Showing 105001 words to 108000 words out of 130717 words

Chapter 36 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

183

ta labarta mata halin da suke ciki da yadda taga hajiya rabi da sadiya a dimauce sun nufi sashen muneeba ta sanar mata,
ummah hadiza tace "yauwa nagode da kika sanar mun nasan maganin yan iska ina zuwa sai anjima zan shigo akwai abinda nasa yarona zai kawomin kiyi amfani dashi"ta kashe wayar ummah hadiza ta kwalawa nusrah dake kitchen kira tazo tace"inasu yaseer din?"

"suna parlor a kirasu ne?"ummah hadiza ta jinjina kai jim kadan suka shigo a tare husnah tayi mugun kyau tayi haske ba wata kwalliya tayi ba hoda ce kawai da man baki sai dauri da nusrah tayi mata ummah hadiza tayi murmushi tace "mashaaaa Allah kunyi kyau yarana dama zancene ko zaku shirya ku fita kuje ku gaidasu innah da momynka da safen nan zasuji dadi"wani farin ciki ne ya lullube yaseer cike da girmamawa yace "yauwa ummah nima nayi tinanin hakan bari muje to Kar mutafi da nusrah ki zauna ke kadai"

"karku damu kuje abinku ni zani wajen yar uwara muyi hira"yayi dariya suka fito ya kashewa husnah ido ra runtse ido suna shiga daki ya rungumeta ya hadeta da kirjinsa yayi kissing kumatunta tace "nima saina rama"tayi kissing kumatunsa ta shafa masa lip gloss zai goge ta bata rai ya fasa da kansa ya daukar mata gyalenta yasa mata sun fito zasu fita ummah hadiza ta tsaidasu "oya ku tsaya maza husnah ga maganinki kisha"ta karba Tasha tana yatsina fuska nusrah na rike da jakarta suka fice.....

***
hajiya rabi takasa sukunin ganin ruwan dake zuba a jikin muneeba a dimauce take kiran number yaseer bata shiga tace "nima gidan nasu zani yanzun nan bari kugani"a fusace ta fita tana fitowa ta hangi motar yaseer ta fice daga harabar layin tayi kicibis da ummah hadiza na rufe gida "ah ah yadai naganki haka kamar wata damusa ina zuwa?kim kullo makircinki ne kikazo kiyi ko kunzo daukeshi ne yauma kusa masa kwaya?"hajiya rabi ta ciji lebe tace "matarsa ce batada lafiya mai dauke da cikinsa shine nazo yazo mutafi asubiti"

yar dariya ummah hadiza tayi tace "ai kin makara sun fice da amarya sun tafi yawon Gaida dangi dayi musu bangajiya"

wata ashar hajiya rabi tayi ummah hadiza ta gifta ta gefenta tabarta nan tsaye ta juya kamar mahaukaciya tayi ciki muneeba na zaune suna magana da Antu sadiya ta shiga a fusace "ummah yadai INA yaseer din ya naganki haka?"a sanyaye tayi maganar kwafa hajiya rabi tayi "wannan makirar matar ta kada kansu sun fita shida husnah"

"sun fita?"tace cikin mamaki da rudewa kawai ta fashe da kuka ta durkushe a wajen suka rurrukota sadiya tace "idan fa bakiyi wani abuba tabbas aikinmu zai kwabe da wanan matar"

"yanzun dai muje asibitin dama ai bamu taba zuwaba muje zanyi maganin yan iska a jikin asibitin nan zamu samu abinda zamu wajen boka gobe"muneeba ta kasa magana tsananin kishi sai kuka takeyi hankalin hajiya rabi yayi mugun tashi a haka suka fice....
******
kwanciya husnah tayi a kafadar yaseer tace "nifa sam banajin dadin jikina gaba Daya"ya kalli madubin dake baya yaga nusrah hankalinta na kan waya ya shafa fuskar husnah tace "zazzabi nakeji da amai dake tasomin"yace "tou kodai muje asibiti ne in mun fito gidansu innah tunda munje mun gaida momy"ta jinjina masa kai tace "yau bamuje mun gaida momy ba sanan matarka baka je ka ganta ba"ta kallesa dan tsaki yayi yace "fushi nakeyi da ita idan mun koma zanje na ganta"ta hararesa ta kauda kai ta maida hankakihta gaban motar ta jikin glass din motar take ganin wani abu dogo sululu lu yana hayowa kamar zai fasa glass din tace "yaseer yaseer kalla kamar maciji"ya kalli glass din gai ganiba yace "a ina husnah"ta nuna masa tana kokarin cakumosa cikin tsoro da furgici Abraham ne ya rikida ya koma maciji kumurci sai huci yakeyi ya bude bakinsa ya zaro harshensa ya kawo mata sara ta kwalla kara ta ruko yaseer motarsu ta soma kaiwa da komowa a titi addua yaserr ya somayi ya riketa dakyau ya taka burki cikin ikon Allah sukai parking a gefen titi yaga kanta ya langwabe ya kalleta cikin tashin hankali ya soma kiran sunanta "husnah husnah?"idonsa ya sauka akan kafarta dake mike jini ya gani yana bin kafarta jikinsa ya soma rawa idanuwansa suka ciko da hawaye jijiyoyin kansa suka firfito rud'u rud'u girgizata yakeyi yana kuka bata motsi nusrah kuka tasa ta ciro waya ta soma kiran momynsu cikin dimaucewa....

yaseer dakyar ya take motar ko ganin gabansa bayayi ya nufi asibiti da ita tuki kawai yakeyi hannunsa rike dana husnah yana murzawa yana kuka


hajiya rabi na ruke da muneeba suka shiga dakin likita inda aka kai sakamakon gwaje gwaje da result,
gyaran murya doctor yayi "ga wajen zama nan"suka zauna dukkansu kallonsa sukeyi dik a tsorace suke ya bude takardu biyu dake hannunsa. yace "too Hajiya wanan Abu da mamaki yake ko ince baa mamaki da ikon Allah"

"likita lafiya dai ko?neyafaru meyasamu muneeba?"

"ehh to gwajin ciki da mukayi na jini ya nuna tana dauke da ciki ga kuma ciki ya tsufa amma scanning yana nuna mana babu komi a cikinta batada wani ciki sai kari da muka dan karami a gefen mararta ta ciki" damm gaban muneeba ya fadi ta zaro ido ta juya ta kalli hajiya rabi wadda cikinta ke kadawa kuuuuu nurse ce ta shigo da sauri tace "likita an kawo wata yanzun nan jini na zuba muna bukatar agajinka ankaita emergency"be jira cewarsu hajiya rabiba ya mike har yakai kofa yace "kudan jirani a reception ba matsala bace"ya fice muneeba wasu hawayene suka zubo mata cikin tsananin tashin hankali ko motsi ta kasa sadiya ta karasa ta share mata hawaye tace "ki kwantar da hankakinki mata dayawa suna haihuwa hk aisu ba Allah bane da zasuce haka ni wanan cikin ma inaji a jikina namijine"muneeba girgiza kai tayi kawai hawaye na gudu a fuskarta tace "nashiga uku"a karaye tayi maganar....

*****
ummah hadiza ta taimakawa momy suka canja Duka zobon dake friedge na gidan sukayi wani da ruwan addua da yaron ummah hadiza ya kawo wanda ayatusshifa'a ce a ciki da ganye magarya da wasu magunguna na karya sihiri cikin farin ciki momy take ta kara godewa ummah hadiza kiran wayar hajiya saude ya katse musu abinda sukeyi cikin tashin hankali suka nufi asibiti.....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*βœπŸ»πŸšΆπŸ»β€β™€οΈ
45
A keke napep suka sauka a kofar asibitin kicibis sukaiyi dasu hajiya rabi suna fitowa muneeba hawaye ke gudu a idonta kallon kallo sukeyi Momy ta hadiyi wani miyau tace "lafiya?meyafaru naganku a asibiti?"hajiya rabi ta watsa mata harara tace "dama ai zaki tambaya mana tunda zakuce bakusan muneeba batada lafiya ba koda yake kun kanainaye mijinta kuna neman dauke masa hankali"tayi tsaki ummah hadiza tace "too Ashe ciwon gaskiya ne shiko yaseer yaga ta kansa mata biyu duka babu lafiya?bari mu shiga muga halin da husnah ke ciki"durkushewa muneeba tayi a wajen tarasa meke mata dadi tsananin tashin hankali take ciki idanuwanta sunyi fururu sunyi luhu luhu sun kumbura momy tausayin muneeba ya kamata ta ruko kafadarta ta dago fuskarta ta kalli momy ta kauda kanta gefe momy tace "sannu Allah ya baki lafiya,muje ciki ummah hadiza"sukai hanyar ciki hajiya rabi ta bisu da harara tayi kwafa tace "munafukai ta Allah batakuba dik wata shedana wanan tsinanniyar ke hadawa shiyasa ta kasa zaman gidan miji"Anty sadiya tadanbi bayansu tana lekawa tacan gefe ta hango Yaseer zai tarosu ta dawo da sauri tace "ga yaseeer na hango zak tarosu kai ko zamu koma ne muji menene"

"ya wuce aljanu"cewar momy tana kokarin shiga motar gida da sukazo dashi haka nan Anty sadiya ta koma ta rike muneeba suka shigar da ita cikin motar tanata yarfa hannu yadda takejin cikinta na juyawa....

"yaseer yadai ina husnah?"ummah hadiza ta taresa tana tambayarsa ganin yana kuka ta gigice "meyasamu husnah yaseer fadamun kardai kacemun husnah ta rasu"ya girgiza kai "bata mutuba ummah Amma jini fa nagani yana zuba sosai a jikinta"cikin momy ya karta jin abinda yaseer yace ta furgita ta danne dan karta tada musu da hankali nusrah tazo da sauri "kuzo ga likita ya fito naga yana tambayar ina wadanda suka kawo Asma'u"da sauri Yaseer ya juya har yanacin tuntube suka nufi dakin likitan yana shiga ko zama beyiba yace "likita yayadai?kungano abinda ke damunta?likita meke damunta meya kawo zubar jinin?"likita ya zauna yayi yan rubuce rubuce su ummah hadiza na tsaye yace "ka kwantar da hankalinka bawata matsala bace babba,saidai babbar matsalar jinin dayaki daina zuba har yanzun"

"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun,likita kace ba matsala bace bayan jini ne ke zuba a jikinta?"jinjinawa yaseer kai yayi yace "Tou bincike ya nuna mana matarka na dauke da ciki na sati hudu"yaseer ya zaro ido wasu hawaye suka zubo masa a idonsa ya kasa magana tsananin mamaki momy ta kalli ummah hadiza tacev"ciki?kardai Aljanin nan yayiwa husnah ciki yaushe husnah ta tare?"hajiya saudece daga kofar shigowa tace "ciki na yaseer ne ki kwantar da hankalinki"yaseer ya sunkuyar da kai cike da kunya damuwa cunkushe kasam zuciyarsa ya dago dakyar ya motsa bakinsa yace "likita yanzun ya zaayi? gashi kace jinin na zuba har yanzun kar cikin ya zube"

"nima mamakin daya kasheni Kenan yadda jini ke zuba idan cikin ya zube zamugani a gwaje gwaje da scanning kuma munyi iya kokarinmu wajen ganin jinin ya tsaya yaki"momy ya girgiza kai ta kauda fuskarta gefe ta share hawayenta momy tace "Tou ni yanzun likita a rubuta mana sallama mana muje gida matsalarta bata asibiti bace"
ya ciro takardu ya kallesu yace "amm muneeba fa?"kallon kallo sukayi yaseer ya hadiyi wani miyau yace "likita ina kasan muneeba?tazo nan ne?"ya gyada masa kai yace "sunzo ina dubata akacemun ga wata patients din to naga banma gansu ba kila sun tafi ne"hajiya saude tace "au itama?tou Allah ya kyauta yaseer kaga ta kanka mata biyu duka ba lafiya duk ga ciki koda yake waccen cikin ya tsufa"likita ya rubuta sallama yace "muje tana dakin Hutu"suka fito a tare,

Abraham na tsaye cikin dakin dik yadda yaso shiga jikinta ya kasa cikin fushi yake mai tsanani cikin jikinta yakeson fitarwa ya kasa a tare suka shigo dakin nusrah da yusrah suna zaune gefenta sunyi zugum zugum likitan ya kalleta ya girgiza kai ya dafa goshinta yaji sanyi kalau yace "bismillah ammafa bazata iya tafiya ba"yaseer ya mikawa nusrah wayarsa ya dauketa cak jikinta duk jini yasata a kafada suka fito a tare sukayi mota dukkansu cikin alhini da tausayin husnah suke babu meyiwa wani magana haka suka shiga motar nu yusrah a napep suka bisu motar tayi musu kadan.....

*****
hajiya rabi zaune a daki muneeba nata jujjuya abinci ta kasaci sukajiyo muryar daddy ya dawo ta mike ta fito da sauri bata gansa tace "ah ah naji kamar muryar alhaji"fitowa yayi daga sashensa da gorar Zobo a hannunsa yanasha yace "ah ah ai naji gidan shiru nadauka babu kowa ne,ina zainab?"tambayar da yayi mata kenan gabanta ya yanke ya fadi yace "yadai naganki wani iri ina zainab?"bakinta na rawa tace "am umm sun fita nima bansan inda sukajeba nadai gansu umm"daddy ya kafeta da ido yace "kince baki gantaba kuma kince kin gansu a ina kika gansu?"sai ta fashe da kukan takaici daddy ya tsareta da ido cike da mamaki yace "kukan me kikeyi rabi?meyafaru?"
"yanzun ace Alhaji yaseer muneeba ba matarsa bace ya tashi da safe saboda ya kwana a wajen husnah yarso yar gaban goshi ace ya kasa zuwa dubata har yanzun batada lafiya asibiti ma nice nakaita yanzun nadawo daga kaita asibiti gashi ance cikin dake jikinta baa gansa ba"gaban daddy ya yanke ya fadi yace "what?baaga cikin muneeba ba?"Yaseer ne ya shigo sab'e da husnah a kafadarsa hajiya saudece ke fadin "ni banso muka shigo nan ba aida sashenta mukaje tunda ga malam din yazo"daddy cikin rawar jiki ya nufi yaserr ya jefar da gorar zobon dake hannunsa gumi ke karyo masa dikda sanyin dake cikin zobon yace "lafiya yaseer?meke faruwa ya naga husnah a hannunka da jini a jikinta?"hajiya zainab kuka takeyi ummah hadiza ta rukota cikin sigar lallashi take fadin "ki kwantar da hankalinki kindaisan halin da kike ciki ko?ki duba kigani kema cikin nan gareki haihuwa yau ko gobe"

cikin kuka momy tace "dik halin da husnah ta shiga nice sila nina jefata ciki sakamakon sakacin da nayi da ita da adduoi da rayuwarta gaba daya"shiru sukayi mamaki ne ya kashe ummah hadiza ganin daddy ya karaso ya ruko hannun momy cikin kulawa da tausayawa "zainab me kike fada haka?kaddara ce baki imani da itaba?ko me kikeso kice banason jin wadanan maganganun marasa amfani wanda Allah ya rigada ya aiko dashi"yasa gefen rigarsa ya share mata hawaye yace "muje babban parlorna ko?ina muneeba itama ta fito tunda gashi mahaifiyarta tace wai baaga cikinta ba"

"baaga cikinta ba?"suka hada baki tsuttt wajen yayi hajiya rabi mutuwar tsaye tayi tana bin daddy da kallo yadda yake rawar jiki akan husnah da zainab wani gumi ne ya karyo mata tsaye take ta kasa koda motsawa saida daddy ya sakeyi mata magana a daburce ta amsa suka shiga cikin dakin.....

husnah kwance kamar gawa malam ya karanto adduoi sosai ya tofa mata a mararta da aka dan bude mata yace "Yaseer kaine mijinta shafe mata marar tata"yaserr yayi yadda akace daddy na tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa idonsa nakan husnah tsananin tausayinta yakeyi minti minti yake girgiza kansa hajiya rabi kuwa dik motsin dady a idonta yakeyi malam ya nisa "cikin yakeso ya fitar matq"

Anty sadiya da hajiya rabi suka kalli juna jin an ambaci ciki sadiya tayi gyatsine tace "ciki kuma?har yaushe akayi daren balle gari ya waye?inace jiya husnah ta tare a jiyan ne harta samu ciki?"hajiya rabi da zuciyarta kamat ta fasa kirjinta ta fito tace "ganemin hanya ko kuma cikin aljanin ne,alhaji naga yaushe husnah ta tare ake zancen ciki?"

daddy cikin rashin fahimta yake kallon yaseer ya sunkuyar da kansa ummah hadiza tace "ciki na yaseer ne tunda mijinta ne kuma akwai aure ko bata tare gidansa ba zata iyayin ciki ai"

hajiya rabi ta karbe zancen "kenan zagayewa yakeyi yanacin amanar muneeba Kenan batare da saninta ba ko?shiyasa har kwana yakeyi saboda ansan abinda aka kulla to asirinku ya tonu"....wata tsawa daddy yayi saida hajiya rabi ta girgiza yace "ke wani irin iskancin magana kukeyi haka ko ince kikeyi?wanan malamin ba bako bane kuma ba namiji bane bazaki iyajin kunyarsa ba?"zaro ido hajiya rabi tayi tace "Alhaji tsawa kakeyimun fa kuma kana ganin munada gaskiya dan dai kawai mubamu da me tsaya mana dan anga mahaifinta ya rasu?"ta rushe da kuka ta rike hannun muneeba ta dagota "muje tashi muje muneeba zan kaiki inda zaayimun maganin matsalarki'ta rukota dakyar take daga kafa yaseer yabi muneeba da kallo itama kallonsa takeyi idanuwanta sunyi jajir,dikda yanajin haushin abinda tayi masa amma tabashi tausayi ganin yadda gaba daya ta sauya....

malam na rike da kan husnah yanata addua yana fesa mata cikin ikon Allah ta bude idonta hajiya saude tayo tozali da husnah tace "Alhamdulillah husnah ta tashi"da sauri daddy ya taho ya karaso ya tsugunna ya tsurawa yarsa ido itama kallonsa takeyi da tsananin mamaki dakyar ta bude baki tace "ina yaya yaseer?macijim ne saresa bako?"take tambaya hawaye na zubowa a idonta dukkansu tabasu tausayi malam yace "Alhamdulillah ta tashi kuma jinin ma zai tsaya ga magani zan baku a bata Insha Allah zata haifi abinta cikin yakeso ys zubar tunda beyi nasarar raba auren nasu ba kuma sai kun tayasu da addua dan a yanzun komi aljanin nan zai iyayi"ajiyar zuciya ummah hadiza tayi tace "kaidai malam mungode sosai Allah yayi maka sakamako da Aljanna shi kuma wanan aljanin Insha Allahu zamuga bayansa"tsaki sukaji anyi suka shiga kallon kallo malam yayi musu sallama yaseer ya taimakawa husnah suka rukota da ummah hadiza suka nufi sashenta....

******
muneeba na rungume jikin Anty sadiya yaseeer yayi sallama a sanyaye fuskarsa a daure ya shigo a dakile ya gaida hajiya rabi ta kallesa itama ta watsar kamar bazatayi maganaba tace "ai nadauka ka sallamata ne yaseer tunanin yadda zaayi in dauke yata nakeyi saidai kuma ina auren ubanku"yaseer ya dago jajayen idonsa ya kalleta zaginsa fa tayi a fakaice wato tana auren ubansu yau da badan ita din surukarsa bace da taga rashin mutunci ya tsugunna gefen muneeba da idonta ke kallonsa tace"yaseer kenan yanzun kasan dani inda na mutu fa?"ta fada jikinsa ta fashe da kuka hajiya rabi da sadiya suka fice yadan janyeta daga jikinsa wani irin karni takeyi yana dan daddaga hanci ta kalli yadda yakeyi da hancinsa tace "ko wari nakeyi?"girgixa kai yayi "umm umm bahaka bane naji karni ne kamar kifi am ya jikin naki?"ta share hawayenta tace "da sauki"ta sunkuyar da kai yace "yanzun menene abunyi?gashi ance cimin baaganiba gashi ya girma"jikinta a sanyaye tace "ehh baa ganiba amma likitan ya tabbatar mana da wasu sunayi. hakan baby ke boyewa"ya jinjina kai yace "Allah ya kara sauki"Allah Allah yakeyi zai fita ta tsaidashi "ummhmm mai kikeso kina bukatar wani abune?"ta girgiza kai tace "kayi hakuri da abinda nayi jiya kishi ne bazan iya jure ganinka da wata maceba ina tsananin kaunarka mijina ina tsananin kishinka zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito nakeji"tausayinta ya kamasa yayi ajiyar zucuya hmm tayi hankali kenan tasan ita tai masa laifi ko?ya zauna yana fuskantarta yace "karki sakeyimun irin abinda kikaimun inayi Miki warning da kakkausar murya idan ba hakaba tamu dani dake bazatayimana kyauba "ta jinjina kai hawaye ke gudu a fuskarta ya kalli yadda lokaci daya ta rame tayi baki gashin kanta a hargitse yake yace "oya tashi kije kiyi wanka zan fita daku anjima keda husnah"ta jinjina kai tace "ba sai naje ko inaba"ta mike da kyar tayi daki ya makale kafadarsa Alamar ko a jikinsa ya fito cikin sauri yayi hanyar waje tsaye tayi ta window din bedroom dinta take kallonsa ya fice ta durkushe a kasa cike da takaici da kunar rai....

*****
hajiya zainab na bedroom dinta ta idar da sallah tana adduoi taji takun shigowar mutum har yanzun kuka takeyi gaba daya bata cikin sukuni daddy ne ya tsaya daga kofa a darare yana kallonta sam ya kasa gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login