Showing 69001 words to 72000 words out of 130717 words
hankali tana kallon cikin dakin duhu ne ya gauraye dakin ta mike ta zauna tana kalle kallo ko tafin hannunta bata gani tace "na makance"Abraham ya amsa cikin muryarsa da yake mata mai dadin sauraro yace "bazaki makance ba inhar kina ganina in kuma bakison ganina to tabbas rayuwarki zata shiga cikin duhu bakinkirin wanda ko tafin hannunki bazaki taba ganiba idan har kin zabi rayuwa dani tou babu abinda zanyi miki husnah zan cigaba da shayar dake farin ciki kamar yadda nasaba"idanuwanta suka kankace bata ganinsa sai sautin muryarsa takeji kamar daga sama ta gansa dib a gabanta cikin duhu saidai fuskarsa na haske yayi matukar kyau wani kallo tayi masa mai cike da jin haushi tace"nafiso rayuwata ta kasance cikin duhu harabada da incigaba da rayuwa da dodo mai mummunan halitta gara na kare rayuwata bana gani banaji kuma bana gani"cikin mamaki da takaici yake kallon kwayar idanuwanta da suka sauya tun jiya zuwa launin ja yace"wanda ya zugaki yake neman shiga rayuwarki yanaso ya kaiki ya baro ne dan shi rayuwarsa ta kawo karshe"gabanta ya fad'i tace"yaya yaseer din?"ya gyada mata kai yayi murmushi mai ciwo yace "husnah kenan anfada miki zan kyale wani ya shigo rayuwarki dik irin yadda muka gudanar da soyayya mai cike da kaunar juna?har yanzun ina sonki kuma bazan taba daina sonki ba nayi alkawari dik wanda yace zai shiga tsakanina dake saina halaka Shi ko waye dan haka ki saurara zaa kawo muku gawarsa tuni na hada mishi mummunan hatsarin mota wanda na tabbatar wanan kwakwalwar ta kansa mai cike da taurin kai tana nan tarwatse a titi "dafe kirji tayi wani jiri ne taji yana daukarta tanayi masa wani kallo ji tayi kirjinta na barazanar tarwatsewa wani irin rad'adi take cikin kirjinta da tukuki ya bude hannayensa "taho gareni matata nayi matukar kewarki"yw fuzgota jikinsa cikin wani irin karfi take kokarin turesa tuni suka fara kici kici itadashi saidai ko motsi ta gafarayi cikin kirjinsa yana kokarin sumbatarta ta runtse idanuwanta tana kokarin kwacewa ta bugu dab jikin bango ji kake kummm ta saki wata irin kara mai ban tsoro"aguje momy da mai aikinsu suka nufi cikin dakin cikin sassarfa,
tsugunnawa yayi a gaban husnah lokacin dasu momy suka shigo yana shafa goshinta jini ne ke zubowa daga goshin nata yana shafa kanta yana hawaye gani sukayi ruwa na d'iga a fuskar husnah cikin wani irin yanayi momy ta shiga girgiza husnah tana fad'in "husnah husnah meyasameki Tashi husnah?"ta kalli larai mai aikinta tace"larai kamar husnah ta mutu shikenan aljanin nan ya kashe husnah hafeez ne tsaye jikin kofar dakin yana jiyo sautin kukan momy daga cikin daki ya saki ledar maganin dayazo dashi daga gidan malam wanda bai tahoba saida yazo dashi ya shige ciki yana fadin"lafiya momy?"ya kalli husnah dake kwance idanuwanta a rufe hawaye na bin gefen idonta momy ta d'ora hannu akai tace"shikenan husnah ta mutu ya kasheta "hafeez yana girgiza husnah Abraham cike da kishi yake kallonsa yatsansa yasa mai tsawo ya hankade hannun hafeez ji yayi an ture hannunsa yana shafa fuskarta cike da so da kauna yasa bakinsa yana hura wajen ciwon gani sukayi jinin dake goshinta a hankali yana bacewa cikin senconds arbain suka nemi jinin suka rasa ya hura mata iska a fuska ta mike da sauri ta zauna tana fad'in "yaya yaseer momy Abraham ya kasheshi"ta fashe da kuka Abraham kuwa shigewa jikin husnah yayi ya mike yana zagaye dakin momy tace"husnah kikace Abraham ya kashe yaseer?"shiru bata amsa ba ta tallabe hannunta tana kaiwa da komowa Wani mugun kallo husnah tayi musu hafeez yace"ba ita bace momy ina zuwa bari inyi maganinsa ya fita cikin sassarfa ya karasa inda ya yarda jakar ledar dayazo da ita ya dauko ya nufi cikin dakin cike da zafin nama....
*****
mutanene cike da wajen an cika makil yaseer na kwance jini na zuba a goshinsa wani cikin mutanen wajen yace"yanzun ya zaayi da wanan bawan Allah?"gashi dai alamar yana numfashi tunda inhar ya muti bazamuga yana numfashi ba"motar yaseer tayi ratsa ratsa glass din trailer data taho tayi kan Yaseer cikin hukuncin ubangiji kamar magic sukaga tanayin baya da baya wani a wajen yace"sai kace aikin aljanu?wai kunga yadda trailer nan tayi kansa kuma tana baya kamar ana tura ta?"daddy ne cikin motarsa tare da alhaji sidi sukaga cikowar mutane yana kokarin tafiya kiran da innah tayi masa yagani yace"anya waban ba accident bane?"sukayi parking a gefen titi ya fito ya nufi cikin jamaar gabansa ne ta fadi daya hango mutum a gefen titi ya kalli montar ya kalli alhaji sidi yace"wanan motar yaseer ce"bai rufe bakiba ya hangi yaseer cikin jini wayarsa yashe a gefe ana kiransa daddy yace"innahlillahi yaseee!!!!"ya kira sunansa ya zare malum malum dinsa yayi jifa da ita a gefen titi ya sungumi yaseer alhaji sidi ya dauki malum malum din da wayar yaseer yana fadin "Alhaji badamasi menene haka kayi magana da mutane"wani mutumi yace"bawan Allah ya zaka daukesa bamusan kokai wayeba kana ikirarin kiran sunansa?"hawaye kebin idon Alhaji badamasi dakyar cikin sassarfa yace"d'ana ne"alhaji sidi yayi musu bayani ya rufa musu baya sukasa shi bayan mota daddy ya zauna gefe driver daddy yaja yace"alhaji ina zamuje?"daddy cikin kuka yace"asibiti zaku kaini "momy jin yaseer shiru ga baba kabiru na jiran isowarsa mutane sun harhadu na dangi ta sake kiran wayar yaseer Alhaji badamasi yana gani ya dauka taji yana kuka momy ta mike zumbur tace"lafiya daddyn yara meyafaru kake kuka ina Yaseer din?"daddy yace"muna hanyar asibiti da yaseer nataho zan taho kiran innah shine naga mummunan hatsari trailer tahau kan motar yaseer "wayar ce ta sumbule a kunnen hajiya saude innah tace"lafiya?meyafaru saude?"fadi takeyib"yaseer yaseer ne"daukar wayar baba kabiru yayi yana tambaya daddy ya sanar masa nan ya hau salati ya soma yiwa su innah bayani da ummah hadiza dukkansu cikin kuka suke neman mayafai da hijabai suka nufi asibitin cikin tashin hankali hajiya saude ko magana batayi haka suka d'uru a mota....
*****
muneeba na zaune gefen gadon ummahnta fuskarta ta bushe da hawaye Anty sadiya na tsakiyar parlor tana maida bayani suna jiyo sautin ihu a d'akin momy sadiya tace"nifa ihun mai aljanun nan ya fara isata gaskiya zaman gidan nan bazai yuwu ba"ummah ta tabe baki tace"ai yanzun ni dawowarki ji nayi kamar an sakani a aljannah wanan shawarar da kika bayar tayi d'ari bisa d'ari dan na tabbatar shida husnah harabada"dariya Anty sadiya tayi tace"mu kuma da tuggu?hahaha aini naga kokarinki ma muneeba"muneeba ta girgiza kai tace "babban abinda ke damuna ma ko"tayi shiru ummah tace"maike damunki fad'amun"muneeba tasa kuka ta basu labarin yadda sukayi daren jiya da yaseer bayan ya gama kwanciya da ita sam bataga alamar nishadi a tare dadhi ba"ummah ta jinjina kai tace"ki kwantar da hankalinki ai sadiya ta dawo kedai shawarar datace ayin nan ita zaayi dan haka kisa ranki a inuwa yaseer naki ne ke kadai"hajiya rabi na cikin magana kiran daddy ya shigo wayarta tace"kunga kuyi shiru kuyi shiru Alhaji ne"ttsit sukayi cikin kissa da karairaya tace "hello darling"gyaran murya yayi ya kira sunanta yadda taji muryarsa a dashe tasan babu lafiya kafin tayi magana yace"muna asibiti tare da yaseer yayi hatsari yanzun haka an shigar dashi emergency"ya datse wayar "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ni rabi Yaseer yayi hatsari suna asibiti"wani mikewa muneeba tayi ta dafe kirji tana fad'in shikenan "aljanin nan ne ummah wallahi shine"cikin kuka muneeba ta fito babu ko gyale sautij kukanta su momy keji larai mai aiki dataji abinda ya faru ta shiga dakin tana kallon yadda husnah ke huci tamkar zaki tace"momy yaseer ne yayi hatsari wai suna asibiti"momy ta yunkura ta mike yaseer ya saita fuskar husnah dake rike da kwankwaso wanda Abraham ne a jikinta ya fesa mata ruwan adduar dake bakinsa a fuskarta yayi kara yasa hannu a fuskarsa ya yanke jiki ya fadi hafeez tuni yayi jifa da gorar dake hannunsa cikin kidimewa yace"yaseer ne yayi accident?"sai kuma jikinsa yayi sanyi ya sadda kansa kasa numfashi husnah ke saukewa a hankali idanuwanta na budewa tana binsu da kallo tace"ya mutu ko?"momy na kallonta tana hawaye ta mike hafeez yace "ku shirya mutafi asibitin"......
yaseer na kwance an nade kansa da bandage Abraham ya bullo ta jikin bango yana jifansa da wani kallo kawai ya shige jikinsa.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN KIKA KARANTAMUN BAKI BIYABA BANYAFE BA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*
*🌑DUHU...🌑*
( *sark'akiya*)
*BONUS PAGE*
*30*
cikin sassarfa hajiya saude suka shiga asibitin yadda suke kuka yasa kowa yake binsu da kallo likita ne ya fito daga ofishinsa nurses suna biye dashi DA folder a hannunsa Alhaji badamasi ne ya hango hajiya saude ya karaso cikin kuka tace"ina yaseer din?"dakin ya nuna mata yana tsaye wajen innah tace"badamasi ashe abinda ya faru kenan?ashe yaseer hatsari yayi muna can muna jiransa nida mahaifiyarsa da yayanka kabiru? ina fatan jikin dai da sauki"ya jinjina mata kai yace "da sauki likitan yace bawani rauni yasamu ba kansa ne ya bugu kuma ya dawo cikin yayyacinsa koda wani lokaci zai iya Tashi"ta daga hannu tace"Alhamdulillah"ta nufi dakin da daddy ya nuna mata hajiya saude na shiga likita na kansa yana rubuce rubuce Abraham ne jikinsu yana binsa da kallo dik tambayoyin da likita keyi masa bai amsa ba hajiya saude yagani ta bude kofar ta shiga dakin likitan ya kalleta take ta hango kamanninta da yaseer shafa kansa tayi tana hawaye tace"sannu yaseer?"ya jinjina mata kai idonsa kirrr akanta har tad'anji tsoro kardai yaseer sanadin hatsarin nan ya samu tabin kwakwalwa irin kallon da yakeyi mata yasa ta soma karanto addua ta tofa masa a fuskarsa ya d'anyi k'ara yayi tsaki ta sake wata adduar ta tofa masa take taga yayi atishawa ta tsaresa da ido tana kallonsa Yasser yana bin ko ina da kallo itama kallonsa takeyi shikenan aljanu sun shafi Yaseer shima tace"sannu yaseer"cikin wata irin murya ya motsa yace"sannu momy ashe inada rabon sake ganinki?"ta jinjina masa kai innah ce ta shigo tace"ah ah alhamdulillah yaseer ya Tashi sannu kaji?"likitan ya kallesa yace "mai kakeji yanzun?"ya jinjina kai yace"banajin komi"ya gyada kai yace"babu abinda ke maka ciwo ko?"yadan dafe kansa yace"kaina ne kawai shima kadan kadan yakeyi"likitan yace"Alhamdulillah yau ma zaa iya sallamarka saidai bandage din kanka da zaka rinka zuwa ana dubaea"yasa kai ya fice,
motarsu hafeez na tsayawa su muneeba suka iso da hajiya rabi sai kuka takeyi daddy ya taresu "ah ah yadai muneeba kike kuka?"cikin kuka ya rukota suka nufi dakin hafeez ya tsaya daga waje momy ta rike hannun husnah suka d'unguma ciki tana kuka tace"Daddy wallahi aljanin husnah ne yaje kashemun miji shine shi yayi sanadin hatsarin nan inajin ihunta a daki dazun ni wallahi bazan yardaba bazan bari akashemun miji ba a raba auren nan inhar aka bar husnah da yaya yaseer to tabbas zai kasheshi"ta fada jikin hajiya rabi tana kuka husnah tsurawa yaseer ido tayi tana kallonsa shima ita yake kallo ta karasa gaban gadonsa takai hannu zata rike hannunsa hajiya rabi ta daka mata tsawa tace"ke dakata abinda kukeyi a dakin zainab rungume rungume shi kikazo kuyi q asibiti salom aljanin ya sake zuwa ya kasheshi?"innah ta karbe zancen "ko yaseer ya rungumi husnah ya kwanta da ita halaliyarsa ce tunda kabiru gashi ya maida auren husnah da yaseer dazun kuma da shedu jiran da ake masa kenan yasamu hatsarin mota"da sauri muneeba ta kalli innah ta kalli hajiya rabi ji tayi jiri na neman daukarta dakin shiru yayi nadan wani lokaci yaseer na kallon momy cike da mamaki yana murmushi itama murnushi tayi masa hajiya saude cikin farin ciki yasan wanan aikinta ne yasani Abraham shine silar hatsarinsa rufe ido yayi ya tuno mummunar halittar daya gani mai girman gaske baka kirin akan titi mai suffar kare,
hawaye ne ke zubowa a idon muneeba daddy yayi gyaran murya yace"tayaya aka maida auren yaseer da husnah batare da an shawarceniba ni uban husnah to ban yarda ba bankuma aminceba babu yadda zaayi asa aljanin nan ya kashe yaseer sanadin husnah"innah tace"to rasa kunya beran tanka?ba wanda ya isa ya hana abinda narigada na bada umarni kuma kabiru yayanka shine ya yanke hukunci idan kuma zakaja da hukuncinsa to"shiru daddy yayi cikin takaici yake kallon husnah ta zauna gefen gadon cikin sanyin jiki tace "nice na janyo maka ko?"ya girgiza kai ya dago hannu ya shafi fuskarsa hajiya saude na kallonsu tamkar bata ganiba tayi murmushi ta kauda kai Abraham na tsaye jikin bango husnah suka had'a ido cikin bakaken kaya yake irin kallon da yayi mata yasa ta kauda kanta ta had'iyi wani miyau yace"yazo miki ko?"ta kallo Abraham fuskarsa ta sauya zuwa kamanninsa dayake zuwa mata fuskarsa tayi jajir yace"husnah kin mun butulci ko?"ta kauda kanta kamar bata gansa ba muneeba ce ta mike ta ture husnah tace"matsa Dan Allah"yaseer ya girgiza kai kawai yana hango tsanar husnah a kwayar idon muneeba"sannu ya jikin naka?"cewar muneeba cike da kulawa ya yunkura ya mike "da sauki"ta gyada masa kai tace"Alhamdulillah ban rasaka ba"cikin kasa kasa da murya take maganar tana kallon gefen husnah tana hararta husnah matsawa tayi tabar wajen ta koma gefen momy,momy ta kalli mutanen wajen bataga hafeez da sukazo tare sashi ba ta fice tasameshi tsaye yana daddana waya "hafeez baka shigaba wajen yaseer dinba"yayi kasa da kai yana sosa keya yace "ehh momy"tausayin hafeeez ya kama momy tace"muje ka gaishesa zan kawo karshen gabar dake tsakaninka da yaseer saboda abinda ya had'a ya raba"hafeez bai fahimta ba yabi bayan momy suka shiga ciki yaseer na ganin Hafeez yasan shi ya kawo su husnah cikin takaici da kishi ya amsa gaisuwar da hafeez yayi masa ya juya ya fice yaseer daga kwance yake ware idanuwansa yana nemanta Bai ganta ba,
tsaye husnah take jikin bango wajen reception kamar daga sama ta gansa a kusa da ita ya tsaya ya harde hannuwa ta d'anja da baya "kinzo nan kinata tunanina ko?"Abraham yace yana murmushi kallonsa tayi cikin takaici tace "tunaninka nakeyi komi ganinsa nakeyi kamar a mafarki bantaba sanin kai azzalumi bane zakayi kisa ba sai yanzun"ya cije baki wani abu na fitowa daga idanuwansa kamar jini yana kallonta cikin tsoro take kallonsa yace "akanki husnah zan iya kashe ko waye yanzun yaci nasarar tashi amma mu cigaba da zubawa dani dashi da dik wanda zai shiga rayuwarki ko waye saina nakasashi"husnah ta tofa masa miyau cike da tsiwa tace"karya kakeyi jinnu kawai Allah ya Fika inace soyayya ce?to banayi bazanyiba nadaina banayi Abraham "ya girhiza kai ya lakuto miyaun data tofa masa yace"da wanine ya tofamun miyau nan saiya gwammace kid'a da karatu husnah amma kasantuwar kece babu abinda zanyi saidai ke dinma kanki na rawa zan dan horaki"murmushi tayi tace"kadade da horani Abraham ka dade da cutata tunda kasamun soyayyarka da kaunarka idanuwana suka makance nakasa babancewa tsakanin mutum da aljani soyayyar da nakeyi maka ta rufemun ido yasa banaji bana gani har yanzun ina sonka saidai ina kokarin yakiceka daga rayuwata koda soyayyarka zatayi ajalina tinda ba jimsinmu daya ba"ta fashe da kuka ta durkushe a wajen ya tsaya akanta yana mata wani kallo momy ce ta fito daga asibitin tana fad'in "husnah!!husnah kina ina?"ta juyo da kanta gefen dama taga husnah durkushe a wajen tana kuka da sauri ta karaso husnah na ganinta tayi saurin share hawaye saidai idanuwanta da sukai jajir tace"kafiya husnah kike kuka? meyafaru?"momy na waige waige ummah hadiza dake tsaye ta bayan wajen tuntuni ta fito ta ruko husnah cikin tausayawa tana share mata hawaye momy kuwa tambayarta takeyi tayi shiru sai lokacin momy ta kalli kayan dake jikin husnah cikin mamaki tace"husnah wadanan kayan ne dama jikinki?"husnah ta kalli kanta ta kalli kayan ta kalli Abraham tace"momy basu bane a jikina badasu nazo ba"ummah hadiza ta jinjina kai tace"kayan sak'i ne wanan zainab na aljanu"Abraham ya kalleta yayi murmushi ya hura mata iska a fuska da sauri ta runtse idanuwanta ta budesu bata gansa ba momy cikin tashin hankali tace "tayaya zaayi mu gifta cikin jamaa da ita da wad'anan kayan?"ummah hadiza ta tube hijjabinta tace"karbi wanan kisa tunda gashi ma ance mutafi da yaseer din gobe zai dawo muje inyaso ni ai dattijuwa ce babu wanda zai kalleni"ajiyar zucuya momy tayi suka rukota dakyar take taka kasa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki kallo sukabisu dashi muneeba tayi tsaki ko kunya bataji tana rike da hannun yaseer wanda gaba daya hankalinsa na kan husnah suka shisshiga mota suka nufi gida....
*****
parlorn daddy aka ajiyewa yaseer pillow ya kwanta hajiya rabi na zaune gefensa da mafici tanayi masa fifita innah tace"yanzun a ina muka kwana badamasi?"ta kalli daddy wanda gaba daya ransa yake a hade yace"banida abinda zance tunda kum rigada kun yanke hukunci ammafa kusani yanzun zaa soma artabu da wanan aljanin tunda kuka maida auren husnah da yaseer"innah tace"babu abinda zai faru aibefi karfin Allah ba"hajiya saude ta jinjina kai ta dubi momy tace "ina husnah?"momy tace "tana daki"hajiya saude tace"da ita zantafi can inyaso yaseer idan yanason ganinta sai ya rinka zuwa kafin agama shirye shiryen komawa dakinta"hajiya rabi taji wani abu ya soki kirjinta tabi hajiya saude da kallo tayi jifa da maficin hannunta daddy yace"ban yarda ta koma ba gaskiya ta zauna a nan na tabbatar idan ta koma cen zaa rinka cutar da muneeba ne"hajiya rabi cikin kissa tace"ashe kasani shikenan yanzun muneeba zata zama yar kallo kenan tunda anyi kutun kutun an hada auren husnah da yaseer ni fatana kartaje wadanan aljanun su cutar da ita da abinda kw cikinta"hajiya saude tace"dole zan tafi da husnah kamar yadda baba kabiru yace"daddy ransa ya baci yace"shikenan tunda an nunamin husnah ba y'ata bace amma kusani ku dauketa dik abinda ya faru kar wanda ya nemeni"ya fice daga dakin innah tace"jeki hado kayan husnah"momy ta mike jiki ba kwari ta Shiga dakin husnah tana kwance lamo akan gado tayi nisa cikin duniyar tunanin Abraham gashi tana tsananin sonsa amma bazata iya rayuwa dashiba a matsayinsa na dodo jinnu mai cutar da mutane momy tace"tashi husnah zaki koma gidan hajiya saude da zama"husnah ta mike