Showing 90001 words to 93000 words out of 130717 words
kokarin shiga gonarsa takeyi idan ta kuresa tsaf zai bayyana mata koshi waye dan ya huce takaicin abinda hajiya saude tayi masa tabbas wanan matar sai ya dau mataki akanta,gyara tsayuwa yayi kafin yace wani abu ta ruko hannunsa tana kokarin cire masa riga badan yaso ba haka ya cire gabaki daya bayason motsi kuna ce a jikinsa ta maganinda karatun alk'urani....narjisu ce ta shigo dakin ta jikin bango wani kallo yayiwa bangon ya juya ya kalli muneeba yaga ta tsaresa da ido mamakin yaseer takeyi kardai shima aljanun sun shafesa,
"Abraham meyasa ka zabi rayuwa da bil'adama a duniyarsu kabaro duniyarmu kazo nan dan cikar burinka?"tambayar da narjisu tayi masa kenan yasa kai ya jufi toilet Tasha gabansa,"Baka amsamun tambayata ba,idan har kai ba mugu bane to me kakeyi a nan?dubi yadda jikinka dik yayi kuna kuna dik sakamakon husnah ne shin wanan husnah bazaka iya rayuwa ba saida ita?tace masa cike da tsiwa da takaici kallonta yakeyi tsaye a gabansa ya kalli yadda gashin kanta ya tsaitsaya takaici biyu ya hadun masa cikin fushi yace batare da bakinsa na motsi ba "ki kaucemun kafin na illataki na halakaki nafada miki kibar shiga gonata da rayuwata ninaga inaso zan iya ko dolene?so kikeyi wanan dake tsaye ta gane ni waye?"ya kalli muneeba da tsoro ya gama cikata kardai yaseer aljanu sun shigesa yadda taga yana kallon gefe daya bakinsa na motsi batasan me yake fada ba,ganin kallon da takeyi masa yasa ya wayance ya janyota ya rungumeta take ta fama masa kunar dake kirjinsa a manne yacev"ashhhg
"yadai menene yaya yaseer?"ya girgiza mata kai "gajiya ce ga tunani dayake cunkushe a zucuyata muneeba"ya shafa kanta "bari nayi wanka na fito ko?"ta gyada masa kai tayi farrr da ido "nayi missing din gwarzon mijina yau ina bukatarka inaso ayimun wanan sucking din"ta kashe masa ido ya girgiza kai ya shige toilet yana shiga ya rikida ya koma kamanninsa mai tsananin girma da ban tsoro juyi yayi yana kallon yadda fatar jikinsa tayi yayi wani huci ya kalli kofar bayin haushin wanan matar yaseer din yakeyi gashi narjisu ta bace yabarta tsaye yasan zataje neman Yaseer ne ya kumasan bazata taba ganinsa ba tunda yana tare da zuhraliyya.....
******
bakin kirin sararin samaniya tayi sakamakon dare da ya farayi kukan tsuntsaye yaseer yakeji ga tsananin kishin ruwa da yakeji dikda wacen aljanar ta kawo masa amma bazai taba iya shan ruwan aljanu ba,
kallom kasan bishiya yayi zuhraliyya ce da kayan saki a jikinta blue black ta kama gashinta gefe da gefe fuskarta fari tasss wasu ne sukazo wajen yana kallon yadda ta mike tana zagaye can kafin ya runtse ido ya bude wajen ya cika da aljanu yan mata da samari yaseer na kallonsu yanaji wani aljani yace "zuhraliyya inaji kamar akwai mutum a wajen nan bil'adama ko?"ta jinjina masa kai ta daga manyan idanuwanta sama ya kalla idanuwansa ya hasko masa yaseer ta tabe baki "yaya Abraham ya Bani ajiyarsa a nan yasa kukaji nace muzo muyi gad'ar a nan banaso nabar wajen"ya jinjina mata kai tayi wani tsalle ta soma rawa tana bada waka nan da nan suka soma yaseer dik abinda sukeyi a idanuwansa sukeyi yana kallom wasu kanana sunatayo itace suna kaiwa manyansu dake bayan bishiyar sunata girke girken abinci hakan ya tabbatar masa da yanzun dare ne dan idan da rana ne bacci sukeyi.....
wata isa ce mai karfin gaske take yawo a sama buuuuu kamar tashin mota zuhraliyya ta d'aga kai sama tayi ido hudu da narjisu,
kawar zuhraliyya tace "ke zuhrali kamar narjisu matar Abraham dama bata nan ance iska taje nemowa da karfi wajen sarki"zuhraliyya ta had'iyi wani miyau a makoshinta tsoro ya kamata fatanta kada narjisu taga yaseer yadda take shawagi cikin duhu cikin bishiyoyi tana kiran sunan yaseer cikin muryar datasaba zuwa masa,
kalle kalle yaseer keyi sama baya ganin komi sai sautin wucewar iska yana cikin sark'ak'iya duhu mai ban tsoro kasa magana yayi tabbas aljana narjisu ce,jikinsa ya kama rawa cikin tsananin kosawa ya kasa amsawa Abraham ya rigada ya daure masa harshe baya ko iya magana inhar dan kansa ne sai in yanason abu,
kamar walkiya zuhraliyya ta bace Abraham ganinta yayi dib cikin dakin muneeba ya fito wanka tana numfarfashi "narjisu narjisu'daga mata ido yayi ta bace muneeba naganin ya fito ta gyara kwanciya tayi kwanciya mai cike da daukar hankali kallonta kawai yayi wani abu ya fito daga idanuwansa ya shiga jikinta,nan da nan ta soma hamma kafin minti daya bacci ya dauketa cikin sauri da zafin nama yabar dakin ya nufi duniyarsu cike da fargabar kada narjisu taga yaseer....
*****
hajiya zainab kwance kan gadonta takeji kamar motsi cikin dakinta takun sahun mutum taji,ta hadiyi wani miyau cike da tsananin tsoro tana kallom kofar daki taga inuwar mutum sanye da kayan bacci tsaye hajiya rabi tayi tana waige waige,momy cikin bakinta ta furta "hasbunallahu wa jiimal wakil,ta fara karanto falaqi da nasi cikin tsoro ta jikin window hasken farin wata ya haska mata fuskar hajiya rabi take ta ganta,sai kawai momy ta kalki hannunta cikin furgici kardai tazo kasheta,adduoi momy ta soma karantowa bataga wani makami a hannunta ba har ta karaso bakin gadon ta waiga babu mai kallonta ta hayo kan gadon tana laluben fuskar momy,runtse ido momy tayi cike da faduwar gaba taji bakin momy tana kokarin tura mata abu a baki momy ta dartse bakinta gamm cikin karfi suka soma kokawa momy taji nauyin hajiya rabi ga cikin,cikin saa da dabara ta cafki dan yatsan hajiya rabi da gurza mata cizo wata yar kara tayi momy ta hankadata ta mike tana fadin "waye wanene?kece wa?"tana kokarin karasawa ta kunna wutar dakin hajiya rabi tayi wuf ta fice daga dakin ta yarda layar a kasa cikin azabar cizon momy,
wuta momy ta kunna haske ya mamaye dakin ta hangi abu a kasa ta karasa ta tsurawa layar ido ta girgiza kai gumi ne kawai ke karyo mata tayi addua ta dauki layar ta ajiye gefen gado ta fada toilet ta dauro alwala tazo ta shimfida dadduma gabanta bai daina faduwa ba ta tada sallah
****
juyi muneeba tayi akan gado tayi furgigit ta tashi tana kalle kalle mamakin ganin globe na dakin kunne takeyi tayi saurin kallon gefenta bataga yaseer ba,ta daga kai ta kalli agogo karfe daya na dare ina yaje?take tambayar kanra cike da tsoro,ta zuro kafa zata sauko taji sautin karar ruwa a toilet tayi ajiyar zucuya har taji wani kishi ya caketa a kirjinta kardai fita yayi ya tafi wajen husnah jin karar ruwa yasa ta koma taja bargo taji wani sabon bacci na lullubeta hakan ya tabbatar mata da yana toilet....
*****
iskar tahowar Abraham yaserr yaji hankalinsa ya tashi sosai idanuwansa sai hawaye sukeyi yanajin narjisu na shawagi kusa dashi yasani idan har narjisu tazo to tabbas zata ceceshi,
"narjisu!!!!!"yaji wata murya na kiranta hakan ya tabbatarwa da yaseer zuhraliyya ce ta fado masa dan be sake hangen inuwarta wajen ba,narjisu wani yunkuri tayi wuta ta fara tartsatsi daga bakinta zuwa bishiyoyi wajen Dik inda ta bullo Abraham take gani ya mamaye ko ina cikin karfi da iska ta ware hannuwanta ta watsa su saiga wani abu kamar mashi kamar walkiya ya haska mata fuskar yaseer,tayi murmushi ta kalli Abraham bata nuna masa taga yaserr ba sai kawai yaga ta canja waje Abraham dadi ne ya lullubesa bata gansa ba yace ya diro kasa ya tsaya yana kallon yaseer yadda yake lilo cikin wahala,
"yadda na kasa rabar husbah ka hanani rayuwa da ita kaima bazakayi rayuwa da itaba nafada maka a nan zaka dawwama har karshen rayuwarka....
****
hajiya saude zaune a tsakiyar gadonta tayi tagumi yanayin yadda yaseer yayi dazun yake dawo mata da kalaman malam wanda ya fada mata "kisa ido sosai inhar dagaske ba yaseer bane bazai iya zaman gidan ba zakiga canji'taja numfashi ta sauke take ta tunada yadda yaserr ya fita yana tangad'i dazun a gaggauce yanayi mata saida safe,dafe kirji momy tayi kardai abinda husnah tafada gaskiya ne kardai ba yaseer bane da aljani suke rayuwa innahlillahi wa innah ilaihi rajiun tace a tsorace wata dabara ce ta fado mata dakyar ta koma ta kwanta cike da kosawar safiya tayi.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
39
Daddy na zaune parlor da safe yayi shirin fita cikin farar shaddarsa yake tasha aiki hajiya rabi ta shigo da flask na tea da cup ta ajiye,sallama sukaji a tare suka amsa Alhaji kabiru ne yayan daddy da innah suka shigo da ummah hadiza daddy na ganinsu ya kirkiro faraar karfin hali yace "ah ah da safen nan kune haka sannunku da zuwa bismillah"ya tashi daga inda yake zaune ya koma gefe "sannunku da zuwa"hajiya rabi tace tana binsu da kallo,wani kallo innah tayi mata ganin ta tsaya kikam taki fita "ba wajenki mukazo ba ga wajen wanda mukazo kuma munyi saar ganinsa shiyasa muka dako sammako"daddy ya sunkuyar da kansa,da sanyin jiki hajiya rabi ta fice ranta a bace,
"ina kwananku"daddy yace cikin ladabi yana gyara zamansa,
"badamasi ka bani mamaki dik naji irin abubuwan dakake shiryawa kuma kakeyi a gidan nan naji komi yaseer ya sanar damu hatta kayan daya siyo kasa ya maida naji komi hakan yasa nazo nida kaina tunda kasa ya maida ni idan na siya kasa ya mayar"cikin fushi baba kabiru ke maganar,daddy bece komiba sai gumi yakeyi wato yaseer ne yaje ya sanar musu kenan lallai yaseer ya girma,
"yanzun nazo da masu gyara kuma nabasu umarni su shiga sashen gidan nan dake gefe a kulle su gyarawa husnah yau da yamma zaazo daga kamfani asa mata kayayyakinta ciki inaso ta tare a yau din nan ko gobe inyaso ka koreta tinda gidanka ne kanka ya juye yarka daya tilo kake wulakantawa yanzun ga uwarta da wani cikin ai innah ta fadamun idan ta haihu shima dan ka wulakantashi da uwar zan tattaresu in kwashe ka zauna da rabi,nazo da kaina ne ba sako ba saboda kasan dagaske nake dik wani iskanci da kakeyi kai ga mai ya nasan komi"daddy yayi kasa da kai cikin ladabi yace"kayi hakuri bazaa sakeba insha Allah"
innah ta d'orada "zanbar hadiza a gidan nan gata sai angama komi dan munyi magana da saude akan zata zauna da husnah saboda lalurarta da magungunanta tunda kai baka damu da jinnun da suke damun yarka ba badamasi mu mundamu kuma jininmu ce zamu kula da ita"innah ta yunkura tace "mutafi kabiru"
"innah ku tsaya mana ku karya bari na kira rabi ta kawo muku"
"bashi mukazo ci ba,muba yunwa ta kawomuba mara mutunci"ta fice baba kabiru baice komiba ya mike Yana kokarin fita aka kirasa daddy bece komiba har suka fice ummah hadiza tace "Bari in leka wajen hajiya zainab"kafin yayi magana ta fice daga dakin,
hajiya rabice ta fito daga daki ta fashe da kukan bakin ciki yanajin haka ya mike jikinsa na rawa"kukan mai kikeyi?meyasa kike kuka?kidaina kuka kiyi shiru yaseer baxai rabu da muneeba ba dan an maida aurensa da husnah kinji muneeba da yaseer mutuwa ce zata rabasu"ta Kara rurin kuka ta shige jikinsa "yanzun Alhaji kenan muneeba suna nufin na yarsu bace ko sun manta kaninka ne ya haifeta? itama ai yarsu ce amma sun fifita husnah akan muneeba ana kokarin fitar da muneeba daga gidan mijinta bayan mijinta yana sonta?"ya share mata hawaye yanajin wani shauki akan hajiya rabi dikda yadda yake cikin bacin rai cikin sigar lallashi yace "ki kwantar da hankalinki ni nasan yadda zan bullowa lamarin baridai husnah ta tare"hajiya rabi najin haka ta goge hawayen kissar da takeyi ya jinnina mata kai tace "Mai zakayi alhaji?"yayi murnushi "ki kwantarmun da hankalinki kidaina koke koken nan banaso kinji banason kukanki"ta langabe masa a jiki tasa hannu ta dauko hularsa ta dora masa ta wani lankwashe ta langabe kai "kayi kyau alhajina kullum kara kyau kakeyi sam kamar ba tsoho ba"yayi dariya yaja hancinta suka fito a tare,
hajiya zainab ta soyo dankali da kwai ta dauko daga kitchen tayi kwalliyarta tasa wani lace blue mai golden ya a jiki tayi matukar kyau cikinta ya fito sosai tana hango tahowarsu ta hada rai tayi kicin kicin da rai tsabar kyaun da tayi daddy saida ya kalleta ya sake kallonta ta dauke kanta ganin haka yasa hajiya rabi shagwabewa daddy kamar zata shige cikinsa,..
ummah hadiza na zaune momy na Shiga ta tareta "ke zainab abinda kike gani kenan a cikin gidan nan?yanzun wanan wulakancin Shi kike fuskanta ina kallon badamasi ko kallo baki ishesa ba,momy ta dire plate din a gaban ummah hadiza tace "ai bakiga komiba ummah hadiza ai wanan kadan ne sanan maganar da kikeyi ta wai be kulaniba nida jiya ya mareni yace bayason ganina a cikin gidan nan?"zaro ido ummah hadiza tayi "mari?"momy ta jinjina mata kai tace "mari dai da kikasani harda kora ya koreni naki tafiya ne nace saida shaida idan kuma ya bani shaida zaiyi dayasani"ummah hadiza ta jinjina kai mamaki ya gama kasheta taja gauron numfashi"dik son da badamasi keyi miki"
"da ne wanan"hajiya rabi ce ta tsaya kikam akansu tayi wata dariya hade da shewa tace "andaiji kunya ankori mutum yaki tafiya saboda tsananin bakim naci miji baya raayinki kin like koda yake yar kwararoce ke"ummah hadiza kuwa cikin zafin nama ta mike ta zabgawa hajiya rabi mari ta dago ta kara zabga mata tana nunata da yatsa cike da masifa da bacun rai "ke rabi ki shiga hankalinki akwai yat kwararo irinki keda kikaje wajen boka kika shiga kika fita kika rabasu aikece yar kwararo ba zainab ba kisani zainab nada daraja da kima a idanuwanmu koda ta kasance batada kowa tafi karfin wulakanci shashasha maciya amana"momy cike da bacin rai tace "dole ki kirani yar kwararo tunda badamasi ya kirani jahila a gabanki jahilci ya kare miki da kikazo jiya kina kokarin turamun laya a baki"... dafe kirji hajiya rabi tayi"ni zakiyiwa sharri zaindb nice na tura miki laya a baki?ni bayan cin mutuncin da kuke shirin yimun saboda kunyi kunyi ku shiga tsakanina da mijina kunki shiyasa kuka bullowa yaseer da maida husnah"ta fashe da kuka "wallahi bazan dauki wanan rashin mutuncin da wulakanci da tozarci ba daddy zan kira na sanar masa koni ko ita cikin gidan nan abu. har ya kaiga mari?"sadiya ce ya fito ta ruko hajiya rabi tana harare harare "kiyi shiru ki kwantar da hankalinki zama daram cikin gidan nan tunda mai gida na kaunarki kuma sharrin da akai miki sai ya bi miki hakkinki"ta watsa musu wani kallo ummah hadiza jikinta na rawa ta cafko sadiya momy ta yunkura dakyar ta rukota "rabu dasu ba irinsu baceke karki biye musu ummah hadiza"zama ummah hadiza tayi cike da takaici,
sallama hafeez yayi a parlorn da sauri momy ta kallesa tace "hafeez?hafeez dama kana nan?"murmushi hafeez yayi yana kokarin shigowa yace "sannunku momy"
"ga waje ka zauna hafeez zauna yau nice zan baka abun karyawa"murmushi yayi "ina kwana momy?"
momy kallonsa takeyi yana kalle kalle jikinta ne yayi sanyi tausayinsa ya kamata yace "momy ina husnah ne? ya jikin nata wallahi nad'anyi tafiya ne hankalina gabaki daya yana wajenta a can inda naje ma har wani mai magani nasamu gashi nazo da maganin"Abraham ha tsaye jingine jikin kofa yana kallon hafeez wani irin kallo yasa hannu cikin izza idanuwansa na fito da wani hayaki amma abun mamaki dik yadda yayi kokari hayakin ya shiga jikin maganin dake jarkar yaki dawowa yakeyi yasa hannunsa yaji kamar anjasa,hafeez ne ya juyo ya dauko ya mikawa momy wadda Baki sake take kallonsa batasan me zatace masa ba,
"ga wanan momy inada tabbas akan wanan maganin da zarar tashashi aljanin nan zai rabu da ita zaiji bayason koda ganinta momy saidai dayake waraka ba lokaci Daya take zuwa ba"momy tai shiru dakyar ta sauke numfashi tace "sannu hafeez hakika kai namiji ne wanda dik macen data sameka a matsayin mijin aure ta dace dan zata samu kulawa,saidai husnah bata nan gidan"damm gaban hafeez ya yanke ya fadi yana kallon momy ya kasa magana ya hadiyi wani miyau ta tsaresa da ido "kayi hakuri hafeez kasan ai akwai auren abokinka a tare da ita ko?"nan da nan idon hafeez suka kawo ruwa ya sunkuyar da kansa kasa sam bayason momy ta hango karayarsa yace "nasani momy amma...."
"hafeez yaseer baya cikin hayyacinsa ne shiyasa amma yanzun haka ma kaga ana gyaran gidansu dake gefen namu ko?yau ko gobe akeso husnah ta tare sakamakon aljanin nan dake damunta"Abraham yayi murmushi hmm basusan dashi Zata tare ba yaseer dansu yana daji a daure,
momy ta kwashe komi ta fadawa hafeez jikinsa yayi sanyi yanajin jiri kasa mikewa yayi kansa a kasa ya kasa magana momy tace"yadai hafeez?"girgiza kai yayi ummah hadiza tayi ajiyar zuciya hafeez ya bata tausayi sosai tasan yadda yake dawainiya da son husnah sanadinsa aka samu husnah saidai already akwai aure akanta...."kayi hakuri hafeez kaji ai yaseer dan uwanka ne ko?"ya jinjina kai ya dago kai idanuwansa jajir yace "bakomi momy ga maganin nata yanzun zan koma ummah najirana zan fita da ita"momy ta girgiza kai cike da tausayawa "ka gaida ummahn naka kaji kuma idan kasamu lokaci kazo inason ganinka"ta jinjina kai ya fice,
"gaskiya ya bani tausayi harda dawainiyarsa gashi yanason husnah"momy ta kada kai kawai ta dauki maganin ta ajiye a gefenta,ummah hadiza tana cin dankalin kadan kadan tace "Bari intashi naje in duba masu aikin nan na gyaran gidan husnah kinsan alhaji kabiru"sukai dariya tasa takalmi ta fice momy tayi shiru tana tunani da nazari...
******
tare da husnah suke aikace aikace a kitchen saidai gabaki daya cikin tunani take da fad'uwar gaba wanda ta rasa dalilin hakan ko ina cikin gidan karatun alkurani ne momy ce ta tsaya bakin kofar kitchen din "laa momy kin tashi kenan"ta jinjina kai "Natashi jiya banyi bacci da wuri ba sakamakon motsi da nakeji a cikin gidan nan"
"nima momy naji motsi dakin anty husnah kuwa buga kofar aka rinkayi natashi yakai sau biyar bana ganin kowa kuma ikon Allah ita tanata baccinta"nusrah tace tana kallon gefen husnah,murmushi kawai husnah tayi tad'an yatsina fuska tace "momy yau tinda natashi nakejin kasala inajin amai"momy ta zaro ido waje "amai fa kikace?"ta jinjinawa momy kai,"tou bari yaserr