Showing 99001 words to 102000 words out of 130717 words

Chapter 34 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

182

soma karanto ayatul kursiyyu da karfi yana kallon ko wani bangare na gidan yana karantawa gidan ya soma juya masa kici kicin kwace turaren maganin dake hannunsa akeyi cikin azama ya kwace hannunsa ya tofawa sashen dayaji an rike hannunsa ayatul kursiyyu da sauri aka saki had'e da tsaki idanuwansa jajir ya nufi kofar shiga sashenta da sauri yaja da baya ganin kayan da suka baro a gidan momy ajiye a wajen ya leka cikin ledar kirjinsa na harbawa yaga tabbas kayan ne daga bayansa yaji ance "kayan da kuka bari can ne natahowa da matata shi babu wanda ya isa ya rabani da matata"yaseer ya jinjina kai cike da jarumta ya shiga parlorn komi ya tsaru a cikin gidan sosai dakin yayi masa kyau karatun kurani yaji yasa yayi ajiyar zuciya kila dalilin dayasa baa shiga da kayan ba kenan ya mike kawai ya fito kicibis yayi da mutum agabansa ya daga ido Abraham ya gani tsaye a gabansa cikin suffar daya saba ganinsa saidai jikinsa a kokkone yaseer ya hadiyi wani miyau mai kauri yaceb"mekazoyi nan?kunar taka harta warke kazo ka kara samun wata?"jinjina masa kai yayi yace "bata warke ba kuma bazan bari ta warke ba bazan taba iya nisantar husnah ba"yaseer bece masa komiba ya gifta kamar zai wuce ya karanto adduoi ya tofa masa take ya bace ya rufo gidan ganin kaskon turaren a gefe ya fadi ya fashe ya rufo gidan ya fito da sauri ya nufi cikin gida,

tana zaune cikin mutane ana hira ya shigo "yaserr ina kaskon kasamu saka turaren kuwa?"ya girgiza kai "ah ah bansamuba saidai na tarar da kayan da muka baro gidan Momy an kawo sanan wanan aljanin ya fitomin yanzun haka munyi artabu dashi kamar ma yanzun bashi kadai bane"cikin damuwa yakeyin magana momy tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ni saude wace irin masifa ce wanan?daga wanan sai wanan aljanu kamar ibilisai?"ta dafe kanta ummah hadiza ta yunkura ta mike "bani maganin"tace cikin dakewa,ya mika mata maganin a sanyaye tace "Bari naje nasaka yanzun zan dawo"yusrah da nusrah sukai tsuru tsuru cike da tsoro ummah hadiza ta fice momyn husnah kuwa dafe kai kawai tayi cike da damuwa ta dago a zabure tace "husnah ina maganin dana baki kisha yanzun?"yaserr ya kalli momy wato dai sun dage sai husnah tasha maganin nan?husnah ta dauki kofin a sanyaye "gashi nan"ta nunawa momy ta kallu yaseer taga ransa a bace kasa sha tayi batason bacin ransa musamman yadda ya kafeta da ido hajiya saude ta saci kallom yaseer ta taso Kamar zata fita ta ruko husnah ta karbi kofin "oya shanyeshi maza maza kafin ranki ya baci wato bazakisha ba saboda mijinki ko?"haka husnah ta kwalkwale ruwan maganin sauran momy ta zuba a hannunta ta shafe fuskarta dashi aiko husnah na gamasha wani jiri ya soma daukarta dakin taga yana juyawa ta mike tsaye ta dafe kanta tana binsu da kallo tayi kasa ta yanke jiki zata fadi momy ta rukota da sauri yaseer jikinsa har rawa yakeyi "kingani ko momy kingani ko shiyasa banaso Tasha maganin nan ko kadam yanzun kinga abinda ya faru bakusan maganin menene ba ko maganin da zai kasheta ne ma oho"momy ta kalli yaseer a fusace "rufemun baki dalla can kishi ya rufe maka ido na tabbatar wanan maganin aiki zaiyi tunda har ta soma ganin jiri"hajiya hafsat kawai momyn husnah suka kama husnah a hankali suka shiga ciki da ita aka kwantar da ita momy ta bubbude windows din cikin dakin,

momy ta zauna gefen gado innah dake sallah,Allah Allah takeyi ta idar cike da jaraba tace "dom meyasa mijinta bayaso zaku bata magani?bakusan a hausance idan mijin mutum bayason Abu aka bashi sai wani abu ya samesa ba?yanzun gashi nan ai yarinya ta yanke jiki ta fadi "hajiya saude tadan canja fuska "haba innah don meyasa zakice haka?dan Allah kada ku camfi wanan maganin zata samu sauki"innah tace "tabbas wani abu yasamu jikata kabiru xan fadawa bazan yarda ba"ta koma gefe ta tankwashe kafa yaseer kuwa ya kawo wuya cikin tsananin bacin rai yake zuciyarsa ke ingizashi yaje yasamu hafeez yaji maganin menene wanan ya bada?ficewa yayi momy na kiransa be saurareta ba ya fice daga gidan,kicibis yayi da Anty sadiya "dama kai zanzo in sama Nace ko zaa kai muneeba asibiti jikin nata yaki gata can a daki amai kawai takeyi tacemun ko gani batayi saboda yadda kanta keyi mata ciwo"shock yaseer yayi a tsaye daidai nan ummah hadiza ta shigo da kaskon wutar tace "lafiya naganku tsaye a nan?"

"ummah muniba ce batada lafiya wai tana ciki amai takeyi da ciwon kai ko gani batayi"tabe baki ummah hadiza tayi tace"kissa dai"yasa kai ya nufi sashen muniba sadiya tayi dariyar mugunta tace "kissa ai bakuga komiba ma sai ya kasa angwancewa da matar aljan tukunna"tasa kai ta nufi sashen hajiya rabi...

ummah hadiza na shiga dukkansu suka zuba mata ido cike da mamaki kallonta sukeyi daga sama har kasa kowa na mamakin yadda taje ta dawo momy tace "hadiza kinsamu saka turaren kuwa?"jinjina kai tayi tace "nasamu sakawa mana naje inajin surutai a dakin amma haka nasaka,ina hanyar dawowa naga sadiya da yaseer"ta labarta musu abinda taji babu wanda yayi magana,

hajiya hafsat na tallabe da husnah idanuwanta a rufe ruff duhu take gani cikin sanyin jiki hajiya hafsat ke shafa kan husnah tace "husnah bude idonki kifadamun ya kikeji yanxun"ta bude idonta tangaras bata ganin komi ta dago fararen idonta tace "banajin komi"ta yunkura ta mike Abraham na cikin dakin yana tsaye gabanta ya kasa karasawa Kusa da ita gaba daya ta canja masa dik yadda yaso ta gansa bata ganinsa tsaye yayi yace "husnah yanzun kin zabi rabuwa dani akan ki zauna da wani kin karya alkawarin da kikamun kenan?"hannu tasa ta toshe kunnuwanta jin sautin wata murya a kunnenta hajiya saude ta shigo "yadai husnah"cikin tsoro da wani yanayi tace "momy wata murya nakeji wai na karya masa alkawari momy kuma ni bansanshiba"

"baki sanniba husnah?nine mijinki Abraham ni din ne baki sanniba?"ta zabura tana waige waige cikin tashin hankali tace "momy kinji Yana cewa wai bansanshiba shi mijina kinjifa nifa bansan wayeba momy tsoro nakeji ina yaya yaseer?"ta jefowa momy tambaya hannu momy ta daga sama tace "Alhamdulillah "suka kallu juna da hajiya hafsat sukai murmushi alamu sun nuna husnah bata ganin Abraham sabanin da sanan yadda take cikin damuwa ya tabbatar musu da maganin datasha ya batar mata dashi daga tunaninta tasamu mantuwa,

ummah hadiza tace "ku fito kuyi haramar rakamu nida diyata amarya da husnah kunga Garin yana had'a hadari kar ruwa ya tsareku,husnah tashi ga gyalenki"ta mika mata babu musu ta karba"Abraham yana tsaye wasu hawaye ke zuba a idanuwansa husnah bata ganinsa? muryarsa kawai takeji dik soyayyar da husnah keyi masa yanzun shikenan bata ganinsa jinsa takeyi shima ta mance dashi?ya bace daga dakin momy suna fita tayi sujadar godiyar Allah yanzun shikenan husnah yau zata tare da yaseer?abinda suka dade suna jira?ta shige dakinta suna kokarin fita hajiya rabi ta shigo gidan harajan majaran kamar an korota suna rike da ita suna adduoi aka shiga da ita....

*****
muneeba ta makalkale yaseer cikin kissa da shagwaba kukan shagwaba take zuba masa dik yadda yaso ya zare jikinsa ya tafi taki barinsa satar kallonsa tayi ta kalli lemon data hada masa da kwayar da sukasa ciki "tin dazun nake cewa gashi kasha kaki ko dan yau amarya zata tare?"ta kwanta a kirjinsa gashin kanta ya hargitse tamkar mara lafiyar gaske "ba haka bane muneeba itama wadda kike maganar batada lafiya gatacan kwance kuma nazo wajenki kinamun korafi umm?yanzun kisha magani ko na kaiki asibiti"ta faki idonsa cike da shagwaba ta fizgo kansa ta hade bakinsu waje daya ransa ya baci sosai mutumin da beda lafiya yake wanan abubuwan ga halin da husnah ke ciki ya janye ta fashe da kuka hawaye biyu biyu ya kalleta yadda ya rame ves ce jikinta cikinta ya fito haihuwa kamar kanka fita yadda cikin yayi girma ya shiga share mata hawaye "ya isa ki daina kuka ina sonki banason abinda zai sameki ko kadan kinji?"ya gyada mata kai tasa hannu ta dauko glass cup din tayi narai narai da ido "yanzun ko abu na baka ma baka karba yaushe rabon da kaci wani abu nawa bayan da aljani naketa rayuwa bansaniba"yayi ajiyar zucuya yace "shikenan bari yanzun zansha kawo banason rigima inace idan nasha dai shikenan?"ta gyada masa kai ya karba yasha murmushin mugunta tayi ya shanye tas ya dire cup din ya tsareta da ido tadan muskuta zata Tashi cikin yanayi na ciwo tace "washhh cikina"tana yarfa hannu "menene kuma cikin ne ko muje asibiti?"wani Abu yaserr yaji yana fuzgarsa kansa na juyawa biyu biyu yake gani nan da nan idanuwansa sukai jajir idonsa har rufewa yakeyi tsananin yadda yake ganin jiri da bacci ya koma yw zauna yaraf,
ta dan gyara zama cike da kulawa tace "yadai?"yace "bacci nakeji sosai gashi na baro husnah"yana hamma yayi maganar ta miko masa pillow "akwai mutane a tare da ita ina ganin kadam kwanta kafin su watse"ya jinjina kai ya karbi pillow yasa ta bayansa ya kwanta ko minti biyu beyiba bacci yeyi gaba dashi tayi murmushi ta mike tana kallomsa ta cije baki "badai rawar jiki kakeyi ba?zakaje ka angwance da matar aljani wadda kake tsananin so kana Wani rawar kafa sai kaje"ta ciro wayarta cike da farim ciki ta turawa Anty sadiya tex,

su innah a tare suka fito dasu hajiya saude motocinsu na wajen gate iska kawai ke kadawa hadari yayi bakinkirin ta dubi ummah hadiza tace "tou ga husnah nan kisa ido maganinta Dan Allah sanan wanda yake hannun mahaifiyarta kije ki karba ya koma hannunki dan alamu sun nuna zamuyi nasara inata kiram yaserr baya dauka fatana dai ba gidansu hafeez yaje ba dan ba hankali garesa ba zan kirasa daddare inja masa kunne"

"insha Allah zan kula da husnah kamar yadda zan kula da yar dana haifa ai husnah yata ce gaba da baya"sukai sallama dasu innah itada nusrah suna daga musu hannu nusrah cike take da kewar yar uwarta databi momy suka juya suka shiga cikin gidan,

husnah na daki taji kamar motsi a kitchen tadan sa kai ta leko tace "wanene?"shiru bataji kowa ba jim ana wasa da ruwa ta diro daga gadon ta shiga kitchen din inuwar mace tagani dishi dishi ta murza idonta ta bude bataga kowa ba ta waiga su ummah hadiza suka shigo"yadai husnah?me kikeyi a nan me kike bukata"

"motsi naji ummah hadiza shine na fito naga inuwar kamar mutum tsaye na karaso banga kowaba kingani"cike da tsoro take maganar idanuwanta suka cicciko da hawaye rukota ummah hadiza tayi zuwa daki "karkiji tsoro da kinji motsi kice hasbunallahu wabniimal wakeel"ta gyada mata kai tace "kidaina lekowa in kikai magana kikaji shiru,ta sunkuyar da kai tanaso ta tambayi ummah hadiza Yaser ta kasa cike take da kunya tunaninsa takeyi tun dazun tanaso ta gansa tsananin kwadayi takeji yazo ya siyo mata abu tarasa inda zatasa kanta kwantar da kanta tayi a pillow yana can tare da matarsa kenan?ta dago kai ta kwalawa nusrah kira da sauri ta shiga dakin taga husnah shabe shabe da hawaye tadan tsorata "lafiya kike kuka?"

"kiramun yayanki a abunda kike kiransa"dariya taba nusrah waya takeso tace tsananin shagwaba da yayi mata yawa nusrah na dialing wayar Yaser akace mata a kasge,

"nusrah ki zauna da husnah bari nashiga gidan can wajen zainab na karbo magani naga dare ya somayi magriba kar ruwan nan ya kece ko?"tace "toh"ta fice,

Cikim farin ciki sadiya ke labartawa hajiya rabi plan dinsu nasawa Yaser kwaya a abunsha hajiya rabi ta gyara tsayuwa tace "kai nayi matukar farim ciki kinga dik rawar duwawum nan da sukeyi nasan cewar yaseer a dakin muneeba zai kwana kinga nan zasu tabbatar bason renom aljanu yakeyi ba"suka sheke da dariya "wai Anty dazun ina kikaje?"

'umhmm gidan boka naje yanzun zam aiwatar da abinda ya bani ya tabbatarmum in zuba abin nan a cikin abincin hajiya zainab dana badamasi da sumci shikenan"suka sheke da dariya sadiya tayi kasa da murya tana dariya kasa kasa tace "shiyasa kike makale a kitchen?"ta jinjina kai ummah hadiza ta shigo jin taku da sallama daga gate sadiya ta fice tayi sashen hajiya rabi ita kuwa saurarawa tayi taji kamar ba nan bane ta wawwaiga babu kowa ta fito da maganin har ummah hadiza ta gifta ta dawo ta tsaya tsaye tana kallom hajiya rabi tana zuba magani,


Abraham ne ya sauya kamanninsa sak ya koma hafeez ya shigo gidan cike da kudirin karbar maganin da hafeez ya kawo sallama yake dokawa shiru ya dan tsaya yadda hafeez keyi daga window momy ta hango hafeez tayi saurin daukar hijab ta nufi hanyar fitowa.....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻
43
tsaye momy tayi tana kallon ummah hadiza da ta tsurawa hajiya rabi ido ganin inuwar mutum yasa ummah hadiza juyowa nuni tayi mata da tai shiru "shhh kiyi shiru karkice komi"tayi shiru ta had'iyi wani miyaun bakin ciki yau ta tabbatar da hajiya rabi asiri tayiwa daddy ummah hadiza ta tako a hankali ta karasa ta ruko hannun momy su shiga daki Momy ta yafito Abraham dake tsaye yana kallon komi tace "taho hafeez na ga shigowarka ai shiyasa ma nataho dakaina nace bari nazo barka da zuwa"a hankali ya tako ya shigo ya tsugunna har kasa "momy barka da yamma"ya sunkuyar da kai ummah hadiza ta tsaresa da ido haka kawai jikinta be bata ba yuwwww taji juwa na neman kadata ta jingina da jikin kujera,

"da magribar nan ga hadari hafeez ka kamo hanya ka taho?"ya jinjina kai yana wasa da makullin hannunsa yacev"momy dama akan maganin nan ne dana kawo nace bari inzo in karba ashe bana husnah nakawo ba na kanwata ne dama biyu na karbo maganin"

"toohhh hafeez gashi anbawa husnah hartasha kardai akwai matsala"ya jinjina kai ya dago kai yaja gauron numfashi ya sauke yace"babu momy kawo sauran maganin zan kawo natan?"tsare Abraham ummah hadiza dayi da ido tana karanto adduoi jin tsigar jikinta na tashi ta tabbatar akwai matsala tace "kai daga idonka ka kalleni"ummah hadiza tace cike da fada Abraham ya hadiyi wani miyau a ransa yace kardai matar nan ta gane niba mutum bane,,momyn husnah ta mike a sanyaye ta nufi bedroom dinta ummah hadiza ta tsaidata tace "zainab Ashe har yanzun da sauranki bakisan sharrin aljanuba ko?ai inda maganin nan bana husnah bane to take husnah bazata samu lafiya ba maana yadda ta daina ganin wanan shaidanin aljanin wanan da kike ganinsa ba hafeez bane aljanine"momy ta tsorata tana kallon ummah hadiza ta jinjina mata kai tace "tabbas Aljani ne?"momy kasa kallon inda Abraham ke zaune tayi ummah hadiza ta mike cikin azama tana kokarin karanto adduoi ganin haka bat Abraham ya bace ummah hadiza ta girgiza kai tace "shedani"

"tou waigo ki kalla"dakyar momy tayi ta maxa ta waigo ta kalli sashen daya zauna wayam bataga kowaba a wajen wata ajiyar zuciya ta sauke saidai a tsorace take matuka ta kasa ko motsi ummah hadiza ta mike jin ruwa na kokarin sauka tace "ina kika ajiye maganin?"momy tayi mata nuni har yanzun kafafuwanta rawa sukeyi data kalli wajen sai taga kamar Abraham na zaune ta wuceta ta dauko maganin tace "wanan yakin daya rage kece zakiyiwa kanki Kuma tunda kingani da idonki ana zuba muku magani a abinci idan akwai wanda baasa maganinba ki sauya ki ajiyewa mijinki gobe zansa akawomin wani magani da zaki amfani dashi akan alhaji badamasi nabarki lafiya "ummah hadiza ta fuce hawayene suka wanke fuskar momy lallai tayi bacci bayan yunkurin saka mata laya a baki yanzun gashi Ido da Ido tana gani ana barbade a abinci,ajiyar zuciya ta sauke ta kallu kular data zuba abinci a ciki iri daya ne abincin da wanda hajiya rabi ta zubawa magani ta dauka cikin sand'a ta fice ta nufi kitchen din harta zuba masa a kula ta juye abincin a leda ta ajiye gefe ta zuba nata ta gyara Kular ta fice....horn na motar daddy taji cikin sauri ta koma dakinta har yanzun cikin furgici take da Aljanin dayazo dazun ta shiga toilet ta dauro alwala anata kiraye kirayen sallahr magriba....

******
tagumi husnah tayi akan kujera two seater nusrah na zaune akan dadduma ta idar da sallah,ummah hadiza ta shigo da sallamarta "ah ah husnah ya naganki zaune kinyi tagumi?"tayi saurin kurkiro murmushi tace "bakomi ummah"

"tou Tashi maza kije kiyo alwala kizo kiyi sallah kema kin zauna kin tasata a gaba tana sallah ke kinyi tagumi ko kinada wata damuwa ne?"girgiza kai kawai tayi idonta cike da hawaye sam tarasa meke damunta wani irin kunci takeji a cikin ranta wanda batasam dalilinsa ba dakyar take taka kafarta ta shiga bedroom dinta ta jikin windown glass taga kamar mutum tsaye ta kurawa glass din ido taga yana budewa yana rufewa wata murya taji ana mata magana wani haske kamar walkiya daga jikin glass din ya taho ya nufo jikinta kafin tayi wani abu ya Shiga jikinta kasa shiga toilet din tayi ji tayi kawai bazatayi sallahr ba bataso ta nemi waje ta zauna "ina miki magana?bazaki kulani ba?"ta juya bataga kowa ba cike da damuwa tace "wai waye keson takurani ne?waye kemun magana"cikin kosawa tayi maganar tana waige waige ajiyar zuciya taji anyi hade da fad'in a sanyaye "husnah mijinki ne ina sonki husnah husnah ina sonki karki rabu dani gashi baki ganina yanzun nayi kokarin ki koma ganina abun ya faskara,amma inaso in kasamce dake karkiyi alwalar nan kinji?"wani abu taji yarrr yadda yayi maganar ya matukar bata tausayi dikda takasa tuno muryar da akeyi mata magana,ummah hadiza ce ta shigo hade da turo kofar ta zabura ganinta "husnah me kikeyi zaune gefen gado ke kadai?inace an hanaki zama ke daya anzo ana miki magana ko?"ta kalli window gani tayi ana hura window yana gaba yana baya yana fadin "karki fada"ta girgiza kai ummah hadiza ta cije lebe "baki sallahr ba kenan?"ta dago kai ta kalli ummah hadiza taga ta tsareta da wani kallo na tuhuma tsoro ya kamata ta girgiza kai "banyi ba ummah nashigo dakin kawai naji banaso inyi ummah kibarni Dam Allah"ruko hannunta ummah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login