Showing 93001 words to 96000 words out of 130717 words
yazo idan kunfita kundawo sai ku biya asibiti ko?"ta gyada mata kai cikin zucuyarta tace idan Abraham dai yazo momy taki yarda da cewar da aljani suke rayuwa....ta fito daga kitchen din cikin sauri ta shiga dakinta tana Shiga mamaki ya kasheta tabar dakin babu gyara amma tabi dakin da kallo hatta gadon an canja zanin gadon to waye?amai ne ya taso mata ta nufi toilet taga kofar ta bude ta dawo da sauri tana leken toilet din bataga kowa ba jikinta ya soma rawa tana kokarin shiga tanajin tsoro kawai kwara amai ta shigayi a wajen sai ynkuri takeyi kwafa taji a gefenta ta kalli bakin gado Abraham ta gani zaune ta dago kai tana hada ido dashi taga yadda jikinsa yayi,ta kauda kai "ke bakiga mijinki ba ko?"kauda kai tayi "kaiba mijina bane mijina yanacan cikin daji wanda yake cikin kaddara sanadinka"murmushin karfin Hali yayi "husnah kenan yanzun dik kin manta da soyayyar da mukasha da yadda muke kulawa da juna ko?kin tsanani kin manta da wahalar Danasha akanki ko?kalli jikina yadda yake konewa sanadin yadda nake sonki nakasa daina kusantar inda kike tsananin kaunar da nakeyi miki,"cikin lallami da tattausan lafazi yakeyi mata magana cike da tausayawa wani kallo ta watsa masa "ni baxan fita dakaiba dan bansaniba ko can daji cikin bishiyoyi zaka maidani"tana maganar tana neman abinda Zata nad'e aman datayi kallon aman yayi kawai ya bace cikin tsiwa ta karaso ta damko wuyansa "waye yace ka gogemun amai danayi?kenan hat gyaran gadon ma da gyaran dakin kai kayi ko?"momy ce ta turo kofar "yadai husnah najiki shiru ko jikin ne?"Momy taga husnah cukume da yaseer mamaki ya kashe momy yaushe ya shigo bataga wucewarsa ba?"ah ah husnah ya kika cukume yaseer meyafaru?kai yaushe ka shigo banji shigowarka ba"sosa keya Abraham yayi yana kallon yadda momy tq tsaresa da ido yace "bana d'anjin dadi ne shine kawai banaso yaran nan suzo su cikani da surutu kuma Baba kabiru na can yasa ana gyaran gidan husnah to nadan tsaya anyi hatsaniya da ummah hadiza "momy ta kalli gefen wuyansa kamar rushi ya farfadi a jikinsa gabanta ya fadi zatayi magana ya mike cikin sauri yana kallon agogo "ina mota suyi sauri su fito mutafi"ya fice kamar walkiya husnah hawaye ke zubo mata "momy wallahi ba yaseer bane ki yarda dani wanan aljani ne yaseer yana can ya batar dashi 'ta durkushe tana kuka cikin tattausan lafazi momy tace"kiyi hakuri kinji yana sauya miki kamannin mijinki ne amma shine ki tashi yanzun kuje kuyi siyayyar kayayyaki kinga idan angama gyaran gidanki yau can zaku kwana"girgiza kai husnah tayi tace "mony kiyi hakuri nibazan jeba shi aljani ne"dakyar momy ta taushi husnah ta yarda ta dau gyalenta idanuwa jajir ta fita a parlor suka hadu dasu nusrah har sunkai kofar fita Momy tace"tsaya bakisha maganinki ba"husnah ta tsaya momy ta dauko galon din maganin ta bata tasha ta shafe mata jikinta da wani turare mai karfin gaske ta fito yana mota su nusrah suka Shiga baya tana bude motar kamshin turarenta ya shaka ya soma tari idanuwansa suka firfito ya kalleta a fusace"husnah koma bayan mota nusrah ta dawo nan bazan iya zama dake kina wanan warin turaren yan borin ba,ni wanan abubuwan da momy take shafa Miki idan kika tarw kin daina shafasu"murmushin mugunta husbah tayi ta bude motar ta fita ta hararesa nusrah ta fita sumi Sumi a tsorace ta Shiga gaban motar ya tada motar layi yakeyi yanajin motar sakamakon azabar da yake ciki sukabar kofar gidan....
******
ummah hadiza cikin dakin husnah parlornta mai girma anfara saka kujeru golden da brown wani wallpaper ne mai daukar ido a parlorn "mashaaaa Allah"anata Shiga da kaya tana gefe tasa waya ta kira innah take labarta mata yadda sukayi da hajiya rabi suna cikin magana mai gadi ya shigo "Assalamu alaikum hajiya kizo inji daddy"tayi murmushi tasan hajiya rabi ta hadota da badamasi kenan tace "gani nan zuwa"tanata zuzuta kyawu irin na dakin husnah da cottons dinta sai aiki akeyi ana Shiga da kaya tun daga kofar gate take jiyo haushin daddy...
*****
cikin iska mai karfi narjisu ke rike da yaseeer idanuwansa rufe yanajin yadda suke karo da bishiyoyi cikin tsananin faduwar gaba yaje addua ce a zucuyarsa kada Abraham yazo yasamesu baya ganinta amma yanajin yadda take rike dashi kamar kugiya kimanin awa daya suna abu daya sautin kukan tsuntsaye da mugayen halittu kawai yakeji gumi ke karyo masa gashi narjisu ta gargadesa karya kuskura ya bude idanuwansa idan har ya bude idonsa zai iya haukacewa,
gashin kanta tayi masa rumfa dashi tasa hannuwanta da zara zaran yatsinta sa kumbarta ta nade jikinsa dashi haka suka shigo cikin duniyar mutane wata irin iska yakeji tana ratsashi yana jiyo maganar mutane daga can nesa ya kara runtse idanuwansa sai hawaye narjisu ta kallesa ta kad'a kai, a kofar gate din gidan hajiya saude suka tsaya,
jinsa yayi tsaye akan kafafuwansa idonsa a rufe tayi murmushi tace bude idonka"a hankali yake bude idonsa wani haske yake gani yana kashe masa ido sakamakon DUHU da yayi kwana da kwanaki ciki kallonta yakeyi ya kasa magana "karka godemun yaseer saidai akwai kura a gabanka nayi maka mai wuyar ko?"ya gyada mata kai hawaye ke zubo masa ya cire rai da zai kara dawowa wanan duniyar kallonta yakeyi tana bacewa a hankali a hankaki harta gama bacewa ya kalli gate din gidan wato gidan momynsa ta kawosa yayi murmushi lallai a aljanu ma akwai na kirki kallon jikinsa yakeyi yadda rigarsa tayi kaca kaca ya shiga buga kofar gidan.....
tafe suke a mota suna hanyar dawowa husnah ta kalli madubin glass na gaba ba fuskar yaseer bace ainihin fuskarsa ce ta taba yusrah dake gefenta ta nuna mata wani irin razana yusrah tayi take ta sume a jikin kujerar.....
*DUHU...WANAN LITAFIN NA KUDI NE 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*
07042277401
08036953516
*SLIMZY*✍🏻
40
tun daga kofar gate ta ke jiyo muryar daddy cikin gidan hakan yasa ummah hadiza ta shiryawa dik wani makirci da hajiya rabi zata kulla da sallamarta ta shiga yana tsaye hajiya rabi na rusa kuka tana sharar hawaye cike da kissa wani kallo Alhaji badamasi ya watsawa ummah hadiza yace "dama iskancin daya kawoki gidana Kenan?abinda kuke kullawa dik be ishekuba har sai kun hada ma hajiya rabi da duka?"kallon hajiya rabi ummah hadiza tayi tace "amma yaya ta..."tsawa daddy ya daka mata tayi shiru yace "tou Bari kiji dik abinda kukeyi kuna ganin bansaniba ko nasani tsaf kuma wanan da kuke ganin na aura babu Wanda ya isa ya rabani da ita dan haka a matsayinta na matar yayanki ki tsugunna har kas ki bata hakuri"cikin tsawa daddy yake bawa ummah hadiza umarni ta girgiza kai tace "ke rabi wallahi baki isa na tsugunna na baki hakuri ba kinyi kadan koda kike matar yayana ai na girmeki ko ban girmeki ba bokanki beyi nasara akainaba"ta watsa mata harara daddy ya daga hannu ya zabgawa ummah hadiza mari "a gaban nawa ma kin sake maimaitawa?ya tabbata sharrin da kuka kulla mata gaskiya ne Kenan hardake idan zainab tayi ai ita kishiyarta ce kedin kishiyarta ce?"ummah hadiza ta dafe kumatunta tana kallon hajiya rabi idanuwa jajir cike da takaici take kallonta "kuma ki ficemun daga gida inhar bazaki daraja matata ba karki sake zuwa inda nake kinji nafada miki"hajiya zainab hawaye ne ya wanke mata fuska kallon yadda daddy yake ciwa ummah hadiza mutunci sabida hajiya rabi yasa kai yabarsu tsaye cike da haushi,.....ummah hadiza ta girgiza kai tana kallon hajiya rabi cikin takaici da tsana tace "yau kinsa d'an uwana ya mareni ko?"hajiya rabi tayi juyi tace "kwarai dagaske kuwa ninafi karfin in mareko da hannuna saidai insaka wanki ya mareki kuma burina ya cika babban burina ma ya sake cika tunda ya haramta miki zuwa gidan"wata yar kwalla ce ta cicciko a idon ummah hadiza,momy ta rukota "kiyi hakuri hadiza ninaja miki dik abinda dan uwanki yayi miki sanadina ne kika mareta amma ki kwantar da hankalinki Allah Baya bacci"ummah hadiza ta jinjina kai tace "karki damu zainab ta tsokalowa kanta tsuliyar dodo ne sai tayi danasanin saka d'an uwana ya mareni a kumatuna yadda ya mareni a kumatuna nayi miki alkawarin sai ya mareki nan bada jimawa ba dan nida kike ganina bakisan ko waceceni ba ko?fada da aljani babu dadi anzo inda nakeso amma sai na tabbatar da na rama abinda kikaimun sai nayi sanadin da kikabar gidan nan tare da tonuwar asirinki sai alhaji badamasi ya dakeki a tsakiyar titi a gaban kowa"hajiya rabi kallon ummah hadiza takeyi shekeke kamar zautacciya rike da kumatunta tayi wata dariya,
"wanan dariyar sai ta zame miki kuka yan uwanki da kika kora kika gujesu saboda talakawa ne su zaki koma wajensu ki kwashi kashinki a hannu"hajiya rabi cikin zuciyarta wani tsoro ne ya kamata kallon yadda idanuwan ummah hadiza sukai jajir tayi ta kasa magana,muneeba ce ta fito daga sashenta taci kwalliya ta saka doguwar rigar abaya baka cikinta ya fito sosai yayi girma tana rike da kwankwaso daya hannunta rike da wayarta tana dannawa tana ganinsu ta sake canja tafiya tana yauki cike da yanga da kwarkwasa ta karaso wajen ta kalli ummah hadiza ta watsar sanan ta dubi hajiya rabi tace "meke faruwa a nan?kukai cirko curko kamar anyi mutuwa ummah?ko ana jimamin cusawa yaya yaseer matar aljan ne?"ta danyi dariya hajiya rabi ta sheke da dariya ummah hadiza tayi kwafa ta galla mata harara tace "ke kumafa?hardasu kaza acin danko an fada miki inba rashin husnah ba ke ance miki ko kallo kin ishi yaseer ne?me zaiyi dake?ina zai kaiki bayan ga wadda zuciyarsa ke mararinso da muradi?"muneeba ranta ya baci ta tabe baki zatayi magana hajiya rabi ta dakatar da ita tace "aiko soyayya ta kare akan muneeba tinda ga dansa nan a cikin muneeba yana girma idan baya sonta bazai bude kafarta ya shigeta ba"muneeba ta shafa cikinta tana sake turoshi ummah hadiza a kufule tace "wanan cikin da kuke takama dashi insha Allah sai kunyi kuka da hawayenku sai ta haifo dan aljani idan har husnah matar aljan ce ke kuma uwar aljani zaki zama"
"aniyarki ta biki"ummahn muneeba tana ruko muneeba dake shirin watso rashin kunya nan suka soma hayaniya daddy ya fito yana ganin ummah hadiza ya zaburo"wai ba nace idan masifa ce zata kawoki gidana ki ficemun ba karki sake zuwa mai kike jira"ummah hadiza tace "ki jira ramuwar gayya kijira ranan da zaa koreki da kanyanki akai"momy ta ruko ummah hadiza cikin damuwa tace "kije wajen aikin nan da akasaki karki damu zan shigo nima idan nayi sallah"ta rukota tana kokarin fita da ita daddy ya daga murya "kema kidawo ki dibi kayanki ki bita ku zama kashin awaki"ummah hadiza ta fice momy ta shigo dakyar take taka kafarta tsabar bacin Rai hajiya rabi tace "anji kunya dai ana korar mutum yana likewa"kallonta momy kawai tayi ta dauke kai hajiya rabi ta ruko hannun muneeba sukai sashenta...
******
sautin bude kofar shiga parlor hajiya saude taji ta dauko kofin data hado tea ta fito da sauri turus ta ga yaseer tsaye taba binsa da kallo ta saki cup din hannunta cike da tashin hankaki bakinta na rawa tace "yaseer?inasu husnah?lafiya hatsari kukayi da kuka fita?"yaseer cikin rashin fahimta yake kallon momynsa hawayene suka soma zubowa daga idanuwansa ta d'ora hannu akai ta fashe da kuka "yaseer kayimun magana ina kannenka daka fita dasu da husnah da kukaje siyayya dazun?ina suke kunyi hatsari ko?aljanin ya sake saka hatsari kenan nafadawa husnah dama kaine ba Abraham ba sai tacemun wai bakai bane aljani ne"durkushewa Yasser yayi yana kukan bakin ciki wato mahaifiyarsa da matarsa da kannensa da aljani suke rayuwa basu saniba?kuka yakeyi ya kalli kayan jikinsa yadda suka fita hayyacinsu dakyar ya motsa bakinsa dake karkarwa kamar ana watsa masa ruwa yace "momy nine yaseeer wanda ya fita dasu husnah banibane aljani ne"dafe kirji momy tayi cikin tsananin tsoro tad'anja da baya tana kallonsa cike da tuhuma da furgici 'Aljani fa kace ban yarda dakai ba kaiba yaseer bane kazo ne kawai ka zautar dani kaine aljani"momy ta juya zata gudu yaseer ya rukota ta runtse idanuwanta gamm jikinta sai rawa yakeyi tana karanto adduoi yaseer ya tsareta da ido yadda take gumi ya tabbatar masa a furgice take sai adduoi momy ke zubowa ta saki wanan ta kama wanan cikin sanyin murya da dasasshiyar murya yace "ki bude idonki nine d'anki yaseer dik adduoin nan da kikayi nida aljani ne aida kin konani momy danki ne yaseer wanda ya dawo daga duniyar aljanu"ya fashe da kuka ya rike kafafuwanta,a sanyaye momy ta bude idanuwa ta tsura masa ido cikin ido kallonsa takeyi tanajin wani yanayi mai wuyar misaltuwa ta tsugunna ta ruko kafadarsa ta dagosa ta tsayar dashi ta kalli kwayar idonsa take ta tabbatar da d'anta yaseer ne tabbas yaserr din da suke gani a matsayin sa ba haka kwayar idonsa take ba ta fashe da kuka tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun wace irin masifa muke ciki?ace dama da aljani muke cudanya bamu saniba?yanzun gashi ya fita dasu husnah da su yusrah nashiga uku karya gudu dasu duniyar aljanu"hankalin yaserr ya tashi ya zube a kasa yana kuka kamar karamin yaro cikin damuwa momy kasa magana tayi takowa tayi ta karasa parlor ta zauna turus a kujera tana rera kuka.....
rungumo yusrah tayi jikinta ganin bata numfashi jikinta ya kama rawa ya kallesu ta jikin mirror yayi murmushi husnah ta watsa masa harara tace "mugu kawai"ya juyo ya kashe mata ido yace "nine mugu husnah ni mijin naki kike cewa mugu kanki daya kuwa?"nusrah dake gefensa zaune ta juyo ta kalli husnah dake rungume da yusrah ta kara kallonsu cikin mamaki "Anty husnah meyasamu yusrah?"ta jikin madubi ya kallesu husnah ta dago ido tayi tozali da yadda idanuwansa suke ta kalli nusrah ta girgiza Mata kai tace "bacci takeyi"tayi ajiyar zuciya gudu kawai yake shararawa Allah Allah yakeyi ya shiga ya saukesu sakamakon yasan akwai matsala ganin zuhraliyya na bin su suna tsayawa a kofar gidan husnah ta rasa ya zatayi cikin ikon Allah tana motsa yusrah ta zabura ta rubtse ido ta kwalla kara jikinta na rawa"Anty husnah a ina mukene?yana tare damu?"ta radawa yusrah a kunne"shhhhh ki daure kinji babu abinda zaiyi miki aibake yakeso ba bake ya biyo ba banaso ya Gane kinga halittarsa"gumi ke karyowa yusrah ta kasa Bude idonta a haka ta fito yace "yadai lafiya yusrah?"ta girgiza masa kai "zazzabi nakeji"
"zazzabi kuma?munfita lafiya kice kinajin zazzabi karmu shiga kisa momy taji haushina"ta kada kai kawai kirjinta bugawa kawai yakeyi,
ta jikin mirror momy ta hangoso suna kwaso kaya wani kulllll taji cikinta yayi mata ta kalli yaseer dake zaune zugum zatayi magana suka shigo a tare wani shock yan biyu sukayi suna kallon yaseer suna kallon Abraham babancinsu kayan jikinsu Abraham ya hadiyi wani miyau ya waske yace"momy wanan fa?karfa ki yarda aljani yazo ya yaudareki"jikin momy ya kama rawa ta kasa magana yusrah kuwa take kamanninsa ya dawo mata ta yanke jiki ta fadi yaseer ya zabura ya karasa yana girgiza ta Abraham yayi murnushi yana kallonsu momy yace "babu yadda zaayi d'an Adam ya kalli aljani ko yaya ne ya zauna lafiya inda a halittata gaba daya ta kalleni da na tabbatar saidai mudawo da gawarta,tare nake rayuwa daku bakusan wayeni ba toni aljani ne"zabura momy tayi ta ruga aguje tayi daki nusrah ta rufa mata baya suka rufe dakin gamm sai rawar jiki sukeyi,
mikewa yaseer yayi suna kallon kallo da Abraham murmushi yaseer yayi masa yace "muguntarka tana gab da zuwa karshe nayi maka alkawarin ni zan kasheka da hannuna"
"idan baka kasheni ba ni kuma zan cika maka alkawarinka in kasheka in dauke husnah mukoma wata duniyar mu rayu yare kamar yadda na rayu da ita"husnah hawaye takeyi cikin daki ta dauko kwalbar maganin da malam ya bata dana ruwan addua ta fito a hankali take takowa ta kalli maganin ta budesa daidai Abraham ya kwalalo ido waje yana kokarin zuba masa mugunta ta watsa masa akansa zuwa fuskarsa ya juyo da sauri fuskarsa tana hayaki yake kallonta idonsa suka canja kala suna yin wani ruwa mai kamar mai jikinta ya soma rawa taji tsoro ta yadda kwalbar maganin kasa ta fadi tasssss hayakin da taga yana tashi a jikinsa da yadda fuskarsa ke salewa yasa ta furgita yaseer ya fizgota jikinsa ya rungumeta yana kissing gefen fuskarta Abraham tsaye hayaki na fita akansa cikin minti biyar yake bacewa a hankali suka nemesa suka rasa ajiyar zuciya yaseer yayi ya sake hadata da kirjinsa yana sauke wani irin numfashi lafewa tayi sosaiba jikinsa kirjinta na harbawa ta rufe idonta yadda kansa ke hayaki take gani ta bude tana kwalla yaserr ya Rabata da jikinsa ya share mata hawaye a hankali "meyasa kike kuka?"girgiza kai tayi tadan ja da baya "bashi bane ya saceka?ya tafi dakai yake zuwa nan a matsayinka"jikin yaseer ya kama rawa "inji dai be tabaki ba beyi miki komiba husnah?husnah kifadamun be kwanta dakeba"ta girgiza kai ta cije lebe "bai kwanta daniba yaya yaserr nagano shi waye su momy ne basu saniba"momy daga cikin daki takejin muryarsu sama sama tadan bude a hankali karar bude dakin yasa suka waiga a tare momy ta leko dakai ta jike da gumi yaserr ya sauke numfashi yace"momy ki fito ya fita ya tafi"a sukwane Momy ta fito tana waige waige "ka tabbatq?ohh ni saudatu yau nice da aljani ido da ido?"ta karasa wajen yusrah da take juyi a kasan tiles taki bude idonta nusrah cikin dimuwa ganin halin da yar uwarta take,ta shiga jijiigata "ki tashi yussy ki tashi baya nan'girgiza mata kai tayi tace"zan iya tashi amma sam banason kara bude idona a rayuwa"momy hankalinta ya tashi ta kalli yaseer ta karasa ta dau wayarta ta shiga Kiran malam ta shaida masa halin da suke ciki tana bukatarsa da gaggawa,
"yaserr ka shiga dakin husnah kayi wanka ka sauya kayan jikinka idan malam yazo ya tafi saimu dunguma mutafi can gidan baban naku a sanar musu da komi daya faru ko?"ya jinjina mata kai ya juya zai tafi ya saci kallon husnah dake tsaye tsumu