Showing 111001 words to 114000 words out of 130717 words

Chapter 38 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

192

yace "biyu maza?dagaske kikeyi saude?"innah cikin farin ciki ta daga hannu tace "Alhamdulillah Alhamdulillah "ta kwashi rawa ummah hadiza da hajiya saude suka shige....

*****
Abraham ihu yakeyi tin yana ihu ya gagara sai wani irin gurnani yakeyi wani irin hayaki ke tashi a dakin gabaki dayansu tari sukeyi cikin dakin husnah idonta dik ya firfito malam ya tsagaita da addua da karatun da yakeyi jin shiru "ka Kone ka yarda cewar zaka rabu da ita?"a wahale Abraham yake cikin wani yanayi yacev"na kone malam kayimun illar da bazan tashiba bazan moruba inaji a jikina mutuwa zanyi zanbar wanan duniyar da soyayyar husnah bil'adamar dana rayu da ita da tsananin kaunarta"yana gama maganar sukaji wata irin kara a tsorace yaseer yayi tsalle kan gadon da husnah ke zaune ya janyota ya rungumeta dakin ke wani irin juyawa wata murya sukaji ta mace "Assalamu alaikum"da sauri Yaseer ya gyara zama jin muryar yasan muryar bazai taba mantawa da itaba yace a hankali kowa na jinsa "narjisu....."malam ya amsa sallamar cikin kwarin gwiwa yace "ke wacece?"basa ganinta dukkansu kowa waige waige yakeyi tace "ni aljana ce narjisu malam ka kona Abraham kayi masa kunar da bazai sake moruwaba karshema ya mutu babu abinda yaja masa face taurin kansa da rashin jin magana da tsananin soyayyar da yakewa god'oyarku"malam yayi hamdala ya kalli yaserr murmushi yayi "zan taimaka masa zan daukesa zan tafi dashi sanan nayi muku alkawarin bazai sake dawowa ba"

cikin wata irin kasalalliyar murya mai cike da wahala da tsananin jin ciwo Abraham yace "husnah.....husnah nabarki husnah ina sonki nafada miki mutuwa ce zata rabamu yau gashi an konani sanadinki sanadin cika miki alkawarin da nayi bazan iya barinki ba"yana gama magana sukaga hayakin dake tashi a dakin a hankali yana bacewa cikin ikon Allah ko minti goma baayiba suka Nema hayakin suka rasa husnah ta kalli yaseer yadda yake a jigace sakamakon rukon da yayiwa aljanu ta rungumesa ta fashe da kuka shima kukan yakeyi yace "Alhamdulillah husnah yau kin rabu da wanan aljanin yanzun zamuyi rayuwa tare cikin kwanciyar hankali"ya dago fuskarta yana kallon yadda take zubar hawaye yace "menene yasa kike wanan kuka?"girgiza masa kai tayi ta kara rungumesa tace "ya bani tausayi yasaka kansa a soyayyar da ba jinsinmu daya ba babu yadda zaayi mu rayu tare a baya da nayi masa alkawarin rayuwa tare nayine a rashin sanin bansan banbancin mutim da Aljani ba banso aka konasa ba saboda kaunar da yakeyimun"yaseer ya shafa kanta yace "ki kwantar da hankalinki husnah idan baa konasa ba bazai taba daina bibiyarmu ba ko kadan kinga konasa shine maslaha"ta jinjina kai ya zare jikinsa daga nata yace "ashhhh wayyoo kafadata"cikin jim ciwo ya sauko daga gadon ya kalli nusrah dake zaune gefe yace "taimaka mata ku gyara dakin tayi wanka bari nasamu malam"ya fito dakyar yake takawa yasamu malam zaune a parlor ya zauna akan gwiwarsa yace "malam mungode bamu da bakin da zamuyi maka godiya"malam ya jinjina kai yace "kaima kayi kokari kai namijin duniya ne inba namijiba babu wanda zai damki aljani cikin suffar kumurcin maciji"yaseer ya sunkuyar da kai malam ya cigaba da magana yace "be mutu ba amma inada tabbacin zai mutu din saidai kasan aljanu sunada hadin kai sosai mu kuma bil'adama munada sakaci musamman da addua karkuga husnah tasamu lafiya sun rabu kuyi tunanin angama yakin ku shagala kar gidanta ya kasance babu karatun alkurani maana kullum ya zama cikin saka karatu koda bacci zaku kwanta banda yawan kallace kallace a ragesu sanan maganin da akace amininka ya bada tabbas shima ya bada gudunmawa kaso tamanin cikin dari wajen samun warakartq yanzun babu wani aljani da zai iya kusantar husnah da sunan zama a jikinta saidai tsoratarwa da abinda baa rasa ba"yaserr ya gamsu da maganganun malam sosai ya bashi wani hayaki yace "karbi wanan kuyi kaida ita inshaaa Allah angama da wanan matsalar"ya karba cike da girmamawa yayiwa malam godiya ya rakashi....

*****
"ummah anya wanan matar batasamu bokan dayafi nakiba kuwa?kina ganin yadda daddy yakeyi miki magana yana amsaki kamar bayaso abin nan ya bani tsoro ummah"hajiya rabi taja numfashi ta sauke cike da damuwa idanuwanta jajir ta dubi muneeba dake zaune ta mummuke kafafuwa tace "al'amarin akwai daure kai sosai muneeba saidai ninasan ta inda zan bullo musu yanzun ba gashi tana nakuda zata haihu ba bazan taba barinta da wanan d'an ba muneeba ke saina kashe dan tunda bansamu na kashesa a cikiba kuma Alhaji badamasi koda ya dawo hayyacinsa dolene ya zauna dani"cikin sauri sadiya ta shigo dakin tana numfarfashi ta rufe kofa dik sun tsorata kallonta sukeyi sun Kasa tambayarta dafe kirjinta tayi tana sauke numfashi tace "tou wallahi hajiya zainab ta haihu naji anacewa yan biyu maza ta haifa sanan naji kanwar yaseer ta shigo cikin gidan nan cikin farin ciki tana fadawa mahaifiyarta an kona aljanin husnah"

"mai kikace sadiya?kinsan me kike fada kuwa?"a haukace hajiya rabi ke magabar jikinta na kyarma dakyar kafafuwanta suka dauketa saboda yadda taji maganar kamar saukar aradu cewar Zainab ta haihu kuma har yara biyu kuma duka maza,baya baya tayi ta zauna dabas akan gado muneeba bataji nauyin cikin dake jikinta ba ta yunkura ta mike tsaye tana kallon sadiya biyu biyu dakyar ta saita natsuwarta ta hadiye wani miyau mai kauri na tsananin bakin ciki tace "kina nufin husnah ta dawo hayyacinta?husnah ta dawo sak mutum kenan ta rabu da aljanin mijinta?"girgiza kai tayi kamar mai aljanu tace "ah ah bazan taba yarda da abinda kike fadaba bazan taba amincewa yanzun zamuyi zaman kishi da husnah ba husnah fa? sanan cikin dake jikinta tana zubar da jini bai fita ba?"sadiya ta jinjina kai tace "tabbas bai fitaba kuma likita ya tabbatar da tanada ciki"a zabure muneeba ta ruko mahaifiyarta kamar mahaukaciya cike da bakin ciki idonta ya rufe tana girgiza hajiya rabi tace 'ummah baxan yarda ba bazan taba Amincewa ba ummah dole zan rabu da cikin nan na jikina cikin da bana yaseer bane ina bukatar cikin yaseer cikin da zai zama nima inaso agansa kamar yadda akaga cikin husnah"ta girgixa ummahntq tana kuka mai cike da damuwa da tashin hankali"ummah kiyi wani abu ummah ki tashi kiyi wani abu dole mu koma wajen boka ya ciremun wanan cikin dayasamun ina bukatar cikin yaseee"

sadiya ta ruko muneeba "ke haukar meye kikeyi haka?kishi ya rufe miki ido kinata zayyano maganganu idan wani ya labe ya jimu fa?"cikin daga murya cike da tsiwa muneeba tace "ya jimu"da sauri hajiya rabi ta ruko muneeba cikin tashin hankalin ganin yadda muneeba ke neman haukacewa ta riketa sosai sauke numfashi kawai takeyi gumi na tsattsafo mata tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi rungumeta tayi sosai tace "ki kwantar da hankalinki gobe zamuje wajen boka nasan koma menene yanada mafita idan ma haihuwa zakiyi zakiyi ki haifowa yaseer dansa kin manta yace dan dake cikinki na yaseer ne? aljani yasa ya dauko kwan yaseer ya shiga jikisa yasa miki?"kallon ummahnta takeyi kamar zararra sam bata yarda da abinda take fadaba cike da damuwa tace "ummah nidai muje gidan bokan yanzun?"sadiya da hajiya rabi suka kalli juna hajiya rabi bazata iyawa muneeba musuba itama tana bukatar boka yanzun yadda komi ya jagule mata tace "kije ki shirya"ta saki mahaifiyarta ta kwashi wayoyinta....
******
cikin dajin babu aljanin da babushi a wajen kallon yadda jikin Abraham ke zagwanyewa fuskarsa gaba daya ta koma kamar gawayi murnushewa takeyi kamar rushin dayayi toka kiran sunan husnah yakeyi a wahalce, zuhraliyya cikin kuka tace "waye yayi maka wanan abun?"narjisu dake gefe tace "shine yakai kansa tsabar taurin kai irin nasa yau bil'adama sun nuba maka halayyarsu na rashin sanin halacci dikda kaine ka kai kanka"tace tana hararar zuhraliyya zabariyya zubewa tayi akansa tana kuka mahaifinsa kuwa dik yadda akayi yayi magana a wajen ya gagarayi yana tsaye dogare da sanda jikinsa a sanyaye cikin tausayawa ya kallesu yadda suka zagayesa yace "ku matsa ku bashi wuri Abraham bazaiyi ba mutuwa zaiyi domin ya konu dayawa"ganin babu wasa a tattare dashi yasa kowa yake kaucewa kafafuwansu basa taba kasa yawo sukeyi akan iska haka suka bace hannunsa dafe da kirjinsa gefen zuciyarsa wani irin abu ke fitowa daga hakoransa da suka kakare waje daya a haka yake motsasu Yana kiran husnah idanuwansa na kallon sama yayinda yake iya hango showing dinsu itada yaseer tana dannawa yaseeer jikinsa haka Abraham ya soma wata shakuwa mai warin hayaki haka kansa ya langwabe cikin wani irin yanayi yace husss....nnh be karasaba ya daina numfashi,


husnah na cikin dannawa yaseer jiki taji kirjinta ya buga haka kawai taji jikinta yayi sanyi Abraham ne ya fado mata kwalla ta cicciko a idonta Yaseer jin shiru ya daga kai tana ruke da karamin towel yaga tana hawaye ya ruko hannunta yace "yadai? lafiya?"girgixa masa kai tayi ta share hawayenta tana matsa masa jiki haka suke jiyo bugun kofa suka saurara da kyau nusrah ce tana numfarfashi tana fadin "yaya yaya yaseerr Anty husnah momy ta haihu yan biyu maza"yadda towel din husnah tayi suka kalli juna da yaseer tuni ya yunkura ya mike ya rungumeta a jikinsa cike da farin ciki tare suka karasa wankan suka fito suka shirya a hanyarsu ta shiga gidan sun jero yayi kicibis da muneeba idonta dik sun kumbura sakin hannun husnah yayi ya karasa "yadai munee ina zakuje da yamman nan?"yatsina fuska tayi kamar bazata kulashiba ganin husnah ta tsaya ta tsaresu da ido yasa cike da kissa ta shagwabe masa tana kokarin rukosa yace "menene ko jikin naki ne?"ya kalli cikin ta shafa cikinta tace "umm umm bakomi zamuje asibiti ne da ummah likita yace mu koma"

jimm kadan yayi ta katse masa tunani "kaci abinci?"ya kalli husnah data dauke kai cike da kishi ya gyada mata kai ta shafa gefen fuskarsa tace "ka kulamun da kanka sai na dawo"

"da naso na kaiku ne"da sauri ta katsesa "ina zaka kana tare da amarya na yafe maka mijina"tayi masa murmushi yabita da kallo dakyar take daga kafa muneeba ta watsawa husnah wani kallo mai cike da tsana irin zamu gamu din nan suka fice driver na jiransu.....

*****
daddy natw rantsuwa suka Shiga "nifa bansan lokacin dana auri rabi ba dan haka babu wani aure a tsakanina da ita mema ya hau kaina da har zan auri rabi saboda cin amana suna tare da zainab?"yaseer turus yayi yanajin furucin daddy suna shiga innah tayi musu nuni da suyi shiru yara sun shigo cikin faraa ummah hadiza ta ruko husnah tace "barka barka husnah Masha Allah aimu nan muka taho muka barku da dan shegiyar can aljan ni malam din ma daga baya mayi masa godiya"husnah ta zauna ta kalli sashen da mahaifiyarta ke zaune ta kalli yaran tayi murmushi take taji wani son yaran ya shigeta ta dauko dayan yaseer ya shigo ya dauka,daddy kuwa ficewa yayi a fusace ya nufi sashen hajiya rabi be sameta ba ya koma dakinsa ya shiga sintiri don me innah zatace bazai rabu da itaba?....

*****
dukkansu dake tsaye akan dutsen cikin tsananin tashin hankali suke ganin babu ko kayan boka a wajen sai fulani dake wajen wani dake saida kwarya a wajen ne ya shaida musu boka ya mutu.....muneeba duhu ta soma gani ko ganin gabanta batayi cikin tashin hankali ta kalli cikin dake jikinta ta kalli ummahnta tace "bo....bokkkka ya mutu ya barni da cikinsa?"ta dora hannu akai tayi baya zata Fadi ummah da Anty sadiya suka tarbota ta saki wata gigitacciyar kara....


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

07042277401
08036953516


*SLIMZY*🥱😒ina boka yaje ni Amina?
48
yaseer ne ya saci kallon husnah da tayi kur'i tana kallon jinjirin dake hannunta wanda tuni ta fada duniyar tunani cike take da takaicin muneeba da tasan dik abinda tayi yanzun tayine dan ta shakar da ita idan hakane kuwa tabbas ta taro march,ji tayi a jikinta ana kallonta ta d'ago kai ta zuba masa kyawawan idanuwanta wani kallo tayi masa mai tada jijiyoyin jiki saida yaserr yaji wani yarrr dikda yasan mai kallon ke nufi hajiya saude taja gauron numfashi ta katse shirun da dakin yayi "niko ina tsananin mamakin yadda akayi badamasi ya auri rabi baya cikin hayyacinsa"ummah hadiza ta gyara zama "ashe abinda yake ranki shine a raina tun fitarsa nake sakawa ina warwarewa gashi innah na neman hanasa rabuwa da ita"innah tayi murmushin manya tace "bani na aikesa aurenta ba dan Haka shine da kansa zaisan yadda zaiyi da ita yasan nayi da ita in yana sonta su cigaba da zama"husnah ta mike tana yatsina fuska "yadai husnah?"ta girgiza kai "inaso in d'an kwanta ne kaina nadan ciwo inajin zazzabi"ummah hadiza ta yunkura "umm bari intashi inje inji da tawa yar"ta ruko husnah "munyi gida sai mundawo"dariya hajiya saude tayi ta girgiza kai suka fice,
gyara zama hajiya saude tayi ganin yaseer na waigensu husnah tasan binsu yakesonyi kafin tayi magana ya ajiye jinjirin "amm nima"

"kaima mene ina zaka?ai zama zakayi akwai maganar da nakeso mu tattauna"ya gyara zama hade da natsuwa dikda hankakinsa rabi yana wajen husnah da suka fita momy ta cigaba da magana "ai shiryawa zakayi ka dauki husnah kuje gidansu hafeez kayi masa godiya dan wallahi harda maganin da hafeez ya kawo ya taka babbar rawa wajen warkewar matarka kuma na tabbatar ba wani abubane ya hadaku babu wani kwakkwaran dalili kawai dalilin be wuce akan husnah ba kar kabari mace ta shiga tsakaninka da Amininka kaji nafada maka"shiru yaseer yayi jikinsa yayi sanyi hafeez amininsa ne tun yana primary school tare sukai makaranta har university sukasamu aiki yanzun gashi sun samu matsala kuma hakan be hana hafeez zuwa gidan ba,sallamar wadda sukajine yasa yaseer jikinsa yin wani shock ya dago da sauri sukai Ido hudu da hafeez da ummahnsa da meenahl ya sunkuyar da kai hajiya saude cike da faraa tace "d'an halak kaki ambato yanzun maganarka nakeyi sai gaka kunzo sannunku da zuwa sannu da zuwa hajiya"ummahn hafeez ta dire jakarta yaseer ya sosa keya yace "sannu da zuwa ummah,ina yini ummah"wani kallo ummah tayi masa tace"haba yaseer ni baxan amsa gaisuwarka ba ai tunda niba uwarka bace ai kabani mamaki koda kuke fadanku kaida abokinka ai be kamata ya shafeniba"yaseer ya sunkuyar da kai cike da kunya ummah tace "toni gani nazo hajiya hafsat ce ta sanar dani haihuwar hajiyq zainab daxun mun hadu a saloon tace ai ansamu yan biyu nace bazaa kwanaba komi yamma sai nazo naga wad'anan jarirai nasa musu albarka"innah ta dauko daya ta mika mata tana fadin "wadanan mazajen masu kama daya bansan ya zanyi dasuba in rinka ganesu"yaseer dakyar ya dago kai suka hada ido da hajiya saude ta kashe masa ido alamar yaja hafeez su fita shine ya mike ya tabo hafeez ,da sauri hafeez ya kallesa yace "man muje mana"shiru hafeez yayi ya mike yabi bayan yaseer ummah ta bisu da murnushi tace "j'airan yara"nan ummah dasu momy suka baje suna zuba hira cike da nishadi minal tuni ta mike ta fice wajensu nusrah a sashen husnah...

yaseer dakyar yasamu ya shawo kan hafeez yayi fushi sosai suna tsaye jingine jikin mota ana kiran magriba yaseer yace"mu shiga ciki mana sashen husnah kaci abinci muyi sallah sai mutafi maida ummah tare"hafeez ya jinjina kai yace "tou muje"tsayuwar motarsu hajiya rabi ce ta dakatar dasu suka tsaya dakyar hajiya rabi da sadiya suka fito da muneeba daga cikin mota wadda idanuwanta suke a rufe taki bude idonta sai wasu maganganu takeyi tana shafa cikin kallo daya zakayiwa hajiya rabi ka hango tashin hankali karara a fuskarta nan da nan tayi bakin kirin ta fita hayyacinta yaseer jikinsa na rawa ya karaso ya taimaka musu aka fito da muneeba daga cikin motar yace "ummah lafiya meke faruwa naganku cikin wanan yanayin"hajiya rabi ta kalli muneeba ta hadiyi wani miyau mai daci cike da damuwa tace "yaseer akwai matsala asibiti biyu mukaje dangane da cikin nan na muneeba baa ganinsa kwata kwata shine kaganta cikin wanan halin gashi dik ya burkice sai kiran sunan husnah takeyi wai husnah ce da aljanunta suka dauke mata yaro"wani kallo yaseer yayiwa hajiya rabi take tayi gumm da bakinta Tasha jinin jikinta dama ba haka ta fada ba yace"badai husnah ba kam saidai in wata matsalar ce tafaru idan hakane zanyi magana da malam da yayiwa husnah magani yazo akan matsalar muneeba "kallon juna hajiya rabi da sadiya sukayi gaban hajiya rabi ya fadi karfa malam yazo ya fadi cewar cikin jikin muneeba bana yaseer bane,cak yaseer ya dauki muneeba dikda nauyin ta hawaye kawai ke gangarowa daga idanuwanta dake rufe ciki bakinta na motsi tana fadin "ni wallahi sai nasamu ciki irin na husnah cikin yaseer shi nakeso banason wanan cikin ummah ki taimakeni ina tsananin son Yaseer kinga ita anga cikinta"yaseer wani damm gabansa ya Fadi mamakin kalaman muneeba yakeyi yana rike da ita suna tafiya tare dakyar hajiyq rabi ke daga kafarta kamar an dora mata Kaya haka suka shiga tare dakin muneeba ya kwantar da ita ya tsugunna a gabanta cikin tausayawa ya kira sunanta cikin wata irin siga mai cike da tausayawa da kulawa "muneeba ki kwantar da hankalinki zaaga cikinki kema ba likita ya fada miki cewar wasu na haihuwar dansu haka ba?inasonki ina son abinda kw cikinki kidaina damuwa"ta bude idanuwanta a hankali saida yaseer ya razana ganin yadda kwayar idonta ta koma kamar gudan jini saboda ja tace"bazaa gansa ba yaya yaseer nafada maka bazaa gansa ba yaseer nidai inason wani cikin banason wanan?"yadda take maganar a wahale yasa yaseer jikinsa mutuwa ya shafa fuskarta yace"shima kina sonsa kuma zaki haifesa ko? inace nine mijinki kuma uban d'an?"ya kafeta da ido itama shi take kallo wasu zafafan hawaye madu zafi ke zubo mata kafarta ya kalla ruwa ke biyo kafarta yayi saurin kauda kansa ganin yadda take hawaye dakyar ya fito daga dakin,hafeez ya ruko hannunsa jiki a sanyaye suka fita,

hajiyq rabi gyara tsayuwa tayi tace"muneeba na rokeki wadanan surutan da kikeyi sune zasusaka asirinmu ya tonu nidake asan abinda muka aikata kiyi shiru ki kwantar da hankalinki gobe zan fita Nemo maganin da zako rabu da cikin ko ki haifesa"wani kallo muneeba tayiwa uwar saida taji hantar cikinta ya kada dakyar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login