Showing 48001 words to 51000 words out of 130717 words

Chapter 17 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

200

zan rubuta a rubuce shedar na saki husnah muneeba shikenan ko?"ta mike ta zauna da sauri jikinta har rawa yakeyi tace "ka rubuta yanzun"ya jinjina Mata kai ya janyo ledar da suka dawo ya cicciro mata kayan daya siya mata yana nuna Mata tana kara shagwabewa a zuwan mai ciki.....
*****
"hafeez ka fadamun gaskiyar lamarin wanan accident din naka ban yarda ba jikina na bani wani al'amari ne tattare da kai wanda kake boyewa bakaso in sani hafeez kafadamun gaskiya"ummah ta tsaresa da ido yayi wankansa fesss yace "babukomi ummah wallahi accident ne ki kwantar da hankalinki naji sauki yanzun ma zan dan fita ne inga wanda ya taimakamun yazo yana kofar gida yanzun haka"ta jinjina kai nan ko malamin da yayi zashi wajensa ne ya kira a waya yazo hankalin ummah bai kwanta ba ta bishi da kallo tana girgiza kai sam batasan meyasa ba gabanta ke faduwa akan hafeez tamkar wani abu zai sameshi takeji,

yana bude kofar gidan yayi tozali da malam ibrahim ya fad'ad'a murmushin "ashe kazo malam barka da zuwa ai na hadu da mummunan hatsari akan hanyata ta zuwa wajenka dazun wanan aljanin ne ya bini kiris ya rage ya kasheni"

Abraham ne yazo a suffar malamin da hafeez ya kira bai saniba yacev"ai kasan su aljanu musamman bakake mugunta garesu sai an mike anyi dagaske sanan"hafeez ya jinjina kai yace "muje ko?"ya bude motar daddynsa da ita zasu fita ya shiga Abraham ya shiga ya zauna a gaba hadeez yayiwa motar key yayi horn mai gadi ya bude gate suka fice..... tafe suke hafeez cike da mamaki yakeyi yana satar kallon malam ibrahim Wanda ke zaune a gefe Abraham ya rikida ya koma yadda yake hafeez na kokarin parking a kofar gidansu husnah yana juyawa sukayi ido hudu da Abraham ya furgita sosai yana kallonsa yana murmushi yace "kadai dage saika rabani da husnah ko?ka dage saika bakunci lahira ko?"hafeez ya girgiza kai cike da tsananin tsoro"Abraham yace "banso na fito maka a ni bane yanzun amma hakan be yuwuba saboda yadda zucuyata ke azalzalata niba mugu bane amma kun dage kaida iyayenku sai kun rabani da husnah ko? niba mugu bane amma kuna kokarin koyamun mugunta sakamakon dagewa da kukayi ganin kun rabani da masoyiyata abar kaunata ko?tou zamu kulla zamu saka kafar wando daya daku dukkanku zan batar dakai zan kasheka"yace cikin kakkausar murya cike da tsananin fushi addua sosai hafeez yakeyi a bakinsa suna kallon kallo shida Abraham ganin adduae da hafeez keyi yasa ya bace daga cikin motar shiru hafeez yayi ya kifa kansa da sitiyarin motar cikin furgici tsaf aljanin nan zai rabashi da ransa amma yaci alwashin ganin husnah tasamu lafiya koda zai rasa rayuwarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan ya tura kofa tozali yayi da husnah zaune tayi tagumi tana ganinsa ta mike ta tsaya ta nufoshi da sauri "yaya meyasameka?"tambayar da tayo masa yasa gabansa ya fadi Yana kallonta cike da tsananin so da kauna ta kalli goshinsa cikin rawar murya tace "kaji ciwo"ya jinjina mata kai yace "zonan zo"ya yafitota tana kokarin zuwa Abraham ya shiga jikinta kallon dayaga husnah tayi masa yasan ba ita bace wucewa tayi ta canja hanya ta nufi bayan gida da ita ya fita a jikinta ya tsaya Yana mata wani kallo tsoro da furgici ya kamata metayi masa yadda taga yana canjawa yasa ta furgita zata gudu ya fuzgota ta fada jikinsa ya matseta cikin karfi tayi yar kara yace "kin isa da aurena ki rinka magana da wani?ba nace ki daina kulasa na bakijiba ko dama ba sona kikeyi ba karya kikeyi?"kishi ya rufewa Abraham ido sam bega hawayen dake zuba a idon husnah ba tsabar azabar dataji rukon da yayi mata ya cigaba da magana yace "babu wanda zai rabeki ya zauna lafiya koda uban daya haifeki ne"ta fuzge daga rukon da yayi mata tana hawaye jikinta na rawa iska ce ke kadawa buuuuuuu a wajen tace "mahaifina fa kace Abraham mahaifina kake zagi?"a Karo na farko da husnah taji zafin Abraham tace "karka sake mummunan furuci akan mahaifina dik son da nakeyi maka zan iya hakura dakai'yana kallonta idanuwansa sukayi fari soll hawaye ya wanke mata ido yace "tou shikenan ki gwada in bakisan wayeni ba zan nuna miki cikakken ni aljani ne bazan taba Bari kiyi rayuwa da kowa ba saini nafada miki kuma zan baki mamaki zam horar dake yadda bazaki kara mun kuskuren abinda kikai ba"ya bace ta durkushe a wajen tana kiran sunansa "Abraham..... Abraham kadawo kayi hakuri nayi kuskure kasan ina sonka"kuka takeyi kamar ranta zai fita tana waige waige tana nemansa cikin kuka ta taho ko ganin gabanta batayi sukai karo da yaseer wanda shima besan da ita ba ji yayi sunyi karo ta fada jikinsa tana kuka ta rungumesa kammm "nasan bazaka nisancemiba Abraham kar kayimun haka kadawo ko nasan bazaka tafi kabarnina"yaseer ya tureta yana kallonta kamar zararriya take kallonsa idanuwanta sunyi jajir sum tattashi yana kallonta tana canja masa cikin wani irin yanayi yake kallonta lokaci Daya idanuwansa ke haska masa wata yarinya mai suffarta wadda yayi rayuwa da ita a Baya saidai besan wacece ita ba...

****
muneeba cikin zumudi take labe a cikin bedroom dinta ta kita ummahnta tana dauka tace"albishirinki ummah"cikin kosawa da son jim mai yar zatace tace "goro meyafaru muneeba"
muneenba tayi murmumushin takaici tace"yaseer ya taho cikin gida da takardar sakin husnah saki uku ya taho ya kaiwa momy takardar yanzun haka"tsalle hajiya rabi tayi cikin tsananin farin ciki tace "Alhamdulillah"suka sheke da dariya hajiya rabi tace ",ina nam inata tunanin abinda yaseer yasha zaisa ya dawo hayyacinsa idan ya dawo hayyacinsa ma a banza tunda saki uku yayiwa husnaj kinga babu aure tsakaninsa da ita harabada"muneeba farin ciki tayi tsalle tana rawa ta kashe wayar


Abraham ne ya shige jikin husnah ya sauya mata kamanni yaseeer gani yayi tana rikidewa ta koma wani gabjejen mutum mai ban tsoro lokacin da take kara nufosa aguje ya nufi cikin gida cikin kidimewa ita kuma husnah tsoro yasa ta zube a kasa tana kiran "momy momy ki gudu ga zaki nan zai kasheku ku gudu"ihunta yasa su momy da hafeez fitowa jin abinda take ambata ita a zaki take ganin yaseeer mai mummunan kama ita kuma ganin yadda take rikida yasa yaji tsoro yayi cikin gida yana sassarfa


gidan ke juya mata iska ta ko ina take kad'awa a hankali takebin ko ina da kallo yana sauyawa bakin kirin duhu ya garwaye ko ina bata ganin gabanta bata ganin bayanta ta kara tsandara ihu ta fadi ta zube.....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE WANDA YA KARANTA BAI BIYANI BA ALLAH YA ISA!!!*

KI BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT NUMBER DAKE KASA KI KARANTA CIKINSALAMA

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WABAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER
[23/09, 21:28] 🥰slimzy😍: 21

Hafeez zaune cikin al'ajabi yake bawa su innah labarin abinda ya faru dashi cike da damuwa hajiya saude ta wuce su suka rage ummah hadiza tace "lallai hafeez ka auna arziki Ashe da wanan mugun aljanin ya rabaka da ranka da mai zamucewa mahaifiyarka na tabbatar batasan inda kajeba"momy cike da tausayawa take kallon kulum fuskar hafeez ta jinjina kai ta sauke numfashi tace "sannu hafeez sannu kaji gashi wanan lamarin bansan ya zanyi dashiba yaseer sam bayason husnah hasalima ya mance da ita bata gabansa hajiya saude ta kasa gane hakan da badan husnah akwai auren yaseer akanta ba babu abinda zai hana ban amince maka aurenta ba dan nasan zaka sadaukar da rayuwarka da farin cikinka dan ganin tasamu lafiya dikda yaseeer ya furta kalmar saki"aguje yaseer ya shigo yana haki "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun lafiya yaseer meyake faruwa?meyafaru kaida waye ko barayi ne?"nuna kofa yakeyi cikin haki yake sauke numfashi yana fadin"itace....itace wallahi dodo ce ba mutum ba"dik a furgice suke suna kallon kofar shigowa cikin rudani innah kakar husnah kamar ta ruga aguje tace"wacece?"yaseer yayi shiru ya dafe kirjinsa yana rike da takardar sakin husnah yace "hus....hus"ya kasa karasa sunan ummah hadiza da hafeez rige rigen ambatar sunanta sukai a tare "husnah?"ya jinjina musu kai momy ta rushe da kukan takaici cike da masifa idanuwanta sun rufe take fad'in Allah ya wadaran wanan aljanin da yake tare da yarinyar nan ya hanata zaman lafiya wanan wace irin masifa ce dik inda yake tsinanne ne shi bazai taba gamawa da duniya lafiya ba mugu azzalumi"hafeez bai jira cewarta ba ya fice aguje shida ummah hadiza da innah wadda keyi baya baya Abraham ne tsaye jikin bango Yana sauraren furucin momy idanuwansa suka kad'a sukai jajir cikin fushi yake mai tsanani danne zucuyarsa yayi yadda jikinsa ke girgiza dakin ya shiga juyawa yana girgiza kamar ana dukan kasa waige waige momy keyi babu kowa sai yaseer dake tsaye kamar an dasashi yanabin ko ina da kallo danne zucuyarsa Abraham yayi dan yadda yayi fushi zai iya fitowa daga jikin bango idan kuwa yayi hakan tabbas momy mutuwa zatayi ganin hafeez ya dauko husnah yasa Abraham ya mike yayi girgiza ya shige jikin husnah yayi mika mai karfi sai gashi ya watsar da ummah hadiza da innah wadda dama baya baya takeyi mikewa tayi ta tsaya tanayiwa hafeez wani mugun kallo idanuwanta sun furfito waje tayi kwafa tace cikin wata irin murya "karka sake kuskuren kai hannunka jikin husnah dan husnah matar aurece idan kuma kayi kuskuren hakan to tabbas zaka yabawa aya zakinta"momy a fusace ta mike tana nuna husnah wadda sam ba ita bace Abraham ne a jikinta tace "karya kakeyi aljanin banza mutumin banza mutumin wofi kai inhar sonta kakeyi tsakani da Allah bazaka taba zama tare da ita kana cutar da itaba mugu Azzalumi kasani akwai kiyama sai anyi mana hisabi da Kai"jikin momy na tsanani rawa takeyin maganar cike da fushi yaseer ya rukota yadda jikinta ke rawa ya zaunar da ita kiris ya rage ta yanke jiki ta Fadi Abraham jingina yayi a jikin bango a jikin husnah gashin kanta ya yamutse ya mimmike shedar ba ita bace ummah hadiza tace "wai ina Badamasi yake ne besan meke faruwa bane yazo ya kira mana malami a Diba yarinyar nan dake tsananin shan wahala"Abraham kallonsu yakeyi cike da takaici yau da adan momy uwar husnah bace yau da sai ya nakasata sai ya maidata abun kwatance batasan baa nunasa da yatsaba take nunasa take masa mugun furuci saboda tsananin son da yakeyiwa husnah yasa yau tunda yake be taba fushi da itaba sai yau darajar husnah tasa ya kyaketa innah ta karbe zancen "ina badamasi yakene shin?"momy ta girgiza kai ta nuna mata sashen hajiya rabi wanda yake a rufe,
idanuwan hafeez sunyi jajir yake takowa gaban husnah wadda ke tsaye Abraham ne yacev"kai da ace mutim na ganin aljani wallahi da sai nayi wasan Kura da kai dan na tabbatar ni dan adam nafika daraja ninkin ba ninkin saboda haka ka matsa kabani wuri kafin in tofeka da ayar Allah"hafeez yace yana kallom Abraham dake kallonsa ido cikin ido kwayar idanuwan husnah kadai yadda ya sauya zuwa kalar ruwan toka babu fari saika furgita,yaseer na tsaye gabaki daya ransa a bace yake haushin hafeez yakeyi ji wani zakewa da yakeyi akanta?wata zucuyar tacewa yaseer meye naka kaida ka rubuto mata takardar saki?mtsww tsaki yayi ya kalli takardar ya riketa da kyau gabansa ya yanke ya Fadi ji yayi yanaso ya kalli fuskarta ya kasa hakuri da daina kallonta tabbas yasan yarinya mai irin kamanninta anan gidan amma meyasa tunda tazo bai tuna da hakan ba?to wace yarinyar ce?dan tsaki yayi ya dago kai suna hada ido ya runtse ido namiji ya gani fuskarsa baka kirin idanuwansa jajir hakoransa a waje ya rufe idanuwansa jikinsa sai kyarma yakeyi tsoro da furgici suka cikasa hafeez ya bude baki cikin karfin hali da dauriya dikda yadda yakejin faduwar gaba ya soma kokarin karanto addua zai tofa Abraham ya shakesa.....

cike da kwarkwasa hajiya rabi ke zaune gaban daddy tana zuba masa shagwaba irinta manyan mata daddy washe baki yakeyi yana zaune dagashi sai singlet gefensa jug ne na juice da aka hada masa yaji magani ga farfesun Naman zabo nan ya dauki cinya ya yaga ya tauna dadi ya ratsashi ya runtse idanuwansa tayi yar dariya tace cikin kissa "yayi dadi ko? nayi makashi na musamman ne nasan zakasoshi idan ka gama akwai alkubus a waccen kular"daddy ya jijina kai yace "dik ni kadai?"ya gyada masa kai hajiya rabi najin bugun kofar da akeyi ta basar amma shi daddy beji ba ta dau remote cikin kissa tace "Bari in kara mana karar tv banaji"zata kara cikin tsawa da daga murya innah ta kwala kira tace "badamasi"da sauri daddy ya kalli hajiya rabi ya ajiye cinyar naman dake hannunsa yana kokarin hadiyewa yace "kamar muryar innah"zatayi magana ta kara kwala masa kira "badamasi ka fito mana sai kace kana zaune da kai?"ya zabura ya mike ya dauki rigarsa Ransa a bace ya bude kofar itama hajiya rabi rai a bace ta biyosa"yanzun dik bugun kofar nan da nakeyi zakuce bakujiba kazo muje husnah babu lafiya Aljanin nan ya tashi zai kasheta gatacan sai rikida takeyi"ran daddy ya Baci ya kalli hajiya rabi tai kicin kicin da rai tace "nice dai baaso aganni nasamu sukuni da mijina babu wasu aljanu wanan yarinyar karya takeyi nina gaji"a fusace daddy yayi gaba innah tana kallon hajiya rabi shekeke tace "to gamandi mai hada uba da y'a makira"hajiya rabi tai mata wani kallo tabi bayan daddy,

hafeez dakyar yajejan numfashi shakar da Abraham yayi masa cikin ikon Allah ummah hadiza da momy jikinsu sai kyarma yakeyi ya sakesa ya kwalla kara wadda daddy na kokarin shigowa sashin ya furgita ya shigo kamar an jehosa yanke jiki tayi ta Fadi idanuwanta a rufe karar faduwanta yasa yaeer saurin kallonta mamakinsa bai ganta a dodon da yake ganinta ba gashin kanta ya rufe gefen fuskarta sai wata yar kwalla dakebin gefen fuskarta.... shiru yayi daga bisani ya kauda kansa hajiya rabi ta saci kallon da yaseer keyiwa husnah ta jinjina kai tabdijan ta zame jikinta ta koma gefe ta turawa muneeba message,

"wani irin abu ne wanan gidana ya koma kamar na y'an bori zainab meye haka wani irin iskanci ne waban haka?"Yana nuna husnah wadda ke kwance a hankaki take bude idanuwanta tana binsu da kallo daya bayan daya tana kallon daddy dake tsaye a fusace a hankali ta mike ta zauna tana murtsuka udo daddy ya dakawa husnah tsawa "ke tashi ki zauna"ta kallesa tana kara kallonsa tadan tsorata yace "dake nake kitashi ki zauna"yana nunata da hannu yace "wani irin iskanci ne wanan kikeyi kega mai aljanu?babu dama in nemi inuwa in Raba in huta sai an kirani gakican kina aljanu?to bazan dauki iskanci ba kinji nafada miki idan duniyar aljanun zaki koma ki koma damacan nayi hakuri dake balle yanzun"hawaye suka zubo a idanuwanta tana binsu da kallo daya bayan daya waige waige takeyi lokaci daya ya fado mata Abraham dinta gabanta ya fadi ya bace ya rikide bata gansa ba baya mata fada tunda take sai yau gashi yayi fushi ya tafi ya barta daddy nayi mata fada ita batason fada yazo ya dauketa su tafi can inda suke rayuwa bazata iya second daya babushi ba muneeba ce ta shigo kamar an jehota idanuwanta suka sauka akan yaseer dake tsaye gefe idonsa kirr akan husnah a karo na farko ta bashi tausayi hawayen da takeyi ji yakeyi kamar yaje ya share mata hawayen,
innah ta katse masa tunani ta hanyar maganar da takewa daddy "badamasi da bakinka kake cewa husnah ta koma duniyar aljanu saboda ta hanaka rawar gaban hantsi da matarka daka aura?baka godewa Allah ba da husnah ta dawo yanzun kakeso ka butulce masa saboda lalurar datake tare da ita?"
cikin fushi dady yace "innah babu wata lalura harda iskanci nafada miki karya ne kawai so takeyi taita daukar hankakina nina gaji bazan iyaba idan tasake makamancin haka saina daureta a gidan nan"daddy ya juyo ya kalli hafeez Wanda tuni kwalla ta cicciko a idanuwabsa tsabar tausayin husnah yace "kai kuma in dagaske kakeyi tunda yaseer ya saketa saika turo iyayenka ka aureta kuje can ku karata da aljanun"...jinnina kai hafeez yayi muneeba ta matso gefen yaseer jim kamshinta yasa yayi furgigit ya juyo sukai ido hudu idanuwanta sun kad'a tsananin kishi tajashi gefe tana masa wani kallo "mai takardar sakin keyi a hannunka baka bawa daddy ba"kansa nadan sara masa ya murtsuke ido yace "au kinganiko tashin hankali da rud'ani yasa na mance"ya janye hannunsa daga rukon dayayi mata ya mikawa daddy takarda daddy karba yayi be tambayi ta ko mecece ba ya rike muneeba ta ja hannun ysser suka fice ko ganin gabanta batayi,

"badamasi kabani mamaki tayaya zakai fushi da yarinyar nan bayan kasan ba yin kanta bane dik abinda takeyi?"daddy bece komiba ya juya a fusace hajiya rabi tabi bayansa takardar hannunsa ya saki a hanyar fita batare da yasani ba,
momy ta share hawayenta ummah hadiza wadda tai mutuwar tsaye ganin masifar da daddy keyi yasa jikinta ya mutu tabbad badamasi bayin kansa bane inba hka ba tayaya zaiyiwa husnah ruwan masifa dik irin son dayake mata dik irin damudaya shiga bayan aljanu sun saceta tsawon shekara goma sha takwas,

hafeez ya karasa gabanta ya tsugunna ya dago kanta ganin hawaye na gudu ta runtse idanuwanta tace "ka daina tabani yaya hafeez ni matar aurece amma yau mijina yayi fushi dani sakamakon kulaka da nayi be tabayimun hakan ba yayi fushi ya tafi ya barni ina kewarsa gashi niba aljana bace ballantana in bace in bisa inbashi hakuri ina tsananin kaunarsa ka fadamun yadda zanyi ya dawo gareni"tsura mata Ido yayi yana hawaye tausayinta ya kamasa ta bude idanuwanta yana hango tsantsar damuwa a fuskarta da tsananin soyayyat aljani sanan dik abinda take fada gaskiyarta take fada,kasa yi Mata magana yayi dole zaije gida yasamu ummahnsa akan maganar nema masa auren husnah....ya mike ya kalli momy kallo daya ya mata ya kauda kai yadda ta fita hayyacinta yace "zantafi momy yamma tayi saida safe"a sanyaye innah tace "d'an albarka Kenan Saida safe"kicibis yayi da takardar da yaseer yaba daddy wanda ta Fadi a kasa ya dauka ya zura a aljihu ya fice....
*******
Abraham cikin dajinsu ya shiga ya tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login