Showing 96001 words to 99000 words out of 130717 words

Chapter 33 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

186

ya kashe mata ido yayi mata alamar ta biyosa,momy na kallonsu ta gefen ido ganin ta noke masa kafada yasa ta girgiza kai "husnah kije daki ki dan huta saiki jira yaseer ya fito ko ?"ta cije baki batason yiwa momy musu cike da kunyq ta juya tabi bayansa suka shiga dakin a tare suna shiga ya rufe kofa ya cire rigarsa ya zauna gefen gado ta tsurawa jikinsa ido gashin jikinsa a kwakkwance saidai dik yadanji ciwo tausayinsa ya kamata ta karaso ta zauna ta bayansa ta kwanto ta rungumosa yasa hannu yana shafa kanta "yadai husnah?menene?"cikin siririyar murya tace "bakomi"yayi murmushi hade da gyaran murya"yau a gidanmu zamu kwana ko?"ta noke taki magana dariya yayi kawai cikin damuwa tace "inajin tsoro"da sauri ya juya ya janyota jikinsa ya rungumeta yana kallon fuskarta "umhmm tsoron me kikeji?"

"Abraham kagafa abinda ya samesa ina gudun ya dawo ramako"murmushi yayi mata ya shafa kanta yayi kissing lips dinta "babu abinda zaiyi miki kinji Allah na tare damu ko?"ya shafa kanta "muje muyi wanka tare"tana kauda kai tana dariya ya ciccibeta ya zare rigar dake jikinta yayi toilet da ita tana dukansa a kirji

*****
"muneeba girman wanan cikin naki nifa yana bani tsoro"cewar hajiya rabi tana kallon muneeba wadda ke zaune ta mimmike kafa a dakin hajiya rabi,
"ummah tsoro kuma kika sani ko yan biyu ne?"
gauron numfashi hajiya rabi ta sauke tace "tou ina fatan biyun ne inaso dai aje asibiti a tabbatar da zaman cikin nan inaso ki haifowa yaseer kyakkyawan saurayi mai kamadashi"
kasa da murya muneeba tayi "momy amma fa kinsan dai yadda aka samu cikin"

"shhhh yo ai ya tabbatar mana da d'an na yaseeer ne koda ya kasance shi ya kwanta dake ai yasa miki dan ne daga jikin yaseee"murmushin farin ciki muneeba tayi tana shafa cikinta.....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻41
rungume da husnah yaseer ya fito daga wanka ya kwantar da ita akan gado yace"karki taso ki jirani nine zam shiryaki da kaina kinji?"ta turo baki cike da shagwaba tana kokarin tashi yace"wai ba nace kada kitashi ba ki jirani nine nam zan shiryaki da kaina"husnah tayi murmushi ta koma ta kwanta ta lafe yana tsaye Gaban mirror ya shafa mai a wajen da turaren daya gani juyowa yayi yace "kigafa ba wani kaya gareni a nan ba"

"ga kaya nan kamar jallabiya naga an ajiye kam gado"kallon jallabiyar yayi hade da murmushi yace "momy kenan wanan jallabiyar tana ajiye da ita kenan gashi yau zan saka"ya dauka yasa tayi kuri tana kallonsa ta lula duniyar tunani,meyasa ta kasa daina tunaninsa?bayan har yanzun akwai soyayyarsa a zuciyarta?tunowa da yadda ta watsa masa ruwan magani tayi furgigit ta furgita ta tashi ta zauna kansa hayaki yakeyi yadda taga fuskarsa tayi hankalinta ya Tashi yana tsaye yana lura da yanayinta ya girgiza kai ya dauko man shafawa ya zare towel din daya nad'eta dashi tayi saurin kare kirjinta "ka rufeni nidai ka rufeni kunya nakeji'tace cike da Yanga yadda tayi da bakinta ya dauki hankalinsa yasa hannu ya cire hannunta daga kirjinta nonuwanta ya kalle dik sun tasa sun dan kumbura ya zaro ido waje yace"husnah?meyasameki?"da sauri ta bude ido tana kalle kalle ta kallesa bata ganeba yace "kalli yadda kirjinki suka cicciko suka kumbura"turo baki tayi ta kauda kai idonta suka ciko da hawaye "nima haka na gansu"ya jinjina kai zucuyarsa cike da furgici kardai aljanin nan yazo ya tattaba masa mata,tsaki yayi ya shafa mata man sanan ya dauko mai da akabata na magani ya shiga shafa mata take taji zucuyarta na Tashi warin turaren ya bugi hancinta ta soma yunkurin amai ya rukota "sannu sannu husnah sannu kinji menene meyasameki?"ta girgiza kai a wahale tace "amai nakeji amma ya kwanta"tausayinta ya kamasa kardai malaria ce ta kama husnah yasan akwai sauro kwanakin nan wardrobe ya bude ya ciro mata kaya ya mika mata ta karba tace "brezia ta"kauda kau yayi "bazakisa ba saboda dubi yadda suka kumbura haba meyasa zasuyimun hakan bayan yau zanyi wasa dasu"ta hararesa ta zura rigar ya kurawa yadda breast dinta suke a tsaitsaye kamar tasa brezia ya shagala da kallonta yaji knocking tsaki yayi "wanene?"

"momy tace ku shirya ku fito gaba daya ga malam yazo"ya girgiza kai ya rukota sai kafkaf yakeyi da husnah tana yatsina fuska ta yane kanta da gyalen abayar datasa suka fito fuskarta tayi wani iri momy ta tsareta da ido har suka shigo parlorn,

malam na rike da kan yusrah yana tofa mata addua a idonta suka zauna sai sambatu takeyi "yanzun malam zan daina ganinsa?"yusrah tace cikin damuwa,

"inshaaa Allahu zaki daina ganinsa dama bada nufi yaso kigansa ba kuma ba halittarsa gaba daya kika ganiba yanzun bude idonki kifadamun kina ganinsa?"a hankali yusrah ta bude idanuwanta da sukai jajir malam ya tsareta da ido "kina ganinsa?"

"bana ganinsa"tace tana girgiza kai,

"tou Alhamdulillah, hajiya yanzun abu nagaba shine yadda zaku tsaya ku jajirce musamman yaseer dan nasan tabbas wanan aljanin be tafi gaba daya ba zai dawo kuma dawowar da zaiyi bazaaji dadiba saidai idan har yaseer ya rike wuta sanan kamar yadda yayi alkawarin kashesa yadda kikace ya kashesa idan ba hakanba shi zai cika alkawari akansa dan yadda yakeson wanan yarinyar ko uwar data haifeta ce zai kashe "gaban momy ya fadi ta kalli yaseer cike da damuwa ta hadiyi wani miyau makwat...."yanzun malam menene abunyi"
yayi shiru ya sauke ajiyar zuciya yace "Abunyi guda daya shine su shiryawa daukar fansa yaseer kansa ya rinka amfani da magungunan husnah idan ba hakaba kuskure daya zaiyi asamu matsala tinda kinga yanzun ba tare zasu rinka wuni gida ba zai rinka shiga jikin yaseer yazo yana mata abubuwa wanda zai kawo matsala a auren"

yaseer jiki a sanyaye ya kalli husnah itama ta kallesa ta sunkuyar da kanta cike da takaici momynta dik ita ta jefata cikin wanan halin gashi ya fada da kansa sanan a zaman da tayi tare da momy ta fahimci yadda takeda mugun sakaci akan abubuwa hawaye suka cicciko a idonta idon yaseer na kanta yana kallom kirjinta gaba daya ya kasa sukuni daya kalleta yakejin wata shaawa na taso masa ya shagala wajen kallonta bemasan malam na masa magana ba saida momy ta daka masa tsawa "kai yaseer meye haka?ana magana kana kallon husnah kamar yau kafara ganinta kajimun iskancin banza"ya sunkuyar da kai yana sosa keya "amm momy banjiba"

"dama ina zakaji hankalinka nakan jar fata?tou yau nima na huta da rashin kunya wanan fitar da zamuyi zuwa can yau ake bikin tariyarku"wani farin ciki ya lullube yaseer sai faraa yakeyi malam ya basa wani magani yayi masa bayani tare da yin hayaki a gidan kafin husnah ta tare momy tayi masa godiya ya tafi suka mike a tare kallon kayan da Abraham ya siyawa husnah sukai suka fara kallon kallo momy ta dubi nusrah tace"daukar wanan kayan zakuyi muje waje a dire mai a bolar kan hanya nasan zai hadu da ita a can ya diba ya kaiwa budurwarsa aljana"nusrah saida ta guntse baki dariya ta taso mata tanata murmushi tana kallon momy "murnushi kikeyimun kenan?"ta girgiza kai "momy nifa bazan iya daukan wanan kayan ba nasani ko yana ciki ma"

momy tace "ohh anan zamu barshi kenan ko?yadda zaizo ya baje kolin sa a gidana ga kayansa to dauka zakuyi"nan aka soma muhawara husnah na tsaye gefe ta tako zata taba kayan yaseer ya fuzgota "ke kina hauka ne zaki taba kowa yaki tabawa ai ko kowa zai taba ke bazan bari kitaba ba"ransa a bace yake maganar ta sadda kanta kasa,

"ku mutafi abar kayan in zamu dawo zamu biya mutaho da malam nida yusrah sai yayi saukar alkurani a daga kayan"momy tayi gaba tana gyaran gyale yusrah a tsorace take har yabzun komi sanyi sanyi takeyi suka fita a tare suka rufo kofar shiga sashen tare suka dunguma a dayar motar yaseer dake gidan suka fice....

*****
innah ce da sauran kannen daddy suka sauka a gidan cikin farin ciki momy ta karbesu ba zata sukai mata dan batayi tunanin biki zayi karamin biki don tarewar husnah da yaseer ba,
"wai nikam har yanzun angon nawa bezo bane? inaso yazo ya zaba koni ko husnah ko mai waccen cikin kamar kwallo"ummah hadiza ta sheke da dariya tace "innah kenan so kike ki daukar mana magana ko kinsam cin mutuncin da rabi tasa mai gida yayi mun kuwa?"innah tadan ja da baya tana kallon ummah hadiza shekeke cike da son karin bayani ganin haka ummah hadiza ta gyara zama momy ta tabata ta girgiza mata kai alamar kada ta fada ta kauda kai "kyaleni zainab nafada gara tasan cewa danta ya kusan kwarkwancewa"nan ummah hadiza ta kwashe komi ta fadawa innah salati kawai innah keyi muniba ce ta fito daga sashen mahaifiyarta da Anty sadiya ganin taron jamaa yasa tayi turus tana kallonsu daidai innah tayi dariya cike da tsokana tace "au bazaki gaisheniba muneeba?ko har yanzun kishin kikeyi dani?dama kin gaisheni mun hadewa husnah kai dayafi dan na tabbatar idan ta tare yau kema da akayimun kishiya dake dena yayinki zaiyi"hajiya rabi ta fito tana fad'in "me kukeyi baku tafi ba inace tace batajin dadi ne?"muniba idonta ya cicciko ta kalli hajiya rabi tace "ummah Ashe bikin tariyar husnah akeyi?"gaban hajiya rabi ya fadi dik dauka wasa akeyi tayi ta kalli cikin parlorn momy ta hangi mutane zazzaune anaya ciye ciye,

"au bakisan yau kishiyarki ke tariya ba ina mijin naku?ko be fada miki ba?"ana haka su yaseer sukai sallama a tare suka shigo da husnah suna gaba momy da yan biyunta na baya wani kallo muneeba tayi musu lokaci daya taji wani abu ya caki zuciyarta kamar mashi DUHU ta soma gani kafin daga bisani ta saita natsuwarta innah kuwa cikin rawan jiki tq tashi tana kokarin gyara daurin zani tace "yauwa Alhamdulillah gashi nan ma mijin namu yazo kai yanzun haka akeyi ashe muniba batasan yau ake tariyar amaryarta ba?"rasss gaban yaseer ya fadi ya kalli muniba ya kalli cikin dake gabanta take yaji wani yarrrr idonta cike da hawaye hajiya rabi tace "kayi magana mana?inace ko dazun ka kwana gidan nan ka fita ashe fitar dakayi zuwa kayi dauko matarka"momy dake gefe tsaye lokacin tace "au bakusan fa da aljani kuketa rayuwa kwana da kwanaki ba,to ba Yaser bane wanan shedanim aljanin ne yake zuwa a matsayin yaseer"wani jiri muneeba taji yana kokarin kadata ta dafe kirji dama aljani take runguma tayi baya zata fadi da sauri yaserr ya rukota tare da Anty sadiya ta kara narkewa kawai ta fashe da kuka kamar jira takeyi,

hajiya zainab ce ta fito daga daki tana fadin "Aljani hajiya saude wallahi jikina ya bani ba yaseer bane nadai kasa gasgata cewar bashi bane din innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ashe mun auna arziki sace yaseer din yayi kenan?"momy tace "mu Shiga daga ciki"ta kalli Yaseer ta watsa masa harara tace "ah sh a cikin mutane take shigewa jikinka kamar wata mage?ko akanta aka somayin ciki ne?ka kaita daki ka dawo yanzun yanzun banson rashin kunya"jikin yaserr na rawa ya rike muneeba tare da Anty sadiya suka wuce sashenta hajiya rabi kuwa ta cika famm kamar zata fashe tsananin bakin ciki yasa ko ganin gabanta batayi haka ta nufi sashenta,

suna shiga sashensu yayi bedroom da ita narkewa tayi a jikinsa ta soma rera kuka shafa kanta yakeyi cikin sigar lallashi "kukan me kikeyi?baganiba nadawo inda bandawoba ina duniyar aljanun fa?"ta girgiza kai ta share hawayenta "Alhamdulillah tunda ka dawo amma yanzun yaseer haka zamuyi rayuwa tare da aljanu?tarewa da husnah yanzun ba karamin masifa bane"Hade rai yayi yace "karki sake kiran husnah masifa kinji nafada miki idan ba haka ba zan sassaba miki akan me?don kawai kaddara tasameta"kuka ta fashe masa dashi "aini nasan baka sona tuntuni dama ita kakeso nasan zan fuskanci bakin ciki nasani"shiru yayi jiki a sanyaye ya shafa sumar kanta gumi ne kawai yake karyo mata kishi yake hangowa karara a kwayar idanuwanta yace "ki kwantar da hankalinki kinga ga abinda kike tare dashi yanzun idan kika tada hankalinki kinga wani abu zai sameki da abinda kw cikinki"cike da shagwaba ta tura baki tace "to ba kai bane yanzun shikenan bani kadai gareka ba bansan yadda zanyi da kishinkaba mijina ina tsananin kishi akanka"fuskarta ce yake gani tamkar husnah irin wanan shagwabar takeyi masa wanda ya fahimci cewar nature dinta ne shagwaba yayi nisa cikin tunani ta bugi kafadarsa tace "kayi shiru"

"yi hakuri husnah"ta kallesa da sauri ya dinke bakinsa wani kallo tayi masa ta juya masa baya yana kokarin janyota yaji wayarsa ma ringing ya duba momy ce be dauka ba ya barta ya fita,

yana fita ta mike ta zauna tayi wata ashar davsauri sadiya ta shiga dakin tana jijjiga kai "tabbas sai kin shirya muneeba sai kuma kin iya kissa dan naga an juyawa yaseer kwakwalwa"muneeba ta kasa magana tsananin tashin hankalin da take ciki....

*****
tsaye suke a zagaye da Abraham tunda ya dawo duniyarsu baya magana dik maganar da baba da mama sukeyi masa fuskarsa ce take fidda wani abu kamar mai bakinkiirin dik shedar wuta a jikinsa musamman wuyansa ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa da nad'in mayafin dake kanta dakyar ya bude baki cikin wata irin murya mai ban tsoro yace "HUSNAH..... yau husnah da kanta ta zubamun abinda zai cutar dani?"wasu hawayene na jini ke zubowa daga idonsa dake fidda wani mai mai har har yanzun hayaki ne ke fita akansa,
daga gefensu wata dattijuwa ce baba kande tace "Abraham ka kasa hakura da husnah ko?husnah ba jinsin ka bace dikda na tausaya maka nasan irin yadda ka nuna mata soyayya amma ka duba kaga yadda wadanan biladama suka kona ka"ya kalleta tana tsaye da sanda a hannunta jikinta na kyarma saboda tsufa yaceb"husnah ina sonta ina tsananin kaunarta nina reni husnah nine na tseratar da ita daga shedanum aljanu lokacin da mahaifiyarta ke kwantar da ita a daki ita kadai lokacin nake zuwa nake wasa da ita harta shiga raina husnah tana sona"

"bata sonka Abraham inda tana sonka bazata taba konaka ba amma kuma wanan karon bazan hanaka daukar fansa akan wanan bil'adamar ba"jinjina kai Abraham yayi tare da wata kuwwa mai karfi saida iska ta tashi cikin dajin bishiyoyi ke kadawa da ganyayyaki yace"saina koma gareta bazan barta haka ba zan dau fansa akanta sanan wanan abun dake cikinta sai ya zama nawa"jinjina kai mamah tayi cikin tausayawa suke kallon yadda fuskarsa tayi kwanciya yayi a kasa saida kasar wajen ta girgiza iska ce kawai take tashi yana dafe da kirjinsa idanuwansa a rufe rufff wanan hawayen na jini nabin gefen fuskarsa cikin tunani yake ita yake gani lokacin da take watsa masa ruwan magani akansa jikinsa na salubewa....tunowa da yadda take tarairayarsa da tsananin kauna da soyayya lokacin da take duniyarsu tunowa da yadda suke kwanciya suna farantawa juna rai yayi yadda take shagwabewa idan tanason abu.....kuka yakeyi jikinsa na karkarwa zuhraliyya ce a gabansa besaniba kallonsa takeyi cikin tausayawa ya bude idonsa yana kallonta tana kallonsa yace "ki kwasarmun kayana dake gidan da nayi rayuwa da husnah ki kai gidan husnah Sabo"cikin damaucewa take kallon yadda jikinsa yayi amma hankakinsa na kanta?tayaya zata dumfari gidansu husnah bayan ga kunar dake jikinsa?bacewa yaui bata gansa ba tana waige waige ina yaje?"


dakin hajiya saude ta dira kayan na inda suka ajiye kallon kayan kawai yayi suka bace ya zarce gidansu husnah da yaseer inda zasu zauna yana shiga gate din yana bin ko ina da kallo yana jinjina kai a hankaki rayuwarsa da ita yake tunawa yana kokarin Shiga ta bango ya kasa dik yadda yayi sakamakom karatun alkurani da yakeji yana tashi a gidan,



momyn husnah ce ta dibo maganin da hafeez ya kawo bayan yaseer ya shigo su hajiya hafsat suna masa fada tace "yauwa ga wani magani nan sa hafeez ya kawo ya tabbatar mun inhar Tasha sun rabu da aljanin nan"

"hafeez kuma momy?"Yaseer yace yana maida hankalinsa kanta cikin kishi yace "ban amince tashaba ai nine mijinta yanzun idan tasha ta warke shikenan fa ya zama shine sanadin rabuwarta da aljanin can bayan nine nayi alkawarin kashesa"cikin takaici yake maganar hajiya saude ta karbo kofin dake hanmun momy ta mikawa husnah dake zaune gefe ta tankwashe kafa ta lula tayi nisa cikin tunanin Abraham,

ummah hadiza ta ciro turaaren da hajiya saude ta bata shigowarsu tace"karbi wanan maza nasa akai rushi gidan kaje kasa turare"ya karba yana kallon sashen da husnah ke rike da kofin magani ya fuce cikin takaici.....

*****
muneeba kuwa tsaye tayi rike da kwankwaso tace "nasha alwashin Bazan taba bari yaseer yayi rayuwat jin dadi da husnah ba ke yau din nan ma bazan bari ya kwana tarw da ita ba"sadiya ta jinjina kai tace "dakyau haka nakeso".....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻
42

A hankali yaseer ya tura kofar gate dinn cikin gidan yana bin ko ina da kallo hannunsa dauke da rushin wutar da ummah hadiza tasa aka bashi tsaye yayi jin kamar ana binsa a baya ya waiga bega kowa ba cikin rashin tsoro da dakewar zucuya yace "waye?"wata murya yaji mai ban tsoro ana magana ko ina na cikin gidan na amsawa "waye kake tambaya?mai gidan ne a cikin gidan ai kasan ko waye kuma kake tambaya"yaseer yayi shiru yana kalle kalle shiru babu kowa bega kowa ba tabbas yasan ko waye jikinsa nadan tsuma ya tattaro natsuwarsa ya ajiye yace "au ka fito ne mukara?ko kazo makasarka ne?"dariya Abraham ya sheke da ita yaseer ya hadiyi wani miyau da dauri ya dire rushin wutar kasa ya mike tsaye yana laluben cikin aljihunsa yana kokarin ciro magani yaga kaskon rushin wutar na yawo a gabansa kamar a hannun wani yake amma baya ganin kowa haka yake shawagi cikin gidan yaseer sakin baki yayi yana kallon siddabarun da akeyi masa ta bayansa yaji mutim yayi saurin juyawa bega kowa ba nan take yaji wata dariyar saidai ba muryar da yaji bace ta dazun wata muryace ko tantama babu ta macece yaji tana fadin "bil'adama akwai tsoro da karfin hali yafaji tsoro yaya"kyalkyalkyal yaji anyi dariya gumi ne ya karyo masa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login