Showing 36001 words to 39000 words out of 130717 words

Chapter 13 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

197

kakkabe zani ta fito da wani turare tayi inserting ta shafe jikinta dashi jinjina kai muneeba tayi ta fice,

karo sukai da momy a hanya tace "barka da yamma momy "momy ta kalli muneeba yadda take faraa taji bata yarda da itaba tace "idonki kenan sai yanzun nake ganinki?"sosa keya tayi tana leken dakin momy,"lafiya dai muneeba"

"lafiya lau momy nadauka yaseer na nan ne dan nabaroshi gida yace zaizo ya dauki husnah su fita"momy ta kauda kai tana kokarin wucewa tace "tun dazun ya dauki husnah suka fita ai sun dade da fita"farin ciki ya lullube muneeba kamar ta kira yaseer amma ta fasa Dan bataso ya ganota jikinta na rawa ta wuce bata sake magana ba momy ta bita da kallo tana girgiza kai cike da takaici....

******
hannun Abraham cikin na husnah yana tukin mota ta kwantar da kanta jikinsa a kafadarsa tace "kasan me wani nishadi nakeji wallahi kamar kada mu koma gidan nan"Abraham ya shafa gefen fuskarta da hannu daya yace"Ah ah zamu koma mana me zai dameki bayan ina tarw dake husnah"zumbura baki tayi tace "tafiya fa kakeyi saidaib inka dawo ni nan da can banason katafi ka barni"dariya yayi cikin shaukin soyayya yacev"husnah kenan kin manta ni Aljani ne?"ta dago kai gabanta yadan fadi yadda ya kira kalmar aljanin ya girgiza ta dikda har yanzun bata gasgata menene aljaniba menene mutum ba yaga tana kallonsa ya jinjina mata kai yace "Aljani idan yaso zai shiga jikin mutum ya zauna, kasantuwar ni aljanine yasa ko bana tare dake kikejin alamuna a tattare dake koda baki ganina sau da yawa nakan zo baki ganniba musamman idan naga su momy"tayi ajiyar zucuya tace "amma meyasa ni Bana iya shiga jikin mutum"dariya ta bashi ya gimtse dariyarsa bayaso ta fahimci cewar aljani abun tsoro ne yace "saboda keba aljana bace ke mutum ce shine banbancin mutum da aljani"tadan tsorata saidai ta karajin sonsa tinda har yana shiga jikinta?murmushi tayi tace "nakara sonka tunda har jikina kana shiga"ya girgiza kai yayi mata trowing kiss yace cab'e ta sheke da dariya hafeez na biye dasu ya karya kwana ya shiga katuwar wata plaza yayi parking mota hafeez a gefen titi ya parker yadda suka ruke hannu da yaseer yasa shi hadiyar wani mugun miyau take yaji kishi ya baibayesa wato yaseer dama yaidararsa yakeyi?dama yanason husnah? dariya husnah keyi hannunta cikin na Abraham wadda kamanninsa a idon mutane yake sak yaseer a idon husnah kuwa mijinta take gani gwanin shaawa suke jerawa sai kallonsu akeyi faraa husnah keyi fararen hakoranta da suka jeru suka bayyana gumi ne ya gama karyowa hafeez ya koma mota,ta jikin glass din shiga plaza husnah taga wani mutum gefenta mai mummunar kama fuskarsa bakinkirin hakoransa na tsakiya kanana na gefe da gefe masu tsawo ta saki razananniyar kara ta runtse ido Abraham ya kalli kansa a madubi yasan shi ta gani ta madubi sakamakon aljanu basa rikida a madubi ta jikin madubin ya hangi hafeez a cikin mota wato yana biye dasu yayi saurin tallabota idanuwanta a rufe mutanen dake cikin wajen sukai cirko cirko tana nuna madubin idonta rufe tace "dodo ...... Abraham dodo nagani a kusa dani bakai nagani ba"hankalin Abraham ya tashi ya tallabota yana kallom fuskarta yadda ta runtse ido cike da tsoro yace "ba dodo bane ki bude idanuwanki bude kigani bawani dodo kinji matata karki sake kallon madubin tunda dodo kike gani"ta bude ido a hankaki tana kallonsa ya zura mata ido da weni irin kallo mai narkar da zuciya tace "kaima ka gani ko?"yace "nagani tashi ammmm mike to"ya tallabota da kyau ta mike ya gyara mata takalmin idanuwanta ta runtse bata kalli glass dinba suka shige ciki bin wajen da kallo tayi yace "to ki zabi kayan dik da kikeso zan siya miki kinji?"tsalle tayi ya ruko hannunta yace "kiyi murna ina tare dake a koda yaushe ki zaba zan fita zan amsa wayar maamah"ta jinjina masa kai ta shiga bin ko ina da kallo ya fice tsaye yayi a kofar plazar yadda wajen ke kokarin yin DUHU a idanuwansa ya tabbatar da narjisu tana wajen yanaji a jikinsa bin ko ina da kallo yakeyi be gantaba amma he can feel her presence a wajen jikinsa ya kama rawa yace "wato sun kwanceta Kenan"yayi kwafa ya koma ciki hafeez kuwa kallon yaseer yakeyi cikin mamaki,

kwando take turawa taji an rike kwankwasonta kamshin turarensa ya bugi hancinta ta kallesa da wani irin kallo da saida yaji yarrrr tayi masa kyau sosai yacev"munzagaya in tayaki"ta jinjina masa kaim....

******
mahaifiyar yaseer shiru tayi tana fuskantarsa kannensa yan biyu guda biyu mata suna gefe ta nisa tace "yaseer ka tabbatar da maganar da kake fadamun gaskiya ne?idan itadin ba yar Alhaji badamasi bace meyasa gwajin jini ya nuna haka?"yaseer ya dago jajayen idonsa cike da damuwa yace "momy nifa ina zargin yarinyar nan aljana ce kawai ba mutum ba sanan babban abunda kedamuna yadda ake hadani da ita wai ni mijinta ne tayaya na zama mijinta ai nafadawa momy idan mani mijinta ne nasaketa"

tsawa momynsa ta daka masa tace "kai yaseer kana hauka ne?to baka isaba idan ma kasaketa dole ka maidata idan kuma baka maidata ba to dama babu idda akanta tunda baka kwanta da itaba amma iname gargadinka karkazo kanamun kuka"gumi ya karyowa yaseer ganin yadda momy ta hakikance yace "momy kukan me zanyi miki nida bansanta ba"momy ta girgiza kai mamakinda al'ajabin yaseer ya cikata tace "yaseer anya kanka daya kuwa anya kana cikin hayyacinka idan ban mantaba ranan aurenka da muneeba kuka kazo kanayi akan kar a aura maka muneeba kanajina jikinka husnarka zata dawo yanzun kazomin da wani zancen banza kana nunamin kamar bakasan husnah ba?"ya kauda kansa gefe ta tsura masa ido sai gumi yakeyi yana tura kai gefe ta jinjina kai tace "tashi katafi zanje wajen malam ya bincikamun idan aljanu gareka su sakeka tin wuri amma kasani Ka tafka babban kuskure tashi kabani waje yau din nan bazaa kwanaba idan nayi sallahr magriba zansa driver ya kaini gidan malam inji inda matsalar take shashasha tashi kabani waje kuma zanzo gidan inga husnar inyi magana da zainab"yaseer ya mike yau mahaifiyarsa dake mugun sonsa itace ta koresa akan husnah?ya Kai kofa ya juyo harara momy ta watsa masa ya fice....

******
ana kiraye kirayen sallahr magriba husnah da Abraham suka fito da siyayya niki Niki wanda ya mugun kashe mata kudi hafeez na ganinsu ya kwantar da kai a mota kada yaseer ya gansa Abraham kuwa kada kai yayi ya bude boot yasa kaya husnah ta shiga yaja motar,

Allah Allah yakeyi yaje ya ajiyeta ya tafi duniyarsu neman narjisu suna isa ya rike kayan suka jera suka Shiga ciki momy tayi alwala tace "yanzun nake cewa shiru"husnah sai faraa takeyi wucewa tayi da kayan dakinta Abraham yace "bari inje inyi sallah momy"ta gyada masa kai ta bishi da kallo ya fito ta window muneeba taga giftawarsa tacewa ummahnta "ummah yaseer ya dawo bari inje"ta mike cike da zumudi"ta fice Abraham na fita ya bace,

yaseer ne yayi parking motarsa a waje daidai nan hafeez ya karaso da sauri yayi parking ko makulli bai cireba ya sha gabansa yaseer ya hada rai yana kallon hafeez,
tuntsirewa da dariya hafeez yayi yana kallonsa ran yaseer yayi mugun baci yace "lafiya ni mahaukaci ne kakemun dariya ko haukar budurwarka ta soma shafarka ne?"

"aikam budurwarmu zakace yaseer ashe dama son husna kakeyi yasa kakemun barazana akanta har kake ikirarin in fita daga rayuwarka?na shaida hakan tinda yau na ganku ido da ido kaida husnah kunje shopping kuna tafe kuna soyayya cike da nishadi"dammm gaban yaseer ya Fadi kallon hafeez yakeyi galala ganin hafeez babu wasa a idanuwansa yasa yace"ni kuma ta yaya ta ina?nidin kagani badai niba kadaiji labarin daddy yabani kudi in kaita shopping ka fito ka fadi haka ba kace ka ganmu tare ba don ni ban fita da ita ba"

"karya kakeyi yaseer niba makaho bane tare na ganku da ita kasani rungumar husnah ko fita da ita shopping bashi zaisa indaina kaunarta ba dan soyayyarta a jinin jikina take kuma kasani haramun kakeyi dan ba aure a tsakaninku"hafeez ya gifta ta gefensa ya wuce cikin gida yabar yaseer baki bude yana bin hafeez da kallo cike da takaici da bakin ciki ya nufi gida cikin sashen su yayi karo da muneeba tana haduwa dashi ta fadada murmushinta shima murmushin yayi mata suka jera tace "yanzun naganka ai a dakin momy ta window injidai ka ajiyeta inda bazata dawo mana ba ko?"dammm gabansa ya fadi shi kuma?ta cigaba da magana "kayi shiru ai naga fitarku nayi hamdala nagodewa Allah mun rabu da Allah kakai"taji yayi shiru tana kokarin bude kofa yasa kai ya shiga ya zauna jagwab a kujera tacev"yadai ya naga kayi shiru meyafaru ni baxan fadawa kowa plan dinmu ba saboda taimakon momy da daddy kayi"girgiza kai yayi yace "muneeba ni banje ko ina da husnah ba hasalima na Dade ina jiranta a waje batazo ba nagaji na buga motata natafi gidan momy"zaro ido tayi tana masa wani kallo "lallai yaseer karka maidani wata mara wayau da hankaki mana ko kuma baa hayyacina nake ba?da idona naganka da wanan kayan fa?"tana nuna yaseer wanda yayi tsuru tsuru cike da tsoro yana kallon muneeba dake kunfar baki ya kasa magana sai kawai ta fashe masa da kuka tace "shikenan sonta kakeyi kaki kafito kafadamun gashi ka fita da ita ka kasa batar da ita kamar yadda kayimun alkawari?"tagumi yayi jikinsa a mace ya kasa motsawa shashekar kukanta yasa ya zabura ya bita bedroom....

*****husnah na zaune gefen gado tana bubbude kaya momy ta shiga tana bun kayan da kallo tace"yanzun sai akai laces da atamfofi dinki ko husnah?"husnah ta jinjina mata kai momy ta girgiza kai cike da kaunar yarta ta ruko hannunta tace "muje ki gaida yayanki hafeez yaya hafeez"husna ta maimaita "hafeez "a bakinta taji sunan ya Mata dadi hafeez na zaune yana daddana waya a parlor husnah ta daga labule ta tsaya tana kallonsa a hankali tace "ina yini yaya hafeez"da sauri ya dago yana kallonta cike da shauki ya kasa boye farin cikinsa husnah ta kirasa da yaya ya mika hannu ya yafitota yace "taho nan".....ummah ce ta kira wayarsa nan da nan ya bata rai shikenan yasan nemansa takeyi be dauki wayar ba yace "ya kike!"ta jinjina kai tace "Alhamdulillah "tana zaune a d'arare momy ta wucesu ta shige dakinta ta tada sallah yacev"husnah ki saki jikinki dani kinji?ni yayanki ne ko?"ya yyada masa kai hade da ajiyar zucuya take taji ya kwanta mata a rai zata rinka magana dashi yana tambayarta tana amsawa har momy ta fito ta samesu yayi sallama da momy ya tafi,

momy na zaune tana jiran shigowar daddy har goma na dare bai shigo ba taga wucewarsa sashen hajiya rabi ta tabbatar yana can ta jinjina kai kawai can kasan zuciyarta nayi mata zafi....

*****
karfe dayan dare husnah ta juya daga gado taji tanajin fitsari da sauri ta mike dakin tana yana juya mata ta murza idanuwanta taga yadda dakin keyi tsoro ya cikata Taja da baya inuwa tagani ta gefenta ta wanan gefen alamar mutum ne a gefenta da sauri ta waiga tace "Abraham...."shiru tayi tozali tayi da mace da bakaken kaya gashi ya rufe mata ido ta sunkuyar da kai wani mugun miyau ta hadiye bakibta na rawa tace "wace....ce"dago kai tayi gashin ya baje a bayanta ta xaro mata idanuwa suka firfito waje ta bude bakinta wasu hakora ta gani masu tsayi sun canja Kala sak horo ta daga hannuwanta taga wasu kumbuna zako zako farare masu ban tsoro dakin na juya mata wata iska na kadawa,

cikin wata irin murya tace "narjisu....narjisu ce husnah nadawo gareki"husnah bakinta na rawa kamar mai jin sanyi tace "narjisu.......narj"sai kawai taga ta malkwaye ta rikida ta koma narjisun data sani haske ya bayyana cikin dakin ta harde hannuwanta a kirjinta tace "kin tabbatar da nidin narjisu ce?"jikin husnah na karkarwa ta kasa magana,

"ki rabu da mijina Abraham idan kinaso ki zauna lafiya idan kuma ba haka ba saina hanaki zaman lafiya sai rayuwarki ta zame Miki DUHU bakin kirin Wanda zaki kasa ganin haske"gumi ne yake zubowa husnah cikin tsoro take narjisu ta rikida ta koma yadda tazo mata dakin ya shiga juya mata winduna suna budewa suna rufewa nan da nan husnah ta shiga waige waige ganin komi na dakin na sauyawa ta Dafe kanta ta runtse idanuwanta ta kwalla kara


zabura momy tayi daga kwanciyar da tayi tace "husnah!!!!"ta nufi dakin husnah aguje......




*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE KI BIYA DARI UKU300 KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN ALLAH YA ISA*

GA MAI BUKATAR BIYA YA TURA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYAN KUDI TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER



*SLIMZY*✍🏻
[23/09, 21:26] 🥰slimzy😍: 16
momy rike husnah tayi sosai tana kokarin tofa mata addua taji an riketa ta matukar tsorata ta dago bataga kowa ba ga duhu daya gauraye dakin hannunta tasa tana laluben wayarta takasa dauka hannunta sai rawa yakeyi harshenta yakasa motsi dik yadda taso tayi addua gani tayi dakin itama Yana juya Mata wani haske ne mai kama da kibiya ya haska dakin husnah ta bude idanuwanta shabe shabe da hawaye sukai ido hudu da narjisu cikin suffarta ta mutum husnah hawaye nabin idanuwanta ta yunkura ta mike dikda yadda tsoro da furgici ya cikata tace "kece kike furgitani?meyasa kike furgitani?"cikin daga murya husnah ke magana tana kallon narjisu wadda ke sanye da bakaken kaya gashinta baje a bayanta ta harde hannuwanta a kirjinta sakyau tace "lallai bil'adama dama kunada karfin hali dik yadda nake kallon kirjinki na bugawa saboda tsananin tsoro har kinada damar da zakiyimun burga da kurari tou bari ki gani"ta dago hannuwanta da kumbunanta masy tsayi ta waresu wuta take fitowa dashi tanayo kan husnah sai taga wutar ta mutu ta fusata ta ware idanuwanta bakake kirin tace "idan har baki rabu da Abraham mijina ba saina nakasaki zan koma rayuwata dake"hushna tace "bazan taba rabuwa da Abraham ba saboda abraham mijina ne infada miki kuma na rayu dashi na ginu da tsananin soyayyarsa koda yake aljani inasonsa ina tsananin kaunarsa bazan iya rayuwa babushi ba"narjisu tace "lallai husnah bakisan meye aljani ba ko bakisan Abraham abun tsoro bane yana zuwa miki a suffar mutum ne amma bari in nuna miki"husnah cikin tsoro take kallon yadda kwayar idon narjisu ke canjawa can ya koma jajir yana fitar da wani wuta da walkiya momy tsananin tsoro yasa ta sandare bata ganin komi face maganganun da husnah keyi sun matukar furgitata hakanvyasa ta sabdare a zaune batasan fitsari na fita daga jikinta ba yar data haifa ce take magana da aljanu take ikirarin bazatavrabu da aljaniba saboda ta ginu da soyayyarsa,
haska mata jikin bango narjisu tayi take bangon ya tsage wani kurgumin daji ta gani mai bishiyoyi Abraham tagani cikin yadda yake zuwa mata a take ta zaro ido Abraham tace bakinta na rawa can taga yayi girgiza ya rikida ya koma katon mutum mai ban tsoro ji tayi cikin dajin yana magana yana fadin "narjisu......narjisu!!!!!dik inda kike ki fito idan baki fitoba na kamaki da hannuna saina kasheki"damm gaban husnah ya rinka faduwa kanta bya juye dakin ya shiga juya mata kanta ke sarawa kamar zai rabe biyu ta yanke jiki ta fadi ji kake rammmmm ta fadi kasa momy ta zabura tayi kanta tana girgizata 'husnah husna husnah kirashi "sai numfashinta dake sauka sama sama narjisu na tsaye akanta tana ware hannuwanta tana kokarin zuba mata wani bakin abu dake fitiwa a hannunta daya zuba a jikin husnah sai taga ya tarwatse tayi kwafa aikin Abraham ne tasan shine ya zuba mata dafinsa da siddabarunsa yasa dik yadda taso watsa mata ruwan ciwo bazata iyaba ta bace jin alamun Abraham a hanyar tahowa wajen husnah.....

rungumeta sosai momy tayi tana hawaye jikin momy rawa kawai yakeyi a hankali husnah ta bude idanuwanta ana kiran sallahr asuba ta kalli momynta tace "Abraham baizo ba momy koh yaushe zaizo karya rabu dani inasonsa bazan iya rayuwa babu shi a tare daniba soyayyarsa tayu gini tayimun tsatsa a zucuyata"momy ta girgiza Kai tace "husnah Abraham ba mutum bane irinki ba mutum bane shi aljani ne kuma babu rayuwa tsakanin mutum da aljani dan haka dole zaki rabu dashi "idanuwan husnah suka kankace tana ma momy wani kallo gani tayi kawai ta fice a dakin tabar mata dakin momy ta jinjina kai tace "tabdijan ina cikin jarabawa"momy na kiran husnah ko waigenta batayiba ta yunkura ta mike ta nufi dakinta alwala ta dauri tazo ta shimfida dadduma ta tada sallahr asuba,

da duhu a harabar gidan ga tsananin sanyi na asuba da takejin haka ta tsaye a harabar gidan tana bin ko ina da kallo wasu hawaye masu zafin gaske suke zuba a idanuwanta can gefe ta zauna a kujera,

tun daga nesa Yaseer ke kallonta a tsorace ya fito da jallabiya a zahiri shi take kallo amma sam hankalinta baya jikinta zuciyarta na can wani waje ya furgita ganin ta cikin wanan yanayi tsaki yaja har ya kai gate ya dawo yace "ke mai kikeyi a nan?"ko gezau batayiba batasan yanayiba bata motsaba ya sake magana da yar tsawa yace "mai kikeyi a nan?"ganin hawaye a idanuwanta yasa jikinsa yin Sanyi wani mugun haushinsa takeji yadda yake kallonta kasam zucuyarta kamar ana hura Mata wutar son Abraham tace "babu ruwanka dani ka kara gaba kabarni a nan ina jiran masoyina sanyin idaniyata"tsaki yayi ya tura kofar gate sin ya fice,

Abraham na tsaye yana kallonta ya durkusa a gabanta wata iska taji mai dadi tana kad'ata jikinta ya sauya nan da nan taji wani sanyi ta bude idanuwanta ta gansa a gabanta ta mike ta tsaya ya rike kunnuwansa alamun ban hakuri ta girgiza kai tace "wai zan rabu dakai?"ya girgiza mata kwi yace "babu abinda zai rabani dake husnah,duk runtsi koda zan rasa Raina muna tare "ta girgiza masa kai tana kuka tace "wai dole in rabu dakai saboda mutum da aljan basa rayuwa tare momy tacemun dole in rabu dakai sanan jiya daddare naganka a cikin daji cikin wata iriyar kama"jijiyoyin kansa ne suka firfito yacev"tabbas ni kikagani a kamata ta ainihi,husnah nidin abun tsoro ne ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login