Showing 84001 words to 87000 words out of 130717 words

Chapter 29 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

184

duniyar Aljanu ce babu wanda zaisan inda kake yaseer har sai na kare rayuwata da husnah dikda babu d'igon sonta a zucuyata sakamakon butulcemun da tayi"yana gama magana ya warware igiyar dake lilo a hannunsa ya cillata sama tayi kololuwa sanan ta dawo ta zarge yaseer tayi sama dashi cikin bishiyoyi can sama haka igiyar ke nad'esa tun daga farko har karshe zuhraliyya ce tazo Abraham yace"ki kula dashi na damka miki shi a hannunki karki bari ya kwance karki bari kowa ya cutar dashi"ta gyadawa Abraham kai tana kallon yaseer can sama sanan ta kalli Abraham tayi ajiyar zuciya tace"yaya Abraham ina gudun narjisu tasan cewar wanan bil'adamar yana nan kasan ta fini karfi zata iyayin komi dan ta lalata maka abunda ka shirya"ya girgiza kai yace"itama zanyi farautarta zan kawar da ita koni ko ita"..motsu mutsu yaseee ya shigayi daga inda yake cikin tsananin tashin hankaki Abraham ya mike sosai ya kara tsayi yakai inda yaseer yake a kulle ya bude hannuwansa husnah ya gani ta had'a kai da gwiwa su nusrah zagaye da ita da malam shuaibu mai gadi sunayi mata magiya tankar zararra haka take zabura zata fita,wasu hawaye masu zafi suka fito daga idon yaseer tausayi da tsananin soyayyar husnah yakeji yana kara shiga jijiyoyin jikinsa runtse idanuwansa yayi take ya tuno da yadda jiya take hawaye lokacin da ya hau kanta waigowa yayi bega yaseer da zuhraliyya ba ya kalli bishiyoyin dake zagaye dadhi yau shine a wata duniyar ba duniyar mutane ba?yau shine a duniyar aljanu?dama cikin wanan kurgumin dajin husnah tayi rayuwa?wasu hawayen ke kara gudu a fuskarsa wani hali husnah take ciki?shine abinda ke damunsa....
*****
yusrah na rike da husnah sukaji mota a kofar gida da sauri nusrah ta zabura "yauwa malam shuaibu gama yaya yaseer din nan ya iso inata kiran momy bata dauka"juyawa yayi ya bude gate Abraham ne cikin motar yaseer sak yaseer babu banbanci yayi parking motar ko karasa rufe kofa Abraham beyiba ya fito cikin dimuwa yana fad'in "menene yasameta?meyafaru ina momy"be jira mai zasuce ba ya dauki husnah tana shusshura kafafuwa yana fad'in "mu shiga cike har yaushe zaku barta a nan ranan na kod'arta "cewar Abraham yana kokarin Shiga kofar parlorn,sautin karatun kurani ne ya gauraye kunnensa kallon speaker yayi sai kittrt ta kashe kanta daidai nan suka shigo a tare dukkansu a tsorace suke ga tsananin tausayin husnah da sukeji yana kokarin kwantar da ita a kujera yaji yusrah na dakatar dashi "yaya yaseer aida ka shiga da ita ciki kawai inyaso sai asa mata karatun kuranin kafin momy ta dawo nasan idan tadawo zaa kira malam"ya jinjina kai cike da gamsuwa ya runtumeta a kirjinsa wani irin bugun zuciya yakeji kirjinsa nayi dikda yadda yakejin haushinta da yadda ya d'aura dammarar koya mata hankali ya kalli fuskarta harta dan rame yayi shiru ya d'ago kai yaga suna kallonsa yace"husnah tabani tausayi sosai nusrah"suma jinjina kai sukayi cike da alhini yusrah tace "don ma bakaga yadda ta fito kamar mahaukaciya ba tun dazun idanuwanta suke a rufe taki budewa wai adaji take"Abraham ya cije lebe ya nufi dakinta da ita ajiyar zuciya dukkansu suka sauke tare da hamdala yadda yaya yaseer ya iso gidan da wuri da basusan yadda zasuyi da husnah ba....yana shiga ya turo kofar dakin ya rufe ruf ya kwantar da ita a kan gado juyi tayi tana bude idanuwanta a hankali ta saukesu akan Abraham take fuskarsa ta sauya ta koma Abraham daga ysseer murmushi yayi mata,ta ja baya ta manne da jikin allon gado "kina mamaki ko?ba mijinki wanda kikaci amanata bane nine dai mijinki aljani wanda kika tsana kike kirana da dodo wanda kikaci Amana kuma a haka zanyi rayuwa dake a matsayin yaseer batare da kowa ya gane hakan ba husnah saboda har yanzun akwai sauran guggubin soyayyata a zuciyarki kina wayancewa ne kawai amma nine masoyinki na asali wato aljaninAbraham"dam gabanta ya fad'i jikinta ya hau tsuma ta had'iyi wani miyau mai kauri tana bin dakin da kallo,shima kallon dakin yayi wani abu ya fito daga idanuwansa take kayan dakin suka sauya zuwa dakinta na duniyar aljanu,ta dafe kunnuwanta zatayi kara da sauri ya toshe bakinta "koda yake bari na kyaleki ko kinyi kara babu wanda zaijiki cikin gidan nan husnah kina tunanin zaki rabu dani ta dadi?kinsan wahalar Danasha da yadda nabi kafin na saceki?ko kinsan tunda aka haifeki kikazo duniya nake zuwa shimfidarki inyi wasa dake a jarinta?lokacin da momynki take ajiyeki tabarki ta tafi aikinta,lokacin da take kwantar dake goshin magriba batare da tayi miki addua ba batadamu dakeba sam sam,ina zuwa cikin gidanku inyi shawagi a hakan nakamu da tsananin kaunarki nike kula dake dik lokacin da miyagun aljanu zasuzo su saki kuka nike lallashinki"kallonsa takeyi ido cikin ido hawaye na bin fuskarta,kwankwasa kofar akayi da sauri ya juya lokaci daya ya koma yaseer yace"waye?"

"nice nusrah yaya dama nace munyi kokarin mu saka karatun kurani kamar yadda momy tace mun gagara shine nace ko zaka taimaka mana yayi'kallonsa husnah kawai takeyi yace"tasamu bacci kubari kawai kuyi kokarin yin abinci kafin momy tadawo"nusrah tace "toh yaya"ta juya ta jikin kofar yake kallon nusrah ya jinnina kai,
wani fitsari husnah taji ganin yadda yayi juyo ya sauya kamanninsa zuwa mummunan halitta mai ban tsoro gajere mai kibar gaske bakinkirin take kallonsa ta tsorata haka ya tako ya hayo kan gadon tanason sakkowa ya fuzgota jikinsa ta tsandara ihu tana hawaye "haba Abraham idan kana sona kuma saika cutar dani?meyasa ka zabi ka azabtar dani da rayuwata?meyasa tun fatko kasan kai waye ka boyemun halittarka yasa na shagala da zanyi rayuwa dakai har karshen rayuwata"yadda take hawaye yasa tausayinta ya kamasa gumi ne ke karyo mata tace "ina yaya yaseer?"tambayar da tayi masa kenan yayi mata wani kallo cike da tsananin kishi wato tambayar yaseer ma takeyi?bazata bashi hakurin amanarsa dataci ba?"husnah meyasa kike tambayar yaseer?kinaso in kashesa ne?"da sauri ta girgiza kai tana fad'in "ah ah ah ah kada ka kashesa dan Allah kadawo dashi naji zanyi rayuwa dakai amma karka tabashi"haushinta yakeji yasan idan ya cigaba da zama zuciya zata iyasashi ya illatata kawai gani tayi ya bace ta durkushe a kan gado ta makalkale pillow tana kuka cike da takaici da tausayin kanta da tsananin haushin momynta Wanda itace dama silar jefata cikin wanan masifar?
*****
shiru cikin gidan babu kowa hajiya saude ke kwada sallama momyn husnah tana sallah tayi gyaran murya "au Ashe sallah kikeyi inata kwad'a sallama baa amsaba kamar ke kadaice ma a cikin gidan"momyn husnah ta sallame ta amsa "nikadai ce hajiya rabi da sadiya da muneeba sun fita babu dadewa sun koma asibiti muneeba babu lafiya"hajiya saude ta tabe baki tace"halan ciki ko?"momy tayi murmushi tace "barka da zuwa kece da rana tsakar nan?"momy ta gyara zama tace "washhh nice wallahi na fita tinda safe ina yaseer?"hajiya saude ta tambaya momy tace "ni ai yau banga yaseer ba ke zan tambaya keda ya kwana gidanki daddynsa na nan ya cika fam yana nemansa muneeba kwana akai da ita babu lafiya,hajiya saude kikabarsa ya kwana da husnah can bayan ga matarsa nan gashi batada lafiya"

"itama husnah ba matarsa bace kenan? dikda yamun laifi hakan yasa ma naje gidansu innah daga can nake mun yanke shawarar zaa fara gyaran sashen husnah zata tare cikin satin nan kafin ayi ciki a gidana dan danki dai sab'ab'awa yayi infada miki yajiwa yata ciwo"kunya ce da farin ciki suka lullube momy sai kuma tace "to hajiya saude ya akai hakan?aljanin yabarsa kenan har ya iya kusantarta?"nan momy ta kwashe yadda sukayi da malam da maganin da ya bayar ta fadawa momy farin ciki ya lullube momy harda hawayen farin ciki tayi tai shiru tana kallon hajiya saude baki bude,

nusrah ce ta sake kiran momy "kai wad'anan yara dake faman kirana tun fitata bansan me sukesoba bari dai in dauka karsu kashemun carji"momynyaseer tayi murmushi idonta ya sauka akan cikin hajiya zainab,ta jinjina kai ta dau wayar "hello"
"momy tin dazun muke kiranki baki dauka kina fita Anty Husnah ta rikice mutanen nata sukazo wai gidanmu daji take gani"dafe kirji hajiya saude tayi momyn husnah dake sauraren nusrah ta firfito da ido waje,

"yanzun ina husnah?me kuke ciki? gani nan zuwa gidan"

"yaya yaseer yazo ai tun dazun saidai kitaho kawai yanzun dai tasamu bacci"ajiyar zuciya hajiya saude tayi ta kashe wayar tana kokarin jan mayafinta "banga ta zama ba gida zani saidai kafin inje gidan zani gidan malam ne insamesa akan husnah in zamuje tarene muje"momy ta rude sosai "ko zamuje tare?"girgiza kai hajiya saude tayi tace "kiyi zamanki kiji da kanki naga abin arziki gashinan saidai naso muyi magana amma hakan bazai yuwuba gara intafi inga halin da take ciki"momy ta jinjina kai cikin sanyin jiki ta zauna hajiya saude ta fice cikin sauri tabar driver waje....shiru momyn husnah tayi take taji wani haushi da tsanar kanta ya darsu a zucuyarta ta furta "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"hawaye suka Shiga zubowa a idanuwanta tambayar kanta takeyi meke damun kanta?shin waye silar batar husnah?take tabawa kanta amsa komi yasami husnah itace sila sakamakon sakacinta....

*****
"boka yanzun fa matar nan ciki gareta na tabbatar da ciki ne boka bana bukatar ya kasance tanada ciki saidai ni insamu"tace cikin tsananin damuwa wata dariya boka yayi yace "dik abinda kikeso shi zaayi da cikin nan idan kince a dauko cikin daga jikinta a dawo dashi jikinki ma zaa iya"ta kalli sadiya,gyara zama hajiya rabi tayi tace "boka da sai nafi kowa farin ciki idan hakan ta kasance inaso kafin inbar wajen nan a dauko cikin matsiyaciyar matar nan azo dashi a sakamun"sadiya tace "niko inaga gara a kashe abinda ke cikinta kisamu naki idan kuma kika haifi dan dake cikinta yazo yana kama da ita fa?"shiru hajiya rabi tayi tace "haka ne kuma kaga boka a halaka abinda ke cikin nata kawai"

"kawai shiyafi"boka ya d'aga wata kwarya sama yayi surkulle hade da Kiran sunan hajiya zainab so uku ya sauko da kwaryar kasa saiga hajiya zainab cikin kwaryar da cikinta "lek'a kigani"ta leka zaune take tana hawaye saidai cikin tsananin mamaki take yadda taga momy da alk'urani a hannunta ya daure mata kai kasa magana tayi ta kalli boka yayi dariya yace "wanan aikin tsafi bazai yuwuba saidai ke zakiyishi rabi"yace a kausashe wani miyau ta hadiye tace "kome zanyi zanyishi matukar abinda ke cikinta zai halaka"ya jinjina kai ya ciro wata laya yar karama da magani a kulle "ki tabbatar wanan layar ta shiga bakinta kota wani hali inhar layar nan bata shigaba to taci abu dauke da wanan maganin an gama amma tabbas sai kinyi dagaske kin jajirce idan ba haka ba abinda ke cikinta zaizo duniya kuma najimi ne"damm gaban hajiya rabi ya fadi zufa ce kawai take karyo mata ta ko ina,
muneeba kuwa cikin kosawa tace "ummah tunda an sallamemu ya kamata muzo mutafi dan yau din nan zan aiwatar da abinda zanyi saina tabbatar yaseer ya tsani husnah wanda zai mata saki uku bai saniba"sadiya tayi murmushi tace "kedai kishi zai kasheki"murgudawa sadiya baki tayi sukai sallama da boka dakyar muneeba ta iya tashi mararta ce tayi mata nauyin gaske kamar cikin ya tsufa....

******
momy na shirin rufe alk'urani taga ana shigowa da kaya cikin gidan Abraham ne ya shigo yana murmushi yace "momy barka da yamma"momy ta rufe tace "yaseer kaine haka?wad'anan kayan fa?"murmushin mugunta Abraham yayi yana kallo ya sadda kansa kasa yace "naje gidan innah ne daga gidan momy shine tacemun husnah zata tare wai shine fa to wasu kudi sun shigo asusun bankina nace bari in siyo mata kayayyaki"momy tayi murmushi tace "allah yayi albarka ,ya jiki. husnah?dazun hajiya saude ta tafi daga nan baa sukuni ba nusrah ta kirata akan ta burkice inaga ma ta biya gidan malam yanzun haka zasu tafi tare"wani miyau Abraham ya hadiye yaji dadin labarin nan dan tabbas idan yaje gidan malam na nan to asirinsa zai tonu zasu gane shi aljanine ba yaseer ba yayi shiru momy tace "yadai?"ya girgiza kai "ah ah bari in karasa sashen muneeba nad'an gaji ne"ta jinjina kai tabi kayan da kallo anata shigowa da hadaddun kayan set na gado wanda sun tasarwa million biyu da rabi momy tace "ikon Allah yaseer kenan"yana kwanar sashen muneeba ya bace daga cikin gidan hajiya rabi suka shigo da faraarta ta tsaida momy dake kokarin shiga daki "ah ah hajiya zainab yadai?wadanan kayan fa zaki canja kaya ne?"momy mamakin ganin hajiya rabi nayi mata faraa takeyi gabanta yadan fadi cikin zuciyarta a hankali bakinta ya furta "hasbunallahu wa niimal wakil"hajiya rabi ta sake washe baki ta jeho mata tambaya momy tace "na husnah ne wanda zata tare"

"tarewa?"suka hada baki harda muneeba ido waje suna kallon momy ta jinjina kai kawai ta wuce tabarsu nan tsaye muneeba wani ashar tayi ta nufi sashenta kamar mahaukaciya.....

*****
shiru malam yayi yana kallon husnah yana karanto addua a bakinsa shi take kallo bakinta nason ta fada musu ba yaseer bane aljanine ta kasa momy ta kallusu nusrah da sukai tsuru tsuru "ina yaseer din?"kallon juna sukai "Yana dakin Anty husnah"

"daga dakin nakefa shigowata bangansa ba"husnah zatayi magana kanta ya sara ta ta dafe kanta malam ya cafki kanta cikin saa ya soma tofa mata addua yana murza kanta da turare....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU....300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN ALLAH YA ISA!!!!!*


08036953516
07042277401


*SLIMZY*✍🏻
37
bankad'a kofar dakinta tayi ta shiga ta yarda gyalenta ta zauna gefen gado ta dafe kanta sadiya tsaye tayi a jikin kofa tana kallon hajiya rabi cikin damuwa da rud'u "lallai matar nan wato manakisar da suke hadawa kenan batare da munsani ba?shirye shiryen tarewar husnah akeyi a cikin gidan nan?tabdijan inko inada rai bazan taba bari husnah kota tare ta zauna lafiya ba"ta mike tana numfarfashi,
"ki kwantar da hankalinki yarinyar nan da ake maganar tariyarta da yaseer ba son yaseer dim takeyiba zuciyarta na tare da Aljan mai zai d'aga miki hankali?abu daya zakiyi ki tada tarzoma idan Alhaji badamasi ya dawo Shi kadai ne zaki bullo ta wajensa ki wargaza komi sanan kisan yadda zaki kafin ki halaka cikin can na waccen bakar dagar kisa masa tsanar cikin yasa a ransa lallai ba cikinsa bane"sharce gumin da ke karyo mata tayi idanuwanta jajir tace cikin dimuwa "kunnamun fankar can ni gaba daya gumi nakeyi ma"sadiya dake tsaye ta daga kai ta kunna fanka ta sa hannu ta gefenta ta kunna makunnin AC ta jikin bango ta dawo ta gefen ummah ta zauna "haba yaya har wanan dan abun zai tada miki da hankali?kin tsaya cikin damuwa bayan ga babban gagarumin makami boka ya baki ai yanzun kwantar da kanki zakiyi ki tabbatar ta saki jiki kin bata wanan maganin taci kuma kisan yadda zaki cikin dare har layar kisa mata a bakinta kamar yadda yace kinga karama ce tsaf zata hadiyeta cikin bacci"murmushi hajiya rabi tayi hade da sauke ajiyar zuciya ta zuge jakarta ta ciro maganin tana jujjuyawa "zainab kenan saidai wata bake ba Baki isa kiyi ciki ki haifesa a cikin gidan nan ba da raina da lafiyata yadda nayi nasarar aure miki miji haka zanyi nasarar halaka abinda ke cikinki"jinjina kai sadiya tayi tace "har naji dadi banaso ki rinka karaya yaya bayan kedin macece mai kamar maza na tabbatar zaki iya"

"zan iya"tace hade da sauke nannauyar ajiyar zucuya ta mike tace "ina zuwa"ta fice sadiya tayi murmushi ta harde hannuwanta a kirjinta....
******
muneeba tsaye a gaban gas ta cika d'akin da kamshin abincu da takeyi saidai bata cikin hayyacinta surutai takeyi kamar wadda ta zare tsananin kishi da ya turnuke ta"ni yaseer zaiyiwa haka?ashe dik abinda suke kullawa Kenan shiyasa har yaje can ya kwana?wanan munafukar uwar tasa sai naga bayanta babu wanda zaisa inyi zaman kishi da matar aljan"tace a fili ta ciro maganin da boka ya bata tasa ma yaseer a abincu tana cikin kwashe abinci taji motsin shigowar mutum tad'an sak'e a gefenta ta juya baya "waye?waye nan wajen?"tayi shiru tana saurare turo kofar Abraham yayi ya shigo ajiyar zuciya tayi ganin yaseer ne Tayi masa wani kallo sanan tq d'auke kanta gefe daya ita a dole fushi,
Abraham ya tsaya daga bayanta ya zuro hannunsa kwankwasonta ya rungumeta sosai badan yaso hakan ba sam bayaso ta harbo jirgin shiba yaseer bane "yadai fushi kikeyi dani?"ta jinjina masa kai cike da takaici sai kuma hawaye ya fara zubowa a idonta yad'an joyota ya hadeta da kirjinsa ya rungumota "nasan kukan mai kikeyi ki kwantar da hankakinki husnah baxata taba kama kafarki a wajena ba kinsan yadda nake sonki ai badan nasoba zaa maida wanan auren saidan umarnin mahaifiyatq"da sauri ta kallesa tana hangi gaskiyar sa a kwayar idonsa ya lumshe idanuwansa Abraham yayi kissing goshinta ta sauke ajiyar zuciya ta kara shigewa jikinsa yayi mata rumfa "yaya yaseer banaso wata mace ta rab'eka tsananin kishin da nakeyi akanka zan iya hallaka kaina dik ranan da na wayi gari ka tare a d'akin wata bayan ni"ya jinjina kai Abraham ya cije lebe ya dan janye jikinsa "nafada miki wanan tariyar badan nasoba zaayita dik abinda zakiga nayi zanyine kawai dan farin cikin momy bawai dan inaso har cikin zuciyata ba kidaina tada hankalinki akan wadda batasan itadin waceceba ma"murnushi muneeba tayi cikin tsananin murna da farin ciki tabbas aikin boka da yayi kafin subaro ya soma aiki yau yaseer da kansa yake fad'a mata wad'anan kalaman?da wadanan kalaman zatayi amfani wajen yakar husnah ta kara tabbatarwa kenan mahaifiyar yaseer baa zaune take ba,ya tsareta da ido tad'an kallesa cikin shagwaba tace "kana kallona nayi kyau ne?"ta juya baya ta kada masa mazaunanta murmushi Abraham yayi yace "sosai kinyimun kyau matata wanan cikin kara miki kyau yayi"tasa hannu ta rufe fuskarta yace "bari in d'an watsa ruwa kafin kingama"ta jinjina masa kai ya wuce yana fita ya rufe kofa yayi mik'a ya kalli bango ya tsage ya shige ta ciki...
*******
tari sosai husnah keyi sakamakon hayakin daya turnuke parlorn cikin tausayawa hajiya saude ta girgiza kai tace"sannu husnah"ta jinjina mata kai idanuwanta sunyi jajir malam ya tsareta da Ido yace"ta wani suffa yake zuwa miki?"tayi shiru bakinta na karkarwa ta sunkuyar da kanta kasa tayi masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login