Showing 60001 words to 63000 words out of 130717 words

Chapter 21 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

198

yasa momy ta zabura hajiya saude da yan matanta suka mike dukkansu momy tace "kinga abinda nake fada miki ko?gata can zata daukar mun magana"suka nufi kitchen din husnah ke shekewa da dariya tana nuna hajiya rabi Abraham na tayata jin wata irin dariya yasa duk suka tsorata nan husnah tayi gumm ta dauki abinci ta kifta masa ido ya fice hajiya rabi tabi inuwarsa da kallo ta kwarma ihu tana kuka daddy ne ya fito daga sashensa cikin sauri sanye da jallabiya "lafiya hajiya menene haka?"ya kalli momy yace "zainab lafiya me akayi mata"Yana kokarin rukota juyawa tayi tana kokarin kai hannunta ta janye maganin bata ganiba wani miyau ta hadiye ta fashe da kuka tace "daddy bazan taba iya zaman gidan nan ba bazai yuwuba rayuwa da aljanu?yanzun na shigo kitchen in zuba abinci kawai naci karo da aljani"suka hada baki wajen fadin "Aljani?"ta jinjina kai daddy dik ya rude yace "aljanin waye to "hajiya rabi ta Kara narkewa jikinsa dikda fitsarin dake jikinta cikin kuka tace "aljanin husnah shima yazo dibar abinci nagansa sai gata tazo nan ta tasani tana zubamun shegantaka bazan iya ba bazan iya rayuwa da jinnu ba"ta rushe da kuka ta runtse idanuwanta tana fad'in "gashi nan gashi nan"daddy ya kara rungumeta hajiya saude tayi mata wani kallo tace "kodai akwai abinda kike shirin kullawa hakan ya faru?"damm gaban hajiya rabi ya fadi da sauri ta bude ido tana kallonta ido cikin ido ta dafe kirji tace "ni kuma mai zan kulla ni rabi sharri zakuyimun dama bakuson zamana cikin gidan nan nasani dukkanku bakuson auren nan"daddy ya rungumeta cikin masifa da daga murya yace "ina husnah?bazan dauki wanan rashin mutuncin da cin fuska ba koba komi rabi uwarta ce babu wasu aljanu sai rashin mutunci data tsira cikin biyu zaayi daya dolene tabar gidan nan ko hajiya rabi tabar gidan nan indai har bazata daina wanan iskancin ba"daddy ya ruko hajiya rabi "muje muje"hajiya rabi dakyar take takawa tana manna kirjinta dana daddy, hajiya saude tace "Allah ya wadaran naka ya lalace"momy kuwa wucewa tayi kawai,

husnah na manne da Abraham yana dibo abinci yana bata cikin nishadi ta ture hannunta tace"Bana ganin lokacin da kakeci gani kawai nakeyi kana kaiwa bakinka lomar karshen nan kuwa kai zakaci"dariya yayi fararen hakoransa suka bayyana ta tsura masa ido yakai cokali baki kawai taga abincin ya bace ta zaro Ido baki bude ya dire cokalin kusa da nata a plate din momy a fusace ta Shiga dakin husnah yadda ta zabura ya tabbatarwa momy gaskiyar lamari tace "kinga abinda dai kika jawomin ko?kingani ko?"ta turo baki "nifa momy banyi mata komiba kinga plate abinci kawai na dibo"Momy kuwa mamakine ya kasheta ta kalli plate din ta kalli husnah tace"kedawa kikaci abincin?"husnah taga cokali biyu ta saci kallon Abraham bece komiba sai gira daya daga mata tace"ehh momy cokali biyu nakecin abincu dashi"momy tace "tou zo ki fita zo maza kafin in sassaba miki"ta mike tana turo baki ta wuce tana waigen Abraham ta fice momy ta rufo kofar

hajiya saude tace"idan lamarin nan bazai yuwuba zainab ni zan dauki yarinyar nan ta koma gidana zuwa kwana ukun da akace zaa maida auren kuma zanyi magana da yaseer akan ya shirya ya fara gyaran wancen sashin ma husnah tunda dama nan akace zasu zauna gidan dake jikin naku momy cike da gamsuwa ta jinnina kai hajiya saude suka fara shirin tafiyasukai sallama ta rakasu har waje...

******
muneeba cikin tsananin damuwa take meyasamu ummah takw kiranta ta sanar mata matsalar dake faruwa bata dauka ta mike tsaye ga tabarya a gefe magani kuma ya zube yaseer ne ta gani jingine jikin kofar bedroom ya harde hannuwa yana kallonta rawar jiki ta kamayi kallon tuhuma yakeyi mata yana kallon tabaryar tace"yaushe ka ahigo sam banji shigowarka ba har kadawo?"tana kallonsa yace "Mai wanan tabaryar takeyi a nan"ya nuna tabaryar da fuskarsa nan da nan ta zube tace "wallahi ina kwancene nakejin motsi cikin dakuin naga gilmawar bera tacan ina tsananin tsoronsa shine na dauko tabarya zan buge nakasa"ta shagwabe murya ajiyar zucuya yayi yace "ta ina beran yake?"ta nuna ya kalli wajen ya juyo "dakin nan dik tiles ne babu yadda zaayi bera ya iya shigowa kodai immergination kikayi"ya shafa gefen fuskarta ya janyota jikinsa ya kwantar da ita ya dauki tabaryar ya nufi kitchen ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah ya kubutar dani"ta dafe kirji yana dosar cikin kitchen din yaji bari ya tsaya jimm to waye a kitchen din dake bari?ya tambayi kansa a hankali ya shiga Abraham na ganin haka ya rufe kofar kitchen din yaseer gani yayi kofar ta rufe take ya fahimci ko waye murmushi yayi yace "ka biyoni ne ka rama abinda nayi maka?"kamar daga sama yaga mutum a gabansa saidai baya tantancewa tsakanin mutum ne ko inuwa yaseer yace"meya shigo dakai nan saahen nawa?"baiyi aune ba yaji hannu a wuyansa an shakuresa yar kara yaseer yayi numfashinsa na hawa da sauka yana kai hannunsa ya kasa rikesa cikin murya kakkausa yace"ka fita hanyar husnah ko in kasheka"idanuwan yaseer sun firfito waje sunyi ja duhu yake gani cikin ikon Allah a bakinsa yake ambatar sunan Allah cikin hukuncin ubangiji take taji harshensa na karanto masa ayatul kyrsiyyu ganin haka Abraham yayi saurin sakin yaseer ya hankadasa ya bugu da jikin bangon kichen din kasa ya bugu ya fadi kasa yana kokarin tofa masa addua ya bace Abraham yasa hannu ya shafi kansa cikin ciwo yace "ahhhshhh wayyoo Allah"yana sauke numfashi ya fito parlor a wahalce ya zauna gani yayi ana wasa da jikin windown parlorn a bude a rufe ko gezau beyiba remote ya dauka ya shiga kokarin canja Tasha zuwa ta karatun alkurani ya kalli agogo magriba ta gabato yaji an kashe tv da karfin gaske ya girgiza kai ya mike zai shiga toilet nan ma yaji yana tafiya ana ingizasa bai fasa ba ya Shiga ya dauro alwala ya fito ya rufo kofar ya fice....

******
"ummah nifa wanan abun ya bani mamaki ummah ina cikin damuwa gashi dai aikin ya tabbata tunda ga ciki ya tabbata likita ya tabbatar mun"cikin damuwa muneeba keyiwa ummah magana tagumi hajiya rabi ta zabga tanayi tana waige waige cikin tsoro tace"ni yanzun tsoron yarinyar nan kawai nakeyi domin yau naga ishara ganin idona Allah ne ya kwaceni hannun aljani,abin jin dadin ma shine yanzun Alhaji ya tabbatar mun dole husnah zatabar gidan nan kuma naji saude tana maganar dauketa daga nan kinga shikenan inta bar gidan nan sauran aikin ninasan yadda zamuyi"cikin sanyin jiki muneeba ta jibgina da jikin gado tace"ummah kina ganin yanzun fa yaseer hankalinsa ya fara komawa kanta abu daya yasa yake kula dani cikin nan dake jikina"ummah ta jinjina kai cikin jimami jin motsin zaa shigo yasa sukai shiru daddy ne ya shigo daga masallaci muneeba ta mike daddy yace "yadai ya jikin naki muneeba"

"da sauki Daddy naji sauki zan koma sashena ne"ta fice babu karfi jikinta ta fito momy da husnah ne a kan dadduma ta tasa husnah gaba tayi sallah ta mike ta cire hijab ta nufi kitchen da sauri waige waige takeyi cikin saa taga ruwan zafi a kan gas an kashe ta diba ta fito Abraham tagani tsaye "mai kakeyi a nan"ruko kwankwasonta yayi yace "naga kuna addua ne kinga in kina adduar nan babu yadda zaayi in shigo "tayi jimm kadan tace"zan rama maka abinda wancen yayi maka ne"ta kalli jajayen idonsa yaseer ta hanga yana kokarin shigowa gate din gidan cikin sauri ta karasa momy ganin husnah ta fita tabi bayanta yaseer na juyowa tana antaya masa ruwa a kafadarsa wani azaba da radadi yaji yana ratsasa ya daga kai yaga waye husnah ya gani tsaye tace "bansoba fuskarka naso in watsawa yadda ka konawa Abraham dina fuska"Abraham na tsaye tana juyowa taga yana mata tafi murmushi yayi ya fuzgota jikinsa yace "ai ban koneba koda na Kone ni zan warke amma shi bazai warkeba"kici kicin kwacewa daga jikinsa takeyi momy ganin haka kawai ta juya tabarsu anan cikin tashin hankaki ta nufi cikin gida husnah ta kona yaseer a jikinsa da ruwan zafi? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ta wuce ciki
.tsamm ya riketa yana addua Yana tofa mata tana kokarin kwacewa "ni ni kadaina watsamun miyau"Abraham ya dumfari yaseer gadan gadan ganin wuta na fita a bakin yaserr ya koma baya yana huci tabbas yasan bazai taba sukuni da husnah ba tunda wanan na gidan wata dabara ta fadowa Abraham cikin fushi yabar wajen yana fita ya rikida ya koma yaseer sak ya nufi gidan momyn yaseer cike da kwarin gwiwa kawai zaije yasameta husnah ta dawo gidanta yadda zai samu damar soyewa da husnarsa batare da kowa ya Gane bashi bane,

cikin karfin hali ta funcike ta barsa nan tana hararsa "karka sake tabani"dariya tabashi ma yasan kila ba ita bace ya taba kafadarsa dake masa zugi ya nufi sashensa yau ma kamar jiya ya ganta a gaban sashen sa tayi masa murmushi wanan karon yaseer ya mayar mata batare da wani tsoro ba yace "narjisu ko?"ta jinjina masa kai tacev"katafi gidan mahaifiyarka yanzun nan kasameta dikda nasan Abraham ya rigaka zuwa"ta bace hankakinsa ya tashi mai aljanin nan yajeyi gidan mahaifiyarsa?shiru yayi tsaye ya laluba aljihun rigarsa yaji makulli kawai ya juya a hanyar fita yaci karo da hafeez da mahaifinsa da kuma kanin mahaifinsa daddy ya fito daga gida cikin faraa ya tarbesu

mari momy ta zabgawa husnah tana shiga ta fincikota husnah hankalinta ya tashi take taji wani yarrr tsoron mahaifiyarta ya shigeta taga bacin ranta karara a kwayar idonta tabbas tasan abinda tayi yasa momy ke fushi da ita dole zataje tabawa yaseer hakuri momy gani tayi husnah ta zube a kasa "momy kiyi hakuri bazan sake ba"cikin bacin rai momy tayi mata wani kallo ta barta nan ta dauko mp ta kunna karatun alkurani a dakin ta nemi waje ta zauna husnah cikin sanyin jiki ta mike ta shige daki ta fashe da kuka......


*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA BIYAV300 KACAL YA MALLAKI NASA WADDA TA KARANTA BATA BIYABA BANYAFEBA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻
26
ta jikin window kanwar yaseer taji shigowar mota gate din gidan tad'an leka lokacin hajiya saude na zaune tana lalubar number a wayarta ta d'ago kai tace "yusrah banason gulma karar mota ne baki taba ji ba ko yaya?"yusrah ta koma ta zauna cikin damuwa tace "momy yayah yaseer ne yazo fa?"da sauri momy ta kalleta tace"yaseer kuma?menene yazo dashi nan gidan bayan yanzun muka baro gidan toko wata matsala ta faru tsakaninsa da husnah ne ko jikin nata ne?"cikin faduwar gaba momy ta gimtse maganarta tozali da tayi da yaseer wani yarrr taji ganin tsayuwar da yayi tana binsa da kallo yaseer baya wanan tsayuwar Abraham ganin kallon da momy keyi masa karta gane ba yaseer bane yasa ya Tako cikin dakin tabi kafarsa da kallo takalmi mai rufi ne yasa tabbas kayan dake jikinsa ne amma kamar ba yaseer ba ya zauna ya dafe kai cikin yanayi na damuwa Momy tace "yadai yaseer naganka a yamutse a hargitse Kamar ba kai ba ni jinakeyi ma kamar kaima aljanun na neman shafarka"Abraham ya shafa kansa ya saita natsuwarsa da zuciyarsa dake tafarfasa yace"momy ba dole ki ganni cikin wanan yanayin ba?kina gani fa abinda ke faruwa yanzun husnah ta konani da ruwan zafi"momy tw zaro ido tace"ruwan zafi fa kace?"ya jiniina mata kai ya nuna masa kafadarsa daidai inda husnah ta kona yaseer rigar a jike momy tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"Abraham yayi murmushi ya hade rai yace"ni momy gaskiya so nakeyi husnah ta dawo gidan nan da zama kawai inaga zaifi idan yaso zan rinka zuwa nan ina jan raayinta har insamu ta dawo hayyacinta tunda kinga gashi zaa maida aurenmu kuma can momy bata wani kula da ita"hajiya saude ta jinjina kai cike da gamsuwa tace "tabbas munyi wanan maganar da ita ban sanar maka bane tukunna sai gobe munyi shawara dasu innah akan maganar amma tunda haka ne ni zan daukota in dawo da ita nan inga ta inda aljanin nan zai rinka shigowa dan kwana zatayi da karatu. kurani"Abraham ya cije lebe ya kalli yusrah data tsura masa ido tun shigowarsa take kallon yanayinsa gabanta na faduwa suna hada ido ta sadda kanta kasa yaji alamun kamar ta fahimci ba yaseer bane ganin kallon da yayi mata ta shagwabe masa "yaya yaseer ni tunda ka shigo ma baka wani kulamu ba nida nusrah"Ajiyar zuciya ya sauke "bana cikin hayyacina ne shiyasa gaba daya cikin damuwa nake yanzun zan tashi in koma"momy ta jinjina kai tace"ya mai jikin?"yana kokarin mikewa yace"da sauki nabarota zataci Abinci zanbkoma Dan Allah momy ki taimakeni ki dawomin da husnah nan"ya marairaice momy tayi dariya tace"mara kunya kawai"ya dagawa nusrah hannu tana daddana waya yace"saida safe Antyn waya"murnushi tayi masa ya daga musu hannu momy ta sauke ajiyar zucuya tace"ni dama nayi tunanin hakan sam ban son zaman husnah can gara ta dawo nan,

yaseer kuwa motarsa ce ta tsaya yana kokarin gyarawa cikin rud'ani yake da tsananin tsoro yana kaiwa da komowa a bakin titi babu kowa ga gari ya soma duhu ya ciro wayarsa yayi dialling wayar momy yaji ko lafiya akace masa yaje gidan momy yana tsaye irin motarsa sak tayi parking a gabansa yabi motar da kallo yana sauraren yaga waye da irin motarsa yazo har inda yaje Abraham ne ya fito da irin kayan jikinsa sak kamanninsa sak wani furgici yaseer ya shiga yana kallonsa cikin duhu ido waje cikin tsananin tsoro yace"kai wannene?"wata dariya Abraham yayi yace "badai bakajin magana ba zakaja dani ko? to mu zuba mu cigaba da fafatawa naje na aiwatar da nufi na, wanan motar da kake gani dama ka barta a nan dan bazata gyaru ba kwata kwata"ya kyalkyale da dariya yana nuna yaseer da tuni gumi ya jikasa "Mai mai kaje ka aikata karka kashemun iyaye karka kuskura zan kasheka"Abraham yana dariya yana nuna yaseer dake karamar hauka ya bace tare da motar tasa yaseer ya bugi jikin motar gumi ya karyo masa ya rasa inda zaisa kansa kaiwa da komowa kawai yakeyi yana juyowa yaganta a gabansa suna hada ido kafin yayi magana batace komiba ta wuce inda ya bude murfin motar tana kallon motar cikin duhu wani haske blue na fitowa daga idanuwanta narjisu ta dubesa tace"zaka iya shiga katafi dikda kayi latti"ta bace yace "narji....."kafin yayi magana ta bace ya dafe kansa meyasa bata tsayawa saurarensa tana tsaye a gabansa murmushi tayi ta harde hannuwanta ganin yana kokarin fadawa kogin tunani ga tsananin tsoro a tare dashi yasa tayi gyaran murya take ya dawo hayyacinsa yana waige waige ya rufe murfin motar ya shiga cikin ikon Allah yana tada motar ta tashi ajiyar zuciya yayi yadau hanya dikda akwai nisa tsakanin su amma ko ganin gabansa bayayi....

******
cikin kissa hajiya rabi ta hada tray da drinks bayan daddy ya shigarda magabatan hafeez cikin babban parlonsa na baki Abraham ne ya shiga yana binsu da kallo ya harde hannuwansa a kirjinsa hafeez ya daga kai kenan yayi tozali da inuwar mutum a gabansa ya juya ya kalli mahaifinsa yaga alamar basu ganiba ya jinjina kai ya maida dubansa garesa wato aljanin husnah ne yazo ya bata masa show kenan?daddy ya shigo da tray hajiya rabi sanye da gyale ta dire na hannunta tace"ina yininku"cikin kulawa daddyn hafeez ya amsa ta fice daddy yace"sannunku nabarku zaman jira ko?kuyi hakuri ga ruwan sanyi kusha Na kira makocina Alhaji sidi gashi nan shigowa "yana rufe baki amininsa kuma makocinsa Alhaji sidi ya shigo da sallamarsa ya mika musu hannuwa suka gaisa yace"barkanku da zuwa"ya zauna gefen daddy,shima daddyn zama yayi yace"Bismillah kusha ruwa"hafeez gabansa ya tsananta faduwa yana kallin Abraham cikin inuwarsa ya gegi jikin daddy ya zauna wani miyau ya hadiye makwat uncle dinsa Na lura da yanayinsa yace"yadai Hafeez?"girgiza kai hafeez yayi daddy yace"tou Mashaa Allah ya kamata mufara gabatar da abinda mukazoyi hafeez ina takardar sakin da yaseer ya rubuta kace zaka kawo ka tsinta a gidan nan?"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi yana kallon daddy ya sunkuyar da kansa yace"Daddy wallahi na duba takardar nan ban gantaba saidai inada tabbaci akan ya rubuta ina zargin ta shiga cikin takardun office dina"daddy yayi jimm ya jinjina kai yace"nima inada tabbacin hakan dan hajiya rabi ta fadamun"

"Tou Alhamdulillah Alhaji badamasi kadai san abinda ya kawo mu ko?munzo ne akan neman izinin Auren yarka husnah ma yaronmu hafeez gashi yace ka bada damar muzo dan yanzun haka da sadakin mu ma mukazo idan har ka amince ka yanke zamu biya"cewar kawun hafeez

kan daddy ya sara masa take yaga DUHU kamar kiftawar ido ya koma daidai yayi murmushi Abraham ya fito da wani abu daga idonsa ya Shiga jikinsa yace "Ayya aini yanzun na fahimcu komi nadawo hayyacina akan maganar taku dama naso hafeez ya kawomin takardar sakin husnah ne amma be kawoba kuma gaskiya akwai auren aljani atare da husnah yanzun kuma tanason mijinta"a tare hafeez da uncle dinsa da daddy suka kalli Alhaji badamasi,aminin Alhaji badamasi Alhaji sidi yace"badamasi kasan mai kake fada kuwa kodai kafara jin bacci ne?auren aljani fa kace?"ya jinjina musu kai fuskarsa a daure yace"kwarai dagaske aljani take aure Kuma bazan iya rabasu ba tunda sunason juna dan haka hafeez ya hakura da wanan aure dan bazan bashiba"

hafeez ya mike idanuwansa a rufe yana kallon inuwar Abraham yana murmushi Yana nunasa da yatsa yace"karya kakeyi wallahi ba yin kan daddy bane daddy da kansa ya bani husnah gashinan ina ganinsa a kusa da daddy aljani ne gashi nan shine ke shafar daddy"hafeez cikin zafin nama Yana kokarin kaiwa Abraham duka ya bugi bango hannunsa ya fashe take jini ya soma zuba mikewa daddyn hafeez yayi cikin rikicewa yake fad'in "kagani ko kagani meye haka kai kasamu tabin hankali ne?"uncle din hafeez ya rukosa Alhaji sidi a tsorace yake waige waige daddy kalle kalle ya somayi yaba kallon hafeez yana kallon mutanen wajen,ran daddyn hafeez ya baci kasa magana yayi ya fizgo hafeez ya wanka masa mari ya dafe gefen fuskarsa ya juyo ya sake sharara masa mari yace "wuce mutafi wuce kafin a illatamin kai dama kasan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login