Showing 30001 words to 33000 words out of 130717 words

Chapter 11 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

174

DAN BAN YAFEBA*

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA 300 KACAL KI MALLAKI NAKI KO KI TA WANAN ACCOUNT NUMBER TARE DA TURA SHEDAR BIYA*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KI TURA KATIN MTN TA NUMBER[23/09, 21:24] 🥰slimzy😍: 13

Daddy ne ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ina yarinyar take?"ya tsaya daga bakin kofa momy batare da ta kallesa ba tace "tana ciki ta d'an kwanta ne yaseer ne ya shiga wajenta Yana ciki"

"Yaseer kuma?"momy ta ansa da "ehh"kawai ta mike tana kokarin barin wajen muneeba ta tsugunna ta gefen kofar da daddy ke tsaye tace "daddy barka da yamma "

"barkadai muneeba kin shigo,kema kinzo ganin husnar da akace ta dawo ne? tana ciki mai gidanki ma Yana wajenta"rasss Gaban muneeba ya fadi ji tayi kafafuwanta sun sage ta kasa mikewa daga tsuggon da tayi hajiya rabi ta karaso tana faraa ta kashewa muneeba ido tace "ki shiga mana ba kince kinzo ganin husnah bane ki shiga"muneeba murmushin karfin hali tayi daddy ya matsa yace ki shiga"

hajiya rabi tace "daddy dama angwama maka farfesun ne nace akawo maka ga dambun shinkafa nayi nasan zakaso abincin gargajiya"daddy ya washe baki yace"mashaaaa Allah ki zubo ki kawomin nan"hajiya rabi ta mike suka hada ido da momy ta kashe mata ido hade da gwalo tana yar dariya wani bakin ciki ne ya lullube momy ta Kasa magana muneeba kasa shiga ciki tayi ta zauna a kujera lallai yaseer wato zuwa yayi wajen husnah?she cant believe yaseer yaje wajen husnah me yajeyi?tambayar da tayiwa kanta batada amsa kenan kishi ya turnuke mata makoshi idanuwanta sun kad'a sunyi jajir saboda takaici kamar ta fashe da kuka takeji,


husnah kallon yaseer tayi tace "meyasa ka shigo Inda nake?ina mijina?me kazoyi waye kai?"tambayar data jero masa Kenan tana kallonsa wani mugun kallo yayi mata yace "ke ki shiga hankalinki ki saita natsuwarki na tabbatar kinada hankali kinsan me kikeyi ba mahaukaciya bace kinzo kina mana zancen mijinki waye mijinki ke kikasanshi kuma kisani idan harke ba yar daddy bace tattarawa zakiyi ki bar mana gida ko ganinki banasonyi"ran husnah ya baci a ranta tace wayeshi wanan?a fili tacev"waye yace maka nima inason ganinka?nima banason ganinka dan bansan ko waye kaiba kazo kana farfadamun magana ance maka nima inason zama a wajenku ne?suwayeku bansankuba kun raboni da ahalina"mtsww taja tsaki ran yaseer yayi mugun baci babu abinda ya tsana sama da tsaki a rayuwarsa,ya daga hannu zai kai mata yaji an rike hannunsa mamaki ya kasheshi ya waiga baiga kowaba yana kokari fuzge hannunsa yaji ya rike Abraham ne tsaye gefen yaseer wani abu na fitowa daga idanuwansa jajir yana Shiga jikin yaseer ji yayi jikinsa kamar ana zuba masa rushi wani shocking yakeji nan da nan sanyi na neman rufeshi jikinsa na rawa yayi kokarin sauke hannunsa sai yaji an saki hannun anyi kwafa tsoro ya kamashi ya juya ya kalli husnah wadda ta tsaresa da ido tana kallonsa jikinsa na tsananin rawa yabar dakin yana fitowa yayi tozali da muneeba tana ganinsa ta mike kallon tuhuma take binsa dashi jikinsa a sanyaye ya kashe mata ido ta kauda kanta gefe tace a can kasam makoshi "muje"tayi gaba yabi bayanta momy tace "husnah ta tashi ko yaseer"ya tsaya yayi shiru kamar ya fadawa momy abinda ya faru sai ya Kasa Yana inda inda bakinsa na rawa yace "ummm ahhh ehh ta tashi momy tana ciki"mamaki ya kashe momy ta girgiza kai yaseer na son husnah tasani wanan abun da yakeyi kadai yake daure mata kai dashi kamar wanda aka canja ta ajiye daddumar da take ninkewa ta wuce ciki ta tura kofar tun daga bakin kofar take jiyo maganarta,

"ina katafi mijina?"a shagwabe husnah keyiwa Abraham magana dake gefenta zaune yace "babu inda naje ina tare dake kisa a ranki ko baki ganina ina tare dake hussy"ta jinjina kai ta shafa cikinta tace "inajin yunwa"yayi shiru yace "yauwa gashi na siyo miki abinda kikafi so"yasa hannunsa ta gefen gado ya bude take saiga bakar leda cike da hollandia da gasasshiyar kaza ya bude mata ya yago kazar yace "bude bakinki matata"Yana kallonta cike da so da kauna ta natso ta manne da jikinsa ta kwantar da kai a kafadarsa ya bata ta amsa tanaci Yana bata hollandia ta gama karba"....momy dake tsaye tana jiyo sautin maganar husnah gaba daya tsoro ya kamata kardai husnah da suka dauko ba mutum bace?cikin tsoro da furgici take ta juya bayanta babu kowa gumi ya jika momy kasa daga kafarta tayi ji tayi ta kasa bude kofar ta shiga ta juya,

Abraham ya kalli sashen kofar yaga tsayuwar momy shi yasa mata nauyin da bazata iya shigowa ta katse musu soyayyarsu ba yana gama bata ya ajiye gefe ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa kanta cikin rawar murya tace "yaushe zamubar nan gidan ni banason zama a nan gidan abraham ka canja mana gida banason wanan mutumin daya shigo dazun"cije baki Abraham yayi idan ya dauki husnah sun koma rayuwa cikin mutane bazata iya rayuwa dasu ba ya shafa gashin kanta ya tallabo fuskarta ta Kura masa Ido Yana kallonta yace "husnah kiyi hakuri kinji? wadanan da kike ganinsu iyayenki ne"damm gabanta ya fadi ta gyara zama daga rukon da yayi mata bugun zuciyarta ya tsananta ta kasa magana bakinta sai rawa yakeyi tace "iyayena....iyayena ai sun mutu"ya girgiza mata kai yace "iyayenki basu mutu ba tsananin kaunar da nakeyi Miki ce tasa na daukeki na maidake cikin dangina"idanuwanta suka cicciko da hawaye yace "shhhh karkiyi kuka ko kina fushi ne dan na daukeki?ki kwantar da hankalinki kinji bazamu rabu ba"ta gyada masa kai zuciyarta na rawa kenan wanan mahaifiyarta ce tace "to meyasa ka daukeni?"

"saboda ina sonki"yace zaiyi magana yaji motsin mutane yace "ina zuwa"sam ba lokacin yakeso tasan shi aljani bane ya gyara mata zama ya shige toilet yana shiga ya rikida ya koma aljaninsa ya bace tabi hanyar toilet din da kallo momy ce suka shigo da hafeez da kanwar momy sai aminiyar momy tare suka shigo suna hada ido da kanwar momy "ikon Allah Zainab Allah maji rokon bawa tabbas wanan husnah ce"hankakin momy baya jikinta kallon yanayin husnah takeyi tana kallon yadda take kallon toilet hajiya hafsat kawar momy tace "husnah"da sauri husnah ta kalleta batare da ta amsa ba kanwar momy tace "husnah menene ya muka ganki hakan ko dik baccin ne kina kallon toilet?"ta jinjina kai tace "mijina ne ya shiga ciki"da sauri suka kalli juna da momy,momy ta jinjina musu kai tace "husnah da kuke gani Aljanu ne suka saceta ta koma rayuwa cikinsu abinda nake zargi Aljani ya auri husnah kuma ta shaku dashi sosai"hafeez ya harde hannuwansa a kirjinsa ya tsura mata ido ji tayi kamar ana kallonta ta kai idonta suka hada ido da hafeez kallon da yake mata yasa ta Kasa jure kallonsa ta kauda kai yayi murmushi ta turo baki tace "ni kadaina kallona"hafeez a Ransa yace "kallonki yana karamun energy ne soyayyarki na karuwa a zucuyata"a zahiri kuwa cewa yayi "shikenan naji nadaina kallonki bari inzo kibani labarin mutanenku jinnn "tayi murmushi taanajin haka ganin husnah na dariya su momy suka fita,

hajiya hafsat tace "tabdijan hajiya zainab kina cikin jarabawa dan wanan babbar matsala ce ga kuma matsalar wanan makirar hajiya rabi"numfashi taja ta sauke tace "kedai bari gashi Alhaji yace gobe da safe kafin daurin aurensa da rabi zamuje asibiti gwajin jini akan husnah ta rigada tace masa ai gwaji husnah ba yarsa bace"

"what?kikace mene?"momy batace komiba jin motsin daddy da muryarsa ya leko yana kwalawa hajiya rabi kira ta fito cikin kwarkwasa eike da tray a hannunta ta jero kuloli dukkansu kallo sukabita dashi baki bude.....

*****
muneebah hawaye ne ke gudu a fuskarta suna Shiga daki ta fashe da kuka ta ruko yaseer ta janyosa bin ta kawai yayi saboda gabaki daya jikinsa kamar ba nasa ba tunda aka rike masa hannu kansa ke mugun sarawa ga dishi dishi da yake gani "yaseer mai kake nufi da zuwa inda husnah take bayan kace baka sonta ba matarka bace?"zaiyi magana ta dakatar dashi kishi ya rufe mata idanuwa ta ruko rigarsa"yau daga zuwa gidan nan har kaje wajenta mai kajeyi?"hawaye na zuba a idonta ya janyota ya rungumeta tsammm a jikinsa dikda pains din da yakeji cikin jikinsa yacev"najene in kankara mata warning tabar mana gida bama bukatar mahaukaciya a cikin gidan mu ba zuwa nayi dan in kulla alaka da itaba munee"ya dago fuskarta yana kallonta idanuwansa jajir ta fashe da kuka "aikaine dik kaja sakamakon bin maganar abokinka gashinan dama baya sona dakai yayi hakan ne dan ya kawo wata rayuwarka a matsayin husnah dan ta dauke maka hankali yasan yadda kakeson husnah"jikinsa na rawa yace "wait you mean abinda kike fada gaskiya ne?"ta jinjina masa kai sarai taga wucewar zuwan hafeez ta window cikin kissa tacev"yanzun haka hafeez na cikin gidan nan sashen momy"ya share mata hawaye cikin kidimewa ya zura takalminsa ya fice tayi saurin share hawaye ta soma dariya.....


hafeez na zaune gefen husnah yace "kinsan meye babancin mutum da Aljani?"ta girgiza masa kai cike da kosawa tanaso tasani yace "mutum kina ganinsa amma aljani baa ganinsa kuma Shi aljani an haliccesa da wuta mu kuma mutane da kasa aka haliccemu sanan jinsin jinn abun tsoro ne hakan yasa mu mutane bama ganinsu saidai su suke ganinmu saidai in sun bude Miki ido kigansu sunada cutarwa sosai"tayi shiru tana tunani Abraham dinta jinsin jinn ne kuma baya cutarwa kai wanan maganar ba haka take ba bata fuska tayi ya zura mata ido wutar soyayyarta na ruruwa a zucuyarsas yace "yadai!"ta girgiza Kai tace"mijina jinsin jinn ne kuma baya cutarwa"yaseer ne ya turo kofar ya shigo yadda yaga hafeez zaine da husnah ta saki jiki ya sake gasgata maganar muneeba saidai ya sassauta ganin kallon da hafeez ya watsa masa ya kauda kai yace "yaushe ka shigo gidan baka nemeniba?"hafeez yayi kamar bazai amsa ba yace "kaida kace nayi silar zuwan husnah gidanku bakason magana dani in kyaleka?"yaseer yana nuna kansa yace "ni?"hafeez yayi masa wani kallo irin ka rainamun wayau yace "waye zai dauki wayarka yamun message?kaine dan haka na dauki abinda kace yanzun ba wajenka nazo ba dan haka ka kyaleni"Abraham Ne ya bullo ta bango ya harde hannuwansa a kirjinsa yana kallonsu husnah kanta a kasa tana ganinsa ta zabura tana kallonsu tace"nidai ku fita ku fita banason ganinku mijina yazo kutafi oyoyo Abraham"kallon juna sukai da hafeez ganin haka yaseer ya fice hannunsa daya kamar an dora masa bulo a hannu ya fice yana huci hafeez kuwa kallon husnah yakeyi cike da tausayi tabbad husnah kafin asamu tasan babancin mutum da aljan akwai wahala amma zai zauna da momy ficewa yayi parlor nam yasamu momy da hajiya hafsat suna tattaunawa.....



daure fuska Abraham yayi husnah ta rude ta Shiga tambayarsa "menene me akayi maka?ka fadamun kaji?"kishi take hangowa a kwayar idanuwansa taja ajiyar zuciya ta fada jikinsa "Kayi hakuri kanajin kishin ganina dasu ko?su suke zuwa inda nake,nafada musu inada miji su daina mun magana"ta kyabe fuskarta cike da shagwaba ya shafa kanta yace"kisan akwai aurena akanki ko?"ta jinjina masa kai yace "dole inyi kishin ganinki dasu dikda dayan dan uwanki ne amma karki sake kulasu daga yau banaso"ya hade rai tace "bazan sakeba kaima karka sake tafiya ka barni"ya jinjina mata kai ya hade bakinsu waje daya yana tsotsan bakinta....


momy na parlor hafeez ta fito tace "hafeez meye yake faruwa naganka cikin wanan yanayin sanan yaseer ya fita shima cikin fushi?"girgiza Mata kai yayi yace "bakomi momy ummah ke kirana zan dawo da safe zanzo inhar husnah ba yar daddy bace zsn dauketa zan maidata gidanmu wajen ummahta sanan zanyi iya kokarina wajen ganin tasamu lafiya ta daidaita"momy kwalla ta ciko a idanuwanta gababta na faduwa tunawa da tayi gobe zasuje asibiti awon jini tace "Allah yayi maka albarka"yan kasan makoshinsa ya amsa da Ameen ta fice hajiya hafsat taja numfashi ta sauke ta shiga bawa momy hakuri sanan daga karshe tace "karki kuskura hajiya rabi tasan kina dauke da ciki"ta gyada mata kai ana kiraye kirayen sallahr magriba suka tafi momy ta shigo ta dade tsaye sanan ta tura kofar zucuyarta na d'ar d'ar tace "husnah"husnah tayi saurin dagowa daga kwanciyar da take Abraham ya fita tace "naam momy"momy ta zaro ido tace "momy kikace?"husnah ta jinjina Mata kai tana kallon mahaifiyarta wani abu takeji game da ita mai wahalar fade ta karasa ta dafata tace "kin yarda ni mahaifiyarki ce!"hawaye cike a idanuwanta husnah tace "ehh nayarda momy ke kika haifeni amma dan Allah karki rabani da mijina ina sonsa dashi na shaku"momy hawaye suka zubo mata ta rungume husnah sosai sun dade a haka sanan ta fito da ita tace "je kiyi sallah ai kinayi kin iya ko?"dariya husnah tayi tace "momy kenan ina sallah mana na iya bari inyi alwala"momy ta shinfida musu dadduma ta fito mata da hijab ta ajiye sai gata ta fito ta gabatar da salloli ta dade zaune a dadduma sanan momy ta bata abinci tace "nakoshi'momy tace "mai kikaci?"zatayi magana taji harshenta yayi mata nauyi ta girgiza Kai kawai tace banajin ci.....tace "bari in shiga daki "momy ta gyada mata kai,

a parlor tasamu su daddy da hajiya rabi tana fitowa hajiya rabi ta hada rai tana hararta momy ta zauna gefen daddy take taji dambun shinkafar ya biya mata rai ta hadiyi wani miyau tana kallo daddy yace "zakici ne?"ta gyada masa kai "yana dariya cike da jin dadi yace "dambun shinkafarki yayi albarka Amarya zubowa yayarki"hajiya rabi cikin kissa tace "toh"tana harar momy ta gefe.....

*****"
tana kwance tana kallon gefe daya ta kasa bacci juyi takeyi tanaso tajita a jikin mininta turo kofar akayi da sauri ta mike ganinsa wani Sanyi taji cikin zuciyarta ya karaso da faraarsa ya Bude mata hannuwansa ta fada ya rungumeta yana sunsuna jikinta numfashinsa na sauka a gefen wuyanta wani dadi ne yake shigarta gantsarewa tayi ta turo baki "ina bukatarka mijina "yace "dagaske"cikin muryar rad'a tace "tou"ya Shiga tube mata kaya yana shafa ko ina a jikinta kwanciya tayi ta bude kafafuwanta yasa kansa yana tsitson hq dinta ruwa na zubowa yana tsotsewa yana shafa gashin dake kwance a mararta numfashi take saukewa nishi yana kara rudewa yana huta harshensa cikin hq dinta tana kiran sunansa "Abraham....ka karamun washhhh Allah na"ya hayo kanta yana matsa monuwanta yana kokarin kai harshensa kunnenta.....

momy jiri ne taji yana neman daukarta jin yadda husnah ke sauke numfashi tsoro fa furgici suka cikata mai tsananin ta fito ta dubata taga ko tayi bacci tajita cikin wanan yanayin hankalinta yayi mugun tashi jin tana kiran sunan Abraham mutuwar tsaye momy tayi ta kasa motsi tanajin tsoron shiga dakin dan batasan yadda zata ganta ba babban burinta gobe ya kasance husnah yarta ce dik yadda zatayi ganin tasamu lafiya zayayi....


yaseer juyi yayi muneeba na kwance a kirjinsa bacci ya kauracewa idanuwansa fatansa gobe yarinyar nan tabar gidan nan shine babban burinsa a rayuwa ga babban abun tsoro abinda yasamesa jiya akanta abun na damunsa har yanzun yanajin damkar da akayi masa lokacin daya kai hannu zsi mareta.....

******
Asibiti,

karfe goma na safe a asibiti tayi mysu duka ilahirin jamaar gidan a asibiti suka hadu da hafeez ya parker motarsa muneeba hannunta na cikin na yaseer sun hada ido da hafeez amma basuyi magana ba dukkansu suna fushi da juna maroon din hijab din momy ne jikin husnah hannunta na cikin na Abraham yana murza Mata hannu tare aka dibi jininta dana daddy dana momy,momy na gefen innah wadda suka samesu a asibiti momy satar kallon husnah tayi taga yadda takeyi da hannu ta kauda kai alamar kamar tana rike da hannun wani numfashin da husnah ke saukewa jiya ya dawo mata a kwakwalwa ta fita hayyacinta.....

hajiya rabi tasha Ado da wani tsadadden kace blue da silver sai kamshi take xubawa tana sanye da gyale da takalmi silver hankalin momy yayi mugun tashi ganin likita ya fito da sakamako sun hada ido da hajiya rabi ta kashe masa ido,nan tasan akwai wani abu a kasa hajiya rabi ta dubi daddy sanye da fararen kaya tace "naga kamar ya fito da sakamakon"yaseer ya zabura yace "Alhamdulillah"ya dubi sashen da husnah take ya watsa mata wani kallo duka suka dunguma suka nufi dakin likita hafeez zama yayi yana daddana waya fatansa kawai husnah ta dawo hannunsa,

suna shiga Abraham yana kallon su daya bayan daya ya shige jikin likitan ya nemi waje ya zauna hajiya rabi murmushi kawai takeyi ganin likita na duba takarda babban burinta shine likita ya cika mata alkawarkn daya daukar mata momy addua takeyi cikin fargaba da tashin hankali suke kallon likitan wanda ya kasance Abraham ya shige jikinsa.....

yayi gyaran murya ya mikawa daddy hannu da sauri daddy ya kallesa cike da kosawa yace "yadai likita?"yaseer ya zubawa likitan ido likita yace "congratulations Alhaji badamasi Asma'ul husnah yarka ce ta cikinka"damm gaban hajiya rabi ya fadi ta zabura ta mike tana mazurai yaseer wani kallo ya watsawa likitan take shima yake jifansa da wani kallo jikin yaseer ya kama rawa kallon kwatar idon likita wanda ya kasance Abraham ya shiga jikinsa......

*WANAN LITTAFIN 300 KACAL ZAKI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUM KIN DAU HAKKINA ZAKI BIYANI INDA BABU DAN BAN YAFEBA DAN BIYAN WANAN LITTAFIN KI BIYA TA WANAN ACCOUNT DIN TARE DA TURA SHAIDAR BIYA*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WABAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA WANAN NUMBER.....



*SLIMZY*✍🏻07042277401
[23/09, 21:24] 🥰slimzy😍: 14

shako wuyan likita yaseer yayi jikinsa na rawa yace "karya kakeyi husnah ba ahalinmu bace ba yar daddy bace husnah Aljana ce ba mutum bace karya kakeyi kaima ba likitan bane"kallon yaseer Abraham yakeyi ido cikin ido ya hade rai wanda saida yaseer ya girgiza ganin yadda kwayar idanuwansa ke canjawa yayi kasa da murya Abraham yace "tabbas kayi gaskiya ba likita bane mijin husnah ne a jikin likita kuma a matsayin likita,dik yadda kukeso husnah tarabu da mahaifinta bazan bari ba dole zatayi rayuwa cikinku tare dani"gaban yaseer ya fadi ya kalli su momy dake kallonsa daddy ya karasa yana kokarin cire hannun yaseer daga wuyan likita yace "ka kwantar da hankalinka yaseer mugodewa Allah dawowar husnah gida,tabbas husnah yata ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login