Showing 102001 words to 105000 words out of 130717 words

Chapter 35 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

202

hadiza tayi batace komiba ta nufi toilet da Ita ta shigar da ita ta dauko buta ta mika mata "maza yi alwala kiyi ina kallonki ki fito zan jiraki kiyi sallah wato an fito da tsurfar hanaki kiyi sallah ko?"babu musu husnah ke alwala tiryan tiryan suna fitowa sukaji anja wani mugun tsaki hade da kwafa husnah taja da baya tana kallom ummah hadiza cike da tsoro tace "kinjifa kinji ummah?"tsaki tayi kawai ta shimfida mata dadduma "oya maza tada sallah kafin raina ya baci idan kin idar kizo kiyi hayaki kafin mijinki ya dawo nina rasa ina yaseer ya shiga ma mtswww"husnah ta tada sallah ummah hadiza na zaune gefen gado harta idar ta kama kanta tayi mata addua tace"tashi muje bazan barki ba nasani ko zai shigo tayaki fira munafukin"ta fuzgo hannunta husnah naso taji meyakeson fada mata tana jin tausayinsa sosai suka fito nusrah tasa tv zatayi kallo ummah hadiza ta sauya tashar zuwa ta karatun alkurani suna nan zaune gaba daya husnah hankalinta ya rabu biyu ta rasa meke mata dadi dan zaman da sukeyi da yaseer a dakin momy tana masa shagwaba yana biye mata ta fara sabawa dashi ko ina yaje oho,take wata zucuyat tace Yana tare da matarsa kin manta ku biyu ne?"wani abu ne yazo mata wuya ya tsaya mata,

"ummah akwai komi a gidan nan ko?me zaa dafa ne?"Ummah ta jinjinawa nusrah kai tace"komi akwai dik abinda kikeso ki Shiga ki dafa mana ni yanzun inata jiran wanan ja'irin yaron ne....
******
momy ta fito da hijabinta ta nufi sashen daddy inda take jiyo muryarsu ta shiga da sallamarta ta zauna yadan kalleta sau daya ya kauda kai hajiya rabi ta watsa mata wata uwar harara "yadai kika shigo me kikazoyi"daddy yace yadda yayi maganar kamar ya sauko momy ta karanto adduoi kafin tace "nazo yi maka sannu da zuwa ne dama naji shigowarka"tabe baki hajiya rabi tayi ta turo dankwalinta gaba tana kad'a kafa suka hada ido batare da daddy ya ganiba tace"yau din nan zaki gaba yau zakibar gidan nan"tayi mata nuni da hannu tana dariya hade da harara dariya taba momy murmushi kawai tayi mata,daddy nacin abinci yadan saci kallon momy suka hada ido wani kallo tayi masa irin kallon da take masa ya gigitasa gani tayi ya ajiye cokalin ya juyo gareta mamaki ne ya cika hajiya rabi ta kalli kular abincin data zuba masa magani ya cinye tasss befi cokali daya ba boka ya sanar matada cewar dayaci bazai gamaciba batareda ya saki momy ba amma gani tayi kamar yanaso ya sakewa momy ta gyara zama cike da kissa ta kalli momy tace "masu ciki kenan nikam zainab yaushene watan haihuwanki?"wani kallo momy tayi mata ta dauke kai daddy yace "badake take magana ba ki amsa mana zainab banason bakin hali kibar ganin na sake dake harna barki kim zauna mun a daki"momy tace "nima bansaniba dan bana zuwa asibiti"daddy ya kalleta ya kalli cikin kyau sosai cikin yayi mata gata nan da kurucuyarta kamar ko yaushe bata canjawa yarasa dalilin dayasa inhar zai ganta zai rinka ganinta tamkar bakin kumurci ko bakar karya sam bayason hada ido da ita zucuyarsa nayi masa zafi ,amma yau yana kallom cikinta tabashi tausayi,ta mike tana daga kafa dakyar tace "saida safe"ya dan bita da kallo hajiya rabi ta kafesa da ido,

momy tsaye tayi a jikin kofar dakin daddy wasu hawayen farin ciki suka zubo mata yau Alhaji badamasine ya kulata?tana kallon yadda yake satar kallonta lallai tayi bacci tayi sake irin saken datayi aljani ya saace mata ya gashi dataje canja abincin bayan ta zuba ta tofa addua cikin abincin yaci gashi har ya kulata?ta girgiza kai tsakaninta da rabi Allah ya isa....

******
muneeba na kwance kirjin yaseer tana shafa gashin kirjinsa dake kwance luff bacci sosai yakeyo dik yadda taso ta juyashi tasamu kansa ya kusanceta ya kasa sakamakon bashida karfi kara rungumota yayi cikin bacci da magagi yace "husnah....husnah ya jikin naki?yadai?"yace kamar bugagge tsaki muneeba tayi yana bacci yana kiran sunan husnah saboda tsabar jaraba?husnah da momy bokansu na aiki amma zatayi maganinsu yau zataga yadda zaayi ya kwana dakin amarya,wata harara tayi masa kamar yana ganinta ta turesa ta zame jikinta Daga nasa,

bugun kofa taji da sauri ta zuro kafarta kasa ta kalli agogo karfe goma na dare to waye zai buga mata kofa yanzun?ummah?ta tambayi kanta badai ummah ba tasan tanacan makale da daddy ta muskuta wani nauyi kafafuwanta keyi bugun da akayi na biyu ne yasa yaserr mikewa furgigit kamar a mafarki yaji bugun yana fadin "husnah ina rigata?"muneeba tayi tsaki cikin kasa da murya tasan ya dauka a dakin husnah yake tace "ka kwanta bari naje na duba waye ke buga kofar"girgiza kai yayi "ah ah bazaki fitaba darene karkije aljanin nan ya daukemun ke ya zuro kafarsa yana lalube cikin saa yaji rigarsa a gefe ya zura cikin duhu yake kallonta mamakin ganinta da katon ciki yakeyi idonsa har rufewa yakeyi tsabar bacci bugu na uku ne yasa yayi saurin kunna fitila muneeba ya gani yana bim dakin da kallo "muneeba?a dakin nan nake dama?"tambayarta yakeyi cikin wata irin murya yace "magana nake miki"sosa keyarta tayi cikin murya mai ban tausayi a sanyaye tace "bacci ne fa ya daukeka shine nakyaleka ganin ka gaji"tsawa ya daka mata "karya kikeyi "cikin sauri ya fice ya nufi bugun kofar yana budewa yaga ummah hadiza tsaye tace "au Yaseer dama dakin matarka kazo ka kwanta?dik kiran da ake maka bakajiba kenan?"ta kalli muneeba dake bayansa ta zumburo baro ummah hadiza ta jinjina kai tace "ehh lallai to Alhamdulillah tunda kana nan Bari intafi na lallashi husnah data shiga damuwa take kuka akanka"cikin wani irin yanayi jikinsa na sassarfa yace "ummah wallahi bacci ne ya daukeni shine bugun kofarki ne ma ya tasheni kila da sai safiya tukunna zanga anan na kwana Dan Allah kiyi hakuri"yasa kai ya fito ummah hadiza tayi gaba tana jinjina kai tqbbas tasan shiri ne tini hakan yasa tazo ta wargaza shirin tasani yana nan ta tabbatar da hakan tun ganin da tayi musu da sadiya da kiran da akai masa tasan shiri ne tabbas zata zaunar da husnah akan kishiyarta dole tana tafe yaseer na biye da ita ana yayyafi sama sama,

muneeba wani ihu tayi cikin dakin tsananin bakin ciki ko gani batayi tayi jifa da kofin dake centre table cikin wani yanayi ta barke da kuka tana fadin "wallahi karyane baki isaba yaseer nawa ne ni kadai yaseer be isa ya kusanci wata maceba saini"ta kwanta a doguwar kujera tana kuka harda bubbuga kafa.....

******
direct dakinta ya wuce ummah hadiza ta wuce nasu dakin itada nusrah,
tana zaune ta mike kafa kan gado ta tsurawa gefe daya ido hawaye na gudu a fuskarta aka turo kofar taji motsin shigowarsa gabanta yadan fadi tayi saurin share hawayenta ta cikin duhu yake hangenta saidai dakin da dan haske kadan sakamakon window data bude wata iska mai dadi tana kad'awa ya karasa jikinsa na rawa "husnah husnah badai kuka kikeyi ba ko?"ta girgiza masa kai cike da dauriya tace "akan me zanyi kuka?meyasa me akayimun?inace kana can tare da matarka ne?"damm gaban Yaseer ya fadi ya hadiyi wani miyau mai daci jin yadda husnah ra jeho masa tambaya badai husnah kashinsa takeyiba kenan itama tana sonsa?katse masa tunani tayi tace "karkayi tunanin kishi nakeyi akanka ko daya bana kishi saidai ina cikin tsananin damuwa sakamakon muryar da kunnuwana kejin amon sautinta bana ganinsa yanzun tunda nasha wanan maganin muryarsa tanayimun tamkar nasanta"janyota yayi ya rungumeta wani farin ciki ne ya lullubesa yadda husnah ke magana sak mutum sabanin baya ko yace jiya jiyan nan kici kicin kwacewa takeyi yadda takejin kamshin turaren da ke jikinsa na bugun kanta amai na kokarin taso mata fuzgota yayi "com on kiyi hakuri nayi laifi bacci ne ya daukeni dakin muneeba kinji?ban kumasan nayiba dan na tabbatar itace sila amma zan nuna mata bacin raina"wato bacci akasashi?yana shafa gashin kanta yana yawo da hannuwansa a jikinta ya sauko da kansa wuyanta yana tsotsar wuyanta yana mata tafiyar tsutsa a jikinta wani yarrr takeji a jikinta ta lafe ta sauke wata ajiyar zucuya ya rungumeta sosai yana kokarin kai hannunsa breast dinta ta rike cikin wata irin murya tace "zafi sukemun"a hankali a daisashe yace "bazanyi miki da zafiba ina tsananin sonsu"ya soma matsa nipples dinta taja numfashi tace aushhhhhh hakan datace ya zautar DA yaseer ya soma mammatsasu yana shinshina jikinta kamshin ta dai na zautar dashi tuni yayi fancakali da rigar baccinta jin abu na zungurinta yadda ta mike tace cikin tsoro "zafi ni zanji zafi?"cikin shagwaba take maganar yace "bazanyi miki da zafi ba yau"murya kasa kasa yakeyi karar faduwar abu yaji tasss a cikin gidan nan da nan suka soma jin kofofi na karo da juna tamkar hadawa akeyi jikinta na rawa tace "tsoro nakeji kanajin ana bubbuga abu"

"shhhhh"yace ya hade bakinsu waje daya ya soma kissing dinta yana kokarin bude kafarta kofa yaji an buga gararam ta zabura ya janyota yasan ko daga ina wanan abun yake.....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*

08036953516
07042277401


*SLIMZY*✍🏻🥱bacci....🚶🏻‍♀️
44
Daddy karfe biyu na dare ya tashi ya zauna yayi tagumi ya rasa abinda keyi masa dadi ya kalli hajiya rabi dake baccinta cikin kwanciyar hankali ya kunna wutar dakin ya zauna gefen gado yayi tagumi cikin bacci taga haske a idonta tadan bude idonta hasken ya gauraye mata ido ta kallesa cikin muryar bacci tacev"Alhaji?"kiran sunansa tayi da sauri ya juyo yana kallonta "yadai ya kika tashi?"ta girgiza masa kai "hasken fitila ne ya tasheni naganka zaune menene ya hanaka baccu?"tambayar da tayi masa kenan kallonta yakeyi shima din besan meye ya hanasa baccin ba inama yanada amsar wanan tambayar, gyara zama yayi ya kwanta kawai yasa hannu ya kashe fitilar rufe idonta tayi ta cigaba da baccinta bayan minti biyar ya mike ya zura takalminsa dake gefen gadonsa ya fito haske ya hanga a sashen momy ya karasa cikin dauke sahun takunsa gabansa na faduwa ya tsaya daga baya baya hangenta yayi akan dadduma zaune alamu sun nuna addua takeyi sakamakon yadda ta daga hannuwanta sama bakinta na motsi ya dade yana kallonta sanan ya juya kamar ance ta kalli kofa tayi saurin shafawa tace"Alhaji?"cikin karfin hali yadan waigo ya kalleta dik adabarce yake yace "naam na fito neman ruwa ne"yasa kai ya tafi girgiza kai tayi ta daga ido ta kalli sama yau kacal Allah ya nuna mata falalar addua domin tasan adduoin da tayi a abincinsa da wanda takeyi yanzun ne yayi tasiri dikda baya cikin hayyacinsa amma alamu sun nuna gaba daya a daburce yake yana kokarin shiga sashen hajiya rabi sukai kicibis da ita ta tsaresa "Alhaji ina kaje da wanan dare?kardai kacemun sashen hajiya zainab kaje?"cikin rudewa take masa tambayar jikinta na rawa abinda bata taba tsammani ba tagani yadan giftata ya shafa kansa yayi tsaki kadan cike da damuwa yace "wallahi nakasa bacci sam bansan abinda ke damuna bane rabi nima kawai fitowa nayi naga sashenta da hasken wuta shine na leka ba wani abuba"dafe kirji hajiya rabi tayi kodai boka yayi mistaking bata maganine?ya bata maganin da Alhaji ke neman dawowa hayyacinsa?tunda yaci abincin jiya take ganinsa kamar wani zautacce,binsa tayi cikin dakin dakyar take daga kafarta tsananin damuwa da rudewa wuceta yayi zai shiga toilet tace "Alhaji me zakayi ne kazo ka kwanta karkazo da rana kana rama bacci idan ma bakada lafiya ne gobe sai muje asibiti a dubaka"

"Alwala nakeso nayi narasa abinda kemun dadi kuma kona kwanta bazanyi baccinba shiyasa gara nayi sallahar kawai"habtar cikinta ta tsarga take ta tuna da furucin boka matukar tabar alhaji yana sallahr dare bata dauke masa hankali ko yana azhkar to tabbas asirin zai karye kuma idan ya karye zata shiga matsala dan yaba tsananin son matarsa, gumi ne ya karyo masa ta mike cikin sauri ta rukosa ta cakumosa cikin kissa ta shagwabe "kasani a damuwa Alhaji idan ba ganinka nayi a kwanceba bazan samu kwanciyar hankali ba gaba daya na rude bansaba ganibka haka ba"saiga hawaye a idonta na bakin ciki a fili kuwa damuwa take nuna masa ajiyar zuciya yayi ta rukosa suna tafiya gabanta na faduwa suka karaso kan gadon da sauri tasa hannu ta kashe fitilar ta cukwikuye shi suka kwanta tanajin yadda yake sauke numfashi da wata irin ajiyar zuciya.....

nusrah mikewa tayi ta zauna gefen gado ta tattaba ummah hadiza dake munshari tace "ummah ummah tashi kiji motsin da akeyi cikin gidan nan nakasa bacci"

"umm umm umm motsi fa kikace ina motsin yake,kai waye nan wani shegen ne?"ummah hadiza tace cikin wata irin muryar bacci dik a daburce take ta mike ta zauna ta sako kafarta ta sakko dippp kasa ta nufi kofa daga bayanta nusrah ke biye da ita har parlorn gani suke haske na haska ko ina kamar ana wasa da touch light jikin nusrah ya kama rawa tace "ummah ummah tsoro nakeji muje ciki nidai muje?"bata rufe bakiba taji an bugo kofa hade da tsaki hade da kwafa,ummah hadiza ta tsaya tana karanto addua tana tofawa ko wani angle na cikin gidan ko d'ar bataji ba nusrah na Labe kamar tasaki fitsari daga bayansu sukaji ance "dik zamuyi maganinsu"wata murya sukaji zuhraliyya ce da wanan muryar nusrah ta ruko hannun "ummah hadiza muje muje ciki kinji me sukace"sai gumi takeyi har tana cin karo da kofa tayi ciki aguje take ummah hadiza taji kamar anyi ruwa an dauke dik buge bugen da akeyi ta kalli agogo karfe uku na dare an kusa kiran sallahr farko kawai tana shiga ta wuce toilet taje tayo alwala tazo ta shimfida dadduma ta soma sallah....

husnah na kwance a kirjin yaseer akai kiran sallar asuba a hankali ya bude idonsa ya saukesu akanta gashin kanta ya bazu a fuskarta yadda ta kankamesa tamkar zaa kwaceshi daga wajenta yasa hannu ya gyara gashin ta a hankali ya shafa fuskarta ya tsareta da ido pink lips dinta yake kallo da idonta a rufe saidai fuskarta tayi ja ya kallesa cikin hasken dakin ya rasa yadda zai gyara mata kwanciya ya tashi yayi wanka yadda ta rikesa a hankali yakeson zame jikinsa tayi caraf ta rukosa ta bude idonta jikinta na rawa ya kalleta "lafiya?"waige waige takeyi bataga komiba shiru wata ajiyar zuciya ta sauke "kinyi mafarki ne?fadamun ko kina ganin wani abu ne?"girgiza masa kai tayi tace "tun motsin da nakeji cikin dare dakyar nayi bacci ina zaka tafi kabarni ni tsoro nakeji"ta makalkalesa ya shafa bayanta ya mike ya zauna ya rungumota yasa hannu ya kunna fitilar gefen gado haske ya gauraye daki ya kalleta ya manta da tsurara suke tayi saurin rufe jikinta da bargo yayi dariya yace "tashi muje ciki muyi wanka to"ta makale kafadarta cikin shagwaba tace "ni saidai ka daukeni'ya kwaikwayeta yadda tayi wata dariya tayi da fararen hakoranta suka bayyana a jere wanda suka kara mata kyau, cakk ya dauketa suka shiga toilet ya kunna shower shida ita suna rungume da juna ruwa na zubowa tun daga kansu Yaseer ya nuna mata yadda zatayi wankan tsarki Tayi yadda yace ya janyota ya rungumeta yana shafata idonsu a rufe duk a jike suke rungume suke da juna yana shafo mazaunanta cikin wata irin murya tace"ba kace munyi wankan tsarki ba?"girgiza Kai yayi cike da shauki yace "kedin ce kin gama gigitani da soyayyarki musamman wanan shagwabar wanan jikin kuwa hmmmm wani sirri ne a cikinsa"dariya tayi sukaji anadan kwankwasawa ya rukota shhhh "ummah hadiza ce tazo tashin mu ne"ta zaro ido tace "haba nidai ba ruwana bari na fita"ya fuzgota yana mata dariya tana dukansa ya matseta a jikinsa yayi mata wanka tas yayi y dauro towel ya daukota suka fito an tada sallah a masallaci hakan yasa yajasu sallah sukayi tare....
*******
karfe tara na safe muneeba dakyar ta motsa kanta na tsananin sara mata sakamakon kukan da tayi jiya jinta tayi sharkaf Akan kujerarta tayi saurin mikewa ta tashi ta kalli jikinta rigar baccinta milk ce taga wani koren abu kamar mai alamar daga jikinta yake fitowa tayi saurin mikewa taga yana bin kafarta mararta ce ta karta mata ta durkushe wajen tace "washhh Allah na"saida gumi ya karyo mata ta rarrafa ta dauki wayarta ta kira Anty sadiya,

tana dauka tace "ah ah kaga yar dake kwacewa amarya kwana har kuntashi ne ko har yanzun be farfado ba?"yatsina fuska muneeba tayi tace "banida lafiya nikadai na kwana"

"garin yaya?ya akai hakan?"tsaki muneeba tayi tace "wanan ummah hadizar mana itace tazo ta biyoshi kai wanan matar anyi makira"Anty sadiya tayi ajiyar zucuya tace "wanan matar sai mun tashi tsaye akanta sanan ke dole ma muhada abinda zatabar gidan'

"nidai kizo wani ruwa ne yake zubowa daga jikina ban gane masa ba dana tashi da safe nagansa kuma ai cikin be kai watannin haihuwa ba"hajiya rabi ce ta shigo dakin ta tarar da sadiya na waya ta katse wayar tace "kinji wai muneeba ce wani ruwa kw zubowa mata a gabanta"dafe kirji hajiya rabi tayi cikin sassarfa tace "ruwa kuma?"Anty sadiya ta zari hijab dinta suka fito a tare momy na harabar gidan tana kiran mai gadi ta hadu dasu sukai mata wani kallon sama da kasa suka watsar hajiya rabi tace "dik biye biyen mutum wajen malamai saidai ya gama alhaji narigada na kwaceshi"momy tadan daga murya tace "inada malamin dayafi boka ni gashinan a sama shime malamina"suka wuce mai gadi ya taho suna magana da momy,

sadiya cikin rashin fahimta suna tafe suna kokarin shiga sashen muneeba tace "waini shin me kike nufi da abinda kikace zaa kwace alhaji"hajiya rabi taja numfashi ta sauke tace "wato kinsan Alhaji jiya kamasa nayi yaje sashen matar nan tsakar dare?nifa ban ganewa maganin nan da boka ya baniba sam saboda daga jiya zuwa yau ni gani nakeyi kamar alhaji zai dawo hayyacinsa"kwankwasa kofar sukai suka shiga ciki....

momy na dawowa sashenta ta kira ummah hadiza a waya cikin faraa ta dauka suka gaisa "ya kwananki da mutanen gidan nace ga abinci nagama ko akawo muku"

"ah ah munci mu ai mun koshi husnah da nusrah da yaseer a tare sukayi mana girki ya kike ya kwanan mai gidan?"momy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login