Showing 66001 words to 69000 words out of 130717 words
ya barsu a wajen hajiya rabi ta rufa masa baya suka nufi daki yaseer yayi mata wani kallo dayasa ta natsu yana nunata da yatsa yace"ke idan kikace abinda zakiyi kenan bazaki tabajin dadin zama dani ba anfada miki ina sonki kamar yadda nakeson husnah ne?a rashin husnah nasameki har kikaga na saki jiki dake banmasan yadda akayi nafara sonki ba wallahi"yayi kwafa ya fice ya nufi sashin momy g dare shasshekar kukanta yajeji ji yayi kamar ana watsa masa wuta a jikinsa tsayawa yayi jikin madubi Abraham na gefensa Yana kallon madubin ya furgita fuskar Abraham ya gani cikin mummunan kama idanuwansa kyar akansa jajir fuskarsa baka kirin ga wasu kunnuwa Masu ban tsoro kayan saki ne jikinsa ya zabura yayi baya yace "A'uzubillahi"momy tace "lafiya?"ya girgiza kai ya gyara tsayuwa gefe yana waige waige bai gansa ba daya kalli madubi sai yaga wanan mummunar kamar husnah na kuka ta taso ta tsaya gefensa kamar ance ta waiga sukai ido hudu da Abraham ta kwalla kara zata zube yaseer ya rungomta jikinsa tsamm ya riketa ta runtse idanuwanta jikinta sai rawa yakeyi yace "husnah kinga abinda nagani"bakinta na karkarwa tace"nagani dama wanan dodon kagani"yaseer yayi murmushi yayi hamdala yace"tou shine kike ikirarin shine mijinki"Da sauri ta bude idonta ya jinjina mata kai yace "aljani baya rikida a jikin madubi shiyasa kikaga kamanninsa haka yana zuwa miki kyakkyawa kamar balarabe ko?tou babu mummunar halitta kamar aljani kinga yanzun sanadinsa gashinan ana kyamarki mahaifinki ya shafa sanadin haka yasa mutuncin daddy ya zube dikda dai ni ya taimaka hk kikeso kiyi rayuwa dashi ana kyamarki dagake saishi dik rungumekin dayakeyi bakisan dodo ke rungumeki ba?"zabura tayi ta zauna tace"dama dodo ne ke rungumenu?"tashin hankali yaseer ya hango karara a idon husnah ya kalli momy tayi murmushi alamu sunyi nasara akan husnah girgiza kai ta shigayi "shikenan ya cutar dani amma ya cuceni asheshi dodo ne mai mugun kama yake canjawa yana zuwa mun ya yaseer yanzun ya zanyi?"ajiyar zuciya yaseer ya sauke yace"karki sake barinsa ya rabi jikinki kinji?"ta jinjina masa kai ta turo baki tace"momy kawai ya sakeni kinga yanzun daddy ma guduna yakeyi"tausayinta ya kamasu momy ta share hawayenta tace"da izinin Allah "ta rungume husnah itama ra rungumeta yaseer ya mike tsaye yace"momy kiyi mata addua bari inje ta kwanta zuwa safiya zan fita zani gidan innah akan maganar momyna datace dole saita koma gidanta"murnushi momy tayi ta jinjina masa kai yasa kai ya fice parlor ya tarar da husnah inda ya barota ta rafka tagumi cikin damuwa da tashin hankali take tana ganinsa ta mike zatayi magana ya rigata"ni zan tafi ki zauna a nan tunda tsoron kikeji"yasa kai zai fita da sauri tabi bayansa tana waige waige ta ruko hannunsa ya kwace hannunsa yayi gaba tana biye dashi,
husnah kwanciya tayi tai lamo idanuwanta basu daina fidda hawayeba kamannin Abraham data gani ya girgizata kodai bashi bane?kai shine tasani yaya yaseer bazai mata karya ba to idan ma bashi bane meyasa ake gudunta sabodashi?ta tabbatar yau Abraham abun tsoro ne tunda mahaifinta ke korarta saboda aljanu momy tace "yadai husnah"cikin tausayawa husnah tayi maganar ta girgiza kai tace "kidaina kuka kinji?"momy ta mike ta fice batare da tayiwa husnah addua ba tana fita Abraham ya fito ta jikin bango ya harde hannuwansa a kirjinsa ta juya baya tana kallon gefe daya tana juyowa suka hada Ido ta zabura ta koma ta zauna tana waige waige cikin tsoro da furgici tace"mai kazoyi?bayan kai dodo ne bansaniba sai yau kake rayuwa dani?ashe ku aljanu abun tsoro ne?dik na dauka kemanninka haka suke tabbas na gasgata hakan tunda narjisu na zuwa mun cikin kamanninku"cikin tsiwa takeyi masa magana ta Kura masa ido cikin ido tana kallonsa"meyasa ka saceni ka kaini cikin danginku dodanni?"furucin husnah ya bugi zucuyarsa yana mata wani kallo itama shi takeyi dikda zuciyarta cike da tsoro take tana kallonsa,"ni ba dodo bace bana komawa dodo bana canja kamanni in koma wani abu daban amma kai kanayi dik mai yasa?"ya tsayar mata yace"dakata husnah butulci zakiyimun?"idanuwanta suna fidda hawaye tace"ba butulci zanyi maka ba nasan gaskiyar lamari yau dikda baa gama fayyacemum komi ba gashi nasan komi ashe dik tsoratanin da akeyi a danginku ina gidanka lokacin ashe aljanu ne mutanenku?baka taba fadamun ba?kadaukeni kaje kana rayuwa dani?bayan nida kai ba halittarmu daya ba?ka cuceni tunda kasa nakamu da sonka alhalin kai ba mutum bane kamata ba halittarmu daya ba"ta fashe da kuka zucuyarta nayi mata kuna Abraham matsowa yakeyi fuskarsa na canjawa tana rikida tana komawa abun tsoro fuskarsa ta koma kamar bayan kada jajir wasu kulali abubuwa ke fitowa daga fuskarsa ya daga hannuwansa take ya soma rikida jijiyoyi na bullowa da wasu kumbuna yana takowa "baki isa kiyimun butulci ba karya kikeyi kina nufin zaki rabu dani ne bayan nima ina sonki?"tsorata tayi ta manna jikinta da jikin bango jikinta sai rawa yakeyi kamar mazari ta shiga girgiza kai tana runtse ido yazo zai kawo mata cafka ta diro daga gado zata fice ta ganshi a gabanta "nima zaka kasheni ne?toka kasheni ka huta ka kasheni"take cewa cikin daga murya momy ta jiyota ta zaburo ta bude kofar tayi tozali da husnah kamar mahaukaciya "momy gashi nan yazo gashinan yazo na tabbatar da shi dodo ne gashinan yana canja kamanni"ya bude bakinsa hakoransa kamar na damusa tagani ta kwalla kara momy ta furgita ainun ta rungume husnah ta rufe kofa husnah na bude ido ta ganshi ya fito ta jikin kofa ta zabura ta dauki abu zata bugawa Abraham taga ya kalli abun ya dawo mata momy ta dojw cikin tashin hankali momy ke addua a bakinta tana tofawa husnah a jikinta ta rufe ido sai gunji takeyi tana gurnani bata iya magana can taga husnah ta lumshe ido bacci ya dauketa yana tsaye jikin bango yana hawaye husnah tasan wayeshi yau sai ya kashe yaseer sai ya illata masa rayuwa tunda ya shiga gonarsa yana tsananin son husnah kuka yakeyi cikin wani irin yanayi ya bace.......
*Y'AN BATI INA SANE DAKU INADA LABARINKU DIK WANDA YA KARANTAMUN LITTAFI ALLAH YA ISA BAN YAFE MAI BA*
*LITTAFIN DUHU 300 KACAL KI BIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA GA MAI BUKATAR SIYA KO BIYA YA TUNTUBI WANAN NUMBER*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*
28
Da safe yaseer ya shirya tsaf cikin kayan aiki sun matukar karbar jikinsa yana gaban madubi yana gyara necktie dinsa muneeba ta shigo ta jingina da jikin bango ta cikin madubi ya kalleta suka hada ido ya basar yace"yadai naganki haka ko bakida lafiya ne?"tambayar da yayi mata kenan yana kokarin juyowa ta girgiza kai idanuwanta sukai jajir tace"sam nakasa Gane maka a y'an kwanakin nan dik ka sauyamun ka tsaneni yanzun wani ji kakeyi da husnah sam baka damu dani da abinda ke cikin cikina ba"tayi kwalkwal da ido ya kalleta ta rike kwankwasonsa ta kauda kai yace"Mai kikeso inyi miki ne muneeba?goyaki kikeso inyi kinaso ki rinka comparing kanki da husnah ko?kinsam cewar keda husnah ba daya kuke a zuciyata ba kowa da matsayinsa da naki matsayin itama da nata banason haka sanan inaso in gargadeki akan abinda kikaimun akan daddy kinji nafada miki idan ba hakaba zan dauki mummunan mataki akanki banason munafurci da rashin mutunci"hawaye ya wanke idon muneeba har zai wuce ta gefenta Ransa be masa dadin ganinta tana kuka ba ko babu komi akwai dansa a cikinta ya tsaya ta gefenta ya juyota kadan ya share mata hawaye yace"kukan na menene banason kukan kidaina kinji ko?"cikin sigar lallashi yayi mata maganar ta gyada masa kai yace "saina dawo zan fita aiki yanzun zan shiga sashen su momy inga yadda suka kwana saboda hankalina bai kwanta ba"nan ma wani mugun haushi da tsananin kishi ya turnuke muneeba ta kasa Masa saiya dawo yasa takalminsa ya dauki makulli. motarsa a gaban tv da wayoyinsa ya rufo kofar fadawa tayi kan gado ta fashe da kuka cikin daga murya tace "nashiga uku maike shirin faruwa dani?kardai yaseer ya dawo hankalinsa nasani dik soyayyar da yakemun dama baya cikin hankalinsa aikin boka ne"take ta tuna da yadda ya kwanta da ita jiya yadda takejin bananarsa na yawo a gabanta tamkar kogi yadda take zamewa tana fitowa dako a matse take gam ta rafka tagumi cikin tsananin tashin hankali take ta mike ta zauna ta mike tsaye ta shiga kaiwa da komowa cikib dakin ta d'ora hannunta akai tana hawaye menene mafita?take ta tuno da Anty sadiya kanwar hajiya rabi zata dawo yau tasan barikinta da tuggunta tasan zata warware musu matsalar dake shirin tunkaro su,
momy na tallabe da husnah wadda ta rame sosai ta tasa tea a gabanta tana kallon gefe daya dik ta rame ta hargitse tana jin motsi ta zabura tace"momy ga Abraham nan"momy ta rukota tana kokarin mikewa cikin tsoro yaseer ya shigo ajiyar zuciya husnah tayi tana ganinsa ta mike idanuwanta ya rufe rufff ta ruga da gudu ta rungumesa tana fadi"yaya yaseeer yaya yaseer ka taimakeni Abraham dodo ne yazo jiya zai kasheni kayimun addua kaji?"tsamm yaseer ya rungumeta sosai idanuwansa ya rufe jin nonuwanta a kirjinsa yasa bugun zuciyarsa ya tsananta momy na lura da yanayin da yaseer ya shiga dikda husnah matarsa ce mikewa tayi ta bubbuga husnah ta janyota daga jikinsa tana kara shigewa jikinsa tana kuka hajiya rabi ce ta shigo sashen ta soma tafa hannu "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun mai zan gani haka?yaseer wani irin iskanci ne zainab ke kokarin sakaka akai da zaka rungume husnah a kirjinka?ko so kakeyi aljanin ya sabauta ka bari in kira daddy na sanar masa halin da kuke ciki"yaseer zaiyi magana momy tace"dakata yaseer karkace komi ni zan bata amsa ko kin manta akwai auren yaseer akan husnah?ko kwanciya da husnah yayi bai aikata haramun ba saboda tuntuni akwai igiyar auren husnah akansa"
"tou igiyar auren aljani kuma fa?ko mutum da aljani take aure?"husnah na hawaye take kallon hajiya rabi idanuwanta sun canja kala saboda kuka tace"a rashin sani yasa nayi rayuwa da aljani wanda ya kasance abun tsoro ban saniba amma yanzun a shirye nake da in rabu dashi ta ko wani hali"yaseer ya jinjina kai hajiya rabi tace "ni zakiyiwa rashin kunya?lallai kin tsotsi nonon zainab bari mijina ya dawo mahaifinki zai zaba koni koke shashasha wacce aljani ya gama dannewa"yaseer yakai kololuwa wajen bacin rai gashi daya bude baki zaiyi magana momy ke dakatar dashi Momy tace"yaseer kama hanya katafi wajen aikinka karkayi latti kaji"husnah ta ruko hannunsa batare da tasani ba ji takeyi tana murza tafin hannuwansa yadda takeyi dana Abraham wani shauko da jin dadi takeji wanda batasan dalilinsa ba ya shagwaltu da yadda take wasa da hannuwansa kusan minti daya momy tace "wai yaseer bazaka kama hanya katafi wajen aiki ba saina bata maka rai"husnah ta kalli momy tace"tsoro nakeji banaso yaya yaseer ya tafi Abraham zaizo ya cutar dani"idanuwanta suka kawo ruwa yaseer ya ruko kafadarta ya zaunar da ita yace"bazai cutar dakeba ki kwantar da hankalinki kinji?da kinga ya kamo hanya zaizo ki karanta...."wayarsa ce tayi ringing yayi saurin dubawa momy ke kiransa ya danna dauka "hello momy?antashi lafiya?"cikin ladabi da kaskantar dakai yake wayar kamar tana ganinsa tace"yaseer kana ina?"ya kalli momy dake tsaye tana kallonsa yace"ina dakin momy zainab amma yanxyn zani wajen aiki dama inada niyyar idan nadawo zan tsaya ta wajenki"ta amsa da "toh shikenan "ya kashe wayar ya kalli agogo a gaggauce ya mike yace"momy saina dawo" ya mike ya fice momy ta matso da cup din tea data hadawa husnah tace "Karbi wanan kisha yanzun kinii?kafin yayanki ya dawo anjima kinii?"tausayin momy ya kamata tana hango tsantsar soyayyarta a kwayar idon mahaifiyarta yanzun ya taji rashinta na shekara goma sha takwas cikin ta sha tara?ta tsare momy da ido har saida tadan tsorata tace"yadai husnah?"ta girgiza kai tace"Babu komi"ta karbi tea din ta kurba wani d'aci takeji yana taso mata tsananin takaici da tashin hankalin da take ciki....
******
hafeez na kwance a daki ya tallabe kansa tun dawowarsu daren jiya yake cikin tsananin damuwa gashi daddynsa yaki saurarensa meenal ta turo kofa kanwarsa tayi shirin makaranta ta dade tsaye baisan ta shigo ba cikin sanyin jiki tace "yayahhhh"ya juyo yadan kalleta ya kauda fuskarsa dake jajir cikin dasasshiyar murya yace "yadai?"murmushi tayi tac"kaje inji su ummah"ya gyada mata kai ta cigaba da tsayuwa yace "ki wuce kibani waje nace ganinan zuwa"ta huya a burgice ta rufo masa kofar ya mike ya zauna yanajin tsananin jiri ya mike ya bude kofarsa yana takowa kansa a kasa ya karaso mahaifinsa yayi masa wani kallo ta cikin farin glass yace"kai bazakaje office yau bane?ko kanacan kana tunanin matar aljan ne?"ran hafeez ya baci zaiyi magana ummah tace"rufemun baki shashashan banza kawai ashe dik wanan abun da kakeyi da firirita iyayen yarinyar suma basuda hankali bantaba sanin Alhaji badamasi dattijon banza bane sai yanzun"hafeez yace"ummah kun kasa gano kan wanan lamarin ba laifin daddy bane wallahi yarinyar nan kunsan batada lafiya ban boye muku ba sanan wanan aljanin bazai taba bari dama wani ya aureta ta dadi ba dole sai ya bullo da surkulle da siddabaru kala kala na tabbatar idan ance muku daddy bashike magana ba karkuyi musu kila ma aljanin ne yayi shigarsa yazo wajen tunda ba yau ya saba ba"ummah tayi kasake tana sauraren hafeez ganin ta natsu yasan zata fahimcesa ya gyara zama yace"haka ranan ya dauketa yayi shigar yaseer da ita nagansu nadauka shine ashe ba yaseer bane nima yayi shigata suka dauka nine nadauketa ashe bani bane ku fahimci wanan abun babu abinda aljani bazaiyiba ganin ya cutar da kai ya cimma burinsa"shiru daddynsa yayi yana kallonsa cike da mamaki yace"idan ko haka ne munyiwa alhaji badamasi mummunar fahimta dan ni yanata kirana a daren ma banbi ta kan wayarsa ba "hafeez ya sauke ajiyar zuciya yayi murmushin jin dadin sun fahimcesa yace"daddy Dan Allah kubarni in taimaki yarinyar nan saboda itadin abun taisayi ce"daddy ya jinjina kai yace"tashi kaje kayi breakfast katafi aiki zamu tattauna da ummahnka"ya mike cikin farin ciki yayi kewarta yanaso ya Ganta yasan halin da take ciki anya ma zai iya zuwa wajen aiki batare da yaje yaga husnah ba?....
*******
zaune take a parlor tayi shiru tana kallon tv a zahirin gaskiya hankalinta na kan tv amma a bad'ini zuciyarta ta lula cikin tunani tashar arewa 24 take kallo tayi wanka tasaka wasu kayan momy tana zaune tayi nisa cikin tunani mutanen cikin tv suka fara sauya mata daga mutane zuwa wata halittar ta daban ta waro idanuwanta tana kallonsu sosai wani namiji tagani kamanninsa sak kamannin da Abraham yazo mata dashi mai ban tsoro jiya yana nufota kamar zai fito daga cikin tv ta mike ta tsaya da sauri cikin sassarfa tasa hannu ta kashe tv tana ajiyar zucuya kafin ta juya an kunna tv sautin murya takeji daga cikin tv"kashewa kikayi saboda bakiso kiyi toxali da dodo?ai tinda kika kirani da dodo husnah ni masoyinki yanzun na sauya daga halittar da nake zuwa miki yanzun kika fara ganina kuma bazan taba rabuwa dake ba"gumi ne ya karyo mata tana waige waige babu kowa a patlorn zatayi magana taji an buga kofar parlorn ta juya da sauri bataga kowa ba tasake juyowa ta kurawa tv ido tagansa cikin fuskar tv ya tsura mata ido idanuwansa na fidda hawayen jini cikin tashin hankali take rawar baki tana fadin "yanzun kukan jini kakeyi saboda ka cutar dani nagano ko kai waye?"ya kafeta da ido ya bude bakinsa ta tsandare ihu aguje momy ta shigo dakin daidai nan Anty sadiyya ta shigo da akwatinta cikin gidan tana fadin "lafiya nakejin ihu gida kamar gidan yan bori?"hajiya rabi ta fito daga dakinta cike da farin ciki ta rangada guda tace "lale marhabin da zuwan yar uwata barka da zuwa"sadiya ta tsaya tana kallon sashen momy shekeke ta sheke da dariya tace "ya nakejin ihu cikin nan kuma ko kishiyar taki ta soma hauka ne?"hajiya rabi tace "husnah ce ta dawo kedai dan gata can aljani take aure matar aljan ce a cikin gidan"Anty sadiya ta dafe kirji cikin shakiyanci tace"banga ta zama daku ba tunda kun koma rabi mutum Rabi aljan"suka sheke da dariya hajiya rabi ta ruko hannunta cikin farin ciki suka shige,
momy ta tallabo husnah tace"yadai?menene husnah?"husnah ta rufe ido tana nuna mata tv "momy gashinan cikin tv bazan iya bude idanuwa na ba"momy ta kalli tv film din gidan badamasi ake maimaitawa tace "husnah ai tv ne wanan film ake maimaitawa bude kiga"husnah ta mike idanuwanta rufe ta nufi daki aguje
******
cikin farin ciki momy ke kallon daddy kabiru yayan alhaji badamasi suna tare a babban parlorn innah yace"ki kira yaseer din yanzun yazo nan ya samemu nina maida aurensa da husnah kuma babu wanda ya isa ya canjamun hukunci daga yau ko ince daga yanzun yaseer yanada damar da zai kusanci husnah tunda matarsa ce"innnah ta jinjina kai tace"dakyau naji dadin wanan hukuncin sanan inaso kafin a gyarawa husnah dakinta kamar yadda hajiya saude tace a tattarota a maidata gidanta kawai nasan zatafi jin dadin zama tunda gasu nusrah da yusrah nan zataji dadin zama dasu"hajiya saude ta jinjina kai tana laluben wayar yaseer bakinta yaki rufuwa ummah hadiza ta rangada gud'a tace "mashaa Allah yaseer ya zama mijin mata biyu "duka suka kwashe da dariya yaseer na cikin driving yaga kiran momy ya girgiza kai ya dauki wayar yace"momy gani nan a habyar gidanki na kusa karasowa banmaje wajen aikin ba"tace"bana gida ka karyo kwana ka taho gidan innah inacan yanzun haka muna tare dasu babanka kabiru"ya jinjina kai ywce"gani nan zuwa"ya kashe wayar ya shafi sajen sa hafeez ya fad'o masa a rai yarasa meye dalilin gabarsa da hafeez sam hafeez ya tsanesa shima bai nemi jin hakan ba"ya dauko wayarsa kamar ya kirasa ya maida wayar ya ajiye ya karya kwanar gidansu innah hankalinsa na kan halittar data raba titin biyu cikin tashin hankali yake kallon wanan dabbar dake tunkaro motarsa kafin ya kauce tuni traila tayo kan motarsa wani karaaa yaji kuuuuuu.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
29
kifa ciki husnah tayi ta runtse idanuwanta tana sauke numfashi data rufe ido shi take gani tadan bude idonta a