mata yana yawan cewa yanason kamshin jikinta koba turare,yawo ya somayi da hannunsa a jikinta tace"yaya yaseer kadaina"Abraham yayi murmushi yana jifanta da wani kallo mai cike da shaawah


momy ce ta shiga dakinsu yusrah suna zaune suna kallo nusrah na danna waya tace"ku dauko radiom dakin bakin can kusa memory card din nan kusa karatu cikin gidan nan yanzun nan shima ayi connecting dinsa da Bluetooth akai dakin husnah kuma karku rinka barinta ita kadai" nusrah tayi narai narai da ido tace"nidai tsoronta nakeji ina tsoron aljanu"momy tayi tsaki tace"tunda dodo ce ko dallah kutashi kuyi abinda nasaku yanzun zan kira malam muyi magana a soma karbar magani,

husnah nagani yasa bakinsa a nononta yana tsotsa yana liliya dayan tace"yaya yaseer ka bari "Abraham ya kasa magana yayi missing dinta sosai hawaye suka ciko a idon husnah tace"kabari yaya yasee"kenan dama yaya yaseer dan iska ne?tace a ranta nusrah data nufo dakin taji husnah cikin wata murya tana fad'in "yaya yaseee ya bari"dafe kirji tayi yaushe yayansu yazo gidan nan?


*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE 300 MAI BUKATAR SIYA YA TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DIN*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

*SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER KO KATIN MTN 08036953516*


*SLIMZY*✍🏻
31
Abraham na rike da kwankwason husnah yana kara mannata da kirjinsa yana in fanta da wani kallo mai cike da so da kauna itama kallonsa takeyi mamakin yaya yaseer takeyi kici kicin kwacewa takeyi ya shafa kanta ya rad'a mata a kunne"kin manta an maida aurena dake?"yace tace cikin wani irin yanayi mai cike da kasala"idan an maida aurenmu yaya sai kazo kana tabani kuma a gidan momy?"shhhhhhh yace"momy ai tasan ni mijinki ne?"jikin nusrah ne yayi sanyi ta tabe baki ta juya ganin gilmawar mutum yasa husnah saurin turesa tace"gashi nan ai yanzun kaja momy ta ganmu"Abraham ya waiga ya kalleta yace"ba momy bace saidai su nusrah bari inje insamesu inci mutuncinsu"tura baki tayi ta hararesa ta zauna gefen gado bugun zucuyarta ya tsananta Abraham na fitowa yayi murmushi ya rikid'a daga kamannin yaseer ya koma kamanninsa yayi mik'a ya kalli kofar dakin yana hangenta zaune gefen gado ya girgiza kai yana tsananin sonta dikda yasan tana sonsa wanan shegen bil'adaman ne ya shiga tsakaninsa da ita amma yanzun aka fara wasan,ya bace,

daga kitchen nusrah ta fito da tray na abinci sukai kicibis da nusra tace"yadai naganki kindawo ina abinda momy tasaki kiyi?"kallon kofar dakin husnah tayi tace"naje na tarar da yaya yaseer ciki yazo"zaro ido nusrah tayi cikin mamaki tace"yaya yaseer kuma shida momy tace tabarosa can gidansu ya kwanta dakin Anty muneeba yayi accident fa?tayaya zai kamo hanya yazo"ta wuceta tace"ni matsamun in kai abincin zanyi sallama idan ma yana ciki zan shiga abuna"tabe baki yusrah tayi ta wuce,

dakin momy yusrah ta shiga ta tarar da ita tana sallah ta zauna gefen gadon ta jira momy ta idar kallonta momy tayi tana kallon hannunta tana jiran karin bayani yusrah tace"naje zansaka karatu na tarar yaya yaseer yazo yana dakin shine nadawo"

"yaseer kuma?au da yace zai biyomu naki yarda shine daya shigo gidan bai fad'amun ba?"momy ta yunkura ta karbi radiom "muje inci masa dan tselen uwa"yusrah ta rufawa momy baya,

husnah na zaune gefen gado nusrah cikin tsoro tace "Assalamu alaikum"da sauri husnah ta juya ta amsa tana murmushi ganin nusrah da tray din abinci ya bata mamaki tace "ah ah yusrah ta kawomin abinci har munci tare fa yanzun"daidai nan momy ta shigo tana fad'in "ina yaseer din?"husnah ta sadda kanta kasa tace"ya fita momy nadauka ma ya taho wajenki ne"

"ta ina zai taho wajena bayan yasan yadda mukayi dashi?nace ya kwanta ya huta shine ya kamo hanya yazo batare da nasaniba ya shigo zanyi maganinsa"momy ta kalli nusrah dake rike da tray a tsaye tace"ki ajiye mata tray din mana"

"momy Anty husnah tace taci abinci wai yusrah ta kawo mata sunci tare"zaro ido yusrah tayi tana kallon nusrah tana kallon momy tace"ni yaushe?"husnah ta yatsina fuska tace "ah ah yanzun fa kika kawo abinci bayan fitarki yayanku ya shigo"kasa magana yusrah tayi cikin dimuwa ta fice daga dakin nusrah ta juya da plate din momy tace "taso muje parlor mu zauna tare banaso kina zama ke kadai, nusrah kai tray din kitchen kuje parlor da Antynki asa tashar karatun kurani"nusrah ta jinjina kai suka fito tare jiki a sanyaye husnah ta fito tamkar wadda aka zarewa lakar jiki to ya akayi yusrah zatace basuci abinci ba alamu sun nuna cikin dimuwa ta fita waye zai kawo mata abinci bayan yusrah?.....nusrah ta fito daga kitchen suka jera suka nufi babban parlorn gidan...

yusrah na zaune tayi tagumi momy ta shiga girgiza kai momy tayi tace"ki kwantar da hankalinki na fahimcu komi na fahimci cewar bake kika kai mata abinci ba jinnu ne"yusrah ta zabura tace "shine sukai shigata?"ta dafe kirji momy ta jinjina kai tace "kwarai kuwa dagaske zasuyi abinda yafi haka ki daina damuwa nakira malam dazun xaizo bayan sallahr isha'i yace,tashi kije kisamesu a parlor "tsoro nakeji"momy tace "ba abinda zai sameki ki kwantar da hankalinki "tayi ajiyar zuciya ta fita,


husnah zama tayi a kasan carpet a d'arare tana bin ko ina da kallo nusrah ta dauki remote din tv bayan ta kunna Abraham ne ya shigo ya shige jikin husnah yana kallon remote din hannun nusrah remote din ya fad'i kasa,tayi tsaki ta tsugunna ta dauka ta canja tasha ta ajiye ya kalli inda remote din yake take taga alamar ana danna remote kuma babu kowa a wajen tashasho sukaga suna fitowa nusrah jikinta ya kama rawa yusrah ta shigo tana kallon yadda tashoshi ke canjawa tace "dallah meye haka ki tsaya mana wajen Tasha daya kin tsaya sai canja tashoshi kikeyi"nusrah bakinta na rawa tace "ba....bani ba nibace yusrah kinga remote din can"ta nuna mata da yatsa sukaga husnah ta kafe tv da ido ko kiftawa batayi a hankali suka juya suka zare jiki sukabar parlorn...suna fita husnah ta mike Abraham yayi dariya a jikinta ya shiga zagaye parlorn yaje ta gefen tv zai taba momy ta fito da karatun mp3 a hannunta suratul bak'ara tace "husnah lalala karki taba menene haka?"da sauri ya dago kai a jikin husnah jin sautin karatun kurani yasa ya sheke da dariya ya yanke jiki ya fadi ya fice daga jikinta momy ta kalli nusrah tace "dama ba ita bace"suka jinjina kai cike da damuwa

******
narjisu ce ta shigo dakin muneeba ta jikin bango Abraham yana zaune kan dadduma kansa nad'e da bandeji bai gantaba batazo masa a yadda zai ganta ba ta dade tsaye tana tinanin yadda zata fito masa ta juya ta Shiga kitchen taga muneeba tsaye tana yanka albasa kamshin girki ya cika kitchen din tayi murmushi tace "wanan abincin saidai ku bil'adama"muneeba ta juyo da sauri taji kamar anyi magana bataga kowa ba tayi tsaki tace "kunnena nayimun gizo"ta cigaba da aiki kamannin muneeba sak narjisu ta koma ta dauko tray da jug din da ta ajiye na zobo ta fito dashi daidai yaseer ya shafa addua ya fito ta dire masa ya kalleta ya jinnina kai yace "sannu da aiki"ta gyada masa kai ta juya baya ta dawo da dubanta garesa tace "ba matarka bace"ya tsura mata ido kawai yaga fuskarta ta canja ta koma wanan budurwar da yake gani gyara zama yayi cikin sassarfa yace"ina kika Shiga?"murmushi tayi masa tace"ina nan ina gefe ne kawai yau nakawo maka agaji da taimakon Allah da yanzun anyi jana'ixarka"ya jinjina kai take ya tuno da yadda trailer ta bugi motarsa cikin seconds yaga tana komawa da baya da baya kamar ana turata kan iska yace "wanan aikin nayi tunanin naki ne dama,Dan Allah wacece Ke?"

"ni matar Abraham ce"tace a takaice take ya gane ya gano cewar wato Abraham na kokarin rabasa da husnah tana kokarin gyara lamarin gudun karta rasa mijinta batare da sanin taimakonsu takeyi ba,"kana ganin taimakonku nakeyi ko?"ya jinjina mata kai tace"tabbas da ba taimako nakeyi ba amma yanzun taimakon nakeyi dikda ina tsananin kishi da husnah yadda mijina ke tsananin sonta"muneeba ce ta shigo dakin daidai yaseer ya bude baki zaiyi magana tace "ah ah kai kadai kake magana kuma?"ya wayance yace "kiranki dama zanyi"tayi turus tana kallonsa yana kallon yadda gashinta ke lilo a bayanta ya burgesa tace "yaushe zobom nan yazo nan?"ta nuna masa ya kalli inda narjisu ke zaune bai ganta ba ransa yad'an baci zuwan muneeba yasa tabar wajen yace"kece kika kawomin halan kim manta ne?"ta dafe goshi tayi shiru tace"na manta kam"ya kalli cikinta da yad'an turo yace"duba kigani cikinki ya fara fitowa"murmushi tayi cikin jin dadi tace "ehh mana ai nadauka kadaina son d'an naka ne zumudin husnah"ta hararesa yace "jeki soyomom kwai please bakina babu dadi inaso inci kwai"ta jinjina kai cike da jin dadi tad'an samu samu sakin fuska wajensa harta fita ta juyo tayi kiasing dinsa ya shafa wajen yayi yak'e ta fice ya mike da sauri yana kalle kalle "ina kike? Dan Allah ki fito"ya wawwaiga bai ganta ba yayi tsaki ya zauna ya dafe kai haushin muneeba ya kama yaseer mema ya kawota?mtswww tsaki yayi yana kaiwa da komowa cikin dakin dan motsi yaji a bayansa ya juya ya dauka itace baiga kowa ba ya zauna ya dafe kansa meyasa ta tafi suna magana?kansa ya dau zafi Yana mamakin yadda sanadin husnah yau shike magana da aljana,muneeba ta fito dauke da plate ta soyo kwai sai zuba kanshi yakeyi ta dire masa a centre table taga ya mike "ina kuma zakaje?bayan kace in soyo maka kwai ko zakaji dadin bakinka gashi na kawo maka yanzun zaka fita"kan yaseer ya dau zafi yasani tunda ya ganta yasan akwai wata matsala dan haka yasa kai ya fice muneeba tabi sa da kallo baki bude ta jinjina kai tabbas tasan saita mike tsaye yadda Anty sadiya ta fada mata dazun ta zauna dirshab tsakar daki,

momy na kokarin kai abinci bakinta ya shigo dakin tace"ah ah yaseer ya naganka haka kamar an koroka?"ya kalli kayan dake gefen kujera yace "momy wad'anan kayan husnah ne?"ta jinjina masa kai tace"kayanta ne kayana ta diba ta tafi dasu taki daukar wad'anan wai wanan aljanin ne ya sai mata"ya kalli kayan yayi tsaki yacev"momy kamar akwai wani abu dake faruwa fa bari inje"momy tad'an tsorata tace"abu kuma?"ya jinjina kai yace "ehh momy kawai tunda naga narjisu"momy tayi saurin kallonsa tacw "narjisu kuma?kaima yanzun ka koma husnah ne aljanun kake gani?"bece komiba zai fita ta tarbesa "Babu inda zakaje da wanan raunin akanka kaji nafada maka ka koma ka kwanta ka huta kabari gobe sai kaje gidan "ransa beso ba ya fice kawai momy ta girgiza kai yanaso ya fita da ita ya siya mata kayayyakin gyara da kwalliya itama ta fito kamar mutim inso samune har makaranta zai sakata kicibis yayi da daddy ya shigo yace "barka dai daddy"d'aga masa hannu daddy yayi yace "barka"yasa kai ya wuce yaseer jikinsa yayi sanyi ya tabbatar daddy fushi yakeyi ya rasa meyasa daddy ke fushi akan maida aurensa da husnah ya dade tsaye ya koma sashen muneeba tana nan zaune ta tasa plate hannunta tana ganinsa tayi ajiyar zuciya tana magana ya wuceta ya nufi daki shi kawai koma ya zaayi sai yaje gidan momy yau,dabara ce ta fado masa yana shiga daki yasan idan yace asibiti zashi babu mai hanasa canja kaya yayi yasa kananun kaya sun karbi jikinsa matashi dan shekara talatin da daya yana fitowa muneeba tace "ina zuwa Kuma?"yayi dan tsaki yace"asibiti zani kaina nad'snyimun ciwo"ta kafesa da ido tanaso ta gano gaskiyar zancen yacev"meye kike kallona?"ta girgiza kai kawai ya fita beko bi ta kanta ba,

*******
husnah ta fito wanka daure da towel ta wanke kanta sosai ya fita fes d'akinta da karatun kurani ta zauna gefen madubi tana kallon kanta gado ta kalla ta girgiza kai tayi murmushi ganin kayan nusrah kan gadonta ta shafa mai data gani da turare mai mugun kamshi momy ta ajiye matashi,ta bude kayan fited gown ce ta tsurawa rigar ido yadda zatasa rigar take tunani yusrah ta shigo tace "har kin fito?"ta jinjina mata kai ta kalli sashen mp3 din yanayi ta rufe kofa ta fita,ta zura rigar sosai ta karbi jikinta ta taje kanta sosai ta dauki ribbom ta maida gashi kam Allah ya horewa husnah tayi mugun kyau orange din atamfa ce da kwalliyar ganye kore jiki shiru tayi tana kallon kanta yadda rigar tabi jikinta kunya ce tayi mugun kamata tana tsaye tana kallon kanta ta nemi waje ta zauna ta tsare mp3 din dake karatun kurani da ido,

yaseer a waje yayi parking yayi mamakin ganin takalmi a kofar babban parlorn yasa kai ya shiga "Assalamu alaikum "yace yana shiga Abraham ya shige jikinsa da sauri wata harara momy ta watsa masa tace "mai kuma ya dawo dakai bayan zuwan dakayi dazun? sarkin soyayya?"kallon idonta Abraham yayi take taji ta kasa maganar tace"zauna"ya zauna "yaya jikin naka?"jinjina mata kai yayi Abraham ji yayi kansa ya buga da malam ya bude wani turare yana kokarin yiwa momy bayani Abraham dake jikin yaseer yacev"ina husnah?"momy ta nuna masa dakinta tace"tana ciki niko tayi wanka ma oho shiga ciki ka tahomin da ita inaso malam ya ganta"malam yace "ya kamata akwai abubuwan da zan shaka mata"Abraham ya mike zumburi ya nufi dakin da husnah take yana zuwa yaji sautin karatun kur'ani kofar dakin naci da wuta ayoyin Allah kasa shiga yayi gashi a jikin yaseer idanuwansa sukai jajir ya fice daga jikin Yaser shiko yaseer kallon kansa yayi yaushe yazo kofar dakin nan?inanw kuma nan?kallonsa Abraham yayi lokaci daya ya mance da tambayoyin da yakewa kansa yasa kai ya shiga dakin tsuru Yaseer yayiwa husnah yana kallonta idonsa yayi tozali da gashinta da tayi parking ashe dik gashin muneeba husnah ta yaga mata?wani miyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login