Showing 75001 words to 78000 words out of 130717 words

Chapter 26 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

196

ya hadiye da yayi tozali da mazaunanta a jikin fited gown yace a ransa tabarakalla....ta jikin madubi ta gansa kafesa da ido tayi to meye yazoyi bayan zuwan da yayi dik ya gama tattabata?turo baki tayi gaba tana kallonsa ya kashe mata ido besan yayi ba ta sadda kanta kasa a sanyaye yace"baki iya gaisuwa ba ko?"gabanta ne ya tsananta faduwa tunawa da yadda ya luguiguita mata nonuwa tadan kallesa yace"taho to"take ta tuna da yadda yayi mata saidai wanan karon bai mika mata hannu ba ya kasa dauke idonsa daga gareta tadauko seconds sanan ta tako cikin wani irin taku mai daukar hankali tana tafiyar hips dinta na amsawa tana kusantosa yanajin wani kamshi dake ratsawa har kwakwalwarsa wanan wani irin turarene husnah tasa mai daukar hankali?.....rugugin hadari yaji ya kalli window yadda garin yayi bakinkirin ya kalleta yace "kinci abinci?"ta gyada masa kai ya zauna gefen gado itama ta zauna gabanta sai faduwa yakeyi ta rasa dalili shiko sam ya manceda momy tace ya taho mata da husnah ya tsudumma kallonta ko kifta ido bayayi ta dan saci kallonsa cikin yanayi na shagwaba da daukar hankali tayi farrr da ido tace"meye kake kallona?"yayi murmushi yace"kin hadu kinyi kyau sosai hussy" matsowa yakeyi yana fadin "wani irin kamshin turarene wanan?"nusrah tayi sallama ta tsaya daga waje tace"yaya yaseee ba momy tace ku sauko kaida husnah ba?"yace "ok ok gamunan"husnah najim haka ta mike da sauri gaba daya kallom DA yaseer keyi mata yasa ta kasa sukuni tana gaba yana biye da ita yana kallom yadda take tafiya mai kama da tausayin kasa Abraham na jikin bango ganin yadda suka jero tsananin kishi ya kamasa ya tunkaro husnah dai dai nan malam dake labe jikin labule sunyi shiri ya watsa mata wani turare taja da baya ta saki atishawa Abraham da sauri ya bace......


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*

*GA MAI BUKATAR BIYA YA TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DIN*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA KO KATIN MTN TA WANAN NUMBER 08036953516


*SLIMZY* 07042277401
32
momy kallonsu tayi had'e da murmushi ta jinjina kai tabbas husnah da yaseer sun dace da juna dafe kai husnah tayi tana k'ara shakar abinda malam ya fesa mata ya fito daga mab'oyarsa yana kallonta ya jinjina kai yaseer ya bishi da kallo komawa yayi ya zauna suna tsaye yace"zo nan ki zauna husnah"cewar malam yana kallonta yana karanto wasu ayoyi idanuwanta suka kad'a sukai jajir ta nemi waje ta zauna yaseer yace"malam kaga fa yadda idanuwanta sukai jajir kar wani abu ya sameta"girgiza kai malam yayi ganin yadda hankalin yaseer ya tashi yace"ko d'aya jinnu sai a hankali musamman wanan da yake maganar ya aureta sai munyi dagaske idan ba haka ba abun karuwa zai rinkayi kuma sunada naci sosai idan suka auri mace har haihuwa suna iya hanata"yaseer ya kalli momy itama kallonsa tayi ta jinjina kai ta kalli yadda husnah ta dafe kai gumi ne kawai yake karyo mata ta ko ina ya dafa kanta ya karanto wasu adduoi ya tofa mata a kanta ji tayi wani yarrr a jikinta a hankali ta bude idanuwanta tana binsu da kallo momy tace"sannu husnah"jinjina mata kai tayi tace "yauwa momy kaina ked'anyimun ciwo"

"zaki samu sauko kinji?"ta jinjinawa momy kai yaseer ya shagala da kallonta wani turare malam ya fiddo daga yar jakarsa yace"hajiya ya zaayi da wanan turaren ya zaayi asamu wanda zai rinka shafa mata shi kullum daddare kafin ta kwanta duka jikinta lungu da sako?"momy tayi shiru tana kallon turaren tace "tou malam nidai y'atake a wajena amma Kuma yanzun suruka tace babu yadda zaayi in kalli tsiraicunta kasan kunya irin tamu ta hausa fulani"yaseer yace "momy ni zan rinka shafa mata"momy ta jiniina kai tace "nayi tunanin haka"

"tou amma fa kaima sai kayi dagaske saboda yanzun wanan turaren shine zaisa bazai rinka rab'ar jikinta ba ko kadan bazai rinka zama tare da itaba shine zaisa ya nisanceta "yaseer ya kada kai ya mike hannu ya karba malam ya ciro wasu magunguna nasha a kwalabe ya mikawa Momy "wanan safe da yamma zaa rinka bata tanasha"momy tayiwa malam godiya sosai yace "ni zan koma duba da yadda garin nan ya had'a hadari sosai kar ruwa yasameni a nan"momy ta bude jakarta ta ciro kudi masu yawa tabashi tayi masa godiya ya fice husnah na dafe da kai yaseer na zaune yana satar kallonta momy tace "wai kai mema ya dawo dakai nan gidan?bayan ga ciwo akanka na tabbata yana damunka kadai kara dawowa ne kawai banda zuwan da kayi dazun"yaseer ya zaro ido yace "ni kuma?yaushe nazo?"hararsa momy tayi kawai ta mike tace "yusrah kutashi muje ciki gashi ana kiran magriba ayi sallah aci abincin dare ko?"sukabi momy yaseer ya matso kusa da husnah numfashinsa yana gogan nata ta d'ago idanuwanta ta d'ora akansa kallon da yake mata yasa ta sadda kanta yace"tashi muje ko?"ta makale kafad'arta cikin sigar shagwaba yace"tashi muje mana ko bazakije d'akin nakiba?"ta gyada masa kai murmushi yayi ya zura turaren da malam ya bashi a aljihu yasa hannu ya d'agota cak ganin yana kokarin daukarta yasa ta shiga mutsu mutsu tana kallon sashen momy tace "ni kada momy tazo ta ganmu a haka ni kabari"dariya yaji tana kokarin kwace masa yace"tou shikenan naji Tashi muje kiyi alwala kiyi sallah nima masallaci zani"daga tsaye ya mika mata hannu ta kama lallausan hannunsa ta rike ya d'agota kafarta ce ta rike ta kasa motsa kafarta yana kokarin janta kafar ta lakwashe tayi yar k'ara da sauri ya tallabota "lafiya lafiya?"

"kafa na yaya yaseer na kasa motsa kafana"ya dauketa cakk ta boye kanta kirjinsa kunya takeji matuka zuciyarta na harbawa ya shiga da ita ciki,

ta jikin labule Abraham ya makale yana kallonsu inuwarsa ta gani bata gansa ba ta kalli yaseer ta kara kallon labulen yaseer ya juya baiga kowa ba yace"shiga kiyi alwala'ta jinjina masa kai haka kawai ta tsincu kanta cikin matsanancin tsoro ya nemi gefen gado ya zauna tana shiga ta gansa a jikin bangon toilet din cikin mummunan kama idanuwansa sunyi jajir wasu ruwa na zubowa na jini a guje ta kwaso da gudu ta fito tana haki ta durkushe "lafiya?"ta girgiza masa kai tana nuna masa cikin toilet din wucewa yayi ciki ya leka baiga kowa ba yana waige waige daga bayansa yaji anyi masa tsaki ya jinjina kai ya fito yace "taho muje in rakaki kiyi alwalar"

"tsoro nakeji yaya yaseer"tace muryarta na rawa,ransa a bace yake yasan tsoratata kawai akeyi ya rukota bata iya taka kafarta ya shiga da ita toilet din duhu kawai take gani yasa ta runtse idanuwanta ya rik'eta da kyau tayi alwalar suka fito ya shimfida dadduma yace "zo kiyi sallahr bari inje masallaci"girgiza masa kai tayi "banaso ka tsaya a nan nidai"kada kai yayi jin ruwa ya kece a garin ya kalli window walk'iya ke haskawa ya shige toilet don yayi alwala tana zaune kan dadduma take ganin windown na kad'awa a hankali labulayen na budewa bishiyoyi masu tsawon gaske take gani d'akin ne ke rikidewa Yana koma mata irin d'akinta nada a duniyarsu Abraham kallon ko ina takeyi kamar wadda ta warke makanta ya fito yace "yadai"nuna masa dakin takeyi da yatsanta yace"yadai?"tace "d'akin yana canjamun ne"

"ba abinda ya canja a d'akin kinji muyi sallah kinga an soma ruwa gashi inaso intafi gida da wuri kar daddy yasan cewa bana gidan yayi fushi dani"ta gyada masa kai suka tada sallah....

******
"muneeba kina nufin tun fitarsu hajiya saude yaseer yabar gidan nan har yanzun bai dawoba?daga cewa ya tafi asibiti?"ta jinjina kai cikib fushi take gumi ne kawai yake karyo mata tace "Anty sadiya tunda yaseer ya dawo hankalinsa na rasa gane kansa nasan wanan shegiyar bak'ardagar mahaifiyar nan tasa ce ta karya asirin da mukayi masa gashi kiri kiri yana neman juyamun baya ko ince ya juya ma tunda hankalinsa gabaki daya ya koma kan sauran jinnu"y'ar dariya sadiya tayi tace"ki kwantar da hankalinki sai munsa auren nan ya k'are tsakaninsa da ita yanzun abinda zaayi zo kiji?"ta rad'a ma muneeba a kunne muneeba kallonta takeyi ta gyad'a mata kai tace "alamu sun nuna so yakeyi ya kwana a can wajen ta tunda har yanzun bai dawoba yanzun zan koma cikin gida ki aiwatar da abinda na fada miki Na tabbatar tunda yanason cikin nan dik inda yake a gigice zai dawo"murmushi muneeba tayi "shiyasa nake sonki Anty sadiya ina matukar jin dadin kasancewarki cikin gidan nan idan baki nan gidan kango yake komawa,suka tafa Anty sadiya ta fita,


momyn husnah na zaune cikin ruwa taji shigowar mutum sadiya ce harta gifta ta dawo ta tsare hajiya zainab da ido ta kalli cikinta da kyau yadda yad'ab tasa tayi shiru hajiya zaibab itama kallonta takeyi cikib wani yanayi na rashin fahimta tace "lafiya?"jinjina kai sadiya tayi tace "ehh lallai abu ya bunkasa tunda gashi ya leko"tayi tsaki ta wuce momy ta kalli cikinta gabanta ya fad'i ta manta da irin rigar dake jikinta saboda cikinta ya fito yasa bataso tanasa kayan da zai nuna,

daddy ne ya shigo dakin fuskarsa a daure tace "sannu da zuwa"ya amsa ciki ciki dik ranan girkinta haka yakeyi baya ma zuwa sashenta yau ma yazo ne kila saboda husnah bata gidan nan,
wayar daddy ce ke kara ya duba muneeba ce yacev"lafiya muneeba ke kirana cikin daren nan?"

ya dauka "hello muneeba ya akayi meyafaru"sautin kukan muneeba ne ya gauraye kunnuwansa kirjinsa ya buga cikin sassarfa yace"lafiya muneeba meyafaru keda waye?waye menene ina yaseer din?"a rikice yake maganar daga inda take zaune ta harde kafa ta kara rushewa da kukan karya tace "daddy cikina da marata daddy ciwo sosai yaseer ya fita tun yamma bai dawoba"ta rushe da kuka "ya fita bai dawo ba yanzun meke faruwa?"ta kwalla ihu cikin wayar tana kiran mararta daga inda momy ke zaune take jiyo sautin kuwwar muneeba tayi saurin mikewa daddy ya kashe wayar momy tacw "lafiya?"wata uwar harara ya watsa mata yace "kinsan komi kinsan koma menene tunda kun dauki husnah daga gidan nan kun kaita gidan hajiya saude ne dan a dauki hankalin yaseer daga muneeba gashi yanzun batada lafiya kukan mararta takeyi kuma kinsan juna biyu gareta"

"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"momy tace cikin tashin hankali kenan dama yaseer baya gidan? hajiya rabi ce ta fito cikin kuka "alhaji ga muneeba can babu lafiya Alhaji ciwon mara takeyi kuma kasan cewar karamin ciki gareta damuwa ma kadai ya isa ya Sanyata tayi b'ari"sadiya ta zunguri hajiya rabi ta nuna mata cikin momy daya tasa gaban hajiya rabi ya yanke ya fad'i,
cikin bacin rai daddy ke kiran wayar Yaseer ringing takeyi amma bai dauka ba yace "Baya daukan wayata"hajiya rabi ta fashe da kuka "ni bari inje in duba y'ata insan halin da take ciki"tayi gaba daddy da sadiya suka rufa mata baya,

*****
nusrah ta kwankwasa kofar dakin husnah kasantuwar Yaseer na ciki da sauri ya mike zai duba mai kwankwasawar ta rukoshi "ina zakaje?"ya kalleta ya girgiza kai "ana kwankwasa kofa ne?"ta jinjina kai gabaki daya a rude take tunanin yadda zata kwana a wanan dakin takeyi komi na dakin ya sauya ita kadai ke ganin hakan ya bude nusrah ce "yaya yaseer momy ce tace wai ka shafawa Anty husnah maganin nan kada ka manta kafin ka tafi tace idan ka gama shafa mata ka sauko kasa" jinjina mata kai wayarsa daya ajiye gefen gado yaga tana haske ya duba miscalls dayawa yagani harda daddy yasan zaisha fad'a dan haka bazai ma dauka ba sai ya gama shafa mata maganin gashi yasan wanan kafar dake ciwo bata rasa nasaba da Abraham ne ya rike mata kafafuwa,

ya karaso "zo zan shafa miki magani,nasan kinji abinda malam ya fad'a dazun ko?"ta jinjina kai gabanta ya yanke ya fad'i tunowa da yadsa ya mammatseta da safe yasa ta kallesa zatayi magana yace "shhhhhh"ya soma kokarin zuge mata zip din rigarta jikinsa ne kawai ya kama rawa wata irin iska mai karfi yaji tana bugawa cikin d'akin hatta da fankar dakin saida ta soma bugawa kamar ana kadawa ya kalli sashen madubi yadda yakeyi kamar ana tursa Abraham ne yake kallon komi na dakin na matsowa yana bugawa cikin tsoro da furgici husnah tace "fanka zata fado mana yaya yaseer"ya zare mata rigar ta kasa wata iska ta bugo window globe din dakin daya ya fad'i kasa tassssss ta zabura ta rungumesa tsamm nonuwanta suka hadu da kirjinsa wani dumi yaji jikin husnah ga wanan kamshin dake tashi mai tayar masa da tsigar jikinta kara matseshi takeyi ganin komi na dakin na motsi ciki fanka sai bugawa takeyi tayi nan tayi nan ya riketa sosai yana kokarin janyeta daga jikinsa tana shigewa cikin tsananin tsoro ta soma hawaye hawayenta na d'iga a kafadarsa tana fadin "Dan Allah yaya yaseer kada ka tafi tsoro nakeji kaji?"

Abraham na tsaye cikin tsananin fushi yake watsa hannuwansa komi na rikicewa a d'akin waigowa yayi gefensa yayi tozali da mahaifinsa cikin kayan saki da sandarsa yana kallonsa farin gemun sa ya kalla ya koma jajir yasan mahaifinsa cikin fushi yake yasa zaiyi magana ya d'aga sandarsa sama saiga wata iska da tasa Abraham yayi matukar tsorata yasan mahaifinsa fushi yakeyi dashi yasan tunda ya saki iskar nan azabtar dashi zaiyi ya fuzgi Abraham suka bace,

kamar kiftawar ido sukaji shiru yadda iskar d'akin ke kadawa haske ya mamaye ko ina idanuwansa ya sauka akan nonuwanta da suka cicciko ya tsareta da ido ita kuwa idonta rufe yake ta sadakar cikin tsananin tsoro......

*kuyi maneji zakujini da yamma insha Allah inada mara lafiya*

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*

07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻
33
muneeba ce kwace shab'e shab'e tana rike da mararta jin takun tahowarsu yasa ta kara volume din kukanta murkususu take tana fad'in "wayyo Allah zan mutu wayyoo marata innahlillahi wa innah ilaihi rajiun yaya yaseer kana ina kadawo?kaji meyasa ka tafi ka barni?"tun daga kofar shigowa suke jiyo sautin kukanta da abinda take fad'a kuka takeyi sosai hawaye ya wanke mata fuska bankado kofar hajiya rabi tayi tana fad'in "nashiga uku muneeba muneeba meyasameki haka?"ta rungumeta tana kallon daddy dake tsaye a kofar shigowa tace "Alhaji kana kallo fa muneeba kwance take tana murkususu dik kiran nan da akeyiwa yaseer bai dauki wayat ba tun dazun ake kiransa kaga kenan ya tafi can ne dama da niyyar ya kwana wajen husnah"ta fashe da kuka momy ce ta shigo dakin sanye da hijab tana kallon fuskar muneeba yadda takeyi tana yatsina fuska tana kuka ta tabbatar da shiri ne murkususu takeyi ganin Momy ta rushe da kuka tace"daddy momy tasan cewar yaseer ya tafi wajen husnah ne saboda dama kafin ya tafi wajenta ya soma biyawa cemun yayi bari yaje wajen momy"ta rushe da kuka ta shige jikin ummahnta ta kara rungumeta ran Alhaji badamasi ya baci ya kalli momy da ta saki baki tana sauraren yadda muneeba ke zuba kirsa yace "zainab kinbani matukar mamaki wallahi kuma dagake har hajiya saude zanyi maganinku kun shirya haka ne daman dan ku wulakanta wanan yarinyar ko shiyasa aka fake da aljanu aka kaita can gidan to gobe gobe idan Allah ya kaimu zani in dauko y'ata in dawo da ita gidan nan tunda rashin mutunci ne"momy tace "Alhaji dik wanan maganar da kakeyi bansan komi akaibafa dan ni banyi magana da yaseer bakida baki ba yadaicemun zaije asibiti a duba lafiyarsa daganan ban sake ganin yaseer ba Alhaji"tsawa daddy ya daka mata saida ta razana tayi baya kamat xata fadi yace "karya kikeyi munafuka kawai duk abinda kuke shiryawa nasani kallonku nakeyi to tun baaje ko inaba asorinku ya tonu gobe goben nan husnah zata dawo gidan nan"muneeba ta kwalla kara ummah ta rungumeta "Alhaji ko zaa kai muneeba asibiti ne?"

"nakira doctor gashinan zuwa zaizo a dubata already yanzun ruwa akeyi kuma kinsam idanuwana basuda lafiyar da zan iya tuki daddare"cikin bacin rai yake maganar cike da haushin yaseer ya fice momy hawaye ne ke zubo mata ta kallesu tana kallon sadiya na boye fuska tana murmushi bataga laifinsu ba sai laifin yaseer daya tafi ya jawo yau ake kiranta munafuka,juyawa tayi ta fice daga dakin tana fita suka saki shewa muneeba tayi zumbur ta mike ta zauna tana kallon ummahnta ta toshe bakinta kar dariya ta kwace mata hajiya rabi tayi murnushin nasara tace"na yarda da tuggunki sadiya yanzun kiri kiri kin had'a abinda ya hargitsa Alhaji na kuma tabbatar yadda yaseer keson cikin nan gobe zai rasa sukuni akan hakan bazai sake waiwayar renom aljanu ba"suka sheke da dariya momy na tsaye ta jiyo muryar sadiya tana fad'in "ni wanan mara hankalin bata gabana yanzun yadda zamuyi da wanan cikin daya leko nakeso musan nayi dashi dan Alamu sun nuna tuni yayi kwari"gaban momy ya fadi ta shafa cikinta ta sake saurarawa da kyau ummah taji tace"wanan cikin ai cikin biyu ne kodai yazo duniya a mace ko kuma ya zama shege dan bazai taba zama d'an Alhaji badamasi ba indai ina raye"hmmmm "ummah kenan ai kawai kashe cikin nan zamuyi idan yazo duniya ko ya zama shege komi zai iya faruwa gara musan nayi dashi tun kafin yazo "hajiya rabi ta jinjina kai tayi kasa da murya momy batajin mai suke fad'a ta saurara da kyau dariyarsu kawai taji cikin dimuwa da rud'u ta soma tafiya ko ganin gabanta batayi cikin rashin saa ta zame ta fadi ta zauna da duwawubta bayanta yayi kara kadan wani radadi ne ya ratsata daga tsakiyar kanta ta dafe kwankwasonta da yakeyi kamar ya balle daddy ne ya taho cikin sauri likita na biye dashi ya gifta ta gefenta yana kallonta durkushe ko kallo bata ishesa ba jin sautin takun takalmi yasa muneeba ta makale jikin Momy tana sauke numfashi daddy da sallama ya shiga likita ya tsaya daga kofa daddy yace "Bismillah doctor shigo"ya kalli hajiya rabi yace "gyarata hajiya ga likita zai dubata ko zamu Basu waje?"cikin fuskar damuwa hajiya rabi tace "bazan iya barin muneeba cikin wanan halin ba har yanzun baasamu yaseer ba ko?"daddy yayi tsaki kawai ya sake ciro wayarsa....

******
d'ago husnah yaseer yayi daga kafadarsa yayo tozali da hawayen dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login