Showing 108001 words to 111000 words out of 130717 words

Chapter 37 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

195

kansa ya kasa gane meke faruwa tsakaninsa da ita dik yadda yakeson shiga harkarta taki bashi fuska yace "zainab har yanzun baki daina kukan ba ko?baki duba abinda ke gabanki zaki cutar dashi"ta dago jajayen idonta ta wurga masa harara ya tako ya shigo dakin jiki a sanyaye ya zauna gefen gado tace "zaman yayana nakeyi a gidanka zaman in haihu nakeyi dana haihu zan kama gabana"gaban daddy ya yanke ya fadi gumi ne ya karyo masa dakyar ya hadiyi wani abu daya tsaya masa a wuya yace "kamar yaya?"tanasane tabbas daddy ya dawo hankalinsa dik abun nan da yakeyi tamkar wani mai bataccen tunani tace "kaida kace in tattara inbar maka gidanka in nemi uban dan da girmana nayi cikin shege?kaida matarka kuka taru akaina"daddy ya girgixa kai yace "matata kuma?nidin mukai miki haka wace matar tawa?"dago ido tayi ta kallesa ta kauda kanta kawai batare da tace wani abuba ya tako zai karaso ta dakatar dashi gababta na tsananin faduwa tanason mijinta sosai tasan yadda badamasi ke tsananin sonta ta kara tabbatar da baya cikin hayyacinsa amma wanen abun dayasha ya dawo da kaso tamanin cikin dari na hankalinsa tace "nidai bana bukatar wata magana dakai kawai kabarni inji da matsalar da yata ke ciki"

"yarkice ke kadai?"ya watso mata tambaya a sanyaye batace komiba ta mike ta gifta ta gabansa ta fice abinta ya dade ya kasa motsi sanan ya fita daga sashenta sashensa ya nufa cike da damuwa da tunani kala kala....
******
"jinin ya tsaya?"tambayar da yaseer yayiwa husnah kenan tad'anyi farrr da ido ta jinjina masa kai "ehh gaskiya niban gansaba dai ya tafi"a yangace tayi maganar ya saki baki yana kallonta mamaki take basa yace "Mai kikeso na siyo miki?"tayi shiru tayi jimm kadan tace "banaso ka wahalar da kanka"yace cikin shauki da kauna "Allah ko?"gyaran murya ummah hadiza tayi musu kunyq ce ta lullube husnah ta rufe fiska yaseeer ya fice yana dariya,

ummah hadiza ta gyara zama tace "ke bude idonki ki kalleni"husnah ta bude ido cike da kunya ta sunkuyar da kai tace "karkiji kunyar mijinki ko kadan kinaji na mace a gidanta yar iska take zama idan kinki waccen karuwar kishiyar taki zata kwace mikishi"tadan bude ido ummah hadiza ta jinjina mata kai tace "kwarai dagaske dan idonta yafi naki budewa amma nima dikda ba yar zamani bace zan budar miki da naki idon zan koya miki yadda zaki karbi mijinki a hannunki kafin wata ta karbe mikishi"husnah tayi ajiyar zucuya ta maida hankakihta gaba daya kan ummah hadiza kamar ance ta waiga taga kamar gilmawar abu tayi saurin kallon wajen ummah hadiza ta kalli inda husnah ta kalla tace "yadai?"tace "wani abu nagani ummah naga wani Abu dogo ta nan"yinkurawa ummah hadiza tayi tace "nusrah ruga ki kiramun yaseer maza ya dawo wanan shedanin yazo"nusrah ta fita jiki na rawa ummah hadiza kitchen ta shiga ta dauko tabarya aguje zaninta na kwancewa yaseer turus yayi ganin ummah hadiza da tabarya yace "lafiya meyafaru?"ya kalli husnah jikinta nata rawa tace "kamar abinda nagani a mota"yaseer idonsa suka firfito yace "yau koni koshi a gidan nan"muryarsa sukaji "ka isa kayimun wani abu kana bil'adama ina aljan karka manta da nidin Zan iya sauya halitta daban daban in kuma yi dik abinda nagadama dan haka bazan taba barin abinda ke ciki. husnah ba"ya fito dankareren maciji ya zagaye gadon yayi mugun girma yusrah da akabari gidan ita tayi saurin turawq momy message ta wayarta Yaseer ji yayi gaba daya wani karfi da kwarin gwiwa yazo masa husnah kuwa cikin tashin hankali take jikinta na rawa yaseer cikin sassarfa yake fadin"karkiji tsoro ki kwantar da hankalinki babu abinda zaiyi miki ina tare dake"girgiza macijin yayi kansa ya rikida ya koma mutum sai sheki yakeyi bakin kirin ummah hadiza jikinta sai rawa yakeyi ta kasa motsa tabaryar dake hannunta yaseer yayi addua ya murza hannunsa ya kaiwa Abraham cafka.....


"momy in zakuzo kuzo da malam kawai ga yaya yaseer nan aljanin nan ya fito masa zasuyi fada karya kashe mana yaya momy"cikin kuka yusrah ke labe tana wayar ummah hadiza sakin tabarya tayi zaninta ya kwance taja da baya zata afka musu sukaji an rukota ta Baya momy ce suka dawo dama basuyi nisaba tafiyarsu da malam yaseer na rike da Abraham ruko sosai yayi masa dikda irin nauyi da yadda iska ke wujijjigasa bai sakesa ba addua kawai yakeyi da karfi gumi kawai ke karyo masa.....


*WANAM LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANRAMUN BANYAFEBA*


07042277401



*SLIMZY*✍🏻
46
momyn husnah na tsaye cikin kitchen ta gama had'a miya taji gabanta na tsananin faduwa ta rasa dalili kashe wutar gas din tayi ta fito da sauri zucuyarta kamar ta fasa kirjinta ta fito yadda gabanta ke fas fas kicibis sukayi da daddy ya fito da makullin motarsa a hannunsa cikin sauri ya rukota yadda yaga tanayi "ke lafiya?meyafaru ko jikin ne?"girgixa kai tayi tace "bugun zucuyata ya tsananta husnah nake tunani tamkar wani abu na samunta hankalina ya kasa kwanciya"tayi maganar fuskarta a daure daddy ya shiga damuwar yadda hajiya zainab keyi masa yana kokarin yin magana ta fizge hannunta ta dauki hijab dinta dake jikin kujera cikin sassarfa ta fito hajiya rabi ma ta fito zata sashen muneeba "ah ah Alhaji lafiya ya naganku haka?meyafaru kuma? halan cikin ne ya zube na husnah"wani kallo daddy yayi mata yace "fatan da kikeyi kenan banason iskanci da rashin mutunci rabi wace irin magana ce kikeyi kamar kinci Kashi?"mamakine ya kasheta "alhaji ni kake cewa wai ina magana kamar kashi"tsaki yayi mata ya fice cikin sauri ta bishi da kallo daddy cikin tashin hankali yake gidan innah zashi ya sanar mata da halin dayake ciki dangane da zainab....

momy na shiga jikinta ya kama rawa jin muryoyin mutane cikin gidan dakyar take d'aga kafa tana shiga su momy da malam suka shigo wuceta sukayi yadda suke cikin sassarfa tace"ah ah meyake faruwa"malam be jira me zataceba ya shiga da sallamarsa yaseer ya matukar jigata yadda yake rike da Abraham yana wujijjigasa saida momynsa ta girgiza ta kira sunan Yaseer da karfi "yaseer "rukota ummah hadiza tayi "ki kwantar da hankalinki saude ga malam yazo na tabbatar zaasamu maslaha wanan aljanin daya addabi rayuwar yarinyar nan"malam bece komiba ya sauke jakarsa ya curu turaruka masu karfi yayi addua dik ya watsa cikin dakin nan da nan katangar dakin ta zamewa Abraham kamar wuta babu yadda zaayi ya fita malam ya kalli yadda yaseer yake a jigace yace "ka sakeshi na dauresa babu inda zashi"yaseer a wahale yace "na sakesa?kana ganin yadda yake a suffar maciji zai iya cutar da husnah"gimi kawai husnah keyi ta sharbe da hawaye kasa motsin kirki tayi malam yace "ai ninace ka sakesa ko?"cikin wani irin azama yaseer ya sakesa ya fadi kasa yadda ya jigata ko motsi yaseer ya kasayi ji yakeyi tamkar ya dauki dutse,
cikin wata irin murya Abraham yace "malam kasakeni in tafi bazan sake dawowa ba karku kasheni kauna da soyayyar husnah ke dawainiya dani wanda na rayu dashi shekara da shekaru"tsumu tsumu su ummah hadiza sukayi momy tace "ikon Allah yau gamu ga aljani bamu gudu ba lallai in bala'i yayi bala'i dolema ka hakura"
gyaran murya malam yayi yace"inaso ka fadamun labarinka kaida wanan baiwar Allahr da yadda akayi ka sarku da ita kuke rayuwa shekara da shekaru harka saceta".....rikida Abraham yayi ya rage girma fuskarsa ta fito karara a jikin maciji wasu hawaye ne ke zubowa yace"wanan itace silar shakuwata da yarta"ya nuna momy dake tsaye jingine a jikin kofa dukkansu suka juya cikin mamaki,

lokacin da ta haihu bayan kwana bakwai ....takan ajiye yarinyar a daki ita kadai babu kowa ta fito tayita sabgar gabanta ni kuma cikin gidansu wajen wucewata ne akwai wata rana nazo wucewa na rinka jin kukan jinjira a daki cikin iska da guguwa na taho ta cikin gidan mahaifiyarta nata aiki a kitchen tana fadin "kiyita kukanki husnah bazan ajiye aikin da nakeyi inzo mu zaunaba inada abunyi"tausayin jinjirar ya kamani na wuce ta cikin dakin na Shiga ina shiga na sauya kamannina na koma mutum sak amma ba babba ba na dauketa na rinkayi mata wasa har tayi shiru jin motsin maman nayi saurin ajiyeta sai naji tana cewa "ah tou waya fada miki barno gabas take gashi ai kinyi shiru"tazo ta dauketa ta bata nono anata kiraye kirayen sallahr magriba ta sake akiyeta har natafi nayi nisa a cikin iska nasake jiyo kukanta nadawo na kula da ita a hakan na saba da ita sosai mahaifiyarta bata taba ajiyeta tayi mata addua a inda ta ajiyeta a nan take barinta tabbas nasha zuwa wajen husnah inga wasu jinnu masu cutarwa wadanda suke sata kuka na koresu a haka husnah ta saba dani sosai tasanni dik kukan da takeyi idan nazo ta ganni tanayin shiru,wani lokaci ma bana zuwa inda zani tare muke wuni da ita tunda koda yaushe uwarta ajiyeta takeyi tayi sabgoginta har tayi wayau sosai bata taba lura da cewae idan ta ajiyeta a daki ita kadai zatajita tana wasa tana dariya ita kadaiba tasha shigowa daukar abu ko yin wani abun ta ganta zaune ita kadai tana wasa nine nake wasa da ita har dauketa nakeyi inyi yawo da ita muyi shawagi in dawo da ita sakamakon mahaifiyarta bata damu da kulawa da itaba,

hawaye ya wanke fuskar momy dukkansu cikin tashin hankali suke da gumi ke karyo musu,wanan dan uwan nata sau dayawa shi yake daukarta yayi wasa da ita shi yake renonta idan yatafi makaranta nakanzo a suffarsa sakk inyi wasa da ita batare da mahaifiyarta ta gane cewar bashi bane akwai wata rana husnah nacin abinci ta zuzzubar a wajen tazo tayita mata fada tayita kuka sai gani nazo tana ganina tace "abokina"tana kallon wani sashe na cikin dakin,

momyn tace "ke waye abokinki kuma?har wani aboki gareki bansaniba?kodai Yaseer kike magana?"husnah ta jijiiga kai tace "ah ah momy inada aboki bakisanshiba yana zuwa ya daukeni mu fita yawo muje can wani waje"momyn tace "kin cika sambatu husnah"ta tafi tabarta na shigo ta rungume ni sosai tanajin dadi yarinyar ta shiga raina sosai yakai daddare ina zuwa wajenta sau dayawa mahaifiyarta zata farka cikin dare ta ganta zaune tana wasa tana magana ita kadai lokacin tana shekara daya da wata takwas bakinta ya bude nine na koyawa husnah magana sosai,bata damuwa zatace "Kar kiyi baccin kiyita zama"mahaifinta yasha tambayarta dawa husnah ke surutai a shekararta bekai tayi wayau haka ba dole akwai wanda ke koya mata hakan amma bata damuwa bata taba bincikar metakeyi ba dikda cikin surutanta tana fada mata abokinta kaza abokinta kaza,tsananin son da nakeyiwa yarinyar yasa bana zama cikin jinsin mu kullum ina tare da ita sakamakon mun shaku har yakai idan zan tafi kuka takeyi zata bini,tsananin kaunar da nakeyi mata mahaifiyarta tasha nemanta ta rasa ta dudduba wurare bata gantaba bata damuwa saidai tace tasan tanacan tana wasa da yaseer sau dayawa ba wajen yaserr takeba wajena take"husnah ta kalli mahaifiyarta idonta jajir cikin tsananin damuwa da jin haushinta

malam yace "tabdijan, Tou ya akayi ka saceta?"yayi girgiza yayi kuww hade da kururuwa yanason guduwa dik inda ya dosa babu hanyar gudu malam ya daddauresa tamau yace "wata rana ana magriba husnah tana wasa wajen gate dinsu yaseer ya taho zashi masallaci ya rukota taxo wajensa tanayi masa surutai lokacin shekararta biyu da sati biyu yace"ki jirani husnah zanzo yanzun bari naje nayi sallah nadawo"ta makale kafada tasa kuka ya fice ya rufo gate din ina tsaye bata ganniba tana juyowa muka hada ido tausayinta ya kamani ba kalli cikin gidan ba kowa sai ita kadai tana wasa mahaifiyarta bata damu da killaceta ba a wanan lokacin manyan shedanun aljanu lokacin suke yawo lokacin cikin gidansu dik mutanenmu ne sun baza kaya tanata yawo na rukota"zaka tafi dani?"tace idonta cike da hawaye na gyada mata kai tace "katafi dani abokina kaji?"na jinjina mata kai nima inasonta banaso daidai da minti daya in nisanceta ina samun matsala sosai da mahaifiyata akan husnah saboda bana zama cikinsu ranan nasawa raina tafiya da ita haka na dauketa natafi da ita cikin iska......bayan natafi da ita nasamu matsala sosai da yan uwana yadda suke kyamarta babu wanda yake sonta hakan yasa dik inda zani da ita nake zuwa nasamu matsala sosai da mahaifanaa akanta tun basu amince da itaba ganin son da nakeyi mata zasu rasani yasa suka amince da ita nina bude mata ido take ganin kowa a suffar mutane a duniyar mu dik wani abu da takeso inayi Mata shi ko menene koda zan cutu kakata wadda husnah tasani da goggo kande itace ta rikemun ita take kula da ita babu me yunkurin cutar da ita dik wanda yace zaiyi hakan kuwa sai inda karfina ya kare a haka nake rayuwa da husnah bana bata abincinmu abincinta nake bata ina zuwa da ita Rafi insa hannu in kamo kifi in gasa mata ta saba dani nasaba da ita tsananin shakuwarmu tasa nasan aurenta ne kadai zaisa mu dawwama tare saidai a yan uwana aljanu akwai mesona wadda itace narjisu itace silar dawo da husnah duniyarku wanda a yanzun take hannunku"

hajiya saude ta kalli momyn husnah ta girgiza kai tace "sakacinki ya jefa husnah cikin halin da take ciki tabbas nakara gasgata cewar baason barin jarirai su kadai a daki batare da anyi musu addua ko ankara musu wani abuba gashi ya tabbata innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"ta zauna dirshan ta fashe da kuka,

kururuwa Abraham yakeyi ya soma rokon malam "Dan Allah kada ka rabani da husnah ina tsananin kaunarta karku rabamu itama tana sona husnah tasan irin gwagwarmayar da nasha akanta ko kafin na aureta"malam ya jinjina kai tabbas akwai sabo da shakuwa tsakanin husnah da Abraham saidai aljani bashida amana kuma bashida alkawari dik yadda zaiso karya kashesa yasan tunda yana sonta bazai taba daina bibiyarta ba,

gyaran murya malam yayi yace "ku aljanu bakuda amana kuma bakuda alkawari idan har na kyaleka yanzun na tabbatar zakayi abinda yafi hakan tunda abinda ke cikinta kake hari idan har na kyaleka na tabbatar abinda zakayi gaba sai yafi wanan dikda irin tausayin da kabani da ganin bakada laifi wajen daukarta mahaifiyarta ce mai laifi"

Abraham yana yawo cikin dakin yana rimi yana hankoro "koda kun kasheni ko kun illatani da soyayyarta na rayu kuma bazan taba daina sonta ba"

furucun da yayi yasa malam yayi yunkuri yayi addua ya tofa masa sanan ya soma karatun alkurani cikin dakin mai girma yana daga murya Abraham ihu yakeyi cikin dakin cikin tsananin azaba,

yadda yake kururuwa da kuwwa ba karamin tausayi yabawa husnah ba kuka ta fashe dashi tanaso ta hana a kashesa ta kalli Yaseer ya cije lebe ta tashi dakyar wani jiri ke daukarsa har yanzun kafadarsa kamar ba tasa ba ihu Abraham yakeyi yana fadin "zaka kasheni kana konani karka kasheni koda ka kasheni zan mutu ne da soyayyar husnah a cikin zuciyata.....

cikin momy ne ya karta mararta taji tanayi kamar zata bude ta durkushe kasa cikin tsananin jin ciwo tace "wash marata".....da sauri ummah hadiza da hajiya saude sukayi kanta....

******
gumi ke karyowa daddy a dakin innah tace "haka zakayi hakuri da auren hajiya rabi da kayi badamasi dikda yadda kake nunamin kamar baa cikin hayyacinka kake ba"wayarsa ce tayi ringing cikin damuwa ya cirota a aljihunsa ya kalla yace "ummah hadiza ke kira"ya dauka ya kara a kunne yana jiyo karatun alkurani sanan cikin numfarfashi yakejin ummah hadiza na fadin "badamasi kazo fa zainab zata haihu"ta kashe wayar ya yunkura ya mike takalmin hagu a dama yasa innah tace "kai lafiya ina zaka meke faruwa"dakyar yace "zainab ce zata haihu"

"banga ta zama ba nima"innah ta yunkura a waje ta yafa mayafinta ta bi bayan daddy dako ganin gabansa bayayi.....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*🫣kuyi maneji yau sunday oga na nan.....🤪
47
a gaggauce ummah hadiza da hajiya saude suka shiga da momy cikin gidanta suna kokarin shiga da ita cikin daki hajiya rabi ta taresu "lafiya?meke faruwa meyasameta"tana kokarin rike momy hajiya saude ta dakatar da ita "ba sai kin riketa ba ina mijin naku yake?"tabe baki tayi ta harde hannuwanta a kirjinta tace "ita zan tambaya tunda ai tare na gansu suka fita"yunkurin nishi momy takeyi gumi ke karyo mata basubi ta kan hajiya rabi ba suka Shiga daki da ita horn din motar daddy ummah hadiza taji ta fito da sauri sukai arangama da daddy "ina zainab din take?"

"tana cikin daki tare da saude inaga abun nan akan gaba take ko zamu barta a gida karta haihu a mota?"gumi daddy ya goge innah ce ta shigo cikin sauri ummah hadiza ta tarbeta "ah ah innah tare kuke kenan dashi"

"ehh yaje gidana muna magana bamu karasa ba saiga kira ina zainab din take ko zamu tafi asibiti ne?"muneeba ce cikin takun kasaita ta shigo sashensu tana tura ciki dakyar innah ta kalleta tace "ikon Allah ke kuma fa? wanan ciki muneeba kodai yaya goma ne ciki haka yayi girman?"murnushi muneeba tayi tace "sannunku ina yini?"hajiya rabi ta taho da kissa ganin daddy "dama yanzun zan kiraka ince ko zakazo muje akai zainab asibiti?"wata harara daddy ya watsa Mata sanan cikin basarwa yace "ummm gani nazo ai sun kirani"yaja gauron numfashi ya sauke ya harde hannuwansa a kirjinsa ya koma gefe cikin damuwa muneeba kallon yadda daddy ya amsawa hajiya rabi tayi da mamaki ta kalli mahaifiyarta wadda ta ruko hannunta dakyar suka nufi sashenta.....

ummah hadiza tabisu da kallo innah ma kallon muneeba takeyi cike da mamaki tace "ikon Allah kenan ku duba yarinyar nan cikin daban uwar jikin daban ni gaba daya tausayi take bani anya bazaaje aji yara nawa ne a cikin ba?"murmushin takaici ummah hadiza tayi "tou ai ance baaga cikin ba"dafe kirji innah tayi zatayi magana hajiya saude ta fito ta jike da gumi sharkaf cikin farin ciki ta rangad'a gud'a tace "Alhamdulillah Zainab ta sauka"jikin daddy na rawa yace "haba metasamu ina take?"yana kokarin shigewa dakin hajiya saude ta dakatar dashi"kada ka Shiga ban gama da itaba inaso ummah hadiza mu taimaka mata nadai yanke cibiya ta sauka tasamu yara biyu maza"cakkk daddy yayi ya kasa magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login