Showing 21001 words to 24000 words out of 130717 words
daya kai narjisu bazasu taba iya shiga ba ya fice,kwafa hajiya babba tayi tace "da sannu zaka kwashi kashinka a hannu da sannu zamu tarwatsaka"ta hararesa maman narjisu ta jinjina kai cikin bakin ciki tace"muje kar rana tayi mana"suka hade waje data suka bace wani daji suka sauka nesa inda Abraham ya daure narjisu suna yawo akan iska a sama suna kiranta "narjisu!!!!!!!narjisu!!!!!!"dajin na amsawa,
a wahale narjisu ta motsa daga kullin da Abraham yayi mata tanajin sautin murya kamarta juraid yana kiranta saidai batada karfin da zata motsa ta amsa sakamakon tartsatsi na wuta dake tashi a jikinta yana zuge mata karfin iska.....
d'aga kai juraid yayi yana hangen hayaki da wani tartsatsim wuta ya girhiza yaja iska ya tashi sama yayi wajen tun daga nesa yake jiyo huci da sauti da gurnanin narjisu saidai ya kasa karasawa gudun azaba da hucin da yajeji a jikinsa na neman hallakasa cikin karfin hali narjisu ke mutsu mutsun kwacewa ta kasa juraid kiris ya rage ya karasa wajen narjisu ya fadi yayi wata kara ya kira "maamah"....
sukai wajen dayake akan iska daga nesa maman narjisu ta haska hasken idanuwanta ta hango narjisu daure dunkule a jikin bishiya tayi kuwwa ta karasa wajen ta shiga kwance narjisu cikin sauri hannuwanta wuta na shiga tanajin azaba a wahale ta kwance ta ta rungumeta narjisu da ta fita hayyacinta tace "saina dau fansa koni ko husnah ko Abraham"mahaifiyarta ta riketa sukabi iska suka sauka a gida......
*****
muneeba na makale da yaseer a daki yana rungume da ita yana shafa wuyanta yace "bakijin kunyar tsirara ke?"ta mike ta tsaya tanayi masa juyi tace "idan banyi maka ba waye zanyiwa so kakeyi kaje waje kaga wasu"cikin shagwaba tayi maganar ya jinjina kai ya lashe baki yace "yau kin hanani fita kin makaleni a gida kinga hafeez sai kirana yakeyi"ta tura baki cikin ranta batasan meyasa takejin haushin hafeez ba batace komiba ta dawo ta haye jikinsa dauki wayar hafeez,
"kana inane wai nake kiranka Baka dauka ka fito gani a kofar gida muje wajen nan ko yau zamuga asmau"yaseer ya girgiza kai yace "wanan asmau wanan asmau bansan irinta ba allah yasa dai yau kaganta mu huta"yadan gyara muneeba da gabanta ke faduwa Asmau?itada ko wanan sunan bataso mijinta ya kira kardai wajen budurwa zasu,ya katse Mata tunani "Bari inyi rakiya zamu dawo"ta rukosa tana kada masa nonuwanta "ni banaso karka dade"yayi kissing nononta da gefen fuskarta ya fice Yana fita ya hadu da momy "yauwa yaseer dan Allah fita zakayi"yaseer cikin girmamawa ya gaisheta "ehh fita zanyi momy amma da hafeez muje mu kaiki saimu tafi"yanayin dayaga momy jikinsa yayi sanyi yasan akan auren daddy da mahaifiyar muneeba ne Suka fita a tare suke tafiya,
husnah kuwa wata kugiya taji tana kamar tana tafiya a iska daga dakinta taganta a waje jikinta yadauki rawa ji tayi ana janta tana ihu sam bata ganin mai janta Gani kawai tayi anyi Sama da ita ta kwalla kara tace "Abraham".....narjisu cikin wata murya take shake dariya cikin wani irin sauti husnah ta tsorata ta cigaba da kiran Abraham tayi sammmmmmm ta runtse idanuwanta numfashinta yana kokarin kwacewa bakinta na motsi ta gagara kasa kiransa.......
DAGA PAGE 10 FREE PAGE YA KARE KU HANZARTA KUYI PAYMENT YAU 300 KACAL GA DETAILS NAN A SAMA
KO KU TUNTUBI WANAN NUMBER 07042277401
*SLIMZY*✍🏻
🌑 *DUHU....*🌑
( *sark'akiya*)
©️HWA
*SLIMZY*✍🏻
Wattpad slimzy33
Daga Marubuciyar:-
🦎 *K'ADANGARUWA*🦎
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN NAIRA 300 KACAL VIP MASU BUKATAR A TURA MUSU TA PRIVATE 1000 DOMIN MALLAKAR WANAN LITTAFI TURA KUDINKI TA WANAN ACCOUNT DIN*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*3126584401*
*FIDDAUSI MUSA*
*FIRST BANK*
*SHAIDAR BIYAN KUDI TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KI TURA KATIN MTN TA NUMBER*
*GA MASU BUKATAR TALLA SU TUNTUBI WANAN NUMBER 07042277401*
*10*
muneeba na ganin yaseer ya fita ta mike ta dauki breziarta tasa tadan ja tsaki haka kawai takejin haushin wanan hafeez din suna tsakiyar soyayya da mijinta farin cikinta yazo ya daukesa sun fita wajen wata Asmau,gababta ya fadi ta sake maimaita sunan Asma'u to ai Asma'u husnah ne kardai hafeez wata husnar yasamu yakeson hada yaseer da ita wata Ashariya tayi ya figi gyalenta ta fito tayi sashensu ummahnta,
rawa hajiya rabi ke kwasa itada sadiyya suna shewa cike da farin ciki muneeba tayi tsaye cike da mamaki tana kallon mahaifiyarta tace "ummah lafiya kike kwasar rawa?"washe baki hajiya rabi tayi cike da farin ciki tace "ke taho taho kiji abun farin ciki ina gab da angwancewa da Alhaji badamasi"dafe kirji muneeba tayi ta zaro ido tace "ummah daddy fa mahaifin husnah batacciya"hajiya rabi ta gyada kai tace "kwarai kuwa ina gab da soma mulki a cikin gidan nan muna gab da zama mune madu gida dan wanan cikin da kike gani zai haifawa Alhaji badamasi d'a namiji dan abinda yakeso yanzun kenan haihuwa tunda husnah ta bace uwar husnah ta zama juya"muneeba tayi ihu cikin murna tayi tsalle suka rungume juna da ummahnta tace "Alhamdulillah ummah kai nayi farin ciki sosai amma inaga ya kamata mu koma gidan boka dan inado yaseer ya zama ko kallon momyn husnah bayayi a cikin gidan nan dan wallahi inajin tsoro kada husnah ta dawo dikda ya mance da ita dan ko maganarta nayi masa bayaso cewa yakeyi besan wata husnah ba bashi kuma da aurenta"hajiya rabi tayi juyi taja burki ta dafa kafadar muneeba tace "kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa hajiyq zainabu da yarta sun gama zama tarihi kedai kawai bari a daura aurena da daddy jibi jumaa kisha mamaki"muneeba ta zauna Anty sadiya ce ta Shiga kitchen ta zubo farfesun kifi a babban tray ta hado da kunun gyada kofi uku ta fito tana taku ummah ta sheke da dariya tace "ki sakata ki wala ki bararraje nima matar gidan ce yanzun"muneeba ta karbi kofin kunun gyada ta kurba wani gardi ya ratsata tace ummah "kinsan haushi ya fito dani yanzun haka daga sashena?"ummahnta ta zauna tana fuskantarta tace "haushin me,"yatsina fuska tayi tace "nifa banida sukuni dan ko mai sunan husnah naji sai naji na tsanesa yanzun yaseer ya fita shida hafeez wai wata Asma'u budurwar hafeez da take zuwa zasu nema"tsaki ummah taja"sai akace miki husnah ce?"ta bata fuska "nidai gaskiya kar yazo ya bani mamaki"sadiya tayi murmushi tace "idan ma itace Ance miki yanzun yaseer zai kalleta ne?ai yanzun kece a gabansa tunda kikasa mai mantau a gabanki kikayi inserting angama"suka sheke da dariya gyalenta ta zame muneeba cikin kwanciyar hankali ta sauko ta dau cokali mai yatsu ta soma dibar kifi..
*****
Husnah jinta tayi a kasa akan kafafuwanta idanuwanta a rufe bata budeba hawaye sun wanke mata fuska murya taji kamar ta narjisu da sauri ta bude ido tana bin wajen da kallo take ta tuno inda suke zuwa da narjisu ne amma meyasa ta fito da ita gashi tayiwa Abraham alkawarin bazata sake fita ba,husnah cikin rawar murya tace "ninace miki inaso in fito?"narjisu tayi yar dariya sanan tace "ai yau husnah kin fito kenan kinbar duniyar Aljanu kin dawo duniyar mutane irinki"husnah ta zube a kasa a gaban narjisu hawaye suka wanke mata fuska gabanta na tsananin faduwa bugun zuciyarta ya sauya tsoro ya mamayeta tacev"Dan Allah karki rabani da farin cikina,Abraham shine farin cikina banida kowa a wanan duniyar faceshi meyasa zaki rabani dashi bayan mundace da juna mun shaku da juna munsaba da juna munayiwa juna wani so mara misaltuwa"tana kuka take maganar rike da narjisu,hankadeta narjisu tayi tace "rabaki dashi shine babban burina yau na cika burina domin kece kikaimun karan tsaye a wuyana husnah ina tsananin son Abraham ina kaunarsa amma ya zabeki ya fifitaki akaina"kad'a kai kawai husnah tayi ta kalli wajen dik tsananin sonta da wanan duniyar wajen yayi mata bakinkirin rayuwa babu Abraham abune mai matukar wahala zata iya rasa numfashinta...."idan Auren Abraham kikeso kiyi narjisu zan baki damar aurensa da ki rabani dashi"narjisu tayi mata wani kallo take husnah taga idanuwan narjisu suna sauya kala zuwa abun tsoro ta gigice ta shiga ja da baya gani tayi narjisu na sauya kamanni zuwa wata halitta ta daban ganinta tayi a tsaye ba akan kafarta ba gashinta ya barbazu ya sakko ya rufe mata ido kumbunan hannunta suka shiga mikewa suna tsawo husnah ta runtse idanuwanta cikin tsananin tsoro nan da nan duniyar ta soma juyawa sama da kasa jiri taji na daukarta ta kwalla kara ta fadi Kasa sunammiya.....
******
Abraham na shigowa ya kalli sashensu yaga wayen yq zama fili yayi cakkk yana kallon ko ina cikin gidan a suffar mutum ya shigo kamar koda yaushe jin ihun husnah da yayi.... zuhraliyya ce ta fito a gabansa yaga hawaye nabin idanuwanta ta yamutse a suffarta ta aljanu yace "Husnah ko husnah babu ita"ta gyada masa kai wani irin abu yaji yana yawo a jijiyoyin jikinsa nan da nan sassan jikinsa suka soma sauyawa yana mikewa ilahirin Ahalinsa suka hadu a gababsa durkushewa yayi a kasa ya saki kuka hade da kuwwa yace "Narjisu ya rabani da husnah ta Debo ruwan dafa kanta daukar husnah tabar wanan duniyar da ita a tunaninta shine rabuwata da husnah,ni Aljanine dik inda husnah take a fad'in duniyar nan saina nemota sai nayi rayuwa da ita kuma idona idon narjisu haduwar mu bazatayi kyau ba"yana kuka yana gunji mahaifinsa ya tsaya ta bayansa ya bugi kasa da sandarsa hayaki ya tashi a wajen yace "na aura maka narjisu a maimakon husnah"ya dago fuskarsa data jike da hawaye Yana kallon mahaifinsa babu alamar wasa a tare dashi ya kauda kai ya goge hawayensa cike da karfin gwiwa yace "dama baku taba kaunar husnah ba,dukkanku babu wanda yake kaunarta tana zaunene a cikinku bakuda yadda zakuyi dani kunyi nasarar maidata duniyarsu kun kumayi rashina dan bazaku taba samuna a tare daku ba"ya mike tsaye yana binsu da wani irin kallo mai cike da kunar rai da takaici dik suna tsaye tsaye babu wanda yayi magana sai zuhraliyya dake kuka tace "tace yaya Abraham Dan allah kada katafi kabarmu ka dawo garemu"beko waigota ba ya fice tayi tsalle ya mike a tsararin samaniya Yana yawo cikin iska Yana kiran "HUSNAH!!!"sautin muryarsa ke amsawa a cikin daji tsautsaye nata shawagi yanabi dazuka masu ban tsoro yanabi cikin bishiyoyi Yana kiran sunanta baiji daga gareta ba yasan bata cikin wanan dajin yasan husnah ta koma duniyar mutane dole babu yadda yaso dik yadda yakaiga kin shiga bil'adama dole ya shiga ya nemi matarsa....
*****
yaseer na zaune gaban mota momy na zaune a baya yaseer suna hira jefi jefi da hafeez wanda gaba daya baya cikin hayyacinsa gudu kawai yakeyi akan titi hafeez ya bugi kafadarsa "Kai kana ganin titi kuwa kaga yadda kake gudu damu ko ka manta mun dauko momy ne"hafeez yadan take burkin motar ya rage gudun yace"wallahi hankalina ya koma kan yarinyar nan so nakeyi kawai mu isa inganta"
"idan tazo ba,in kuma batazoba haka zaka dauki na annabawa ka koma gida da wanan makauniyar soyayyar da kakeyi hafeez yama sunan yarinyar kace"tsaki hafeez yayi ya harari yaseer,dariya yaseer yayi cikin kaurara sunan yace"yauwa na tuna Asma'u"da sauri momy ta katse musu hirar ta hanyar sa baki "Asmau kace fa yaseer sunan budurwar hafeez Kenan kuma surukata? Allah sarki sunan husnarka Kenan yaseer"momy tayi maganar a raunane tace "zanso naga wanan Asmau taka ko takai yata kyau"hafeez yace "zaki ganta ummah koda yake kince Asibiti zamu saukeki ko?"momy tayi jimm kadan ta duba agogon wayarta tace "zazzabi ne yake dan damuna da ciwon Kai zan shiga ne abani magani a duba BP na,kuma inaso inje gidan Alhaji(kakansu husnah mahaifin daddy)yaseer najin haka tausayin momy ya kamasa yasan karar daddy zata kai a harabar Asibiti sukayi parking ta fito ta wuce,
hafeez ya gyara zama yace"wai abokina karka cemin daga auren muneeba ka mance da soyayyar yarinta ka mance da husnarka naga ko maganarta bakason yi husnar da kake yawo da hotonta kana kallo husnar da ka kwallafa rai akanta da tabbacin zata dawo tun bayanta"bata rai yaseer yayi kamar bai taba dariya ba mamaki da al'ajabi ya kashe hafeez yace"wai shin lafiyanka idan ka daina Sonta ka fada mana da bata rai in anyi maka maganarta wato muneeba ta kasheka da soyayya ka mance husnar da akace tare akai goyon cikinta dakai"daga masa hannu yaseer yayi ya tsuke fuskasa cike da takaici yace "dik waye ya baka wanan labarin na kanzon kurege kaima ka shiga sahunsu daddy kana maganar wata husbah da bansanta ba bantaba ganinta ba shi daddy ma har cewa yake an dauramun aure da ita kajifa"galala hafeez yayi Yana kallon yadda yaseer ke masifa kamar ya ari baki yaseer yace "to dik ta kare ku dainamun maganar wata husnah idan ma da ita nabarta sakinta zanyi dikda bansan da aureba an laq'anamun yau zan saketa zan samu dadddy in fada masa nasaketa"hafeez ya girgixa kai bece komiba ganin ran yaseer ya baci akan zancen husnah sai kawai ya dauko wayarsa ya jingina da jikin mota ya fito da hoton husnah yana kallo yana murmushi muneeba ce takira yaseer jiki na rawa ya dauki wayar ta narke masa daga can bangaren tace "sweet ka bude WhatsApp dinka na tura maka da sako"jiki na rawa ya kashe wayar ya kunna data yana budewa ya shiga contact dinta hotonta tsirara ta tura masa ta rubuta i miss you daga kasa nonuwana kaikayi sukeyi"ya sandare a zaune ya lumshe ido yana zooming hoton data turo masa yana kallo cike da shauki.....
momy na zaune gaban likita ya bude result din test dinta yace "baiwar Allsh shekararki nawa rabon da ki haihu dikda naga kedin ba wata babba bace"Gaban momy ya fadi tayi shiru likita ya sake mata tambaya tace "ummm shekara goma sha takwas "ya jinjina kai yace "Masha Allah congratulations a gwajin da akai miki ya nuna kinada shigar ciki na sati tara"zaro ido momy tayi cike da mamaki ta kasa gasgata abinda likita ya fada kallonsa kawai takeyi saida ya sake magana tace "likita kodai Baka auna daidai ba ciki fa kace?"..
"ehh ciki gareki ko kina ganin kinyi girma da haihuwa?"ta girgiza Kai wasu hawayen farin ciki suka zubo mata ana gab da tozartata sai Allah bai tozartata ba rashin husnah shekara sha takwas kenan yau Allah yayi mata babbar kyauta ta goge hawayen farin ciki ta karbi result din tayi godiya ta anshi magungunan da aka rubuta mata ta fita ta siya ta wuce da sauri cike da farin ciki saidai kasan zucuyarta ciwon abinda daddy ke shirin yi takeyi ta nufi sashin da suka ajiye mota tayi sallama ta shiga hafeez ya tada motar yace'momy amma idan mun kaiki can ajiyeki zamuyi ko?"tace "ehh ku ajiyeni ku tafi abinku kawai"hafeez farin ciki ya lullubesa ya tada motar momy kwantar da kai tayi a jikin mota ta lumshe ido tana tunanin yau itace dauke da ciki.....
******
husnah kamar zararriya haka take tafiya tana waige waige cikin mutane saidai ta kasa barin wajen gani takeyi kamar narjisu zatazo ta tafi da ita shawagi takeyi wani mutumi ya tsaya Yana kallonta yace "kai Allah yayi halitta a nan wajen amma saidai ba hankali mahaukaciya ce"ta matso kusa dashi jin yana hausa yasa cikin farin ciki tace "mijina nake nema Abraham "
"mijinki kuma ni ta ina zan san wani mijinki Abraham bansanshiba kije ki nemeshi kawai ina tafiya kicemun mijinki"ta tsaya tana binsa da kallo ta koma wajen da suke tsayuwa ta tsaya Rana ke dukanta bakinta ya bushe da kishin ruwa saidai miyaun bakinta daci yakeyi mata sakamakon tashin hankalin da take ciki na rashin Abraham a tare da ita idan har baizo garetaba tasan tata takare tasan mutuwa zatayi ta durkushe a Kasa ta hada kanta da gwiwa tana rizgar kuka dik wanda zai wuce sai ya kalleta ya wuce fuskarta ta tura a cikin kafafuwanta ta hada kwi da gwiwarta,
tun daga nesa hafeez yake fadin "gata can wallahi itace"wani burki yaja wanda saida yaseer yaji tsoro momy ta zabura tace "wacece au biyowa kayi dani ta wajen budurwarka ja'irin yaro kawai?"ficewa yayi kawai ya nufi wajenta bda sassarfa yadda yaga ta hada kai da gwiwa ya tsaya akanta yana sauraron sautin kukanta tana fadin "Abraham.... Abraham"shine abinda take Fadi hafeez yayi turus tabbas wanan itace dan muryarta ce jijiyoyin kansa ne suka fiti sukai Rudu rudu idanuwansa sukai jajir bugun zuciyarsa ne ya tsananta jin alamar mutum a tare da ita tayi saurin yunkurawa zata rikesa da sauri taja da baya ganin bashi bane yace "Lafiya Asma'u?"ta share hawayenta tace "Dan Allah Ka taimakeni mijina nake nema"
"mijinki?"yace gabansa na tsananin faduwa Kenan dik wanan kamuwar da yayi da tsananin kaunarta dama matar aurece?......ta jinjina masa kai tace "ehh mijina mijina nake nema mijina dam jinsin jinnn"tace batare da wata damuwa ba dan batasan meye jinn ba ja da baya hafeez yayi cike da rudani da tashin hankali....
Abraham kuwa yawo yakeyi babu wanda ke ganinsa saidai a suffarsa ta mijin husnah yake yawo a yadda take ganinsa kyakkyawan matashi mai kirar yan shekara talatin da biyar gabaki daya ya sare sai yaji bugun zuciyarsa ya tsananta muryarta yaji tana fadin "mijina nake nema"waige waige ya shigayi ya kwala mata kira "husnah"......da karfi kamar daga sama ta jiyo muryarsa ya zabura tana waige waige hafeez addua yayi cikin zucuyarsa yace tabbas "akwai matsala".....
momy tace "yaseer kodai zaka tafi wajen hafeez ne kagansa can tsaye da wata yarinya kamar bafullatana anya ba matsala a wajencan kalli yadda aka taru ana kallo yaseer ya daga kai yace "shirmen banza ne irin na hafeex ya kamu da son yarinya baisan wacece ba momy gashi can yanzun an baibayesu kamar wasu mahaukata"a fusace ya bude motar ya fita momy tayi shiru sanan ta bude motar saidai gabanta ya tsananta faduwa ta nufi wajen.....
*DIK WANDA YA KARANTA MUN NOVEL BAI BIYABA DA HAKKINA KUSANI ZAKU BIYANI A INDA BABU MASU TURO ALERT IRI DAYA MA KU CIGABA DA SANNU ZAMUYITA CAFKEKU*
*NOTE* FREE PAGES SUN KARE KO ZAN KARA MUKU ZANBAKU