Showing 57001 words to 60000 words out of 130717 words

Chapter 20 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

179

zata sanar dashi zuwa gobe ko jibi zaazo ayimun tambaya"wani miyau ta hadiye tausayin hafeez ya kamata tabbas hafeez nason husnah amma ya zaayi da auren yaseer dake kanta?takardar ya mance ya zura a aljihu yayiwa yaseer wani kallo ya fice muneeba ce ta kira wayar yaseer da sauri ya dauka yace "yadai munee?"yaji tana kakarin amai ya rikice yace "momy bari inje indawo muneeba batada lafiya naji amai takeyi ma"ya fice cikin sauri narjisu ce ta fito cikin suffar mutum kyakkyawar budurwa ta tsaya a jikin kofar shiga sashen su yaseer tana ganinsa tayi masa sallama tana murmushi kallon rashin sani yakeyi mata da kallon tuhuma.....
*Afwan my people gobe akwai bikin sister na adan dagamun kafa zuwa jibi insha Allah kunsan hidimar biki nagode sosai da kauna*

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN KIKA KARANTAMUN BAKI BIYANIBA BANYAFEBA*

GA MAI BUKATAR SHIGA WANAN TAFIYAR YA TUNTUBI WADANAN NUMBERS DIN...

07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻24

kallon rashin sani yaseer yakeyiwa narjisu tayi murmushi tace "nasan bakasan koni wacece ba ko?"ya jinjina mata kai cike da kosawa yace "bansaniba saikin fada ke wacece daga ina kuma kike?"shiru tayi daga bisani ido cikin ido tace masa "ni aljana ce,"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi bakinsa ya shiga karkarwa yana kokarin fara addua ta daga masa hannu cike da isa narjisu tacev"dakata karkayi addua ka cutar dani ka kona ni don niba cutar dakai nazoyi ba"dakyar ya hadiye wani miyau yace "Mai kikazoyi?dama aljani yana kulla alaka da dan adam ne bata cutarwa ba"muneeba ta sake kiransa ya kalli wayar a gaggauce yana takawa zai wuceta tace "nazo in taimakeka ne akan husnah na tabbatar kaje wajenta baka ganinta ko?"da sauri ya juyo yana kallonta yace "ya akayi kikasani"murmushi Narjisu tayi tace"ba saika tambayeni ba saboda ina bibiyar rayuwar husnah sakamakon mijina dake aurenta shi yasa mata abinda ko kazo bazaka ganta ba ya zuba mata abun a jikinta sakamakon tsananin kishi da yakeyi dakai da waccen abokin naka"gumi ne ya karyowa yaseer bata jira mai zaide ba ta daga hannunta sama ta bude baki wani abu na fitowa daga cikin bakinta fari kalll hannunta da wani ruwa mai haske mamaki ya kashesa yadda ruwan baya zuba daga hannuta kafin yayi magana ta watsa masa yaji wani yarr yayi baya ya runtse idanuwansa take ta bace ya wawwaiga bai ganta ba cike da tsoro yake kallon gefe da gefensa bai gantaba dakyar ya taka kafarsa yana tafiya yana waige bai ganta ba gashi ta tafi bai ganta ba bata bari taji ta bakinsa ba tura kofar dakin yayi da sauri ya shiga ganinta warwas a kasa tana juyi tayi amai ko ina ya karaso da sauri ya tallabota jikinta yayi mugun zafi yace "yadai muneeba lafiya?maike damunki umm?"cikin rudewa yake tambayarta ya ciccibeta cak ya nufi toilet da ita dikda baya cikin hayyacinsa a wahala tace "naci abinci ne nayi amai ina ganin jiri kaina nayi mun ciwo"cike da shagwaba take maganar ya zare doguwar rigar dake jikinta ya cillar gefe ya tara ruwa yayi mata wanka tas ya fito da ita ya nadeta a towel ya nufi parlor ya gyara wajen sanan ya dawo ya tallabeta yace "yanzun muje asibiti ne?"ta yatsina fuska ta girgiza kai ya shafa gefen fuskarta yace "meyasa bazamuje ba a duba aga maike damunki?'cikin shagwaba tace "nafada maka ciki ne?"ta tura kanta cikin jikinsa cike da kunya yayi murmushi ya shafa kanta ta kara shigewa jikinsa yace"to zan Kira likita azo gida a dubaki"ta gyada masa kai yana kokarin tashi ya fita tace"ina zakaje?"ta tsaresa da ido ya sosa keyarsa kamar bazai fada Mata ba yace "zani sashen momy ne akwai maganar da muke tattaunawa kinga husnah gata nan ta dawo"da sauri ta mike ta zauna kishi ya taso mata tana masa wani kallo kawai saita fashe da kuka nan da nan hankakinsa ya tashi yace"ya isa kukan me kikeyi?meyasa kike kuka kidaina kuka karki cutarmun da abinda ke cikinki kinji kiyi hakuri"a rude yake maganar ganin yadda ya rude yasa ta kara rurewa da kuka.....

******
sauke numfashi takeyi ta danne kofa ya tsura mata ido waige waige takeyi ta fada jikinsa ya rungumeta sosai yace "kina sona?"ta dago kai da sauri ta kallesa tace "ina sonka mana Abraham ina tsananin kaunarka meyasa akeson rabamu nidakai?"ya shafa kanta ya kwantar da kai a kamta cikin murya mai kama da rad'a yace "saboda ni aljani ne shiyasa akeson rabamu kuma ni ina sonki kema kina sona"sosai ya bata tausayi "tou meyasa bazaka koma kamar mu mutane ba kaga shikenan sai mu cigaba da zaman auren mu ko?"ta dago kai tadan janye jiki daga jikinsa ya jinjina mata kai yace "babu yadda zaayi in koma bil'adama nima da inada halin hakan husnah da nakoma kodan in cigaba da rayuwa dake cikin kwanciyar hankali"....
bankado kofar akayi "husnaj husnah fito nan kin makale a daki tare da aljanin ko?"cewar momy fuskarta a daure husnah ta kalli Abraham ta wayance tace "baya nan fa momy niba kowa a tare dani"tanayi tana kallon sashin da Abraham yake momy tace "tou wanan waige waigen na meye kikeyi ko sunzo ne?fitowa zaki parlor mu zauna kinajina ko dan malam yace a daina barinki kina zama ke kadai a daki"ta nunawa husnah kofa "wuce mutafi"husnah ta saci kallon Abraham ya jinjina mata kai alamar ta fita momy tayi gaba husnah na biye da ita Abraham ya matso ya rike hannunta a tare suka fito parlorn ta nemi karshen kujera ta zauna momy ma ta zauna daga gefe kamar ance ta waiga ta juya taga husnah na murmushi tana gintse fuska tana gabtsarewa Abraham ne ke mata cakulkuli hannunsa daya ya damki nononta yana matsawa ta saki yar kara momy ta zabura tace"ke lafiyarki kuwa meye hakan?"husnah ta daure ya zumburo baki tana gunguni tana fadin 'ni babu mai rabani da mijina"ya matse yatsanta tayi yar kara tace "ahhhnnnn kabari nidai"momy ce ta shiga waige waige tana neman turaren da malam ya bata sama ko kasa ta nemeshi ta rasa ta mike ta nufi dakinta tana dubawa tuni Abraham ya dauka ya bude hannuwansa yana nunawa husnah ta zaro ido murya kasa kasa tace "kadauka ashe"yayi murmushi ta nemi abun ta rasa momy saude ce ta shigo da yan matanta guda biyu Abraham na ganinta ransa ya baci husnah ta kallesa da ido gudun kar hajiya saude ta fahimci ba ita kadai bace yace "banason wanan matar idan naganta raina baci yakeyi ji nakeyi kamat inshaketa"nan da nan jiniyoyin kansa suka fito husnah ta bata rai momy cikin faraa tace "ah ah husnah kece zaune a nan ke kadai ya naji shiru ina momyn naki take'a dakile husnah tace "tana ciki"a fusace momy ta fito tana surutai tana fad'in "shikenan sun sace sun sace turaren shima maganin dake cikin dakin can bari in dauko kafim shima su dauke"

"ah ah zainab ya naganki a burkice haka?meyake faruwa"kuka momy ta fashewa da hajiya saude tace "wanan yarinyar ce aka kawo malami dazu"ta kwashe abinda ya faru tafadawa hajiya saude mamaki da al'ajabi ya kasheta ta nemi waje ta zauna ta cire gyale tace "tabdijan akwai babbar matsala"momy hankalinta tashe ta bude dakin husnah tana Shiga ta kalli kan gadon a burkice alamar ba ita kadai bace ta bude wardrobe saiga jarkar maganin wata ajiyar zuciya ta sauke ta dauka ta fito dashi hajiya saude tace "ni yanzun abinda ya kawoni akan matsalar yaseer ne yasameni dazun Alhamdulillah yaseer ya dawo hankalinsa tinda ya tuno da husnah"momy ta zauna ta jingina da kujera tana sauke numfashi dakyar tace "tou ai ya rubuta takardar saki saidai nida idona banga takardar ba "hajiya saude ta kad'a kai tace "ya fadamun nima inaso asan inda takardar sakin take yadda zai yagata batare da kowa yasani ba"daddy ne ya shigo yace "aiko karya kukeyi naji tattaunawarku ashe gaskiya ne maganar da hajiya rabi ta fada saboda kinjini da mummunan kama kukace karya ne to tafadamun takardar sakin na hannun hafeez kuma na umarceshi da yazo da ita tare da magabatansa"gaban hajiya saude ya fadi ta ciro waya cikin sauri ta kira layin yaseer,

yana rungume da muneeba doctor ya tabbatar masa da tana dauke da ciki yana cikin farin ciki saidai dayan bangaren zuciyarsa bayaso ya rasa zukekiyar yarinyar nan gashi babban damuwansa yanda akayi idan yazo baya ganinta saidai yaga alamar tana wajen ana magana da ita, "hello momy"...yace cikin kosawa da rudewa tace"kazo kasameni a sashin momy"

"ok ok ganinan zuwa"ya gyara mata kwanciya ta ruko hannunsa cikin shagwaba zatayi magana yace "momy ce tazo take kirana"ta jinjina masa kai ya shafa gefen fuskarta ya fice yana fita muneeba ta mike ta zabura ta zauna ta leka ta window taga tafiyarsa cikin sauri jakarta ta bude ta ciro kwarya da maganin da boka ya bata akan ta fasa ta farraka tsakaninsa da husnah ta jinjina kai tace"idan kunsan wata bakusan wataba zan farraka tsakanin yaseer da husnah harabada saidai ta cigaba da rayuwa da wanan aljanin amma badai yaseer ba"cikin kishibta sa yadda boka yace ta shiga kitchen ta dauko tabarya bata ganiba tana shiga cikin store taga tabaryar ta fito mamaki ne ya kasheta ganin yadda maganin ya zube batare da antaba ba ta kalli cikin dakin bataga kowa ba waye ya kwance maganin a ledar ya zubar a kasa?tambayarr da tayiwa kanta kenan ta zauna gefen gado tana rike da tabarya kanta ya dau zafi ta dafe kanta wata dabara zatayi ta aiwatar da wanan abun?ajiyar zuciya ta sauke ummahnta zata kira suyi shawara ta jefar da tabaryar ta nufi parlor inda tasa wayarta a carji....

da baya da baya take tafiya cikin damuwa take yayi karo da ita gabansa ya fadi ya gabta tabbas itace amma meyasa dazun dayaje be ganta ba?cikin wata irin murya yace "husnah"damm gabanta ya fadi ta tsaya cakk jin muryar da aka kirata ta kasa juyowa shima ya kasa takawa ya tafi kusan seconda talatin sannan ta juyo sukai ido hudu wani Abu taji ya caki zuciyarta tayi saurin ja da baya ganin shine saidai ta kasa dauke idanuwanta daga garesa ya yafitota yace "zo nan"kasa musa masa tayi a hankaki take takowa yana kallon surar jikinta da Saida ya hadiyi wani miyau makwat ta karaso yace "ina zaki naganki a nan?me kikeyi zo muje cikin gida"ji yayi daga bayansa ance "ina ruwanka da wanda take tare dashi?nine nan take tare dani inace ka saketa?to meyafi saura?"juyawan da zaiyi yayi kicibis da hafeez wanda ba hafeez bane Abraham ne Abraham kallonsa yakeyi da mamakin yadda akayi ya iya ganin husnah a yanzun bayan abinda yasa mata a jikinta na bazai kara ganinta ba ya kalli fuskarsa take ya hango wani abu wanda ya tabbatar da narjisu ce itace ta karya masa wanan abin ya ciro takardar dayabi hafeez ya dauko ya nuna masa "gashi nan shedar saki dan haka ba sauran aure a tare da kai da ita"yaseer ya karanto ayatul kursiyyu cikin zafin nama ya tofa a fuskar hafeez wanda tuni ysseer ya gano ko waye yayi kara ya runtse idanuwansa ya saki takardar ya bace,

ajiyar zuciya yaseer yayi ya duka ya dauki takardar cike da tsananin farin ciki yasa hannu ya yayyagata husnah kuwa tsoro ne ya kamata dan tasan Abraham ne wanan ita baa hafeez take ganinsa ba tace "meye ka tofa masa a ido kagani yatafi ka kashe masa ido ko?"ya girgiza mata kai yace "ban kashe masa ido ba kinji zo muje"ya ruko hannunta suna tafiya a tare yana juyowa yana kallonta itama juyowa tayi taga ita yake kallo ta sunkuyar da kanta kasa narjisu ce ta shige jikinta suka Shiga a tare Turus daddy yayi ganinsu Tare da husnah sum shigo kallom juna momy da hajiya zainab sukayi cikin farin ciki daddy yace 'ke husnah ina kikaje daga ina kike?"ta kalli yaseer tayi murmushi tace "muna tare da yaya yaseer ne tun dazun daddy"mamaki ne ya kashe yaseer jikinsa na rawa yace "eh eh muna tare daddy naganta a wajene shine muke magana na shigo da ita"hajiya saude tace "da kyau dama abinda ya kawoni shine in sanar dakai innah daga gidanta nake akan maganar yaseer da husnah cewae ranan jumaa zaa maida aurensu"murmushi yaseer yayi cikin tsananin farin ciki ya kalli husnah ta sakar masa murmushi dik abin nan da akeyi momy na kallon kwayar idanuwan husnah tasan ba ita bace ba haka kwayar idonta take ba saidai bazatayi magana ba dan tanaso ko hajiya rabi zata mutu a maida aurensu,ta daddy cikin fushi yace "Tou yw zanyi da mutanen hafeez da nace su turo sanan nace hafeez ya tahomin da takardar sakin inga hand writing din yaseer in tabbatar da hakan saboda gaskiya bazan amince da hakan ba dan hajiya rabi ta sanarmun muneeba na dauke da ciki haka?"daddy ya tambayi yaseer ya fadada murmushi ya sunkuyar da kansa yace "haka ne daddy na kira doctor ma dazun ya dubata yanzun haka na barota tadan kwanta ne"daddy farin ciki ya cikasa hajiya saude murmushi tayi ta kauda kai tace "Allah ya inganta"husnah ta wuce su ta shige daki yaseer ya bita da kallo yana kokarin mata magana daddy yace "ka koma kaje ka kula da matarka tunda batada lafiya yanzun dai gobe ko jibi zanga hafeez zan tabbatar da hakan ingaskiya ne"yaseer ya jinjina kai daddy na fita ya zauna kujera ya dafe kai momy tace "yadai yaseer?"ya kada kai ya basu labarin yadda sukayi da husnah da aljaninta a waje momy tace "da kyau gara da kayi hakan kada ka kuskura ka rinkajin tsoronsa"yaseer yace"wata aljana dazun tazomin wai narjisu"hajiya saude ta dafe kirji tace "nashiga uku gida ya zama na aljanu kai kuma? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun "yaseer yayi murmushin karfin hali yace "ki kwantar da hankakinki"ya kwshe komi ya fada musu cikin alajabi dik sukai shiru suna mamakin wanan masifa,

******
husnah zama tayi a kasa warwas tana mamakin yaushe ta shigo dakin ta ina?waye ya kawota tambayar da tayiwa kanta kenan Abraham ya bullo ta jikin bango tana ganin idanuwansa da fatar idonsa ta tsorata yadda idanuwansa ya sale ta mike jikinta sai rawa yakeyi ta kasa magana yace "kinga abinda dan uwanki yayimun ko?yana shirin kwaceko daga wajena ko?hmmm yana shirin haka rami ya birne kansa da kansa Kenan "cikin rashin fahimta take kallonsa tausayinsa ya kamata wata tsanar yaseer taji ya dira a zuciyarta tace"yaseer ne yayi maka haka ko?ka kwantar da hankalinka nima zan rama maka saina konasa da hannuna"cikin fushi take maganar Abraham yayi murmushin jin dadi yace "kin tabbatar da hakan?"ta gyada masa kai tana ruko hannunsa suka kwanta kan gado tana kallon fuskarsa tana shafawa a hankali a hankali ya runtse idanuwansa ta shafa cikinsa tace"kana jin yunwa ko?"ya bude ido sa da sukai jajir tsabar azaba yace"idan ina tare dake banajin yunwa bana jin kishin ruwa"yana kokarin janyota ya rungumeta tace"bari in zubo mana abinci inajin yunwa"ya zauna yace "karkije nine zani in zubo idan kika fita bazaa barki ki shigo daki ke kadai ba"ta jinjina masa kai tana murmushi ya mike ya fito ya wuce su momy a parlor yana shiga kitchen ya tarar da hajiya rabi tana barbada magani a abinci harde hannuwansa yayi yana kallonta lallai wanan bil'adamar yace a ransa amma zanyi maganinta rikida yayi ya koma lafcecen kadangare jangwalagwada kansa har sheki yakeyi......


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 NE KACAL MAI BUKATA YA TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN....

07042277401
08036953516


DIK WADDA TA KARANTAMUN LITTAFI BATA BIYABA ALLAH YA ISA!!!!



*SLIMZY*✍🏻
25

d'ago kai hajiya rabi tayi sukai ido hudu da lafcecen kadangare jangwalagwada kansa har sheki yakeyi ta dauki muciya tace "wad'anan masu aikin anyi yan iska wato kitchen din suka bari a bude shine kadangaru suka shigo ji wani kadangare sai kace ba kadangareba kosasshe yayi girma"tayi kan kadangaren ta d'aga hannu zata kwada taji kamar an fuzge muciyar anyi jifa da ita tayi saurin zatayi wajen muciyar kawai taga muciyar na matsawa ta murza idanuwanta ta kara matsawa taga muciyar ta matsa jifa tayi da kyalen dake hannunta na magani ta kwarma ihu sam babu mai jinta yayo kanta kadangaren aguje tayi jikin bango ta hade hannuwanta biyu cikin magiya ta soma rokonsa "Dan Allah kayi hakuri nasan kaiba kadangare bane na tuba Dan Allah"hannuwanta sai rawa yakeyi gumi kuwa ta jike kashirban tana rokonsa ya bude bakinsa ya zaro harshensa taga yadda harshensa yake kawai taga ya bace ta wawwaiga bataga kowa ba ta dafe kirjinta tana sauke numfashi mararta cike da fitsari ta tsugunna zata dauki kyallen maganin daga bayanta taji ance "ban tafi ba ina nan me zakayi dashi?zakiyi cuta ko?"a hankali ta shiga juyowa bataga kowa ba yace"gani nan a bayanki juyo ki ganni mana"girgiza kai hajiya rabi tayi jikinta kamar an zuba Mata shicking tace "umm umm umm umm ba saina juyi ba"yace "saifa kin juyo idan baki juyo ba tam"da sauri ta juya tayi tozali da inuwarsa jikin bango zabgegen namiji ta gani mai masifar tsawo da jiki ta zube a kasa tana murza kafafuwa yacev"au ihu zakiyimun?"ta kada kai tasa hannu ta kama bakinta gani tayi yana tahowa tuni ta saki fitsari Nabin kafarta,

husnah fitowa tayi daga daki zata wuce momy tace "ina zakije?banaso ki shiga kitchen din nan kibari idan hajiya rabi tagama ta fito sai ki shiga"hajiya saude tace "mutum da gidan ubansa ace bazai shiga ba kikasani ko yunwa takeji?"husnah tayi fuskar tausayi ta rike cikinta tace "yunwa nakeji momy "hankakin momy be kwanta da shigar husnah kitchen babbabu yadda ta iya ta barta ta nufi kitchen din har tana tuntube garin sauri tana shiga taga hajiya rabi baje a kasa ta d'aga kai tayi tozali da Abraham yana tsaye yana murmushi ta dafe kirji tace "har naji dadi nadauka katafi ne ai daga zuwa Dibo abincu"cikin sigar shagwaba tayi maganar hajiya rabi da ta jike sharkaf da gumi ta kalli husnah dake magana take ta fahimci aljamin husnah ne,husnah ta karaso kitchen din tace "tou mai kakeyi a nan?kaida wanan matar?"ta nuna hajiya rabi da baki ya kyalkyale da dariya yace "kalli fitsari tayi a wando hussy"tayi saurin kallon hajiya rabi da take murza kafa fitsari na bin kafafunta ta kyalkyale da dariya jin shewar husnah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login