Showing 51001 words to 54000 words out of 130717 words

Chapter 18 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

206

tsakiyar bishiyoyi yayi ihuuuuuu da har saida dajin ya amsa ya mike yayi tsalle yana yawo a sararin samaniya yayi kuwwwa dajin gabaki daya ya sake amsawa mamah da zuhraliyya suke kalle kalle cikin tashin hankali suke waigen ta inda zai bullo zuhraliyya tace "maamah wanan yaya Abraham ne kuwwarsa ce kururuwarsa ce"zabariyya ta rugo da gudu bishiyar da suke tace "Abraham ke ihu cikin dajin nan tamkar yana cikin wani yanayi"cikin damuwa tayi maganar,


hawaye ke zubowa a idon Abraham Wanda suke rikidewa suke komawa jini hawaye yakeyi hade da majinu yaba gunji cikin kuka yakw fad'in "niba mugu bane niba azzalumi bane amma dik wanda yayi yunkurin rabani da husnah tabbas hukuncin da zan dauka akansa zai sai ya rinkamun kallon mugun aljani.....tayaya na shaku dake husnah a matsayinki na bil'adama ina tsananin kaunarki zaayi yinkurin rabani dake"hawaye ke gudu a fuskarsa suna komawa jini ya daga hannuwansa yayi ihu ya fadi kasa karar da yayi tasa dajin tasa dajin ya girgiza bishiyoyi suka shiga faduwa suna karewa iska hade da guguwa ke tashi dik aljanun dake dajin sun shiga rudani ganin Abraham zaune dirshan akan katon dutse yana kuka yana kiran sunan husnah.....narjisu ce ta fito ta gabansa tsaye tayi a gabansa rigarta har kasa ta rufe mata kafa gashin kanta ya bazu a bayanta data gaba ta dago kanta dake sunkuye wata irin dariya tayi tace "kad'an kenan daga halin bil'adama Abraham meyasa bazaka rungumi jinsinka karabu da itaba ko soyayyar dole ce?kana azabtuwa da soyayyarta?mu kuma muna azabtuwa da kaunarka?"wani irin kallo yayi mata wanda tasa habtar cikinta ta kad'a ya miko hannunsa zai damketa ta bace,

yar sandar dake hannunsa wadda yake busawa a hankali yana hawaye ya tuna runtse idanuwansa yayi take ya tuno da husnah lokacin da yake fita da ita saman dutse yanasa hannu cikin ruwa yana damko kifi yana gasawa yana bata,ya bude idanuwansa da duka sauya kala ya mike yana taku kafarsa kamar ta tsaga kasa haka ya tsaya akan dutse yana wata sarewa da sandar yana busawa yana hawaye....


kwance take kan gadonta tayi lamo ba barci takeyi ba sautin sarewar busarsa takeji a kunnenta ta zabura ta zauna tana kalle kallen cikin dakin bugun zucuyarta ne ya tsananta tasa hannu ta dafe kirjinta da yake bugawa kana iya kallon bugun zucuyarta ta zuro kafarta kasan gadon ta Diro waige waige takeyi tana jiyo saitin muryarsa yana busa yana hawaye durkushewa tayi akan gwiwarta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin rawar baki da zazzabi dake son lullubeta tace "Abraham kadaw....oooo natuba ina tsananin kaunarka nasaba dakai soyayyarka zata illatani kadawo tun numfashina bai daukeba karasani"shesshekar kukanta yana iya jiyo sautin kukanta tsayawa yayi da busar yana sauraren kukanta shima kukan yakeyi yana bukatar kasancewa da ita yanaso ya rungumeta yaji dunin jikinta yayi missing nonuwanta masu laushi da dadin tabawa ga wata matsananciyar shaawarta dake damunsa....

momy a hankali ta tako ta tsaya a kofar dakin husnah tana jiyo sautin kukanta tana Ambatar sunan Abraham cike da tashin hankali a kasa ta kwanta tana juyi minti minti takw mikewa ta shiga waige waige ko zata gansa....wani irin iska mai sanyin gaske yake kada husnah da Asuba ta muke ta runtse idanuwanta tana kallon window yadda yake kadawa gani takeyi kamar shine zaixo wajenta.....


yaseer juyi yayi akan gado idanuwansa a rufe amma fuskarsa cikin kwayar idanuwansa husnah yake gani yadda yaga rana haka yaga dare ya bude idanuwansa ana kiraye kirayen sallah asuba muneeba na kwance a kirjinsa ta baza gashinta har fuskarsa ya kauda gadhin ya tsura mata ido yadda take bacci yake kallo a zahiri kuwa hankakinsa da zuciyarsa na wajen waccen yarinyar yana shafa kan muneeba yana bubbuga bayanta cike da kulawa kansa na kallon ceiling lokaci guda ya tuno da fuskar nan tata mai ban tsoro ya runtse idanuwa dik motsinsa muneeba ba bacci takeyiba Allah Allah takeyi safiya tayi su fita cikin tashin hankali take bazata taba iya bacci ba dan tanaa gani kamar yaseer zai dawo hayyacinsa ya tuna da husnah gashi tayi masa karyar tanada ciki dole ta ziyarci wajen boka

******
hajiya rabi ce tsaye gaban daddy yana shirin fita hannunta rike da hularsa cikin kissa tace "nace kasamu karanta takardar da yaseer ya baka kuwa?"waige waige ya shigayi yace "au kinga jiya tsabar takaici bansan inda na jefa takardar nan ba wallahi"murmushin mugunta tayi tace "Tou ka tambayi zainab kila itama ya bata takardar saika karanta tata tunda taka ta bace ya jinjina mata kai ta durkusa ta mika masa hular tace "au inaso zan fita goggo batada lafiya zamuje nida muneeba mu dubota"daddy ya jinjina kai yace "yakamata dani zaaje"gaban hajiya rabi ya fadi tayaya daddy zaice dashi zaa itada zata ziyarci wajen boka yacev"amma akwai aikin da zanyi inaga yar tafiya ma zanyi gaskiya"murnushi hajiya rabi tayi tacw "har nasoma murnar zamu ka gaida goggo koda yake ba sai kajeba zan iya isar maka da sakonka"ya jinjina kai tace "allah ya tsare "ameen"ya fice dadi ya kasheta,

momy rike da plate na siyayyan kwai da doya da source na hanta da tea mai kauri tana lallabin husnah sam takicin abincin kallon bango kawai takeyi tana sauraren zuwan Abraham tayi missing dinsa sosai ta saba dashi shikadai ke debe mata kewa da soyayyarsa ga shaawarsa datakeji tarasa dalili ruwa kawai ke zuba yana jika mata pant momy kuwa tausayin husnah ne ya lullubeta batasan lokacin da ta soma hawaye ba,ta mike ta fice sukai kicibis da yaseer ya shigo,

Abraham ne ya bullo ta jikin bango jikinta ne ya bata ya shigo dakin saidai yaki bari tagansa yanaso yadan horata ne mikewa tayi tana jinjina kai "kazo Dan Allsh kana ina ka fito ina tsananin kewarka"murmushi yayi har yanzun cikin fushi yake ji tayi an rungumota ta baya ta waiga bataga kowaba bata ankara ba taji hannuwa cikin rigarta ana mulmula kan nonuwanta cike da kwarewa runtse idanuwanta tayi tana sauke numfashi.......



*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE 300 ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI DIK WADDA TA KARANTAMUN BATA BIYABA ZATA BIYANI HAKKINA RANAN DA BATADASHI*

TURA KUDINKI 300 TA WANAN ACCOUNT DIN
πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»
3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER



*SLIMZY*✍🏻
[23/09, 21:29] πŸ₯°slimzy😍: 22

runtse idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi ke zubowa ta dago hannunta tana kokarin d'orawa akan hannunsa taji ya cire hannun daga kirjinta ya janye jikinsa ta waiga bataga kowa ba ta mike tana magana cikin sanyin murya "kadawo gareni nayi kewarka awanni shida da suka shude kamar shekara shida da wata shida nayi na rashinka Abraham"bakinta ke rawa tana maganar jingina yayi a jikin bango yana kallonta ko kifta ido batayi waige waige kawai takeyi tanaji a jikinta yana cikin d'akin Amma fushi yakeyi da ita ta dafe kanta kamar zararriya tace cikin tsawa "wai ya kakeso inyi ne?meyasa zakayimun haka baayi maka laifi a baka hakuri Dan Allah ka fito idanuwana suyi tozali dakai ko zan samu sassaci. rad'adin da nakeji a zuciyata"ta share hawayenta tana saurarawa ko zaiyi magana,

yaseer da sukai kicibis da momy kuwa muryar husnah yaji ta daki dodon kunnuwansa ya saurara da kyau murya mai tsananin dad'i yaji tamkar tana busar sarewa wanan muryar yakanyi mafarki da ita sanan yaso yasan mai irin muryar nan a yarinta gashi yazo ne yaga yadda ta kwana yace "momy ya naganki da plate din abincin kin fito kina kuka?ita yarinyar bata karba taci bane?"momy ta girgiza kai tace "bata karba ba tayaya zata karba bayan ta kwana tunanin aljani?ta kwana kuka saboda tsananin soyayyar da takewa mutumin da ba halittarsu daya ba"shiru yaseer yayi tsuntar kansa yayi cikin tsananin faduwar gaba baisan lokacin da yace "bani plate din abincin"galala momy tayi tana kallonsa takasa magana sa hannu yayi ya karba da cup din tea din jikinsa na rawa gashi yayi shirun zuwa aiki momy ta rakasa da ido tana kallonsa ko kiftawa batayi,

daddy ne ya shigo dakin cikin shirin fita sai kamshi yake zabgawa momy kallo daya tayi masa ta kauda kanta cike da takaici shima haushinta yakeji yace "ina takardar da yaseer ya baki jiya?"shiru momy yayi cikin zuciyarta tace takarda?tabbas taga lokacin da yaseer yaba daddy takarda amma ita be bataba tace "wace takarda kuma?"hajiya rabi tana kokarin shigowa tace "takardar sakin husnah daya rubuta mana ai biyu ya rubuta yaba daddy nasa ya baki dayake bakiso arabashi da ita yasa kika boye naki na daddyn ma kika dauke"daddy ya dubi hajiya rabi ya jinjina kai yace"da kyau yaseer ya saki husnah ko?dama ai bai dora mata idda ba tunda ko tarewa batayi ba batamasan da auren ba yanzun ta mijinta aljani takeyi dan haka nasan yanzun yaseer yaje aiki zan kirasa a waya aida ransa inji sanan ya rubutomin sabuwa saboda hafeez inbashi aurenta suje su karata dama shi ya tattagota ninafara ko kwanto ma akanta dikda ban tabbatar ba"yana gama magana yasa kai ya fice bai jira ta bakin momy ba,gaban momy kuwa dukan uku uku yakeyi wato yaseer takardar sakin husnah ya rubuto?hajiya rabi ta katse mata tunani tace "tunanin me kikeyi zainab?"ta sheke da dariya tace "husnah itada yaseer saidai ido dan tuni nasa yaserr ya rubuta takardar saki uku zaa damkawa yarki idan ma kinga takardar kin boyene to karyarki Tasha karya idan kinga yaserr be sawakewa husnah ba to niko shi wani ya mutu ne"momy ta watsa mata kallo mai cike da tsana tacev"tirre da halinki rabi dik kutungwilar da kike kullawa wallahi ta Allah bataki ba burinki bazai taba cika ba kuma yaseer da husnah babu Wanda ya isa ya rabasu dan tun husnah na cikin yaseer ke dawainiya da ita dan haka sihirin da kukayima yana gab da karyewa dan yanzun haka yaseer na cikin dakin husnah yana ciyar da ita"shekeke hajiya rabi ke kallon momy ta sheke da dariya tace "mafarkin da kikayi jiya ko tabadai ciki tare da mijinta aljani yana kwanciya da ita"tasa kai ta wuce tana dariya momy tayi kwafa maganar hajiya rabi na karshe yayi mata matukar zafi hajiya rabi kuwa ranta ya sosu cewan da tayi yaseer na tare da husnah a daki dan haka yasa ta nemi waje ta labe,

momy kuwa tsaye tayi jikin labulen dakin tana iya hango yaseer yana rike da plate din yake taku sautin takalminsa a tiles yasa tayi saurin juyowa tanayin ido hudu dashi ta mike fuskarsa ce ta shiga canja mata ta koma yaseer ta rikide ta komata Abraham tsoro ya kamata tadan ja da baya cike da fargaba take kallonsa tana ganin yadda yake rikida,ganin tanaja da baya yasa yaseer dan furgita ta zauna gefen gado bakinsa dakyar yasamu damar fusta addua ayatul kursiyyu yayi Abraham na tunkarosa ya koma da saurin jin zafi da hucin wuta a tattare da yaseer rikidewa yayi ya shige jikin husnah wani abu daga idon husnah ya fito zirrrrr kamar walkiya ko shocking Yana wuta ya shiga bakinsa ji yayi harshensa ya daure jikinsa sai tsuma yakeyi bugun zucuyarsa ya tsananta yana zama a gabanta Yana kallonta ita kuma a Abraham take kallonsa shi kuma tuni fuskarta ta rikide masa ta koma abun tsoro fuskarta ta koma baka kirin irin yadda yagani jiya take hakoranta suka zazzago masu tsayi guda biyu idanuwanta a warwaje gadhin kanta kamar kaya yaseer ya runtse ido dakyar ya kira sunan Allah kamanninsa suka koma nasa sak tace "meyasa kake canjawa kana komamun Abraham yanzun naga ka rikide ka koma mutumin nan daya rungumeni jiya"a sanyaye tayi maganar idanuwansa a rufe ruff baya kallonta daya bude ido kamanninta ke sauyawa haka ya dibo abincin a hankali yace bude bakinki "ta bude bakinta batare da tayi masa musu ba ya bata ta kara karba a haka yake bata har sau biyar daga bisani yaji wata iska mai karfin gaske ta mamaye dakin windows din cikin dakin ke kadawa fanka ta fara zazzagowa kamar zata fado ya juya yaga wardeobe dinta na buguwa yanayo kansa da karfin gaske aka fincike plate din abincin aka wurgar gefe ji kake tasssssss tasa hannu ta toshe kunnuwanta aka angije yaseer daga gefen gadon ya fadi kasa wata murya yakeji tana magana sam naya fahimtar me ake fadi ya mike cike da tsoro saidai ya kasa gudu ya kuma kasa kallon inda take ganin drwer nayo kansu yasa hannu ya fuzgota ta suka Fadi kasa ta fada kirjinsa kamar kugiya aka dauketa aguje momy ganin wanan dramer ta shigo dakin ganin yaseer warwas a kasa tace "an tureka ko yaseer tashi tashi"tana kokarin rukosa yayi murnushi yace "zan iya tashi"ya mike ya juya ya kalleta rabe a gefen gado sai gumi takeyi ta bishi da kallo ya fice yana fitowa a idon hajiya rabi ya fito ta zaro idanuwa waje tana kallon yaseer cike da tsananin mamaki tasa hannu ta murza idanuwanta tabbas shine a hankali ta taka ta koma sashenta dakyar take taka kafarta saboda yadda jikinta yayi nauyi jiri na nenan daukarta....

ko ganin gabansa yaseer bayayi ya fito kicibis sukayi da muneeba ta zuro hijab tana sauri da slippers a kafafuwanta turus tayi ta kallu agogon wayarta tana kallonsa cikin tuhuma tace "yadai har yanzun baka wuce aiki ba?me kakeyi a sashensu momy naga kamar daga nan ka fito"nannauyar ajiyar zucuya ya sauke tana kallon yadda kwayar idanuwansa suka kada cikin tuhuma take kallonsa gabanta ya tsananta faduwa ruko hannunta yayi ya shafa cikinta yace "babu komi mun dan tattauna da daddy ne yanzun ma sauri nakeyi zan fita in tafi"ta waiga bataga motar daddy ba tace "ai daddy ya dade da fita naga fitarsa ta window"gabansa ya fadi bayaso ranta ya baci sam yarasa meya shiga jikinsa yakejin yana damuwa da wanan yarinyar sam yar da ko ganinta bayasonyi bayi rasa nasaba da kamannin da yake gani da wata yarinya dayasani a baya kwalla taji ta cuko a idanuwanta ganin ya rasa me zaice masa kawai ta gifta ta gefensa ta wuce juyawa yayi yana kiranta "muneeba muneeba"ta juyo yadda idanuwanta suka kada yasa yaji ya damu saidai sauri yakeyi yayi latti dole ma ya wuce yasan idan ya dawo akwai daru ya kada kai ya wuce cikin damuwa da tsananin faduwar gaba ya bude mota ya shige yaja ya fice,



cikin kuka ra fad'a dakin ummahnta wadda ke tsaye tana kaiwa da komowa tana sakawa tana kwance yadda zatayi da wanan lamarin da yake shirin bullowa muneeba ta fada kan gado ta fashe da kuka tace "ummah nashiga uku yaseer zai dawo hankalinsa akan husnah yarinyar da tuni muka dauke masa hankali akanta idan ya dawo hayyacinsa na tabbatar tawa ta kare a gidan nan gaba daya tarewa zaiyi wajenta dikda dai nasashi ya rubuta mata takardar saki"ummsh ta karaso tace "mummunan tashin hankalin da nake ciki kenan takardar saki kuma yabawa daddy saidai daddy ya yar da takardar yanzun haka baa ganta ba"zabura muneeba tayi tace "shikenan tawa ta kare nashiga uku ummah kiyi wani abu ya zamuyi mutafi wajen boka gashi karyar ciki nayi masa sam banaso hankalinsa ya koma kan waccen matar aljan din"ta Dora hannu akai kuka takeyi hawaye na zuba ummah ta dafata tana kasa da murya tace "ki kwantar da hankalinki inada tabbas akan boka nakan tudu matsafi ne na gasken gaske na tabbatar sai yasa husnah tabar gidan nan dan haka na yanke shawarar mu shirya yau muje wajensa inaso yanxun ki kwantar da hankalinki yarinyar da rainon aljanu ce me zaayi da ita? itama durkusar da ita zamuyi yarda ko sallah kin taba ganin tunda ta dawo tayi?dan haka kara burkitar da ita zamuyi nida zanga aljanin ma zance ya sake saceta tashi maza kije ki shirya"muneeba ta share hawaye cikin kidimewa tace "karyar cikin da nayi fa?"hajiya rabi tace "zamuje wajen boka akan hakan inta kama a sama miki ciki dik zaayi kedai tashi maza kije ki shirya"ta mike cikin sauri a kidime tasa hijab din gaba a baya ta fito kicibis sukai da kanwar momy mahaifuyar husnah kallon kallo sukayi ko gaisheta batayi ba tsaki taja mata ta watsa mata harara ta wuce,

momy na zaune ta zabga tagumi batasan zuwan yar uwar tata ba ji tayi an dafata ta zabura ta juyo cike da furgici ta dafa kirjinta tace "har kin tsorata ni ya naganki haka?da sassafen nan?"zama tayi gefenta tace "dubi yadda kika sauya?kina nan kina sakacin naki ko?ina husnah"momy ta nuna mata dakin da husnah ke ciki kwance tace "tana ciki takicin abincu saboda aljaninta jiya sun samu matsala yadda yake zuwa suyi hira su wuni tare bezo ba"jinjina kai tayi tace "tabdijan lallai kinyi sakaci aljanin ke shigowa har cikin daki?kina jinta tana maganganu kamar zautacciya zainab?sakacin da kikayi ya saceta shi kike Shirin karayi?kina zaune batare da an nema mata maganin da zasu rabu ba?wai ma tsaya kin tabasa karatun kurani ko kina azkar ke kanki balle kisata tayi ki koya mata?husnah na tabbatar ko sallah batayi tunda ta dawo ko?"momy jikinta ya mutu ta tsare yar uwarta da ido taja nannauyar ajiyar zucuya ta fashe da kuka tace "wallahi wallahi damuwa tasa dik na rikice narasa yadda zanyi"tsaki tayi mata kawai ta mike ta nufi dakin da husnah take.....
*******
hafeez ya gama shiri ya makara zai fita ya tuno da takardar daya dauka ya saka a aljihunsa da sauri ya karasa basket din kayan wanki ya dauko wandonsa ya ciro takardar abinda yayi tozali dashi ne ya kare ware iso ya sake karantawa yaseer ya saki husnah?ya karasa sakin da yayi mata?ya jinjina kai amma shin daddy yasan hakan da momy?take zucuyarsa ta bashi amsa basu ganiba kenan takardar ya kawo bai samu basu ba ta fadi shi ya dauka ya gani i har daddy da momy da husnah basu ganiba bata saku ba ya kamata ya maida takardar nan yasa takardar a aljihu ya fito yana sauri sai kamshin turare yake zubaea ummahnsa tace "to dan gidan daddy albishirinka"cak ya tsaya ya juyo yana kallon ummah ta jinjina masa kai yace "yesssss..... daddy zai dawo ko?"ta jinjina masa kai meenahl ta fito itama tsalle tayi yacev"alhamdulillah ummah daddy zsi dawo a daidai dan Alhaji badanasi yace in turo maganar auren husnah"ummah jikinta a mace ta daga masa kai zuciyarta cike da tsoro ya fice cikin farin ciki aiki zashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login