Showing 3001 words to 6000 words out of 130717 words
da ya Abraham ne "shiko gaba yayi suka had'a ido da zabariyya ta kashe mata ido suka fice idanuwanta sukai jajir suka cicciko da hawaye tace "goggo kande kina ganin ya fita da ita bayan yasan yadda take sonsa idan nayi magana yace wai ai kanwarsa ce"hajiya babba dake bakin kofar shigowa ta karbe "saidai ki mutu husnah ya fita da ita kinaji kina gani zaa daura aurensa shida ita kuma bakida yadda zakiyi keda kikazo kika zame mana karfen kafa inda badan yana sonki bama me zaki zaunayi a cikin gidan nan?"hawaye ya wankewa husnah ido sam goggo kande hakan beyi mata dadi ba hajiya babba tace "fice daga daki zanyi magana da yar mijina sakarya kawai tsinacciya iyayenki na can sun mance dake kina nan"....damm gaban husnah ya fadi iyayenta kuma Abraham ya fad'a mata iyayenta sun mutu Kuma kannen mahaifinsa ne su meyasa hajiya babba ke jifanta da wad'anan furucin? ta goge hawaye inda sabo ta saba da maganganun hajiya babba wanda sam batasan me take nufi ba ta fito zuciyarta cunkushe da bakim ciki ta dade tsaye a harabar gidan sai shige da fice mutane keyi cikin gidan tunda ta taso bai taba fita da ita ko kofar gida ba har ya aureta idan kasuwa zasuje ma a cikin gidan kasuwar take gani kawai takeyi anacin kasuwanci tanaso ta fita taga yadda waje take a hankali ta soma taka kafafuwanta har ta iso babbar kofar gidan zata futa tasa hannu zata bude kofa taji wani abu yajata baya da karfin tsiya bata sake ganin kanta ko inaba sai a kofar shiga dakinta...waige waige ta shigayi cikin dakin aguje ta haye sama tana tsallake matakala.....
tana shiga dakinta taga komi ya canja bata ganin komi sai tsananin DUHU....
rufe idanuwanta tayi kamar mai bacci tana jiyo taku tayi lamo akan makeken gadonta kashe fitilar dakin akayi ta zabura ta zauna tana kalle kalle bataga kowa ba can taji an sake kunna wutar dakin rarraba ido takeyi sallama tajiyo a bakin matakalar hayowa sama ajiyar zuciya tayi tana fitowa tayi tozali da ita dariya tayi tana tsallake matakala da gudu taje ta rungumeta kawarta ce aminiyarta wadda tare suka taso tana auren aminin mijinta "barka da zuwa wanan ziyara ta bazata haka?"murmushi tayi tace "mijinki ya kirani yace inzo ya baroki kina fushi inzo in lallasheki kinsan kece ta gaban goshinsa tabe baki tayi tace "ashe yasan meyayi tunda ya fita da yar uwarsa kuma matarsa da yake shirin a aura masa ta biyu"jinjina kai tayi tace "zai aureta ne saboda iyayensa idan ya amince kenan bakiga ita da narjisu su suke sonsa ba amma Shi basa gabansa'tabe bakintayi ta zauna tace "kinsan meke damuna?"cikin wani irin yanayi na damuwa tace "tsoratar dani da akeyi cikin gidan nan hansa'u narasa menene mafita inda matsalar take",hansa'u tayi shiru tana wani tunani ta yaya zata sanar da ita gaskiyar lamarin?idan ta sanar da itama bazata byarda ba tunda haka ta taso batasan kanta ba ballantana husnah na ganin yanayin kawarta ya sauya sai tayi tunanin ai maganarta ta bata mata rai sai kawai ta canja musu hira.....
*****
zaune suke a parlorn gidan dukkansu a kasan carpet wani dattijo ne ke zaine a kujera yace "Yusuf bana aura maka yar uwar husnah bane dan na warware aurenka na husnah hasalima tunda aka haifi husnah na mallaka maka ita a matsayin matarka tun husnah na tsumman goyo na aura maka ita dan haka dik inda husnah take akwai aurenka akanta kuma idan ta dawo zata dawo a matsayin matarka idan allah yasa zamu gana da ita"Yasir ya sunkuyar da kai yana hawaye yace "daddy inaji a jikina husnah tanada rai babu abinda yasameta saidai tana wata duniya ta daban indai tana nan a raye dik inda take zan nemota in dawo da ita gareni dan da soyayyarta na rayu"Kishi ne ya turnuke muneeba wadda itace aka aurawa yaseer wadda ta kasance ya ga husnah yar kanin baban husnah ce tare ake rikesu sakamakom mahaifinta ya rasu dik gida daya suke....daddy ya kalli mahaifiyar husnah wadda tayi zugum yace "me zakice"ta girgiza kai ta mike tana kuka ta shige daki Yasir shima kukan yakeyi batan husnah ya dawo musu sabo yau shekara da shekaru tabe baki mahaifiyar muneeba tayi tace "Allah yayi muku albarka"daddy yace 'rike hannun matarka ka tafi"ya kalli muneeba sam baya sonta ko kadan bayajin d'igom kaunarta a cikin zuciyarsa husnah yakeso yana tunawa da yadda yake wasa da ita tana shekara biyu haka ya mike yana kallon dakin mahaifiyar husnah ji yakeyi kamar idan ya shiga zaiga husnah haka suka fice muneeba tasha lullubi suka nufi gidansu dake dayan bangaren cikin gidan babban family house ne....
*****
hadari ne ya hadu yayi bakinkirin hankalin husnah ya tashi tana cikin daki cikin tsananin tsoro zabariyya tayi nasarar shiga tsakaninsu tun kafin ya aureta ma kenan?dakin ne ya soma jujjiya mata yana gudu ya mike tajiya tsundum kamar a cikin kogi ruwa ya kawo mata wuya d'aga hannuwa takeyi tana neman taimakon tana ihu tana fad'in Abrahma!!!!!....zahraliyya ce ta shigo ta ganta cikin wanan yanayin tayi saurin riketa tana girgizata "anty husnah anty husnah"shiru babu alamar numfashi a guje abrahm ya shigo ya ciccibeta da sauri ya fita da ita iyayensa dik duka fito hajiya babba tace "ina zakaje da ita?"cakk ya tsaya ganin daddynsa a tsaye yana kallonsa yasan halinsa hakan yasa yace "zan fita in kaita asibiti ne"daddynsa yace "babu wani asibiti da zaka kaita narjisu ta fad'amun Komi akanta dan haka zan aura maka daya daga cikin narjisu da zabariyya zan raba aurenka da husnah tunda ba jinsinka bace.......husnah ta bude ido tana kalle kalle ta dire daga hannunsa furucin daddynsa ke yawo a kwakwalwarta ta yaya daddy zaice ita ba jinsin sa bace bayan Abrahm shine jini da tsokarta shine sanyin idaniyanta ta rayu da soyayyarsa?hawaye takeyi Abrahm ya harzuka yabi bayan daddynsa ita kuma zahraliyya ta riketa suka nufi sashenta da ita.....narjisu tayi murmushin mugunta tace da sannu zakibar gidan nan gaba daya ba rabuwa DA abrahm kadai ba.....
Abraham yace "daddy tayaya zan rabu da husnah bayan kasan irin soyayyar da nakeyi mata?"...daddy ya kallesa zaiyi magana Abrahm yace "husnah nadauke da cikina"....zabariyya dake tsaye tana saurare tare da adduar allah yasa daddy ya aura mata shi taji furucinsa zubewa tayi a kasa tana hawaye.....
******
yaseer na rike da hoton husnah tana yar shekara biyu tana rike a hannunsa wanda shi be wuce shekara sha uku ba suna dariya yana hawaye muneeba ta turo kofa yayi nisa a kallon wanan hoton yaji an fuzge hoton daga hannunsa iska ta fitar da hoton aguje yabi hoton da gudu ya fice muneeba taji wani kululun bakin ciki ya tsaya mata a mak'oshi tace "da sannu zan mantar dakai husnah ko ana ha maza ha mata......
*MASU BUKATAR SHIGA GROUP DAN MALLAKAR WANAN LITTAFIN SU BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN*
ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
3126584401
fiddausi musa
first bank
*SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO 07042277401*
*DOMIN TURA KATIN MTN TA WANAN NUMBER ππ»08036953516*....
*SLIMZY*
π *DUHU....*π
( *sark'akiya*)
Β©οΈHWA
*SLIMZY*βπ»
Wattpad slimzy33
Daga Marubuciyar:-
π¦ *K'ADANGARUWA*π¦
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA KARKU BARI A BARKU A BAYA BAYAN KADANGARUWA GA WATA SABUWA*
*DOMIN SHIGA WANAN TAFIYAR 300 NAIRA NORMAL GROUP VIP WADANDA ZAA TURA MUSU TA PRIVATE 1000*
*3126584401*
*FIDDAUSI MUSA*
*FIRST BANK*
*SHAIDAR BIYA 08036953516 KO KI TURA KATIN MTN TA NUMBER*
GA MASU BUKATAR A TALLATA MUSU HAJARSU SU TUNTUBENI TA WANAN NUMBER 07042277401
*3*
muneeba ta dafa kafad'ar yasir da yabi hoton husnah da kallo yadda hoton ya bace ba karamin razanashi yayi ba ya dubi muneeba yace "kina ganin hoton husnah ya bace kamar an figeshi a hannuna ya akayi haka?"tuhumarta yakeyi ya tsareta da ido sai kawai ta fashe masa da kuka ganin kukanta yasa jikinsa sanyi ya janyota ya rungumeta ya kamata zuwa yanzun ya mance da husnah amma babu yadda zaayi hakan ta kasance sakamakon husnah wani bangare ne na jikinsa rabonsa da ita tun suna yara dikda an daura masa aure da ita kila ta mutu gashi an aura masa yar uwarta ya rungumeta yace "is ok'ta share hawayenta ta kwanta a kirjinsa bugun zuciyarsa ya tsananta yadda hoton husnah ya bace a hannunsa kawai yake gani a idanuwansa abu kamar tsafi?muneebah kuwa tana karantarsa tsananin kishi ne ya cika mata zuciya tunanin yadda zata mantar dashi husnah takeyi amma tasan da taimakon mahaifiyarta da anty sadiya kanwar mahaifiyarta tasan zata samu mafita dole ma zuwa safiya ta shiga cikin gida garesu mikewa tayi ta zare jikinta daga nasa besaniba yayi nisa a duniyar tunanin husnah ga kansa dake sara masa....
******
tashi tayi ta zauna husnah tayi shiru tana bin dakin da kallo cikin tsoro da furgici gani tayi wata inuwa ta gufta cikin toilet dinta ta zabura zata gudu taga kofar ta rufe tayi yunkurin tura kofa amma ta kasa sai ta fashe da kuka wata irin murya ce mai ban tsoro tayi amsa kuwwa a cikin dakin ta kallu ko ina bataga kowa ba tasa hannu zata toshe kunnuwanta kawai taga bango ya tsage inuwar mace ta fito tace "tsoron meye kikeji?bayan kinyi nasarar auren masoyina baki da sauran zaman lafiya har sai Ranan da kika dauki kafarki kika barmin masoyina da duniyarmu"jikin husnah sai tsuma yakeyi kamar kiftawar ido taga ta bace ji tayi an bude kofar da sauri ta waiga Abraham ne ya Ganta a kid'ime yace"lafiya ya naganki haka meyafaru?"ya ajiye ledar daya shigo da ita gefen gado ya bude hannuwansa yace "taho ki fad'amun"ta shiga nuna jikin bangon da yake a tsage har lokacin tana fad'in ta nan ta shigo wata inuwa ce ta shigo ta nan wai masoyin....."bata karasa ba taji kanta ya sara mata ta dafe kai tace "aushhhhh Abrahm kaina"ya rungumota Yana fad'in "me tace inuwar wacece husnah bakowa kin tsorata ne bansan meyasa kikejin wanan tsoron ba"ta runtse idanuwanta ta bude ta saukesu a jikin bangon ganin komi tayi ya shafe bataga komi ba tayi shiru tanaso ta tuno abinda takeso ta fad'a masa ta kasa sai kawai tayi murmushi tace "share kawai,na mande Abraham meyafaru naganka cikin wani yanayi kaida daddy ko?"ta kyabe fuska cikin shagwaba tace "kayi hakuri kaji koma menene yanzun ka fad'amun"shiru yayi yana kallonta tausayinya da soyayyarta na ratsashi dik duniya babu wanda ya isa ya rabashi da husnah sai allah sanan bayajin dik azaba dik runtsi zai iyayi mata kishiya zai had'a soyayyarta data wata bayan tsananin soyayyarta yasa shine ya reneta da taimakon goggo kande,tace "kayi shiru"ya janyo ledar daya shigo da ita fresh milk ne da hollandia sai gasasshiyar kaza ya dage mata gira yace "abinda kikeso nayi miki tsaraba dan nasan na fita kina fushi Dani saboda na fita da zabariyya"ta turo baki tace"ai na manta gashi ka tunamin"yayi murmushi yace "kici wanan ina zuwa bari in dauko plate"ya mike ta janyo hollandia ta soma sha sakamakon yunwa da takeji tun fitarsa yana fitowa yayi karo da narjisu a jikin kofa tanayi masa lab'e ya daka mata tsawa yace "meye kikeso kikazo kika labe kina sauraren mu?"idanuwanta suka saura kala sukai jajir kamar jini tana kallonsa tace "au Akan husnah zakayimu. masifa akan husnah zaka wulakantani saboda kasan yadda nake tsananin kaunarka"nuna mata hanyar matakala yayi yace "zoki fice fita?"ya daka mata tsawa,jikinta na rawa take taka matakalar dakin tsawar da ya buga mata yasa ko ina na cikin d'akin ya amsa wani haske ne daga cikin idanuwansa ya fito jikinsa na karkarwa narjisu tana taka matakalar dakin tana hawaye ta fice ya juya kenan ya had'a ido da ita dammm gabanta ya fadi cikin kibtawar ido hasken dake idonsa ya dauke kamar walkiya tace "mijina kaga abinda nagani a cikin kwayar idanuwanka?"cikin yanayi na tsoro take maganar,murmushi ya kirkiro yace "Babu komi sai soyayyarki dake cikin kwayar idanuwana"murmushi shi tayi ya rukota zasu shiga ciki daga bayansa yaji an Kira sunansa da kakkausar murya,waye wanan mai gangancin kiran sunansa da kakkausar murya?ya juyo a fusace narjisu ce rike a hannun mahaifiyarta sai mahaifiyarsa da suka shigo tare yana kare musu kallo yadda narjisu take kuka kamar ya kasheta tace "banajin tsoronka dan wani karfi ko iko naka Abraham banajin tsoron dik abinda zakayi karka kuskura ka wulakantamun yarinya akan matarka wadda ta kasance ba ahalinmu ba matarka data kasance jinsin bil'adama kana matsayin jinsi na jinnnn"yadda tai maganar a kausashe yasa ya kalli husnah wadda ke tsaye kamar an dasata kallon da yayi mata ne yasa wani abu daga cikin idonsa ya fito ya shige kunnenta kallonsa takeyi cikin damuwa meyasa batajin abinda suke fad'a tasa hannu a kunnenta ta sosa ta sake kallon bakin mahaifiyar narjisu wadda har lokacin magana takeyi "Abraham kasani bazamusa Ido muna ganin kana wulakanta yan uwanka ahalinka ba akan wanan halittar"ta nuna husnah dake tsaye cikin bacin rai Abraham yake kallonta yasa hannunsa a kwankwasonsa ta cigaba da magana "kaine silar dalilin dayada dukkanmu muka koma mutane a idanuwanta sakamakon kaunar da kake mata yasa mukai hakan sakamakon yadda mahaifinka ke matukar kaunarka to wallahi zamusa kafar wando daya dakai akan wanan tsintacciyar yarinyar idan kaki inada dama da karfin da zansa a cillata duniyarsu"zuwa lokacin idanuwansa sunyi jajir hikinsa sai tsattsafo da gumi yakeyi mahaifiyarsa na tsaye takasa magana ganin bacin rai a idanuwan Abraham tasan zai iya aikata komi akan husnah tuntuni yake kokarin dauketa su koma duniyar mutane amma bazata lamumcu ganinsa cikin wanan jinsin ba wanan yasa suka amince da bukatarsa,
muryarsa a kausashe tana amsa kuwwa a cikin wajen muryarsa ta asali ya saki yace "shine babban kuskuren da zakiyi a rayuwa rabani da husnah bazan duba dangantakar dake tsakanina dake ba zan azabtar dake dik wanda ya kuskura ya nunawa husnah wata duniyar ta daban bayan wanan da muke ciki zan wulakantasa zan masa azaba mai tsanani"narjisu na tsaye ta zube kasa tana kuka lallai Abraham mahaifiyarta yake fad'awa wanan maganar?lallai yayi babban kuskuren da koda zai rabata da ranta saita aikata masa abinda ciwo zai kamasa yasan shedanci irin nata,mahaifiyarta tace "mu zuba nidakai a cikin gidan nan sanan mu zuba zama da wanan yarinyar kaga yadda zata koma,zo muje"ta fuzgi hannun narjisu suka fice,
mahaifiyarsa ta kasa magana saboda yadda taga rayukansu duka sun baci,husnah na tsaye na kallon bakunansu kamar bebiya batajin me suke fada ko kadan mahaifiyarsa zatayi magana ya d'aga mata hannu tana kallon yadda kwayar idonsa ta sauya yadda cikin d'akin wata iska ke kad'wa tasan ransa yayi mummunan baci....tace "Abraham kayi hakuri zan kawo karshen wanan abun amma dan allah karka dauki matakin da zaka kassara rayuwata nasan kanason wanan jinsin fiye da yadda kake sonmu mu iyayenka"ruko husnah yayi yaga tana hawaye ya shafa gefen fuskarta tana fad'in Abraham banajinka banajin abubuwan da kuke fada kaidasu maama...banaji kwata kwata kunnuwana sun dod'e banaji ko kadan"ya waiga ya kalli mahaifiyarsa lokacin maamah tagane abinda yayi ta kad'a kai ta fice cike da damuwa,rungumeta yayi yana shafata yace"husnah meyasa bakiji yanzun bakijin abinda nake fad'a miki husnah ina sonki sosai banason abinda zai rabani dake"ta d'ago fuskarta jike da hawaye mamaki ya kasheta yadda taji abinda ya fad'a tace "inaji nasoma ji ina jinka yanzun....meyasa kake tunanin abinda zai rabani da kai?...ka manta kaine jinin dake yawo a jikina?dakai na rayu tun ina kankanuwata tun mutuwar iyayena bansan kowa ba sai kai dakai zan mutu dakai zan gama rayuwa bansan wata rayuwa ba face wadda ka d'orani akai bansan wata duniya face wanan duniyar da muke ciki nida kai da yan uwanmu"damm gabansa ya fad'i yana kallonta maganganunta na dukan kirjinsa tabbas yasan yayi nasara dan husnah batasan komiba batasan kowa ba face su batasan wata duniya ba balle ta babance tsakanin jinsin mutum dana aljan ba ta ruko hannuwansa "meyasa nake ganin damuwa a kwayar idanuwanka?"....ya girgiza kai ya ruko kanta ya had'e bakinsa da nata ya shiga tsotsar bakinta yaba yawo da hannuwansa a cikin jikinta yasa harshensa cikin kunnuwanta yana kad'wa nan da nan taji jikinta ya sake shi kawai take bukata saidai bai taba kusantarta ba ko sau d'aya gashi hans'au na bata labarin yadda auratayya take amma sam ita batasan haka ba haka yajata ya kaita d'aki ganin dare ya farayi ya cire mata kayan jikinta ya tsunduma wata duniyar babu inda Baya lasa a jikinta ta Mutu da tsananin soyayyarsa jikinta ya saki haka ya kyaleta ya rungumeta yaga sauke numfashi hannuwansa akan kirjinta yana wasa yaga bacci ya d'auketa mikewa yayi ya k'ara kallonta wani walkiya ta fito daga idanuwansa yasa mata nauyin bacci sosai bayaso yayi kuskuren da yayi jiya ta tashi baya ganshi a kusa da ita ga rikid'ewa yayi ya bace ya nufi can bishiyar da yake zuwa daddare....
******
shiryawa yayi tsaf tazo ta bayansa ta rungumesa tace "muje madubi ka kalli kanka"ya girgiza mata kai tace "wai meyasa bakason kallon madubi?"ya shafa gefen fuskarta yayi murmushi ya d'uka daidai kumatunta yayi kissing yace "saina dawo mai Zan siyo miki?"tace "komi ma kadawo da wuri kaji inaji. tsoro"ya gyada mata kai ya fita tayi ajiyar zuciya ta fad'a kan gadonta tanajin nishadi tuna yadda Abraham ya tafiyar da soyayyarsa takeyi wata irin shaawa taji ta taso mata ta runtse idanuwa tanajin sabuwar kaunarta a sassan jikinta......
cikin babban parlorn ya Shiga baiga kowa ba sai sautin muryoyinsu yakeji a d'akin mahaifinsa yadda suke cece kuce akan aurar masa da narjisu ko zabariyya yana Shiga sukai shiru Banda kanin mahaifinsa wabda ya kasance mahaifin narjisu ne yace "idan har bazaa aurar masa da jinsinsa ba to tabbas ya zama dole yarinyar nan ta matsa daga cikinmu dan munaji muna gani bazamu rinka ganin Abraham yana wulakanta yan uwansa akanta ba"... abraham ya tsugunna gaban mahaifinsa yace "barka da war haka"....d'aga masa kai da hannu yayi shaidar ya amsa zaiyi magana yace "ka shiryawa auren daya daga cikin yan uwanka ko duka biyun dan munajin ciwon auran wadda ba jinsinka ba"yana gama magana ya nuna